← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 113

Sashe 56

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin Daddy ya gabatar da bukatarshi Dr Barau ya rigashi da cewa
"Musaddiq har yanzu bai gama servn ba?

"saura watanni in shaa Allah Daddy ya bashi amsa yana dariya,

"okk to ba matsala gobe akwai yara 6 da za'ayi ma interview a

*EXXONMOBIL*

ka turomin shi sai su hadu su 7,
in ya karbi nysc cert dinshi sai a hada a cikin takardunshi,

cike da farin ciki Daddy yace "ina ne Exxonmobil kuma?

Dariya sosai Dr Barau yayi yace "Nigerian EXXONMOBIL, Oil nd gas company ne,
American multinational oil nd gas cooperation,

yanzu ake daukar yara,
so gara yaran mu su samu tun yanzu, kaga nan gaba sun dade a ciki, lokacin da karfin mu zai tafi sukuma lokacin zasu mike,

Fadin irin farin cikin da Daddy ke ciki ba kadan bane,
dama kiran da yayi mishi kenan,
matakin farko da zai fara sanya Musaddiq zama cikakken mutum shine aiki,
in yaga ya fara samun kudinshi na kanshi zai nutsu sosai ya nemo girma ya daura ma kanshi,

godiya sosai yayi Dr Barau sannan ya kashe wayar,
Mummy dake tsaye da flask a hannu ya fada ma,
ita ma cike da farin ciki ta sauka kasa ta kira dukkan yan uwanshi ta fada musu,

Raudha dake lagos tasan in ne Exxonmobil,
dan haka ta fara koda gurin tana sanyawa Mummy shirin fara nemo mishi mata yar masu kudi ko sarauta,

dariyar farin ciki Mummy tayi tace
"ba sai kin fada ba,

Matar Little dina zata zamo yar gata gaba da baya,

yar da iyayenta basa kyashin kashe mata dukkan dukiyarsu,
yar da zata ayi aman kudi daga ko wani bangare,

biki ne wanda nake shiryashi tun kafin yau,

biki ne na garari.......

Mrs Tijjani Shattimah......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣8⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

*Kaduna, Niger, Abuja, Nasarawa, direct,*

wani dan saurayi ke tsaye jikin zungureriyar mota yana busa taba yana fadin sunan garuruwan da zasu,
nan aka fara tururuwar shiga motar kowa na fadin inda zashi,

cike da hanzari ta karaso gurin motar tana fadin kaduna,
kallon motar saurayin yayi yace

"Baba motar ta cika saidai Ko zaki hau baya kan kaya, 

"karfe nawa wata motar zata zo to,  ta fadi cikin gatsali

"keeee yane... kike min magana kamar wani danki,
in zaki jira motar karfe shida na yamma ki jira in baki iya jira wareee,

Cike da mamakin rashin ganin tsufanta tace
"kai da uwarka baku da tsofaffi a gidanku ne,
yaran yanzu sun fitsare kafarsu, basa ganin girman na gaba dasu, gaskiya anyi asarar haihuwa wallahi,
ta karashe tana kokarin jan jakar gana most go dinta,

"tare ta yayi da sauri ya busa ma fuskarta hayaki hade da cewa,
wallahi bazan duba tsufanki ba zan yaga miki chuna,
zigidir zan miki anan gurin kika sake sako sunan gyatuma ta,

A fusace tace "nace kaci uwar ubanka,
kaji min dan iskan yaro,
ni nan da ka ganni bani da mutunci, zan iya yi maka mummuna illa in baka maida hankalinka ba,

"ehhhhh yeeeeeeee,

ya saki ihu hade da chukumar jakar Goggo yayi wurgi da ita,

nan jakar ta yage  kayan ciki suka firfito,
wata katuwar kwalba wacce take nade a zani ta tarwatse ruwan cikin ya bata sauran kullin dake cikin wasu takardu,

ďaga hannu yayi zai kai mata mari drivern motar yayi saurin rikeshi,

"kyaleta GARO,
barta ta shiga bayan boot din ta zauna,

kallon Goggo yayi wacce ta tsurawa kayan da ta kwana tara a hanya tana nemansu,

wani irin tukuki taji a zuciyarta tayi kukan kura ta kama wuyan Garo,

Dagewa yayi iya karfinshi yayi wurgi da ita gefe hade da zaro zarbebiyar wuka mai kyalli,

nan take Goggo ta maida hankalinta ta mike tana kukan wayancewa hade da cewa mutanen dake rike Garo
"yanzu dan Allah in ba sauyin zamani ba wannan yaron banyi jika na uku dashi ba,

"Na sha tara kikayi dani dan mai cin-----

toshe mishi baki drivern yayi yace
"yi hakuri Garo,
nasan laifinta ne,
ka barta ta shiga mota mu tafi,

maida wukar yayi yana ta muzurai hade da hararar Goggo,

sum sum ta wuce tana kallon jakar da ta sha wahala ta kashe makudan kudi dan samo su,

"tuno kashedin da bokan yayi mata na ta kula da kayan domin a shekara sau daya ake samun sa'ar samunsu,

wasu zafafan hawaye ta share zuciyarta a dagule ta nufi bayan motar inda kayan mutane suke,

"tana zama taji kukan talotalo a cikin wani kwali a bayanta,

Tagumi ta zuba saboda shiga wani yanayi da tayi,
yanzu ya zatayi ta sake samun wannan sa'ar,
bazata ta taba bari tayi wata daya da Anni da papy ba tare da ta illata su ba,
so takeyi taga bayansu dukkansu,
so takeyi ta mallaki zuciyar Baffa da gidanshi baki daya ita kadai kamar yadda tayi a baya,
daga ita sai yarta da jikokinta,

Tana cikin wannan tunanin mai cike da takaici drivern yace ta bashi kudi,
"nawa ne?
, jaka goma sha biyu,

"jaka har goma sha biyu, abin na sat-----
ganin Garo a bayanshi yasata saurin sauya maganar zuwa
"abin har yayi sauki haka,
fito da lalitarta tayi ta bashi kudin ciff,
irin kallon da Garo ke mata yasata saurin sunkuyar da kanta, shaff ta manta da yar posan kudinta a gefe,
tana jin motar ta fara tafiya, ta dago kanta,
tunane tunane ta shiga yi marasa dadi har bacci yayi gaba da da ita....

Mikakkiyar tafiya sukayi ta tsawon awa 8 saboda ana yi ana tsayawa Sallah  da cin abinci,

Suna daidai *kawo* suka fara shelar kowa ya hada kan kayanshi domin yanzu yan kaduna zasu sauka,

Goggo da bacci yayi gaba da ita sam bata san sunayi ba,
haka drivern baisan kaduna tace ba,
da yake yan kadunan basu da yawa ko minti biyar basuyi ba suka daga zuwa garin gaba da zasu,

saboda tsabar baccin gajiya ko kuma ince hakki, saida suka kai bus stop din tafiyarsu da Goggo,

Nan drivern ya tasheta a gajiye dan bacci yakeji matuka,

a firgice ta tashi tana laluben poss dinta tana fadin har munzo Kawo?

Wani kawon? drivern ya tambayeta cike da kosawa,

"Kawo ta kaduna ďan nan,
tsaki yaja yace "dan Allah Baba fito kar in miki rashin kunya,

fitowa tayi cikin rashin fahimta tace "ban gane ba, ina ne nan,

rufe boot din yayi yace "je ki tambayi wadancan, ya nuna wasu gungun mashaya a gurin ya wuce yana mika hade da wakar dan kwairo ta "mai dakin gabas,

Zaman dirshan Goggo tayi a garin da bata san ko ina ne ba,

saboda baccin da ta tika idonta ya soye sam bata jin shi,
ga muguwar yunwa tana ji,
ga bakin cikin satan da akayi mata,

Tashar cike take da mashayan da basu da aiki sai na shaye shaye duk minti,
mayafinta ta cire tayi matashi dashi, ta rasa yadda zata fassara irin hau din da hauta a wannan rana,

saboda tsabar takaici har sambatun bacin rai takeyi,
ga tsabar ciwon kai da ya sata a gaba, 

Wani mai butar shayi ne ya gifta tayi saurin kwala mishi kira,

dawowa yayi da sauri dan a tunaninshi siya zatayi,

"sannu ďan albarka,
nan wani gari ne dan Allah?

"Tashar Akwanga!
bakisan a Nasarawa kike ba,

wani kululu Goggo taji ya taso mata,
nan take hawaye ya wanke fuskarta,
da yaron yaga ba siya zatayi ba yayi saurin mikewa ya nufi gurin wadanda suka kirashi,

kuka mai hade da majina Goggo tayi shi a daren ranar,
maimakon ta saduda tasan hakki ne ya fara dawainiya da ita sai ta kara kullatar bayin Allahn da zata sake ninka zunubbansu akanta....

Motar dake tashi da asuba zuwa kaduna tabi tanata roko su sata ko a sama ne,
tana cikin wannan magiyar taji muryar da ko a mafarki taji ta zata ganeta,

"Rilwanu ta fadi bakinta kamar gonar auduga,
daga ina kake?

Nuna mahaifinshi yayi yace daga Benue muke zamu wuce kaduna,

wannan Mahaifina ne,
kamar yadda na fada miki zan dawo dashi kaduna in nema mishi magani,
da yake a cikin duhun subahi ne sai basu samu damar ganin fuskar juna ba,
nan dai Goggo ta shiga aljihun kaskastaccen bawan gidanta Rilwanu......

Firgai firgai ta shigo gidan yunwa kamar zata kasheta,
a lokacin har masu ginin sunzo,

da masu gyara mata daki da masu karasa ginin da ake buga kwano,

goge idanuwanta tayi dakyau ta fara dubawa ko ba gidanta ta shigo ba,
dakin waje shi ya tabbatar mata da gidan ta shigo,

zagaye dakunan tayi hade da fadawa dakinta,

wani irin ja baya tayi cikin firgicin rashin ganin ko tsinke a dakinta sai ma hake haken kasa da akeyi ana sa tiles masu kyalli,
nan take yunwar da takeji tayi murabus a cikinta ta fara fadin,

"uban waya saku fasa min daki, ina kuka kai min kayan daki?
Tabdijam,

wallahi hukuma ce kadai zata rabani daku,
ashariyya ta fara kundumo musu babu kakkautawa,

Muryar Papy tajiyo daga tsakar gidan yana sallama,
fitowa tayi da sauri har tana tuntunbe,
tana fitowa Baffa ya murda kofa ya fito yana amsa sallama,

baki ta saki tana kallon yadda muhammadunta ya canza a cikin yan satittikan da ta tafi ta barshi,

gaba daya an aske farin gashin dake gemunshi da kanshi,
tsufanshi ya boye sai wani annurin kyau da yake fitarwa,

Bugaggiyar shadda blue ce a jikinshi sai hula da takalmi masu matukar kyau, ga wani uban kamshin turare da yake fitarwa,
duk su biyun ta kalla taga kayan nasu iri daya har dinkin ma,
bata kara shan mamaki ba sai da jiyo sallamar Daddy,

kallon hanyar shigowar tayi taga ya shigo da danyar gezna ash,
bayanshi Musaddiq, Hafeez da Jamal ne suma sunyi kyau sosai,

*Zuri'ar Atika*

ta fadi a hankali,
wata juya ta fara ji wacce ta sanyata yin zaman dirshan,
Papy ne ya fara isa gareta yana fadin

"subhannallah, Inna lafiya?
ina kika tafi har wannan lokacin kika barmu da jimami,
bata iya yin magana ba sai kukan takaicin da ya kufce mata,
taruwa sukayi akanta harda Baffa suna mata sannu, dan yanayinta na marasa lafiya ne,
dakin waje suka shiga da ita Baffa ya tsaya a kanta yana mata tambayoyin inda ta shiga,
Chapter 56 · 0% Book details