← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 113

Sashe 106

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har wannan lokacin su Daddy basu san da zaman junior ba dan basu ganshi ba.....

Su Mummy bayin Allah suna can dai a rabe har lokacin,
sunga karshen asali,
kowacce a cikinsu tana cike da dana sanin rayuwa..

Raliya da Reemah ne kadai ke kai kawo a kitchen suna hada hadar haďa lunch,
sai Husna, Maleekah da Nadeeyah dake tayasu,

Maleekah da Nadeeyah hira sosai sukeyi kamar sun dade da sanin juna,
gasu dukkansu wayayyu babu wacce ke jin kunyar yin magana...

Bayan sun dan taba abinci duk suka nufi waje dan yin Sallah..

su kuma matan suka nufi daki dan yin tasu a can...

Gyara parlon Husna da Nadeeyah sukeyi suna hirar yaushe gamo, labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan take bata, ga mamakinta bata ji inda tace "Musaddiq yayi aure ba, sharewa tayi ta kauda tunaninshi a ranta domin yanzu tana son tayi moving forward...
rashin ganinshi a cikinsu ya tabbatar mata yana can yana rayuwarshi cikin jin dadi....

Duk wannan budurin da akeyi Musaddiq na cikin daki ya kure volume suna game shi a dole bayason jin wani abu da ya shafi su Badariyya....

Ganin little Nadeeyah tayi bacci ne ya sashi gyara mata kwanciya ya shiga ya watsa ruwa,
kananan kaya yasa wadanda suka fitar da kyawunshi sosai,
yanzu girma ya sanya Musaddiq ya zama moderate,
wannan kibar duk babu ita,
sai tsawo sosai da dan murjajjen jiki,

kwantacciyar kasumbarshi ya taje ta kwanta lup a fuskarshi, turaruka masu kamshi ya feshe jikinshi dasu sannan ya kashe wutar dakin,
Sallah kawai zanyi in nemi abinci,
abinda ya faďi kenan haďe da murďa kofar dakin ya fito....

Ta sama ya leko yaga ko an ragu a parlon,
ganin bakowa ya sashi fara tafiya cikin kasaita dan isa gurin steps din, 
kamar ance ya sake kallon gefen console,

Tsaye ya hangota ta maida gashinta gefe tana kokarin cire dankunnenta a jikin rigarta,

Hannayenshi biyu ya daura akan karafen da ke kewaye da saman yana kokarin ganin fuskarta ta mudubin...

Haaaa...

ta faďi bayan ta cire dan kunnen, maida gashin baya tayi ta naďe shi ta goge fuskarta da hannunta sannan ta fara kokarin nade gyalen,
jin kamar wani abu yabi ta kunnenta yasata noke wuyan dayan dan kunnen ya sake makalewa, wannan karan ya shiga da karfi,
ajiye gyalen tayi ta fara dambe dashi tana tsaki....

Tunda fuskarta bayyana a gareshi ya shiga rudani,
da sauri ya mutstsika idonshi yaga ko gizon da ta saba yi mishi ne,
ganin dai mutum ce a tsaye ya sashi sake dubawa da kyau ko Maleekah ce,
yadda yaga tayi da baki kamar zatayi kuka yasa shi lumshe ido kirjinshi sai lugude yakeyi...

"Husnaa...
yaji ta faďi da muryar neman taimako,

A hankali kafarshi ta fara janshi,
shidai yaki gasgata idanuwanshi wadanda suka tara ruwa a lokacin..

Saura kaďan ya isa gareta yaji wani kamshi mai dadi acn gurin na bugo mishi,
zuciyarshi ce ta ingiza hannunshi ya dagoshi da niyyar taimaka mata...

Mamma...
we am back..

Juyowa tayi da sauri ďan kunnen ya fita a kunnenta gaba ďaya,

kyammm..
idanuwansu suka makale cikin na juna,
nan fa zuciyoyin da suka daďe suna kewar juna suka fara zubar da hawaye a junansu, 
daga Nadeeyah har Musaddiq babu wanda jikinshi baya rawa, babu kamar Musaddiq da a lokacin yake jinshi kamar mutum mutumi,

Cikin karfin hali da dauriya Nadeeyah ke kokarin raba idonta da nashi amma sam zuciyar da ta daďe tana ďoki da marararin ganin mahaďinta taki bata haďin kai.....

A tare Hilal da Musaddiq suka shigo parlon suna ďan taba hira,
hirarsu makalewa tayi da sukayi arba da abinda ya sosa ran Taheer..

Hannun da Musaddiq ya ďaga yasa a gefen rigarta ya cire mata dan kunnen har lokacin bai dauke idonshi cikin nata ba...

Badariyyah data fito daga kitchen ta tsaya kallonsu zuciyarta sai rawa takeyi hawaye ya shiga yi mata ambaliya..
a yanzu tasan mai gadi ma rayuwarshi tayi mata nisa bare Musaddiq..

Mamma..

Junior ya faďi yana girgiza mata riga,
a firgice ta kalleshi cikin sanyin murya tace

"Ummm,
ina kaje?,

"Munje yawo ni da namesake,
yace shima sunan mu ďaya haka ne Mamma?

Gyaďa mishi kai tayi ta karbi ledar hannunshi ta ajiye ta wuce kitchen da ďan gudu gudu tana maida numfashi.....

Bayanta Junior ya fara kokarin bi Musaddiq ya rikoshi da sauri,
dafashi yayi ya tsuguna kirjinshi na dukan uku uku yace

"My Twinny,

Zaro ido Junior yayi yace

"Yayyy
*MMK*  right?

Yess...
Musaddiq ya faďi jikinshi samm babu kuzari..

Kallon inda Taheer yake tsaye yayi ya taho da sauri yace
"Daddy, zo kaga strangern da na gani a Hallmark,
i told u he is just like me,
har gaban Musaddiq ya janyo Taheer yace
"Kaga idonshi irin nawa,
i will not lv here sai nayi grabbing face dinshi,
sketch din da nayi baiyi kyau ba....

*Daddy.....*

Musaddiq ya dinga maimatawa a cikin ranshi,
dakyar ya iya dago kanshi suka haďa ido da Taheer,
nan take halittar nan marar dadin faďi a baki ta shiga motsi a zukatansu...

Ganin haka Hilal ya karaso gurinsu da sauri yana murmushi,

"Hey Kyari,
ka ganeshi, Uncle din su Nadeeyah,
ashe all this while Nadeeyah is with him..
sun kula da ita sosai da gudan jininka,

Janyo Junior yayi kusa da Musaddiq ya haďe hannayensu guri ďaya yace
"He is ur blood Kyari,
ur flesh and blood..

"Tell him ur name,
Hilal ya sake cewa ma Junior cike da doki,

*MUKTHAR HILAL MUSADDIQ KYARI* a.k.a *MHK TAHEER* ya karashe haďe da damke hannun Taheer....

Runtse ido Musaddiq yayi yanajin dukkan nauo'in biyu a cikin zuciyarshi,
farin ciki da akasin haka,
a hankali ya buďe idonshi ya sake tsugunawa a gaban Junior, janyoshi yayi ya rungumeshi tsamm a jikinshi..

Wasu zafafan hawaye ne suka shige tsere tsakanin idanuwanshi zuwa kuncinshi,
da sauri junior ya raba jikinshi da nashi saboda jin ruwan hawaye da yayi a kafaďunshi,

"Hey twinny, ya faďi a dan tsorace yana ja da baya zai koma gurin Taheer,
rike hannunshi Musaddiq yayi yana girgiza kanshi wasu hawayen na fitowa kamar ana ingizo su,

"Daddy...
Junior ya fara faďi yana kokawar kwace hannunshi cikin na Musaddiq,
a tsorace yake matuka dan bai taba ganin zubar hawayen babba ba,

Cikin sanyin jiki Hilal ya tsuguna a gaban junior,
dayan hannunshi ya kamo yace "My dear he is ur Dad too,
ur biological father,
go to him,
he is *MUSADDIQ KYARI*
His name is connected with urs...

Juyawa Taheer yayi wani makoko ya tokare kahon zuciyarshi,
hawayen da yaketa matsesu suka zubo daga idonshi..

"Noo...
Junior ya faďi haďe da fisge hannunshi daga dukkansu,
da gudu ya koma gurin Taheer ya rungume kafafuwanshi ta baya,

"Dis is my Dad,
his name is also connected with mine,
"Daddy plss tell them u are my biological father ya karashe bayan ya dawo gaban Taheer ya tsaya..

Daga kai Taheer yayi sama ya share hawayen da ya sake taruwa yana neman zubo mishi, dan kar Junior ya gani,
ďagoshi yayi ya daurashi a kirjinshi yace
"He is ur father Sweetheart,
i'm ur father and ur name sake is ur father too,
we are all ur Dad..

"Only one is my biological,
who among the three?
ya tambaya idonshi kyamm akan Taheer,

Runtse ido Taheer yayi maganar da yake kokarin yi ya kakare mishi a makoshi...

Share hawaye Anty Saude tayi ta karaso ciki da sauri ta karbi Junior,
"Ina ka shiga My dear,
ko abinci baka ci ba, and all ur so called fathers basu damu da su baka ba,
duk kace bakayi dasu muje kaci abinci..

Kwantar dashi tayi akan kafadarta ta wuce cikin kitchen dashi,
tayi hakan ne dan ya samu nutsuwar sanin ainihin mahaifinshi,
duk nauyin Junior a wannan lokacin Anty Saude ji tayi yayi mata shafal,
zaunar dashi tayi akan kujera ta kwalawa Nadeeyah da ta hangota acan baya kira....

A gaggauce Mummy tabi bayan Anty Saude itama idonta cike da kwalla,
samm bata damu da ganin su Daddy tsaye curko curko bayan gama kallon abinda ya faru ba..

Tana shiga ta kankameshi tana kuka mai sauti haďe da sumbatar ko ina na jikinshi...

Cike da kyankyami kamar zaiyi kuka yace

"Momma,
plss lts lv dis house...

Mummy bata damu da kyankyaminta da yaji ba ta sabashi a jikinta ta durkushe gaban Nadeeyah tana kuka tana rokon gafararta,
cikin kuka Nadeeyah ta tsuguna tace
"Dan Allah Mummy ki bari,
we are all humans, we are bound to mk mistakes, walhy ban rikeki a raina ba..

"Kuskurena yakai girman da za'ayi min koma meye,
sakarcina ya hanani hango alkhairan dake tare dake Nadeeyah,
yanzu wannan jikan nawa da kuskurena ya sanya fitarshi bazan taba yafewa kaina ba,
dan Allah kuyi hakuri ta karashe cikin matsanancin kuka....

Su Anty Reemah da suka shigo gurin duk idonsu ya ciko da hawayen tausayi,

Raudha da Radiya ma cike da Kuka suka tsuguna a gabansu suka shiga ba Nadeeyah hakuri...

Hamdala Raliya tayi a cikin ranta sannan ta sake godewa Allah da yasa dukka yan uwanta da mahaifiyarta suka gane kuskurensu...

To kukan ya isa a miko min jikana in bashi abinci,
dariya Mummy tayi ta Saki Junior da yake a matse dama,
da sauri ya koma gurin Anty Saude ya ďane jikinta haďe da kwanciya ya runtse idonshi....

Sai a hankali zai saba,
kunsan yanzu ne ganinku dashi na farko,
sai kunyi hakuri da koma meye...
yadda Anty Saude ke maganar cikin fitar da tsammanin zamanta tare dashi ya sanya Nadeeyah barin kitchen din da sauri,
ta riga ta gama yanke hukuncin zama da Taheer,
babu wani dalili na tausayi ko wani abu da zai canza mata ra'ayinta,
Halaccin da zatayi wa bayin Allahn nan kenan, ta kare rayuwarta tare dasu.....

Gyaran murya Sarki Tidjani yayi yace
"Hukumullahu laa Ajabun, hukuncin Allah ba'a mamaki akanshi,
abin da ya kawo mu daban sai gashi Allah cikin ikonsa mun haďu da abinda muka shekara da shekaru muna nema.....
Chapter 106 · 0% Book details