← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 113

Sashe 80

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty Reemah, Hilal, Hafeez da Husnah kuwa suna tsaye rai a bace suna masifa kamar zasu ari baki,
shigowar Daddy da Papy shi ya farkar da ita...

Tunda ya farka ya lura da yanayinta,
bai kulata ba ya nufi bayi yayi alwala dan yaga garin har ya fara haske,
a yadda ya barta haka ya sameta, wannan karan idonta a rufe yake wani baccin take son sake yi, gyara hannun jallabiyarshi yayi ya zauna a gefenta haďe da taba kanta,
a hankali ta buďe ido ta kalleshi,

"Har ka idar da sallah?

Kwantar da kanta yayi kan kafaďunshi yace
"yanzu zanyi,
shine baki tashe ni ba ko?

Cikin magagi tace
"Nima banyi sallah ba,
bacci ya hana ni,

zaunar da ita yayi sosai yace
"whatt,
ba dai bacci ba,
sai dai shaiďan,
tashi maza muyi sallah,

Mikewa tayi jiki ba kwari tabi bayanshi sukayi Sallar,
suna idar da sallar taji duk wani baccin da takeji ya tafi,
sai dai kasalar da ta kasa barinta,

Bayan ta gaisheshi ta fita dan zuwa kitchen haďa ma Mummy break fast,
karar tv da taji shi ya bata tabbacin akwai mutane a parlon,
a nutse ta karasa saukowa ta nufi parlon dan duk tunaninta Mummy ce ko Anty Radiya,

turuss... tayi tana kallon Faidah wacce ke kwance daga ita sai mini skirt da wata yar riga wacce iyakarta cibi,
kwanciyar da tayi bai boye komai na surar jikinta ba,
kirjinta kuwa ya bulluko kamar zai faso rigar kayan kirjin su fito,

Saman ta kalla taga ko Musaddiq ya biyota, ganin baya gurin yasata saurin karasawa gurin Faidah rai a bace,
gaba daya tsoron da takeji nata ta nemeshi ta rasa,

"Baiwar Allah,
gidan nan ba na mata bane zallah akwai maza, dan Allah ki tashi ki canzo kaya,

Mikewa Faidah tayi tana murmushi tace
"Ba matsala bane dan ya ganni a haka,
musulunci ma ya yarda in kana neman auren mace ta bayyana maka surar jikinta kafin ka aureta,
karki damu dani je kiyi cookun ki,

Ran Nadeeyah in yayi dubu to duka sun baci,
baki yin kanshi yakeyi,
bata san lokacin da bakinta ya furta cewar

"Ke bakiyi kama da tsarin matan mijina zai ruďe akan surarsu ba,
bance shi nawa bane ni kadai, amma fa ki sani ko zaiyi wani auren sai dai ya nemo wacce ta fini ba wai ya koma baya ya dauko wacce bata kaini ba...

"Ahayyyyyeee.....
Faidah ta faďi tana tafa hannu,

wacce ta fiki me?
kyau?
Kudi?
Asali ko me?
Ko dayake banda lokacinki,
nasan a cikin abun da kike takama dashi nafiki su 99%,

Asali shi kadai zaka fini ka cuceni,

Faďa min menene asalinki?

Waye mahaifinki wanda ya kamata ya zamto ado a gareki?

Waya sani ma ko irin yan fashin shanun nan ne aka buďe musu wuta suka arto nigeria neman maf---

Zazzafan Mari Nadeeyah ta sauke a fuskar Faidah wanda saida ta dauki lokaci mai tsawo tana tattaro confidence dinta kafin ta iya aiwatar dashi,

sauke marin yayi daidai da sakkowar Mummy daga sama...

"Kaii kaii,
me nake gani haka?
Mari fa?
Mummy ta faďi tana karasowa har tana missing steps kafarta na gurďewa,

ko kallonta Nadeeyah batayi ba dan a lokacin ji takeyi kamar ana hura wuta a cikin zuciyarta,

Kuka Faida ta fashe dashi ta rungume Mummy wacce ta rufe mata jiki da hijab din da ta sakko dashi,

"Subhanallahi.. Nadeeyah me yayi zafi haka harda mari,
in baki dubi cewa ba sa'arki bace ai kya duba cewa ita bakuwarki ce,

"Bakuwarku dai Nadeeyah ta faďi cikin ficewar hayyaci,
ranta yayi matukar baci,
ba'a taba aibata mahaifinta har haka ba,
abun ya haďe mata biyu ne,
ga kishi ga tabo iyaye,
mai hankali ne kadai yasan halin da zuciyarta ke ciki a wannan lokacin,

Sakin baki Mummy tayi tace
"Ni kike fadama bakar magana,

gefenta tabi ta haye sama ba tare da ta kulata ba zuciyarta na tafasa,
ta gaji da zaman nan na kaskanci da takeyi,
badan tana jin soyayyar Musaddiq har cikin jininta ba wallahi da babu abinda zai hana ta tattara kayanta ta gudu ta bar musu gidan,
to bazata iya rabuwa dashi ko na second ba dan tayi matukar sabawa dashi,
ta dai ďauki alwashin kwatar ma kanta yanci gurin duk masu neman muzanta ta,
dakinsu ta shiga ta sameshi yana baccinshi hankali kwance,
key tasawa ďakin ta karaso kusa dashi ta cire hijab dinta ta shige cikin jikinshi taja musu bargon,
rungumeta yayi sosai yace

"Har kin gama?
a shagwabe tace
"um um, bacci nakeji, in na tashi zanyi,
bai damu ba dan yasan yadda yaganta da ta tashi,
yadda jikinshi yayi mata rumfa yasata manta duk wani bacin ran da ta kwaso daga kasa tayi luppp har bacci yayi gaba da ita....

Karar waya ce ta tashi Musaddiq daga nannauyan baccin da sukeyi,
hannu ya mik'a ya lalubota a gefen gadon..

kokarin zare jikinshi yakeyi a hankali dan kar ya tasheta yaji ta kara kankameshi haďe da sake gyara kanta a kirjinshi,
hannunshi ya tura cikin gashinta yana squeezing dinshi a hankali,

kallon wayar yayi yaga sha ďaya saura sannan ya duba kiran da ya zama missed call,
bin bayan kiran yayi asap,

"Yallabai hw far

"Ango kasha kamshi,
daga ďaya bangaren Zubair ya amsa cikin zolaya,,
"Hutu dai ya kare,
ga kuma wani hutun zaizo,
tafiya Singapore 3month course kuma oga yasa sunanka,
kaga sai kayi honeymoon dinka hankali kwance,

"Woww Musaddiq ya faďi da karfi har Nadeeyah na farkawa a ďan firgice,
murmushi yayi a hankali yace "sorry baby,
"yaushe ne tafiyan Zubair?

Dariya sosai Zubair yayi yace "Kaji shi, dama aikin ya isheka ko, to next week ne,

"Mashaa Allah, bari mu fara shiri, gobe zan zo aiki tun 8 in shaa Allah,
"To Allah ya kaimu ango,
a gaida min amarya,

"Gata nan tana amsawa,
tace bakazo kaci abincin amarya ba,

Dariya Zubair yayi yace "kace mata har sai ta gaji da gwauro,
in na fara mata sintiri sai ta rufe min kofa...

Dariya sukayi dukkansu sannan suka koma wata hirar daban...

Daga Nadeeyah har Musaddiq basu san kalubalen dake cikin aure ba,
har gara Nadeeyah tasan Hakuri da juriya sune ginshiki a zaman aure,
shiko Musaddiq da ya tashi cikin gatan da babu fatawar komai sai ta sakarci duk daukarshi aure kawai jindadi ne da mace,
ka bata abinci,
ta kula dakai tayi maka duk wasu bukatu,
bai san ainihin tushen aure shine Hakuri da jajircewa ba,
bai taba hasaso wani tashin hankalin da zai sauya rayuwarshi na nan tafe cikin kankanin lokaci ba....

Jiyar da juna daďi sukayi a wannan safiyar saboda murnar zasu kadaitu da juna na tsawon lokaci ba tare da tashin hankalin yan uwa ba,
abun da basu taba yi tare ba shi sukayi ranar wanka,

Nadeeyah har mamakin yadda ta saki jiki dashi cikin kankanin lokaci take,
kwata kwata duk wata kunya tata ta rasa inda tayi balaguro,
sosai take son jinta like a jikinshi a koda yaushe,

Kananan kaya ya saka wadanda suka fitar da ainihin kyawunsa..

Hannunshi Nadeeyah ta kamo ta zaunar dashi akan madubi tayi brushing gashin kanshi da kwantaccen sajen gefen fuskarshi..

"Kayi kyau sosai sosai,

kewayeta yayi da hannunshi ya daura kanshi kan ruwan cikinta haďe da lumshe ido yace

" *I can't quantify my love for you, it's more than the sand under the sea. Like a snail cannot live nor survive without its shell, I cannot live without you cos with you, there is life....*

Bata san sanda ta sanya hannu ta rungume kanshi tana shafawa ba saboda daďin da kalaman sukayi mata,

"I can't live without u either,

Zaunar da ita yayi akan cinyarshi cikin raďa yace
"Sure?

Gyaďa kanta tayi haďe da kwanciya a jikinshi,

Oya muje muyi breakfast, to 12 yanzu, munyi latti,

Buďe bakinta tayi a firgice dan shaff ta manta bata yi ma Mummy abinda ya kaita kasa dazu ba,
abubuwan da suka faru ta shiga tariyowa cikin kwakwalwarta,

"Na shiga uku!
ta faďi a hankali dan tuno yadda tayi ma Mummy dazu wanda sai yanzu taga rashin kyautuwarsa,

Ganin idonta na shirin tara ruwa Musaddiq yayi saurin mikewa haďe da cewa

"Hey calm down,
ai ba yin kanki bane,
Mummy will understand,
nasan sun karya ma by nw,

Jiki babu kwari dan bata san abun da zata tarar ba in ta fita parlon tace

"To muje in haďa maka breakfast, sai inyi saurin daura lunch,

"Kindai kusa hutawa,
in mukayi tafiya ko cup bazaki dauke ba,
so nakeyi kafin mu dawo ki zama big madam,

"kaga nima sai in dinga daukarka a wuya na,
ta faďi tana dariya haďe da bude kofa,

dariyar shima yayi ya biyota yana cewa
"impossible,
ko hannuna bazaki iya ďagawa shi kaďai ba,

Ringing din da wayarshi keyi shi ya hanata bashi amsa ta sauka kasa tana dariya,

ganin ba kowa a parlon ya sa tayi tunanin ko suna daki ne,
kitchen ta wuce taga komai tsaff kamar yadda ta barshi da daddare,
bata kawo komai a ranta ba ta fara dafa mishi indomie dan itace mai sauki,
tana yanka albasa taji muryarshi a bayanta,

"Amm dazu da kika fito da safe wani abu ya faru ne?

Gabanta ne yayi mugun faďuwa ta cigaba da yanka albasa tace

"wani abu akace maka ya faru?

Wukar hannunta ya karba ya juyo da ita yace

"I trust u Nadeeyah,
daga bakinki kawai nakeson jin gaskiyar magana,
banason ki boye min komai,

Kasa ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara sintiri a idonta,

"Uhmm tell me!

"Ni bansan yadda zan faďi maka ba,
duk yadda suka faďa maka daidai ne,

Zai sake magana yaji wayar ta sake ringing,
da yake suna gab da juna taji duk abun da Anty Radiya tace a wayar,

"Ka fito ne ko har yanzu kana like gurin wacce ta zagi mahaifiyarka har ta koreta a gidan danta?

Kashe wayar yayi jikinshi ya fara rawa yace

"Plss tell me Nadeeyah,

tafiya ta fara yi dan kukan da takeyi na neman cin karfinta,

"Kaje dan Allah,
duk abinda aka ce maka nayi nayi ne,

Ranshi ya fara baci da kalamanta ya juyota da karfi yace

"A bakinki nake son ji,

a harzuke ta ture hannunshi tace
Chapter 80 · 0% Book details