← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 113

Sashe 5

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hon Hilal yayi yace muje ko mum, bata bashi amsa ba sai ma harara da ta bishi dashi,

mamma tayi dariya tace Hilal Allah ya kiyaye hanya ka gaida abbanka kaji,
zaiji kawai Hilal yace ya tada motar sukayi gaba.....

Mrs Tijjani Shattima......
[04/12 09:45] Meela Adeel: 8⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

Washe gari karfe 8 a gidan Anty Reemah tayi wa Hafiz,
a kitchen ya sameta tare da Yan aikinta suna ta aikin abun karyawa,
da fara'arta ta tarbeshi tasa ya wuce parlor,
sai da ta kammala komai tasa shi ya karya sannan ta dawo gurinshi,

Wace sana'a kakeyi? Tambayar da ta fara yi mishi kenan,
kanshi a kasa yace "dako nakeyi da wheelbarrow,
wheelbarrown naka ne? Ta sake jefo mishi tambaya,
a'a ya fadi yana mai girgiza kanshi, haya nake daukowa duk yini dari uku nake bashi,
Good anty Reemah tace tana gyara zamanta,
Hafiz ka saurare ni da kyau kanaji ko,
gyada kanshi yayi yace inajinki anty,

da farko dai zanso insan sana'ar da kake sha'awar yi, ka ture batun dako, dan banga amfanin sa ba,

sunne kai yayi yace walhy anty bani da wani idean sana'a yanzu sai dai in kika bani shawara bazanki dauka ba,
ajiyar zuciya tayi tace
"to akwai mijin kawata a railway station yana sana'ar fruits,
zan mishi magana in hadashi da kai sannan zan baka jarin da zaka tsaya da kafafunka ka rike mahaifanka da yan uwanka,
basu da kowa a duniya sai kai Hafiz,
hakkinka ne ka kula dasu da ilimin su,
nasan kana nema, rashin Jari ne ya taushe ka amma inada yakinin in na baka zaka kula da hakkinsu,
Dan Allah Hafiz karka bari suyi kuka da kai ko ba dade ko ba jima na rokeka da Wanda bama gani amma shi yana ganin mu,

mikewa daga zaunen da yake yayi ya durkusa yace wallhy zan rike amanar su in ban rike amanarsu ba tawa zan rike,
nagode sosai anty Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen anty Reemah ta fadi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Maryam,
sun dade suna magana sannan sukayi sallama, tace "gobe in shaa Allah zaka fara Zuwa ka koyi yanda sana'ar take,
zan turo maka kudin a account dinka, in baka dashi ka bude dan gara in baka su a hannunka,
Allah yasa ka fara a sa'a,

Ameen ya Allah nagode kwarai Allah ya kara daukaka,
Ameen ameen Hafiz ban kuma ce ka fadawa kowa ba,
ka rike shi sirri a tsakanin mu,

angama anty babu wanda zaiji in shaa Allah,

nan suka dan taba hira har kusan goma yayi mata sallama ya tafi cike da farin ciki....

Duk nuku nukunki sai kinje Nadiya,
Baffa mahaifina ne duk abin da yake min badan baya sona bane tunda shi ya kawoni duniya,
Nadiya da bata da mafita tace "zanje mamma rigar ce taki shigana,
zama ta shige ki ne matso in zage miki zip,
matsawa tayi badan ranta yaso ba mamma taja mata rigar ta shige tsaf kamar a jikinta aka dinka,

gashi ya shige maza daura dankwali muje,
dankwalin ta daura ta yafa gyale duk ranta a jagule,
ta tsani wulakancin su Badariyya, tasan Sam haduwarsu ba Mai dadi bace kullum suka hadu sai sun tozarta ta kuma babu Mai hanasu,
daukar zainab tayi ta bi bayan mamma suka fita hade da rufe gidan...

Gidan cike yake da 'yayan kawayen mummy da iyayensu da ita kanta,
suna can ciki anata wasa da ciye ciye,
iyayen kuma suna hira hade da Shewa,
can gefe kuwa su Reemah ne ita kannenta sunata hira babu Wanda ya lura da zuwansu,

hakan ya ba Nadiya daman zama can nesa dasu tana kallon yaran dake dakin 'ya'yan hutu kawayen su badariyya,

zainab da hankalinta ya gama tashi da tulin kayan wasan yara sa'aninta ta mike a jikin Nadiya tace anty zanyi wasa,

Nadiya ta zaunar da ita tace ki bari su gama kema sai kiyi kinji,

gyada kanta tayi tanata binsu da ido suna wasa babu kakkautawa,

Mamma kuwa tana can gurin su goggo da mummy da kawayenta sunata hira, tunda ta gaishesu ta nemi guri ta zauna a kasa itama, babu Wanda yace musu ga abinci haka in za'a ba yara barka da sallah babu wanda ke kallonsu,
sallah kadai ke tada iyayen Sannan su dawo su cigaba da hira,

"Suwaiba tashi ki tattara gidan nan tunda baki San abinda ya kamata ba sai an fada,
muryar goggo ta dakin kunnen daukacin mutanen dake cikin parlorn,

da sauri mamma ta mike tana murmushi ta fara tattare kwanukan da suka ci abinci,
kwala Kiran Nadiya tayi tace taho ki fitar min da kwanukan nan,

zaunar da zainab tayi ta mike sum sum ta karbi kwanukan hannun mamma tayi waje dasu,

Badariyya dake kwance tana game a iPad dinta ta bita da ido cike da rainin wayau,
tsaki taja ta cigaba da danna iPad dinta,
ta rasa dalilin dayasa ta tsani Nadiya,
bata jin ko digon kwayar Santa a cikin zuciyarta,
tasan tafi Nadiya dukkan gatan rayuwa, haka kyau karyarta ta nuna mata, can kasan zuciyarta ta jiyo yayi amsar kuwwar "KYAWUN JIKIN FA" tsaki taja tace saidai jikin Shima dan bamu gama girma bane amma Nadiya babu abin da ta fini dashi,

Husna da Laila yar kawar mummy suka bita da kallon mamaki sukace to waye ya ce Nadiya tafi ki wani abu,
gimtse fuska tayi hade da runtsa ido dan bata San maganar zuci ta fito fili ba,

A ranar babu wani abu da ya shiga tsakaninta da badariyya saboda Hilal da yayi kaka gida a parlorn, Kasa katabus tayi saboda tsoron Kar ya sake marin kyakykyawar fuskarta,
ta tsani abin da zai taba fatarta koda kuwa kuda ne,,

Yaji mamma tayi ma Reemah da yawa na tafiya sannan tayi ma musaddiq dambun kifi da nama,

murna sosai sukayi sunata godiya,

sai bayan Isha mamma ta fara shirin tafiya,
dakin Baffa ta shiga Wanda yake cike da 'ya'yan mummy da ita kanta suna meeting ana ciye ciye,
durkusawa tayi tace Baffa mu zamu tafi sai da safe, to madalla sai da safe suwaiba,
yaki taho zainabu ki karbi kudin mota,
nokewa zainab tayi saboda rashin Sabo,
mamma tayi murmushi tace "quiwa gareta, ,
toooo... to ta rike kanta ta cinye, sai Allah ya tashe mu ki gaida Adamun,
to zaiji Baffa,
ta waiga tace masu sai da safenku,
to sai da safe duk sukace suna masu kai nama bakinsu..

Reemah dai kai kawai take girgizawa cike da takaici,

yafito Hilal tayi da hannu tace maza yaje ya sauke su a gida,

kunkuni ya fara yi yana buga kafa,
musaddiq ya mike yace bani mukullin,
da sauri ya wurga masa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarshi, a can bakin gate ya tarar dasu suna kokarin fita,
Mota ya bude yayi musu hon yaja ya isa gaban su,
bude musu yayi yace mamma muje in kaiku,,
ayi haka.... mamma ta fadi tana rike baki,

bakomai ku shiga muje,
baya suka shiga ya ja motar suka wuce....

********
Tun daren suka gama shirye shiryen komai na tafiya,
ba kananan kudade daddyn shi ya turo na siyayyar tafiyarshi ba, mummy da kanta ta shirya mishi kaya suna ta hira cikin farin ciki,
Yaya wata nawa zakayi? Husna ta tambayeshi tana bude ledar dambun naman da mamma tayi mishi,
mummy tayi dariya tace shekara nawa dai, ai sai kin ganshi kawai, Husna tace "tabdi har shekara anya mummy zai iya zama kuwa, shi da baya ko iya kwana a wani gari,
shafa kanshi mummy tayi tace "can ma ai gida ne ko little? ,
gyada kai yayi ya kwanta kan cinyarta yace but I will miss you so much mummy,
i will miss u more my baby,
ka kwantar da hankalinka zan dinga zuwa ganin ka a kai kai kaji,
um kawai yace yana kallon Badariyya dake mishi kallon shi din baida wayau,
tsaki yaja ya mike ya nufi dakinshi,
rainin Badariyya a gareshi yayi yawa,
lallai taga gadon barcinshi amma babu komai with time Shima zai zama jajirtacce marar daukar raini in shaa Allah ya fadi yana mai karfafa zuciyarshi.....

Mrs Tijjani Shattima....
[04/12 09:46] Meela Adeel: 9⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

HAPPY NEW YEAR, Allah yasa mun shigeta a sa'a AMEEN....

2017 is unforgettable... Allah yayi Maka Rahama Babana...

"Kilode sis"...
Husna ta fadi tana zungurar Badariyya da tayi tagumi tana kallon Kasa,

tsaki Badar ta ja tace "nothing bacci kawai nake ji,

Husna ta tabe baki hade da kwanciya tace
"to ai sai ki kwanta,

Badar ta dan kashingida ta runtse ido kamar mai bacci,

har cikin ranta bata son tafiyar Musaddiq,

duk da yawan samun sabanin da sukeyi tafi son kasancewarshi kullum a gida tana mishi koda kallon raini da wulakancin da ta saba ne,

to in ya tafi wa zata dinga gani,
Husna tayi mata kadan a cewarta,
duk da sa'oin juna ne amma a koda yaushe Badar gani takeyi ta girme ma Husna nesa ba kusa ba saboda tsantsar sangarta da d'agawa,

tunanin hanyar da zata bi ta hanashi tafiya ta shiga yi,
ta dade tana tufka da warwara kafin daga karshe ta samo mafita,..

a hankali ta Mike ta murda kofa ta fita ,

dakin mummy ta nufa dan tasan bata ciki tana can gurin musaddiq,

drawers ta fara janyowa ta shiga binciken visan musaddiq da aka kawo mishi jiya,

da kyar ta gano inda take cikin wata karamar jaka,

dariyar farin ciki ta shiga yi a ranta tace zanga yadda za'ayi ya tafi ba wannan,

hannu tasa zata fara yagawa taji an Fisge visan  a hannunta,

saurin waigawa tayi dan ganin ko waye,
Husna ta gani tsaye tana kallonta cikin ido,

"haba Badar yanzu muguntar taki har ta kai haka,
meye amfanin yaga mishi visa,?
tun fitar ki na biyo ki dan nasan ba fitar alkhairi kikayi ba,
akwai abin da kike shirin kulawa da shurun da naga kinyi,,

mtswwwwwwwww Badar taja dogon tsaki tace "dalla malama bani,
ni nace miki yagawa zanyi,

to me zakiyi dashi? husna ta tambaya fuskarta dauke da mamaki,

ban sani ba Badar ta fadi tana mik'a hannu zata kwace,
kaucewa husna tayi tace wallahi bazan baki ba,
sai dai ki kwata ta karfin tsiya,
Chapter 5 · 0% Book details