← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 113

Sashe 3

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin zafi yace ''I usually give people more chances dan dey deserve, but once am done am done,!
waye sa'an ki anan, tun dazu kina ta zuba rashin kunya an kyaleki shine kike kokarin wuce limit dinki,
ya kalli musaddiq cikin kunan rai yace
''kanwar kanwarka ta tsaya tana fada maka magana kai kuma kana tsaye kamar gunki, u'r pathetic wallhi mtswwwwwwwww, yaja tsaki hade da daukar wayarshi yace ''wannan dalilin ya hanani shigowa gidan nan,
kallon Anty Reemah yayi yace  ''plss lets go Mum,,

faduwa kasa Badariyya tayi tana ihu tana shureshure tana fadin ''Allah ya isa mugu azzalumi,
wayyo Allah na mummy ya tsinka min kunne,

da gudu mummy ta karaso ciki dan duk budurin da akeyi bata sani ba tana can bayan kitchen tana duba masu yi mata hidima.....

Mrs Tijjani Shattima....
[04/12 09:43] Meela Adeel: 5⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

Ya ya, me yake faruwa? kukan wa nakeji kamar Badar,
da gudu ta ruga jikin mummy, Hilal ya bita a guje ya daga hannu zai kai mata duka mummy ta daka mishi tsawa, ''kulll karka sake ka taba ta, rasa kunya berar danga,

ko girgiza baiyi ba bare ya saurari abinda ta ce ya sauke hannunshi a bayanta,

wani ihun Badar ta sake saki kamar wacce ake yankawa,

kallon gurin da suke mummy tayi cikin bacin rai tace'
''Reemah dan iskanci kina tsaye danki zai raunata min 'ya, babu Wanda yayi yunkurin hanashi,
kuma saboda rashin ta ido ya iya Zuwa har gabana ya narka mata gudumar hannunshi a baya,
to wallhy bazan dauka ba, ko ki rama mata ko kuma ni in rama mata da kaina,

Raliya tace ' ''haba mummy, ya za'ayi mu shiga fadan yara,
Badar ce fa bata da gaskiya, rashin kunyarta kullum dad'a k'aburi yakeyi,
babu Wanda ya isa ya fada mata taji,
daga fitowarta babu ko gaisuwa ta fara magana cikin isa da rashin kunya,
thank God akwai Hilal a nan,  da dukan da zan mata wallahi sai yafi haka,

mummy ta saki baki cikin mamaki tace me tayi ne waiii,

Husna ta kwashe duk abinda ya faru ta fada mata,

mtswwwwwwwww mummy taja tsaki tace
''to karya ta fada, duk Wanda yaga musaddiq yasan baida cikakken hankalin zaman duniya,,

Sam baisan inda yake mishi ciwo ba,
bai San darajar kudi ba saboda baya nemosu, kashesu kadai ya iya yi,
da yasan darajar kudi bazai daukesu ya kaisu muhallin suwaiba ba saboda bata da bukatarsu,
bata ma San me zatayi da su ba,

bai San su kudi ana kaisu inda in suka shiga zasu fito da mafiyinsu ba,
a'a kawai shi ga mai tausayin banza ya dauki zunzurutun kudi ya kaiwa suwaiba,
K'ara kaurara murya tayi tace "wallhy tun muna Shaida juna ka fita kaje ka karbo kudin nan, kafin wani azal ya afka musu,
ka bar mata dubu biyar din da na saba bata kuma ka tabbatar ka kaima kanwar Hajiya Nafeesa kana Jina ko,?
kasa dago kanshi  yayi saboda kwallar da ta taru a idonshi,

wani karamin tsaki Hilal yaja yayi waje cikin kunan rai,

Kiyi hakuri mummy, Anty Reemah ta fadi cikin taushin murya,

hakuri daya zanyi inji kudi na a hannuna,

Radiya da Raudha suka kalli musaddiq suka ja tsaki,
Radiya tace
''haba little dubu dari biyu fa,
kaima kasan kayi rashin hankali,
mutanen da duk iya rayuwarsu basu taba rike dubu goma ta kansu ba,

"Raudha miko min wayata maza in kira mama suwaiba dan Kar ma ganin kudin ya sa su kirkiri amfani da shi, dan su kudi kana ganin su amfaninsu ke zuwa ko ba budget,
gara ko man Mota mu Sha dasu Kinga sunyi mana amfani,

dauko wayar Raudha tayi ta fara latsawa,

''ba sai kin kira ba Raudha ga kudin nan nazo dasu ta fada cikin sanyinta had'e da karasa shigowa cikin parlon,

ajiye zainab tayi ta tsuguna har kasa ta gaida mummy,
ta ciro kudin cikin jaka ta mik'a mata tana murmurshi,

tun bayan tafiyar musaddiq ban yarda aiko shi kikayi ba,
nasa a raina ko mantuwa yayi shiyasa na biyo baya,
da na kiraki kika tabbatar min kin aikoshi sai na ajiye har Malam ya dawo shine yace in dai kawo in tambaya da kaina,
tunda na doso naji maganganu sai na tabbatar mantuwa yayi ya kawo,

nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,
ameeeen!!!
mummy tace hade da karbar kudin,

Matsananciyar kunya ce ta lullube Reemah da Raliya,

Musaddiq kuwa daki ya wuce ba tare da ya dago kanshi ba hawaye sai ambaliya suke a idonshi ,,

dambun kifi mama suwaiba ta dauko a Jakarta ta ajiye a Kasa kusa da mummy tace ''gashi ba yawa da fatan kunyi sallah lafiya,
''kalau suwaiba,!

to alhamdulillah Allah ya Maimaita mana,

"ameen ya Allah" mummy ta fadi ta wuce daki rike da kudinta a hannu,

waigowa mama suwaiba tayi fuskar nan dauke da murmushi tace duk Ina kwananku,
da sauri anty reemah ta karasa gabanta tace Ina kwana mamma,
lafiya lau Ant--Dan Allah ki daina cemin anty mamma, Reemah ta katseta da sauri,
murmurshi tayi tace to na daina, yaushe kuka zo,?
hannun zainab ta kama tace "dazu muka zo ina su Nadiya da Hafiz,
Hafizu ya tafi gurin aiki Nadiya kuma tana gida,

yau bata zo mana yawon sallah ba, Raliya ta fadi tana karasowa gurinsu,

har mun shirya tace Wai kanta na ciwo shine nace tayi zamanta a gida,
nan suka shiga taba hirar yaushe gamo da anty Reemah da bakin ciki da kunya sukayi mata katutu a zuciya,
kallon fuskar mamma takeyi wacce kyawu da fara'a suke boye ainihin bacin ranta,

Mama suwaiba jarumar mace ce mai tsananin kawaici da boye bacin rai, kullum fuskar nan cikin murmurshi take......

Kad'an daga cikin abubuwan dake faruwa cikin zuri'ar mu kenan anty,
laifin duk na su Baffa ne, su suke nuna fifiko saboda abin duniya,
soyayyar abin duniya ta rufe musu ido sun mance taimakon Yan uwansu na jini sai dai bare na neman suna,,
har ga Allah nayi niyyar kaiwa Baffa kudin dan na je har gidanshi,
abin da naga sun ma Nadiya shi ya karya min zuciya har zuciyar ta rinjaye ni da aikata hakan,
bansan abin zai kwabe haka ba, da ban kai ba,
da na jira dawowar Daddy sai in karba in kai musu, yanzu nasan "ransu bazai musu dadi ba" ya karashe cikin shashshekar kuka,

share mishi hawaye tayi tace
"Ya Allah ka karfafa min raguwar zuciyar Diku nah,
har yanzu kana nan da halinka na kuka,
lokaci ya canza Little, yanzu ka fara girma u are not a child anymore,,
tashi kaje kayi wanka muje gida,
akwai wani surprise din da na shirya maka,
cikin sanyin jiki ya tashi ya shiga bayi,, 

Tagumi Reemah tayi tana tunanin hanyar da zata bi ta wanke zukatan bayin Allahn nan,
Allah ya sani bata da masaniyar halin kuncin da suke ciki, ita dai tasan suna da wadatar zucin da zaisa kullum ka gansu cikin farin ciki...

Mrs Tijjani Shattima....
[04/12 09:44] Meela Adeel: 6⃣
Ayi min Afuwa pls wasu hidimdimu ne suka rike ni, Ina Mai baku hakurin jiran da kukayi nagode matuka da kauna, Ina kaunarku har cikin raina Yan uwana... In shaa Allah zaku jini kullum yanzu

°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

Ashe gaskiyar babanku ne da yace kila mantawa Musaddiq yayi,
hakan ce kuwa ta faru, dan kudin na Baffa ne,
tayi tayi ma in amsa nace mata a'a kudin sunyi yawa, mamma ce ke maganar cikin sakayawa tana kallon ya'yanta,

Nadiya dake kulla kankarar kuka, tace "nima dai mamma jiki na ya bani ba namu bane,
dan dai naga kin kirata ne shiyasa na dauka da gaske ne,
  Alwala Hafiz ya karashe hade da addu'a yace "mun gode Allah ma da yasa ba muyi amfani dasu ba, wannan din ma da ta bamu Allah yasa musu albarka,
"Ameen mamma tace hade da mikewa ta nufi cikin daki, babu wanda a cikin su ya karanci ainihin bacin ranta saboda fuskarta dake dauke da murmushi...

******
Hey handsome duk wannan cika da batsewar na menene?
Come on chill my guy,
yau fa is my day banason kowa yayi fushi a cikin ta,

Kara tamke fuska yayi hade da jan dan karamin tsaki ya mike yace
  "bansan me ke damun zuciyarka ba, bana cika mu'amula da masu irinta saboda wata rana haushin su zai sa inyi musu tsana marar misaltuwa,

u'r my uncle nd friend as well bana son abun da zaisa inji haushin ka,
nowadays masu irin zuciyarka basa samun nasara a komai saboda sanyinsu,

"sanyinka yasa kana namiji kai kadai a gidanku amma kowa ya rainaka harda BADAR for dat matter,
yaushe aka haife su?, dey are just 9! if am nt mistaken,
kuma ka tsaya a gabansu kana wani kuka,

gaskiya ka bata min rai, just go nd have fun Kar in bata maka naka ran, Hilal ya karashe fadi yana nuna mishi kofar fita da hannu,

"sannu ubanshi, Anty Reemah ta fadi tana karasa shigowa dakin,
Hilal ka fita idona walhy, bana son iskanci,
kasan inda zaka dinga nuna wannan bakar zuciyar taka,
kai a kullum duk inda kaje sai Kasa mutane sun tafi da kai a baki,
meye amfanin rashin hakuri, abin da hakuri bai baka ba wallahi rashin shi bazai taba baka ba,
duka nawa kake kaima da kake barin zuciya tafi karfinka,
wallahi kayi gaggawar sauke bakar zuciyarka har mu bar kasar nan in ba kanaso inyi mummunan saba maka ba, sakarai kawai,
"haba anty sorry mana,  ba fa wani abu yace min ba, musaddiq ya fadi cikin tausasawa hade da kama hannunta,

kallonshi tayi cike da son halinshi tace ko baice maka komai ba meye amfanin abun da yayi a gida,

"mum nifa babu abin da nayi, kawai dai gaskiya ce bakwa so, shiyasa Sam bana son shiga gidanku saboda ni ba na gani in kyale kuma in nayi kuce nayi rashin kunya, Allah ma yasan akan gaskiya na-- rufe min baki anty reemah ta fadi hade da bige bakin a hankali,

Janta musaddiq yayi suka bar dakin tanata masifar da Sam bata karbeta dan ba sabawa tayi ba,
Chapter 3 · 0% Book details