← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 113

Sashe 23

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kicibus tayi da yaro ya shigo da zabuwa an yanka ta,
dariya tayi tace "ko baka fada ba nasan Bala ne ya aiko ka,
gyada kai yaron yayi ya fita da gudu,
albarka ta shiga shi mishi saboda kullum sai ya kawo musu halastacciyar dabba gidan sunci,
maryam ta mikawa zabon tace "maza tayi amfani da ruwan zafin ta gyara shi,
amsa tayi cikin ladabi ta gyara shi hade da bankareshi yadda zaiyi kyaun gashi,
kafin Mamanta ta fito har ta fara gasashi cike da kwarewa,
saida ta gama tass sannan ta sa a karamin bangaji ta wuce ta kaima Aisha....

Saboda dadewa bata huta ba,
da kuma karancin bacci da take samu yasata ta kai har bayan isha'i bata tashi ba,
babu wanda ya tasheta saboda yanayin da take ciki, saida tayi bacci mai isarta sannan ta tashi tana mika hade da salati,
ganin duhun dakin ya sanyata mikewa zubur ta fara lulube,
dan hasken dake tsakar gidan ta hango ta tsagin tagar dakin,
ajiyar zuciya tayi ta dauki mayafinta ta rufe kanta sannan ta fito waje,
kamar jiranta yaran sukeyi ta fito suka kewaya ta suna kallonta,
magana Aisha tayi mata tace "kije kiyi alwala kiyi salloli sai kici abinci kiyi wanka..

Tana idar da sallah suka kewaye ta da abinci da fura da kuma gasashshen zabo,
tuwon taci sosai tana hamdalla a zuciyarta,
rabon ta da taci irinshi tunda kaddara ta kaita auren Baffa,
saida taci tayi katt sannan ta kora da ruwa,
naman ne kadai bata ci ba saboda sam batason jin kamshin gashi, Ba karamin horata Ma'u tayi ba da gashinta na kullum,
wanka tayi da ruwan zafi mai dadi sannan ta dawo inda suke ta zauna,
rokon Allah ta shiga yi da ya barta a cikin su har Allah ya kawo sanadiyyar da zai hadata da Abbunta da kaninta Ateek,

kallon irin zaman da sukeyi takeyi mai cike da tsafta da kaunar juna,
yaran gidan duk suna kaunar junansu haka basa yi ma wacce ba uwarsu ba rashin kunya,
matan kuwa kullum cikin hira suke da karatun al kur'ani, wani lokacin kuma mai babban suna ta tarasu dukkansu harda makota ta basu tarihin Annabawan Allah da iyalensu, da irin gwagwarmayar da suka sha,
shiyasa a ko da yaushe gidan yake a cike da mata da maza,
koda yaushe gidan baya rabo da abin ci da kuma sha saboda yawan sadaukarwar da sukeyi.....

Shigowa gidan yayi fuska dauke da murmushi ya kalli ahalin gidanshi ya kara samun nutsuwa a cikin ranshi,
a kullum kara godewa Allah yakeyi da ya hada shi da Aisha da kuma sauran matanshi masu fahimta da lura,
Zama yayi a tsakiyarsu ya kalli Atika yace "Barka da zuwa cikin Ahali na,
nayi matukar farin cikin jin zamu samu jininki a cikin zuri'ata,
ina miki fatan Allah ya sauke ki lafiya, daga nan sai mu tafi can kasarku da dan da zaki haifa..
Ameen matan shi suka ce cike da farin cikin addu'ar,

kallon Maryam yayi yace "Malama Maryama ku koma can gefe ke da kannenki zamuyi magana da iyayenki,
mikewa sukayi cike da ladabi suka koma wata tabarmar a kusurwar dakin Saude matar Hardejo ta uku,
Aisha ya kalla yace "mun kusa samun siriki,
cike da farin ciki laure tace " Alhamdulillah, wanene ke son Maryama?
Bala,
Bala ne ke sonta, dazu ya turo mahaifinshi, na kuma ce na bashi,
cike da farin ciki dukka matan suka ce mashaa Allahu,
Allah yasa alkhairi, Allah ya basu zuri'a dayyaba,
Ameen Hardejo ya fadi ya kalli Aisha da taki amsawa saidai murmushi kawai takeyi, ita a dole kunyar diyar fari,
nan fa suka shiga tsokanarta cike da nishadi kamar ba kishiyoyi ba.....

*BAYAN WATA BIYAR*

●●●●●●
*Mummunar Kaddara*

Har lokacin Baffa bai waiwayi gida ba, yana can yana neman kudi saboda ya tsira mutuncinsa da na iyalinsa,
kullum cikin tunaninsu yake, ciki harda Atika da sam bashi da masaniyar tana dauke da cikinshi,
cikin kudirar ubangiji neman da yakeyi Allah na sa mishi albarka a cikinsa dan har ya samu ya siya dan gida mai daki uku ginin siminti na jaka biyar da rabi a cikin jalingo,
a wannan lokacin ne ya yi niyyar zuwa gida dan ya tattaro iyalinshi ya fara sabon zama dasu mai cike da jin dadi..

A cikin watanin da suka shude aka daura auren Maryam Da Bala Shaho,
murna a gurin shaho ba'a cewa komai saboda yadda ya dauki malam da ahalinsa, bauta ce kadai bazai iya masa ba,
domin kuwa ya taimaka mishi gurin samun rayuwa mai inganci da tsafta...

Atika ma tayi bul bul, cikinta yayi girma sosai har yayi mata nauyi,
gaf take da shiga lokacin haihuwarta,
kula ta musamman take samu a gurin Hardejo da matanshi,
ba irin kayan da basu sak'a ma jaririn ba tun kafin
Zuwanshi duniya,
a wannan lokacin Atika ta dan fara jin fillanci kadan kadan, dan in aka mata magana zata ji amma mayarwa ke mata wahala....

Ita kuwa Ma'u tun da ta tafi can garinsu ukari bata dawo ba sai dai aiken mugun abu da take ta yo wa Atika da cikin jikinta,
haka duk juma'a sai ta bi motar katako taje garin dan taga ko mijinta abin kaunar ta ya dawo sannan ta shiga gurin Haire ta bata sakon magungunan da take kaiwa Atika dan cikin ya zube,
bata san Haire watsi takeyi da maganin ba, domin ita mace ce mai tsananin tsoro,
tunda ta amshi musulunci ta daina duk wani aikin sabon Allah, dama wani lokaci ma'u ke zugata suyi tare,
yanzu ko da ba ta nan, kullum tana gidan Hardejo daukar karatu...

Yau ma kamar kowace jumma'a ta gama shirye shiryenta na mugun kullinta, ta dauko su Bingel ta shiryasu dan yau in ta tafi bazata dawo ba,
tasan da tana garin babu abin da zai hana ta kashe dan dake cikin Atika,
yanzu kuwa ta dauki alwashin kashe har Atikan saboda in ta barta to fa Hardejo sai yasan yadda yayi ya sake sata cikin rayuwarsu,
gara kawai ta kashesu gaba daya..

A daidai kwanar da zata sadasu da hanyar kauyen suka hango cincirindon yan ta'adda, babu kaya a jikinsu sai wukake rataye a kafadunsu da kugunsu,
tsayar da motar sukayi suna ta wasa wuka a kasa,
fitsari Bingel ta saki ta fara ihu tana kuka,
sakko dasu mutanen sukayi suna mazurai,
cikin wani irin yare suke tambayarsu ko su musulmai ne, drivern da yake yana yawon safara, Kuma yasan musulmai sun fara yawa yace "eh shi musulmi ne,
nan take suka farďeshi sukayi wurgi da gawar,
Ma'u jiki na rawa tace "Dama kai musulmi ne ka dauko mu?
Ta fara tambayar karen motar, girgiza kai karen motar yayi yace ni cikakken mabiyin Addinin sarki *HAWAIZU NA UKARI* ne, Dariyar keta mutanen sukayi suka ce "ina za ku?

Ma'u da ta gama samun mafita tace "Gembu,
kauyen da Malam Hardejo ya cika shi da musulmai,
zamuje ne domin yi musu magana akan abin da sukeyi mara kyau,
sun yarda bautar iyaye da kakanni sun dauki wani addini da Hardejo ya kawo,
cike da farin cikin samun Nama ogan yace "dama mun dade muna son kai farmaki kauyen,
mai girma *SADUN* ya dade yana bamu labari akan malamin da yayi wa kauyen kawanya da musulmai,
ku shiga mota ku jagorance mu dan mu aikata abin kirkin da za'a dade ana tunamu dashi har duniya ta dade.....

A kofar Gidan jauro Ma'u ta sauka da ya'yanta,
tayi musu nuni da gidan Hardejo, tace musu zata dubo dayan malamin ko yana nan zata zo ta samesu,
wucewa sukayi; ita ma ta kama ya'yanta ta ruga da gudu ta shige gidanta ta turo,
babban fatanta shine su fara yin layyarsu da Atika,
can kuryar daki ta shige ta kwantar da ya'yanta hade da tsoratar dasu dan kar su tashi suce zasu fita,
saida ta tabbatar bacci ya daukesu sannan ta fito ta tsaya a tsakar gida tana kasa kunne,
ita dai in bukatarta zata biya Kowa ma ya mutu,
yanda taci alwashi a kauyensu na cewar Baffa bai isa ya mata kishiya ba,
kuma kawai sai gashi banda kishiyar har 'yan uba gare ya'yanta,
inaa sam in ta bari hakan ya faru to bata cika jinin *MANASIR* ba....

Kamar yadda suka saba taruwa a kofar gidan ranar jumma'a maza da mata yau ma hakan ne ta kasance,

Kamar daga sama sukaji tsayuwar motar katako a kansu,
babu wanda yayi yunkurin katse sallar saboda a iya saninsu kauyen nasu lafiya lau yake domin musulmai sun danyi rinjaye a garin yanzu,
tun ba ma komawar shaho cikin musulunci tsundum ba,
a sujjadar karshe suke sukaji an fara kai musu farmaki,
basu sallame ba har lokacin saida suka gama zaman tahiyar karshe,
suna sallemawa kowa ya fara neman hanyar tsira,
kewaye su yan ta'addan sukayi suka dinga sarar jikinsu,

"Allahu Akbar
Malam Hardejo ya fadi nan take gurin ya dauka, a nan fa Shaho da mutanenshi suka tuno da dabanci suka tube kaya suna fadin Allahu Akbaar,
suka nufi yan daban,
Rashin makamai ne ya cucesu shiyasa duk fadan da sukeyi aka sassari su shaho,
cike da karfi Shaho yayi kokarin fusge katuwar wukar jikin ogan,
nan fa yasa ihu ya fara sararsu iya karfinshi,
a take samarin garin suka shiga gidajen kusa suka dauko makamai,
ciki harda Barde mahaifin shaho,

shi kuwa Hardejo sallah ya koma ya cigaba dayi yana rokon Allah ya kareshi da dukkan jama'ar musulmi,
(idan Ajali yazo)
babu makawa sai an tafi,
babu addu'ar dake dauke ajali a jikin mutum,

kamar hadin baki arnan kauyen suma suka fito da makamansu,
"in ka san farkon rigima to fa baka san karshenta ba,
Rigimar da Ma'u ta hada saboda san zuciyarta ya haifar mutuwar rayuka da dama,
Ma'u bala'i ce a cikin alummar musulmi....

Shaho ya jigata iya jigata,
shi kadai ne mai karfin dake yakarsu,
sauran arnan garin abin da yasa sukaci galaba akansu saboda daga cikin gidan suka fara gurin matan,
saida suka karkashe matansu da ya'yansu sannan suka fito suka hada hannu akan mazan,
dama ba karamar tsana sukayi wa Hardejo ba,

wani a cikinsu mai siyar da barasa yayi kan Hardejo da gatari saboda shi tuni yake hakonshi dan hani da yayi da shanta ga daukacin musulman kauyen yasa shi ya daina ciniki,
Chapter 23 · 0% Book details