← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 113

Sashe 39

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abun taji ya tsarga mata tun daga kwanyar kanta har tafin kafarta,
yadda yayi kiran sunanta ta ya sake kashe mata jiki dan duk duniya banda Babanta babu mai kiranta da Umm Nadeeyah,
bata amsa shi ba ta fara tafiya da niyyar barin parlon,

*Nadeeyah*

ya sake fadi a hankali yana kallonta,
tsayawa tayi kamar zata saki fitsari saboda tsabar tsoron yanayin shi,
bai karaso inda take ba yace "dawo ki zauna,
akwai maganar da nake so muyi,
bata motsa daga inda take ba tana tsaye har seconds sittin,

Murmushi yayi ya kara takowa yazo har inda take,
kamar me rada yace
"matsayinki ya kai in biyoki inda kike,

kamar zatayi kuka ta juyo tace "um um dan Allah uncle kayi hakuri, zan dauko dankwali na ne,

"Ya riga ya gama fahimtar yanayinta na tsoro yayi murmushi mai kashe zuciya yace "naki wayan,

hular kanshi ya cire ya mika mata yace "ki rufe kanki dashi, saurin maida hannunta baya tayi tace "Dan All-- "karki hada ni da Allah, yayi saurin katse ta a kasalance,
hannu yasa ya dago habarta ya sanya idanuwanshi cikin nata, kokarin sauke idonta tayi jiki na rawa, yayi girgiza mata kai alamar a'a,

karkatar da kanshi gefe yayi, gaba daya soyayyarta tana neman maidashi zautacce,
ya mance matsayin malami yake a gareta,
suffofinshi na shagwababben Momma suka bayyana,
a hankali yace "plssss!!!
bata bari yayi magana ba tayi saurin runtse idonta hade girgiza kai,
bata taba shiga yanayin da yake kokarin sanya ta a ciki ba,
rufe idonshi yayi shima yace "karki hana ni plss,
akwai abun da ya ke kokarin karya duk wani lago nawa,

*Soyayya*

ita gayyaceni zuwa gareki ba tare da shirya ma zuwanta ba,
tell me,!!
kina son in barta ta sanya ni na rankwafa,
bani da wani sauran sukuni tun ranar da na fara ganinki,
kiyi min agaji,
ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki,
sonki ya gama shiga cikin jinin jikina,

Shuru ne ya dan ratsa gurin na minti daya,
bugun zuciyoyinsu kadai suke jiyowa sai numfashinsu dake gauraya da juna,

A hankali ta bude idonta wanda ya zamo kamar hadin baki shima ya bude nashi,
da sauri ta dauke kanta hade da rugawa ciki da gudu,

saida ta isa daki sannan ta fara maida numfashi..
jin karar ruwa a bayi ne ya bata tabbacin Husnah na ciki tana wanke jikin ta har lokacin,
a gefen gado ta zauna ta runtse idonta,
ta kasa fassara yanayin da take ciki, wani abu ne yake ta mata yawo a cikin kwanyarta..

karar wayar Husna ta ji tayi saurin mikewa ta dauko ta a gaban madubi,
sunan da ta gani ne ya sanyata dauka,
tun kafin tayi magana yace
"kina lafiya,
bata amsa ba tace "ina wuni Ya Hilal ba ita ce,
"i knw ya fadi yana dada jinjinawa zuciyarshi da take saurin daukar haske akan kusancinta da Nadeeyah,
tana dauka jikinshi ya bashi ita ce,
"ya school, hope kina kokari ko,?
cikin nutsuwa tace "umm ina yi,

lumshe ido yayi ya bude yana kallon kasan office din da yakewa aikin zane yace
"Good, babu ruwanki da kowa kamar yadda nake fada miki kullum,
karatunki shine gatanki,
bana san wani abu ya shiga rayuwarki yanzu,
i want u to be successful kin gane ko,

gyada kai tayi kamar tana gabanshi tace "in shaa Allah,

in yana waya da ita ya kan manta duk wata zuciyarshi da bata san raini,
yakan manta ko shi waye duk da har yanzu bai taba nuna mata alamar soyayya ba,
so yakeyi ta zama macen da ko ina a duniya za'ayi alfahari da ita,

"Zeemarh na gaishe ki,
yau dakyar taje makarantar islamiyya wai ni zata bi,
murmushi Nadeeyah tayi tace "Allah kuna lalata ta ne,
anjima zan kira Anty ince ta dinga zane ta,
"u are on ur own ya fadi hade da cewa kema musa a zaneki kuwa, sai ayi 50-50,
dariya sosai tayi wacce ta sanya Hilal nishadi,
zatayi magana kenan taji Anty Raly na kwala mata kira,
sallama tayi mishi ta kashe wayar ta fita da sauri,

kallo ta bita dashi fuskarta dauke da Murmushi, tace
"Nadeeyah daga hannu sama mu godewa Allah,
da sauri ta daga dan bata san me zasuyi ma adduar ba,
bayan sun gama adduar tace "Allah ya kawo miki taimako,
yanzu Taheer ya fita a gidannan,

kaii yau saboda farin ciki bansan yadda zanyi ba,
kin gama dacewa duniya,
lahira kadai zaki nema,
Nadeeyarmu ce zata zama matar Taheer surukar Anty Saude,

wannan dadin ina zan kaishi yau,
rufe fuska Nadeeyah tayi ta kasa gane ainihin yanayin da take ciki, na farin ciki ne ko akasinshi,

kalaman Hilal ke mata yawo a zuciyarta, wanda sabonsu ke bata mamaki duk da har yanzu tana shayin shi,
ga kuma zazzafar kaunar da ta gani a idon Taheer,
rungumota Anty Raly tayi tace "saura 3 to months ki gama school, lokacin ne zamu fasa maganar nan,
wallahi dadi yau kamar zai kasheni,
daki Nadeeyah ta wuce da sauri tana nazarin abubuwan da suka gifta tsakaninta da Tahir......

********___*******

Turjiya takeyi a kasa tana ihu tana fadin "indai yaya Jamal zaije itama sai taje,
dariya Hafeez yayi yace
"Haba autar mami,
yaya jamal fa ba bin mu zaiyi ba,
ni da Papy kawai zamu tafi,
kiyi hakuri kinji,
fitowa yayi yana gyara button din rigarshi yace
"fada mata gaskiya mister,
dani za'a,
dan Allah kafin mu dawo ki mutu tunda ni sa'anki ne,
wani ihun ta saka wanda ya sanya Anni da sauki ya samuwa fitowa tana fadin Jamal zan ci maka mutunci akan yarinyar nan,
turo baki yayi yace "haba Anni, kina ganin yarinya ta rainani,
da nayi aure da wuri da na dire wacce ta fita ya karashe hade da rankwashinta,

jikinshi ta shige tana ihu tana yakushinshi tana fadin "babu inda zakaje walhy,
ni sai dai mu tafi tare,
tureta yayi yana dariya yace "zan gani yau,
ji min rigima fa,

fitowar Papy ne ya sanyata zuwa gurinshi tana kuka,
daukarta yayi yace "haba mamana,
kaduna fa zani ba nan kusa ba, zo kiji a kunne,
mika mishi kunnen tayi yayi mata rada,
dariya tayi ta kalli Jamal tana mishi gwallo,
har suka shiga motar tana tsalle tana ma Jamal gwalo tana cewa "an mishi wayau wooo,
dariya sukayi dukkansu a motar,

ta window ya leko yayi mata nashi gwalon shima kamar yaro karami,
janta Mami tayi suka wuce daki dan kar Jamal ya sake ballo mata august...

Karfe Hudu da minti ashirin suka shiga garin Kaduna,
tunda suka shigo cikin garin Papy yaji jikinshi ya mutu,
shidai yasan meeting yazo yi a Kaduna state university,
amma yanzu ji yakeyi kamar wani abu mai muhimmaci akasin haka ne ya shigo dashi,
Hotel din da aka kama musu Hafeez ya kaisu sannan ya yi musu sallama ya wuce da niyyar dawowa da safe...

Washe gari bayan sun gama komai karfe biyu Hafeez yazo ya daukeshi,
suna Hira Hafeez yace "mishi daga gidan kakanshi yake,
baiji dadi ba jiya kwana yayi yana gudawa,
da gangan ya fadi haka dan hakar shi ta cimma ruwa,
in ma suna da dangantaka to suna ganin juna a yau zasu gane su kuma warware mishi komai,
gidan Baffa ya wuce direct kamar yadda Papy ya bukaci zuwa gaisheshi,,

A daidai kofar gidan yayi parking,
cike da girmamawa ya bude mishi kofa yayi mishi iso har cikin gidan,
fuskar Ma'u ke fuskantar hanyar shigowa, kamar an manne ganinta a fuskar papy,

kallon Baffa tayi ta dago ta kara kallon Papy,
Da sallama ya shigo ciki ya karaso ya tsuguna ya gaida Goggo,
motsi kawai bakinta keyi amma ta gaza furta ko kalma daya, kamar ance Baffa ya dago nan Allah yayi ma fuskokinsu gamo,

ko wanne saida ya tsorata da ganin fuskarkokinsu cikin na juna.....

Mrs Tijjani Shattimah......
[18/03 8:06 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣8⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Dammmm.....

gaban Baffa yayi mummunar faduwa,
karasa mikewa zaune yayi har lokacin bai dauke idanuwanshi kan Papy ba,
shi din ma Papy hakan take gareshi,
saboda tsananin faduwar gaba bakinshi ya gaza furta koda kalma daya ne,

Hafeez dake bayansu ya tsuguna zuciyarshi wasai saboda a yau yana tunanin warwarewar SARK'AK'IYAR da ya shiga watanni bakwai da suka wuce,

kallon Baffa yayi hade da dan taba kafadunshi yace "Baffa wannan shine Papy wanda nake zaune a gidanshi a Gombe,
a razane Baffa ya dawo hayyacinshi yace "au to madallah, an gode fa,
Papy bai amsa shi ba ya zauna sosai zuciyarshi sai kai kawo take, ko tantama bayayi wannan mahaifinshi ne da Anni ta dade tana fada mishi,
kamannin sun wuce kamanni kawai,
tabbas akwai jini mai karfi a tsakaninsu,
gaishe da Baffa yayi hade da tambayar jikinshi,

Goggo ce ta iya amsawa babu inda a cikin jikinta bai saki ba,

saida sukayi kusan minti biyar a zaune babu wanda ya sake magana,
kowa da abun da yake tunani a ranshi,
karfin Hali Baffa yayi dan ya gama hange hangenshi a yan uwa yasan babu wanda ya rage mishi na kusa,
sannan yasan dai bashi da wani ďa banda wanda ya binne da hannunshi,
kuma yasan bai taba yin aure a wani guri ba bare har yayi tunanin ya barta da cikinshi,

wannan abun al'ajabin kamanni sun yi yawa,
bazai iya jure barin shi a ranshi ba,
dole yana bukatar sanin daga inda halittar nan mai tsananin kama dashi ya fito,

kallon Papy Yayi yace "dan nan idan bazaka damu ba ina so inyi maka tambaya,
takalma da safa Baffa ya cire ya gyara zamanshi sosai a kan tabarmar,
ganin yatsun kafarshi ya kara daga hankalin Ma'u,
shin meke shirin faruwa ne?,

magana Baffa zai fara-- tayi saurin katseshi tace "daga mutum yazo gaisheka sai ka tsareshi da magana, ka sani ko sauri yakeyi,

Murmushi Papy yayi yace "babu komai karki damu,
ko bai tsayar dani ba nima babu inda zani domin akwai wani al'amarin da yake shirin faruwa,
Chapter 39 · 0% Book details