← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 113

Sashe 38

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eh ita, matar akwai kirki, tana daraja makotaka, Anty Rally ta bata amsa hade da wucewa daki ta dauko Hijab,
kayan suka dauka Nadeeyah ta rike jug din kunnun Aya suka fito suka wuce gidan dake jikin na Anty Rally,

Gida ne kayatacce wanda za'a iya sanyashi cikin jerin 1st 5 din gidajen masu kudin layin,
kafin ka karasa cikin main house din ma sai kayi tafiyar 5mins,
babu abin da kake ji sai motsin flowers da karan water fountain din dake tsakar gidan,
suna karasawa kofar palon Anty Rally ta tura suka shiga ciki,
wani irin kurda kurda suka shiga yi suna hawa sama suna sakkowa cikin wani under ground,

sanyin A.c da daddadan kamshi ne ya tabbar musu da isowarsu parlon,
cire takalmansu sukayi suka shiga ciki hade da Sallama,

kyakykyawar mace wacce a kiyasi zatayi shekara Hamsin da biyar ta amsa musu,
murmushi ta saki tace "Raliya ce a gidan namu,
kusa da ita Anty Rally ta matsa ta sauke Fadil tace "ina wuni Anty,
daukar fadeel tayi tace "lafiya kalau Raliya,
Fadeel dina yayi wayau,
ina babanshi,?
murmushi Anty Raly tayi tace "yana nan lafiya,
Hada baki Nadeeyah da Husnah sukayi suka gaisheta,
kallonsu tayi tana murmushi tace "lafiya kalau, ina kika samo kyawawan yara haka,
nuna Husna tayi tace nasan waccen bayan kamannin da kukeyi nasan tana zuwa Legacy,
waccen fa ta nuna Nadeeyah da idonta yaki daukewa a kanta,
itama kanwata ce Anty, cousin sis dina,
ayya, mashaa Allah, tabarkallah dasu, ta fadi har lokacin bata dauke idonta a kan Nadeeyah ba,
zatayi magana kenan ta jiyo muryarshi daga can cikin daki,

"Momma nifa wahala kike bani, ban ganshi ba,
dafe kanta tayi ohh gosh *TEE*
a cikin blue trolly fa nace,
cikin shagwaba yace "shi fa na duba babu,
"anya Tee glasses dinka basuyi expire ba ta tambaya cike da tsokana,
rufe akwatin yayi ya fito yace "ni fa yanzu ko babu su ina gani,
bai kula da su anty Raly ba ya kwanto ta bayanta yace "kin gani sweetheart,
babu su ko yanzu a idona,
dariya tayi tace "gaskiya ne babyna,
hannu tasa ta dauki glass din tasa mishi a ido tace "to yanzu koma may be ka iya ganinsu,
dagowar da zaiyi yayi tozali da wacce ya kira da damuwar zuciyarshi,
da sauri ya gyara glass din ya sake kallon inda take ko gizo take mishi,
ita din ce zaune tare da Husna,

kallon Fadeel yayi yace "Boy ina Mummy,
dariya Anty Raly tayi tace "gani kusa da kai, gaskiyar Anty ne sai ka koma an duba idon nan,
daukar Fadeel yayi yace "zan baku mamaki,
yau ma ba glass zanyi driving,
on a serious nt Anty saude tace "in ma wasa kakeyi kayi saurin daina shi,
koda wasa ban yarda ka fita babu su a idonka ba,
kana ji na ko?
Dariya yayi sosai dan dama tsokanarta yayi ya wuce da Fadeel dakinshi...
ganin Nadeeyah a gidanshi,
a mahaifarshi ya sanya shi zama on top yau,
jinshi yakeyi kamar sabon mutum,
ashe yanzu in shaa Allah samunta bazai mishi wuya ba,
rungume fadeel yayi yace "knwing ur mother is a blessing to me...

Yafi minti talatin rike da fadeel yana mishi wasa,
karar wayarshi yaji yasa hannu ya dauko a aljihu,

"ka kawoshi zasu tafi ne, da sauri kafin ta kashe yace momma kice su tafi zan kawo shi,

cike da mamakinshi ta kashe wayar tace "zai miko shi inaga yayi bacci ne, nagode sosai Raliya,

a'a haba Anty babu godiya a tsakaninmu anty Raly ta fadi tana murmushi,
sallama su Nadeeyah sukayi mata ta amsa cike da fara'a,
bayan Nadeeyah tabi da kallo tana Nazarin wasu abubuwa, har saida ta kurewa ganinta sannan tayi ajiyar zuciya ta fara bude kulolin abincin....

Mrs Tijjani Shattima
[15/03 12:04 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣7⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

*JIGON RAYUWA*

Kallon Mamaki Anty Saude ta bishi dashi,
kayan da ya shiga dasu sanye a jikinshi ba dasu ya fito ba,

wannan karan Ash Shadda ce a jikinshi,
yayi kyaun da shi kanshi ya yaba, babu ta inda Taheer bai hadu ba, ya hada komai da duk namiji zai yi tunkaho dashi,
matsalarshi daya ido,
ciwon idon da ya samo asali tun yana yaro gurin wasansu na yara,
babu inda ba'a kaishi dan duba idon ba,
saidai ya dan samu sauki amma bazai bar ciwon duka ba,
a karshe har iyayenshi suka hakura suka dawo asibitocin ido na nigeria,
a nan ne suka daurashi kan magunguna har idon yayi kyawu sosai,
da taimakon Allah da taimakon glasses dinshi da suka kara fito da ainihin kyawunshi yake ganin abun da ke nesa..

Zaunar da Fadeel yayi akan kujera ya dauki nama daya cikin soyayyun naman da Anty Raly ta kawo,
zama yayi kusa da Anty saude ya kai naman bakinshi yace "Momma zan fita,
"Ina zuwa kuma? ta tambaya hade da ajiye plate din hannunta,

Murmushi yayi mai matukar kyau yace "zan mika Fadeel gida, sannan zan je aiken da zuciyata take ta min kullum,

"Hannunshi ta kama da sauri tace "Fara isar min da aiken TEE, fada min sakon in taya zuciyar taka adduar samun karbuwar sakon,
nata hannun ya rike shima zuciyarshi na kai kawo, farin ciki ne cike a cikinta na ganin tana gab da samun abin da take so, lumshe idonshi yayi , kana hango yanda gashin idon ya kwanta ta cikin glass yace "i'm in love Momma,
wani irin numfashi ta saki wanda zai tabbatarwa da mai kallonta tana cikin matsanancin farin ciki, "wacece Taheer?
wacece wannan?
ya Allah kayi mata albarka,
share hawayen da ya zubo mata tayi, tace "bani labarin ta Tee, "murmushi yayi dan dama yasan yadda zatayi reacting kenan,

yace "calm down Momma, with time zaki santa,
kuma nasan zaki sota,
ni dai addua'arki nake bukata, ina son ki dage da addu'ar samun nasara,
inason zuciyata ta kasance da ita a duk bugun numfashina,
tun ranar da fara ganinta har zuwa yau kaunarta ce ke kara tasiri a cikin ruhina,
"rungumeshi tayi sosai tana fadin Alhamdulillah a jere har sau uku,
jin kukan da takeyi yana neman yayi yawa ya sashi saurin raba jikinshi da nata,
hannu yasa yana share mata hawayen hade da girgiza mata kai,
a shagwabe yace "kina so in bata kwalliyata ne,
sai ma na fasa in bawa zuciyata hakuri tunda aikenta nasa min ke kuka,
dan mari takai ma fuskarshi tana dariya tace "tashi maza ka tafi, Allah ya baka dukkan sa'a my boy,
daukar Fadeel yayi yace "Ameen Momma,

kallon farin ciki ta bishi dashi hade da mikewa ta isa gaban hoton mahaifinshi,
rau rau idonta yayi tayi saurin maida hawayen hade da fadin "tun bayan rasuwarka Taheer dinka bai sake yin farin ciki ba,
yau!! a karo na biyu a rayuwarshi na ganshi cikin farin ciki,
kasa controlling hawayenta tayi tace "we missed u alot Abba,
Allah yayi maka rahama,
adduoi ta shiga jerowa mijinta da danta,
saida ta gama ta share hawayenta ta kira Abida mai mata hidima dan ta tattara parlon....

Sau biyu ya taba shiga gidan Anty Raly tun zuwanta unguwar,
motar da ya dauko daga gida ma ta musamman ce kai kace garin zai bari ba kusa da gida ba,
sai da yayi zaman minti uku a ciki sannan ya kashe ya dauki Fadeel,
mai gadin na ganinshi ya tsuguna har kasa ya gaisheshi dan babu wanda baisan dan gidan Hajiya Saude ba a unguwar,
bude mishi kofa yayi ya shiga,
Baya yaja zai tsaya ya hango Husnah ta fito ta nufo gate din,
tana ganinshi ta kara sauri tana fadin "uncle da kanka ka kawo shi,
mika hannu tayi ta dauki Fadeel hade da ce mishi tana zuwa,
mai gadin ta kira tace "ina lawalli, kace yaje ya siyowa Anty Gas, cikin girmamawa ya amsa ya fita da niyyar zuwa kiran lawali driver,

Dawowa gurin Taheer tayi ta sake gaisheshi,
tambayoyi ta fara jefo mishi, "uncle dama kai dan Anty saude ne?
ai na santa,
bansan kai danta ba,
kasan last year ka fara teaching a school shiyasa bamu san kai danta bane,
she is very nice, kasan akwai lo--- katseta yayi yana dariya yace "ashe haka kike da surutu,
to tunda bazaki bani gurin zama ba bari in tafi,
da sauri tace "laaa sorry uncle muje dan Allah,
bai bata lokaci ba ya bita hade da addu'ar Allah ya bashi karfin gwiwar sanar da ita,
parlon Baban Fadeel ta bude mishi tayi mishi iso har ciki ya zauna,
har zata zauna sai tayi saurin mikewa tace "bari in kawo maka ruwa,

murmushi yayi yace "na dauka zama zakiyi da sai ince ashe baki iya tarbar baki ba,
dariya tayi ta wuce kitchen,

Suna shiga kitchen Fadeel ya saki Kashin da ya fito daga pampers har rigar Husnah,
wani irin ihu ta saki wanda ya sanya Nadeeyah da Anty Raly zuwa kitchen din,
dariya Raliya tayi na yadda Husnah ta bata baki hade da tale riga da kafarta,
da sauri ta dauki Fadeel da ya fara bata mata kitchen da kashi tayi daki dashi,

kallon Nadeeyah Husna tayi tace "dan Allah ki kai mishi juice parlor,
bata tsaya yi mata bayani ba ta wuce daki tana ware kafa,
dariya Nadeeyah tayi ta shirya juice a tray,
duk tunaninta Baban Fadeel aka shiryawa abinci a parlon kafin ya dawo,
bata damu da yadda gashinta yake a bude ba saboda tasan bai dawo ba,
gyara wanda ya dan zubo ta gefen idonta tayi ta wuce parlon,

sam bata kula dashi ba saboda kujerar da yake zaune tana baya, duk wanda ya shigo parlon in ba ya lura dakyau ba bai kula da na zaune a kujerar,
ganin babu abinci a parlon yasa ta dube dube,
sai da ta razana saboda ganin bazata da tayi mishi,
da sauri ta ajiye tray din jiki na rawa hade da bugawar kirji tace "ina wuni uncle,
bai amsata ba ya tako har inda take tsaye shima kirjin nashi bugawa yake yi sosai,

"murya can kasa yace "bakina ya kamata ya fara furta wannan, an yini lafiya *Umm Nadeeyah*
Chapter 38 · 0% Book details