← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 113

Sashe 109

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu wani mai baro wanda ya lodo karafe da langar kwanon aluminum tsofaffi ya taho dan wucewa yana jin wakarshi,
tsayawa yayi a gefen gidan su Baffa dan siyan rake ya parka baron a gurin,

Fitowar Goggo keda wuya wata langa mai tsini ta kama yaďuwar fatar cikinta,
da yake gurin gangare ne nan fa sukayi kasa ita da baron kaifin langar yayi fata fata naman cikin Goggo,

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai mutanen gurin suka fara faďi haďe da yin kanta da gudu,

Dakyar aka samu aka zare wasu parts din langar a jikinta,
har lokacin tana da rai sai ihun azaba kawai takeyi cikin sarkewar murya,
da sauri Papy da me baron suka dauketa suka yi gurin mota da ita, jinin dake zuba a jikinta ba jinin wasa bane,
ga tsagu da cikinta ya samu can ciki ana iya hango wasu daga cikin kayan cikin,
suna isa gurin motar Papy ya kalli Daddy da suka fito gaba dayansu yace

"Bude motar Alhaji muje,

Ďauke kai Daddy yayi yace
"Ba'a mota ta ba,
kallon Raliya yayi dan ita kadai ce tazo da mota yace
"Kema in kika dauka ban yafe miki ba,
yana kaiwa nan ya shiga motarshi yayi gaba ba tare da ya kalli kowa a cikinsu ba,
samm babu digon tausayinta a ranshi bare har ya kai ga taimakonta,

Papy ya rasa yadda zaiyi dan tashi motar na gurin Hafeez, motoci suka fara tsayarwa na haya,
duk motar da ta tsaya in taga yanayin Goggo sai tayi gaba dan kar a bata musu mota,

Cikin tsananin tashin hankali mai baron yace
"Ko zamu dauketa cikin baro na, ni zanyi tukin sai ku biyomu a mota,
da wannan shawarar aka dauki Goggo aka sata a cikin baron bayan an shimfida bargo aka rufe mata jiki,
tausayin rai da matsawar Anni su suka sa Baffa bin bayansu,
gudu sosai mai baron yakeyi dan yana tsoron mutuwarta a sanadiyarshi,
go slown da suka tarar shi ya sanya shi yin yanke ta wani lungu dan su isa asibitin da wuri,

Yana shiga kwanar yayi tuntunbe da katon dutse wanda hakan yayi sanadiyyar subucewar baron yayi wani kwaron kudiddifi da Goggo,
ihuu ya saka yabi bayan su,
yana isa yaga baron makale  jikin wani dutse ita kuma Goggo kwance kan wani katon dutse kanta yayi fata fata,
cike da tsoro yaron yaja baronshi jiki na rawa ya bar gurin dan kar hakan yayi sanadiyyar shiganshi wani hali...

Motar da suka hawo na biyowa lungun sukaga mutane sunyi dafifi a gurin kudiddifin,
da sauri Papy ya dakatar da mai motar ya sauka yana tambayar abun da ke faruwa,
labarta mishi wani yaro yayi sannan yace sunbi mai baron basu ga inda ya shiga ba..

Cikin tashin hankali Papy ya biya wasu yara majiya karfi yace su cirota,
koda suka cirota har lokacin bata mutu ba saidai ta jikkata iya jikkatuwa,
babu ta inda jini bai zuba a jikinta,
fashewar da kanta yayi ya sauya halittar fuskarta,
azabar da take sha a lokacin har gara ta gwammaci mutuwa da rayuwa,
to saidai inda matsalar take bata san me zata tarar bayan mutuwar ba..

*(Allah a'alamu, shi kadai yasan hukuncin da zaiwa bayinsa masu mugun hali iri ko kuma kwatankwacin na Ma'u, Bawa bai isa ya yanke ba domin shi Allah mai gafara ne a lokacin da yaso, ta yiwu mutum ya sha iya wahalarshi a nan duniya a ranar da zai koma ga Allah, ta yiwu kuma sai anje can, wannan Allah buwayi gagara misali shi kadai yasan daidai.... Allah ka datar damu da aljanna firdausi, ka tsarkake zuciyarmu kasa mufi karfinta)*

Kudi mai yawa Papy ya bawa mai motar sannan ya yarda zai dauki Goggo a boot,
asibiti mafi kusa suka isa saboda jinin dake zuba a jikinta,
kin karbarta sukayi dan acewarsu yafi karfinsu a wuce general hospital,
Mummy dai kuka kawai takeyi tana fadin
*Astagfirullah ya Allah*,
mai motar da aka sake roka ya wuce dasu General hospital,

koda suka isa emergencyn kanshi a cike yake da marasa,
dakyar aka samu aka shiga da Goggo wacce babu abunda bakinta ke furtawa sai wayyo na shiga uku,
Boka Garbuji kazo ka taimakeni,
duk yadda likitoci suka kai da kokarin tsaida jinin abin yaci tura domin zuba yakeyi kamar ana kara wani a jikinta,
allurar bacci sukayi mata dan ta samu tayi bacci suyi mata aiki,
itama allurar sam taki aiki a jikinta,
sai ihu kawai takeyi,
a haka sukayi mata aikin azaba na karaďe dukkan sassa na jikinta,
bayan sun gama suka barta a gurin suka bada alluran da za'a siyo ko zata samu bacci,

Anyi mata allurai uku amma samm taki rissinawa bare tayi bacci,
ga fusge fusgen azaba da takeyi tana kiran sunan bokayenta ko zata samu taimakonsu...

*A wannan ranar Goggo bata san ko waye bazai tseratar da mutum daga abinda dake rubuce ba, domin in har ganyenka na zaman duniya ya bushe har ya kai ga faďuwa kasa to fa babu wani tsumi ko dabarar da zai hanaka faduwa kasan nan kaima*...

Har karfe goma na dare Goggo na abu daya,
ita bata rintsa ba ita bata bar na kusa da ita sun runtsa ba,
duk yadda ahalinta suka so tayi salati abin yaci tura domin suna diga aya zata dura musu ashar tace basu san abun da take ji ba..

*Kwatan kwacin hakan bayin Allah da kika sa aka kashe suka ji, su da basu dauki zunubin kowa ba ma kenan kin wahalar dasu, bare ke da kika kwashi na mutane marasa adadi...*

Karfe 2:40 na dare jikin Goggo ya kara tsamari,
domin a yanzu samm ta kasa kwanciya,
jikinta kuwa babu komai sai rigar da aka saka mata,
ihuu kawai takeyi wanda yake ratsa ko ina na asibitin,

Mummy da ta rage ita kadai ta dinga zubar da hawaye haďe da ambaton Allah..

Wata zabura da Goggo tayi babu wanda ya ankara sai ganinta akayi a can waje asibiti domin ita Mummy mai jinyarta ta tafi makewayi..

Ihuu kawai takeyi tana tsallen azaba tana kiran sunaye kala kala,
dinkin da akayi mata a ciki nan take ya warware saboda rashin kwarin jikinta da kuma sabontakar dinkin,

Warwarar dinkin tayi daidai da tahowar motar wasu gayu wadanda suka sha giya sukayi tatil,
saboda yanayin duhun garin da kuma yanayin buguwarsu sai jin wani kara sukayi wanda yasasu taka birki,
shurun da sukaji babu wanda yayi magana yasa drivern yin ihu haďe da sake kara volume din motar fiye da da ya takata suka wuce,

securityn dake dutyn dare ne ya fito yana ihun neman taimako, ihun da yakeyi shi ya janyo hankalin Mummy da attendance din dare wadanda suke yawon nemanta a harabar asibitin,
da gudu suka nufi gurin shi suna tambaya ko lafiya,
ganin ya nufi wata katangar dake tsallaken asibitin yasasu binshi a baya suna daďa tambayar ko lafiya,
suna isa gurin tambayarsu ta makale a makoshi domin Goggo suka gani hange jikin tsinin karfen katangar wanda ya burma cikinta har baya,

Kuka sosai Mummy ta sanya tana kiran sunanta domin har lokacin da sauran ranta tana ta gumshekar azaba wacce tafi kama da ta mutuwa,
Da kyar security's din ciki da suka fito suka zarota suka nufi ciki da ita,

Karasawarsu ciki keda wuya ta damki cikin inda ciwukan suke haďe ciza harcenta da karfi har saida jini ya fito,
ihun karshe da ta saki yayi daidai da daina motsa kafarta da kuma sakin dukkan jikinta,

Ajiyar zuciya wata nurse tayi taja zani ta rufeta ta kalli Mummy tace

"Saidai hakuri,
ta mutu!!

Bazan mutu ba Goggo ta faďi a wahalce haďe da yayewa ta damki hannun nurse din,
irin jinin da ya zuba a jikin Goggo ya isa dukkan karfinta ya kare,

A tsorace Nurse din ta fincike hannunta taja da baya da sauri, dan minti ďaya baya tabbas taga mutuwa a tare da Goggo..

Sunan Mummy ta fara kira a hankali saboda duhu ya fara ziyartar ganinta,
daga nesa Mummy ta amsa dan tsabar tsoron irin rayuwar da Goggo ta ďibo,
gaba ďaya yanayinta ya canza daga farar bafulatana wacce tsufa ya tattare fatanta zuwa wani irin yanayi na ban tsoro,
jinin dake zuba a jikinta gaba ďaya ya kafe dan babu ragowarshi a jikinta,
karfaffiyar zuciyarta wacce rashin imani ya kesashar ita kadai ke aiki a jikinta...

Babu wanda a dakin bai bata mutuwa ba saboda irin ukubar da tasha kuma take kan sha,
a lokacin nan mutane da dama sun sake tsorata da Allah domin shine ke da ikon yin wannan abun al'ajabi,,

Sake kiran sunan Mummy Goggo tayi a karo na uku,
a ďarare ta matso kusa da ita tace "Gani,

"Yanzu duk wannan azabar da nake ciki bazaki iya zuwa ki kiramin wani bokan ya fidda ni ba,
duk abubuwan da nayi a baya saboda ku nayi shi,
amma ni yanzu abu ďaya da zaki min in fita daga wannan azabar bazaki iya ba.... 
babu wanda ya fahimci abinda Goggon ke faďa sai Mummy domin ita kadai ce a gefenta,

Cike da damuwa Mummy tace "Shin har yanzu baki saduda kin san Allah daya bane?
Har yanzu kina tunanin akwai wanda ya isa ya hanaka yin aure bare ya hanaka mutuwa,
lallai kuwa in dai wannan azabar da kika sha ta tsayin watanni bata nunar miki hanyar Allah ba babu wata azaba da zata maidaki daidai,
Mutuwarki itace alheri ga dukkan yan uwa musulmi,
domin ke ďin anno-----

wata damka Goggo ta kai mata wacce idonta bai nunar mata gefen da ta kaita ba saboda duhun da ya fara rufesu,
a hanzarce Mummy ta mike haďe da fincikewa wanda hakan yayi sanadiyyar kai Goggo kasa,
zafin faďuwar ya sanyata sakin ihun karshe wanda daga shi bata sake cewa komai ba sai fisga da jikinta yakeyi yana dukan gadon..

A wannan lokacin mai daukar rai ya ziyarci tsohuwa Goggo wacce tayi kisan ban mamaki kuma take tsoron mutuwar kanta,
a lokacin Goggo ta dandanin azabar da matattun da suka mutu a sanadinta suka dandana,
babu rayuwar da bata tunano ba kafin ganinta ya dauke baki ďaya....

*(Kullu nafsin za'ikatul maut,, Duk mai rai sai ya dandani mutuwa)*...

*Anzo a banza an koma a wofi...*
Chapter 109 · 0% Book details