Sashe 15
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani irin kallo Shaho yayi mishi, baice dashi kala ba ya bi ta gefenshi ya karasa kusa da yarinyar,
gyara rigarshi yayi zai zauna saurayin ya tureshi ya tare gurin zaman,
"Na fada maka, yarinyar nan bakuwa ce,
alama yayi mata da hannu yace ",ga motar da muka zo can je ki shiga ki jirani,
gurin kwarababbiyar motar shanun ta nufa ta haye tana ta kalle kalle jikinta duk a mace,
wani irin ihu Shaho yayi har saida matan dake gefen bukkar suka tsaya da tatsar madara saboda firgici,
saurayin dai bai girgiza ba sai ma kara komawa jikin motar da yayi ya tsaya,
sauran mutanen gurin suna kallonshi cike da mamaki suna tsoron irin hukuncin da Shaho zaima saurayin,
tunkarar motar shaho yayi gadan gadan,
cikin harshen larabci saurayin yayi wa budurwar magana,
a firgice tabi umarnin shi ta kwanta kan kujerar hade da runtse idonta,
yana isowa gurin ya dunkule hannu ya kai wa saurayin naushi, gocewa yayi ya daki karfen motar har saida ta girgiza,
kafin ya kai mishi wani naushin saurayin ya kai mishi a baya,
nan fa suka fara kokawa sosai,
ganin da shaho yayi saurayin yafi karfinshi yasa shi zaro wata sharbebiyar wuka ya zabtari naman gefen kanshi,
Nan fa jini yayi tsalle ya fallatsa har fuskar budurwar,
wani irin ihu ta saki tana fadin "Ya subhanallah, Ya Hayyu ya kayyum bhi rahmatika astagithu"
cikin zafin nama saurayin ya sake yin kan shaho,
kafin ya karaso kusa dashi ya sake luma mishi wukar a ciki,
ihu mutanen gurin suka shiga yi, wasu na tausayin saurayin wasu na kuranta shaho,
kaca kaca shaho yayi wa saurayin da wuka sannan yayi wani ihun murnar ganin ya samu galaba akan saurayin,
bakin motar yayi yana maida numfashi,
"wayam"
ya gani babu kowa a ciki, dube dube ya fara yi yana fadin ina ta shiga, ina yarinyar nan ta shiga, babu wanda ya lura da sanda yarinyar ta bacewa gurin, nan Shaho ya hargitsa gurin da nemanta...
Da sassarfa ya isa gida ya turo kofar gidan gam harda kara sanya wani karfe,
"Ma'u, Ma'u am,
da sauri ta fito daga sakarkari hannunta rike da yar jinjira,
lafiya dai irin wannan kiran me muka samu ne,
sauke budurwar yayi a bayanshi ya kwantar da ita akan wata tabarma,
ajiye jinjirar ma'u tayi cikin daki kusa da wata yar yarinya da bata wuce shekara 8 ba,
da sauri ta fito tana mai zumudin sanin inda mijinta ya samo yar MAKKA, dan su duk wani balarabe a gurinsu dan Makka ne,
" kawo di yam ma'u, ya fadi yana mata firfita hade da share jinin fuskarta,
ruwa ta debo cike da koko ta mika mishi ta zauna a kusa dashi,
a hankali ya fara shafa mata ruwan a fuskarta da hannunta,
Ajiyar zuciya tayi mai karfi hade da fashewa da kuka tana kiran sunan "HABEEB"
toshe mata baki yayi da sauri saboda jiyo ihun su shaho a bayan gidanshi,
cikin harshen filatanci yacewa ma'u tayi saurin shigewa daki da ita,
kama hannunta tayi suka shige can kuryar daki ta turata cikin wani yayi ta daura mata kaya a kanta,
kafin su kai ga taba kofar bukkar mai gidan ya fito daga gidan yana mika, tsayawa su shaho sukayi yace "Kai Baffan Bingel da Boddo kaga wata yarinya Makka da bakin kaya,
hamma ya kakaro yace a ina zan ganta ni da na tashi daga bacci yanzu,
wucewa sukayi suna ta maganganu cikin fushin rashin ganinta, muryar shaho ya jiyo daga can yana fadin "babu abinda zai hanashi kasheta in ya ganta,
da yaso ya sameta yayi yadda yake so da ita amma yanzu kasheta zaiyi dan in ya barta zata iya zama barazana ga rayuwarshi, jin haka yasa Baffa cikin tashin hankali yayi saurin komawa cikin gidan,
A kofar sakarkari ya samu ma'u zaune tana damun fura da nono, ganin da tayi ya shigo a firgice yasa ta mikewa ta nufo shi, "lafiya?, ta tambaya tana kallon yadda jikinshi yake rawa, daki ya jata yace "ina bakuwar balarabiyar nan,
maza fito da ita mu nemi wani gurin mu korata dan walhy rayuwarmu tana cikin hatsari, ya kwashe duk abin da yaji shaho ya fadi ya gaya mata,
cikin dakiya irin tata da jarumta tace babu inda zaka kaita in ba iyayenta ne suka zo neman ta ba, ya zama dole a samu me tsawatarwa shaho,
abubuwan da yakeyi a cikin garin nan ya isa haka,
kallonta yayi galala yace "wa kike ganin zai tsawatar mishi?,
ki fada min wake da wannan zarrar?
kwaryar damunta ta dauko tace "nidai na fada maka babu inda zata,
ta wuce daki tana tsuma tana fadin babu wanda ya isa ya taba makka,
"sunan da ta rada mata kenan tun kafin taji sunanta,
ita zuciyarta ta tafi can tunanin in iyayenta suka zo to fa zasu musu alherin ganin sun taimaki yarsu,
kuma zata kafa tarihin ita ta fara taba jikin balarabiya a duk fadin tsirarun musulman da suka musulunta a kauyen,
cire kayan tayi ta dago yayin ta fito da ita tace "sannu hai yar budurwa,
fito muje ki sha fura sai kiyi wanka,
raba dara daran idanuwanta ta fara yi dan ko kalma daya bata dauka cikin kalaman ma'u ba, hannunta ta riko suka fito waje ta shimfida mata sabuwar tabarma ta nuna mata tace "zauna,
bata fahimta ba haka ta kuma kama hannunta ta zaunar da ita,
furar ta mika mata ta dauka ta fara sha hawaye na zirarowa daga cikin idanuwanta,
tunanin kaninta takeyi dan shekara 6 a duniya wanda ta zamo gata a gareshi gaba da baya,
ko a wani hali yake yanzu Allah masani,
ludayi uku tayi ta miko ma ma'u..
Amsar kwaryar tayi tana fadin "hai har kin koshi, da kin kara kadan ta fadi tana miko mata, Girgiza kai tayi saboda ta fahimci nufinta tace "Alhamdillah, Jazakumullah khairan"
yashe hakori Ma'u tayi tana dariya har can cikinta tana kyakyato shi,
dariyar murnan jin yaren larabci, da kuma ganin ita kanta balarabiyar makkan a gidanta takeyi,
saida ta gama dariyarta tace "hai Baffan Boddo an je gidan kawu suwidi in fadowa su inna wuro munyi bakuwa mai tsarki yar Makkah,
takalmin robarta ta janyo me ruwan bula tasa a kafarta, ta yayo dankwalin saka ta rufe kanta ta fara tafiya,
ta kusa taba kofar Baffa yayi saurin tareta yace "A wala hakkilo na" ("baki da hankali ne?)
Kinsan irin halin da zaki samu a ciki in kika gayyato mana mutanen gidan Kawu Suwidi?, kince bazata bar gidan nan ba na hakura ta zauna amma ki sani babu me shigo min gida bare ya ganta ya jaza min masifa,
tana nan zaune nasan za'a zo cigiyarta a lokacin sai in mikata gurin iyayenta,,
kalonshi ma'u tayi fuskar nan cike da gamsuwa tayi kamar ta yarda din da gaske,
yaye dankwalin kanta tayi tace "Haka ne, na manta ne ina ta zumudin kai rahoto dan kawai in burge su inna wuro,
yanzu bari inje in sata tayi wanka sai ta canza kaya a wanke na jikinta, gyada kai Baffa yayi cikin jin dadi ya koma daki kusa da yaranshi ya zauna yana shafa kan karamar dake kokarin tashi..
Murdaddiyar sarkar murjanin gwal din da ta cire kafin ta shiga wanka ma'u tayi ta juyawa a hannunta tana dariyar farin ciki, "Aiya Ya Allahn Hard'ejo,
(sunan yayan mijinta kenan malamin da ya fara kawo musu musulunci kauyen),
ji wani "kuje ndade' (sarka) kamar ba hannun mutum bane ya kerashi, sashi tayi a wuyanta tace "wannan ko matar Ardo Laminu bata da irinshi,
kaii ya zame min dole in je gidan su inna wuro dan bazan bar wannan daddadan labari ya wuce ban basu shi ba,
ai ni ko da wannan maka wuyar aka barni na tsira,
daki tayi da sauri tana magana kamar zararra,
kayanta dake cikin wani akwatin katako ta dauko sababbi na fulani tace " Baffa zan bata wannan kayan nawa tasa saboda a wanke wadancan,
gyada mata kai kawai yayi dan mamakinta bai barshi ya bude baki yayi magana ba,
ma'u da ko dankwalinta bata iya bawa wani aro shine har ta dauko kayanta da bata taba sasu ba zata bawa wata tasa, lallai yar makkah ta ciri tuta..
Sosai kayan fulanin suka mata kyau a jiki saboda tsabar kyawunta,
lallausan gashinta ma'u ta shiga kitsashi da kyar tana yi yana warwarewa,
haka dai tayi mata irin nasu na fulani ta dauko mata su sarka da abun hannu duk dan ta mantar da ita sarkar gwal dinta...
Mrs Tijjani Shattima...
[07/03 6:31 AM] fareedah: •• ZUMUNCINMU A YAU •• 2⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah
Hanyar sama Badariyya tayi da gudu tana shashshekar kuka kamar ranta zai fita,
kofar dakin Daddy ta shiga bugawa kamar zata ballata,
da gudu mummy ta fito daga bayi jiki na rawa ta bude kofar,
Daddy kuwa zaune yayi yana jiran ganin me mishi irin wannan bugun kofar da safiyyar nan,
jikin mummy Badar ta fado ta sake kecewa da wani kukan,
waigawa tayi ta kalli Daddy da ya rike kanshi yana tsaki,
waje ta jata ta rufo mishi kofar, ta kama hannunta sukayi dakin ta,
zaunar da ita tayi a kan gado ta shiga rarrashinta,
saida ta tabbatar ta fara samun nutusuwa sannan ta tambayeta abinda ya faru,
karya ta shiga rerowa mummy cikin wani sabon kukan,
"Ya Hilal ne yayi min dukan tsiya,
wai saboda Nadeeyah taje tana wanke wanke kunama ta harbeta,
shine yaje ya taso ni ina bacci wai tace mishi ni nasa ta,
kuma tace mishi wai na hana a bata abinci jiya har tayi bacci,
sannan a gabana Ya Musaddiq ya dauketa ya sata a mota suka kaita asibiti wai kafin su dawo in tabbatar na gama wanke wanken da ya rage------- ,
Wani irin kunci da tukuki mummy taji a ranta,
"Hilal din ne ya dake ki?
gyada kai Badar tayi wasu zafafan hawaye na sake bin kuncin ta,
'irin kallon da Musaddiq ke ma Nadeeyah shi ya fi komai taba zuciyarta,
kwanciya tayi jikin mummy ta runtse idanuwanta saboda ganin hanun Musaddiq da takeyi cikin na Nadeeyah,