← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 113

Sashe 104

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Full light aka saki wacce ta haska gurin da suke,
basu saketa ba sai sa hannu da sukayi suna kare fuskarsu suna masifar dalilin haskasu,

A haka Hilal ya bar motar ya fito da sauri ya nufi inda suke,
ganin haka yasa dayan me makami sakinta ya zaro wuka a cikin aljihunshi ya tsaya a gaban Hilal,

a ruďe Maleekah ke rokon Hilal da ya koma kar su kashe shi,
bai ma san abun da ta ke cewa ba dan hankalinshi yafi tafiya gurin dayan dake luguiguitata,

Tsugunawa kasa yayi da niyyar cire takalminshi yayi saurin jan kafar mai rike da wukar,
sara ya kai mishi a hannu kafin ya ankara yajishi a kasa,

sosai saran ya shiga hannun Hilal wanda baisan dashi ba saida ya danneshi ya kwace wukar haďe da tattakashi,
shiko dayan na ganin haka dama ba cikin hayyacinshi yake ba yayi saurin ja da baya,
kamoshi Hilal yayi ya nakaďa mishi mugun dukan da duk suka kasa motsi,
wurgi yayi da wukar haďe da yin gaba yana mai dafe inda jinin ke zuba,

A guje ta biyo bayanshi ta kwance dankwalin kanta tana kokarin kama hannunshi dashi,

ture hannunta yayi da karfi har ta kusa faďuwa ya buďe motar ya shige,

"Ta inda kika bi kikazo nan ki bi hanyar ki koma masauki..
yana kaiwa nan ya tada motar da karfi yana shirin janta,

buďe kofar tayi da sauri tace

"Heartless being,
so zaka iya tafiya ka barni a nan a matsayina na bakuwarku?

"Kokarin banbare rikon da tayi mishi yayi ya kasa saboda tayi mishi mugun riko,

kallon cikin idonta da yayi jawur yayi yace
"let go off me!

Sake dukunkuneshi tayi haďe da noke wuya,
yadda tayi da baki tana shirin fara kuka ya sanyashi kashe motar haďe juyar da kanshi gefe,
ganin haka yasa ta sa hannu ta buďe bayan motar sai a sannan ta sakeshi tayi saurin shigewa ciki..

kuka sosai ta shiga rerowa kamar karamar yarinya,
gaba daya ta tsorata da Nigeria gani takeyi kamar in ta sake kwana ďaya za'a iya kasheta bayan an lalata mata rayuwa,

Jan motar Hilal yayi ya maida ita masaukinsu,
sosai kukan da takeyi yake taba mishi zuciya,
sakkowa yayi ya buďe bayan motar,
"Its late, i want to go home,
dago kanta tayi ba tare da ta kalleshi ba tayi saurin bin dayan gefen ta ruga ciki da gudu tana sake yin wani sabon kukan...

Rufe motar yayi da niyyar bin bayanta sai wata zuciya ta haneshi da yin hakan,
motar ya shiga ya tada ya canza wata hanyar da ya tabbatar zata kaishi gida domin gudun sharrin dare da na mutanen da suka samu matsala.. ..

Washe gari tun asuba Maleekah ta shirya ta wuce dakinsu ummi...

Bugu sosai tayi ma kofar wanda ya sanyasu mikewa a tare dan ganin mai dukan kofar haka,

"Lafiya?
Ummi ta tambaya haďe da janyota cikin dakin,

Jakar dake hannunta ta ajiye ta karasa kusa da Abbu tace

"Abbu ka shirya mu tafi yau plss,
i hate Nigeria,
yadda takeyi kamar zatayi kuka ya sanya shi zaunar da ita haďe da tambayarta abun da ya faru,
labarin abun da samarin nan sukayi mata ta bashi sannan ta kare da cewa

"Ta rantse bazata sake kwana a kasar nan ba!

Jin haka Sheik ya bata hakuri akan ta bari ya gama yan uwanshi dan yayi niyyar tafiya dasu,

"Noo Abbu,
ka tsaya ka tafi tare dasu,
we will go with Jamal nd Ruwaidah,
gamsuwa yayi da maganarta bayan ya tabbatar da hakan ya gamsar da ita...

Karfe goma na safe dukkan ahalin suka iso masaukin Sheik,
bayan an gaggaisa duk suka haďu sukayi breakfast cike da kaunar juna sannan suka shiga hira sosai,

Matan na bangarensu haka mazan ma,
anan ne Sheik ke sanar dasu komawar Maleekah ya kuma ce tare zasu tafi dasu Jamal,
cike da murna Papy ya amince dan dama cikin hutu suke,
shi kuwa Jamal aiki ake nema mishi,

"Na dauka sai tayi sati daya itama?
Daddy ya tambaya yana dariya,

Murmushi Abbu yayi yace
"Akwai abinda zai maida ita, sannan she is not comfortable here,
kaga ita kadai ce mace,

"Sai in kaita gurin Husna,
itama dan bazata iya zuwa bane shi yasa na barta a gida,
Hafeez yayi karaff ya amshe saboda yana matukar jin dadin ganinta,
ko ba komai tana ďebe mishi kewar mutane biyu a idonshi,

Dariya sheik yayi yace
"Bazata yarda ba ai, next time zatazo ta dade muku in shaa Allah,

nan suka kauda zance suka shiga wani zancen daban na tsara inda zasu je ziyara ya ga yan uwa wadanda suka jibanci yayarshi ko sukayi zama tare,
Kaduna... nan ne gurin da suka tsara tafiya washe in Allah ya yarda.....

Karfe sha biyu na rana jirgin nasu zai tashi hakan yasa Jamal yin wasu yan siyayya near by dan bada shiri yazo ba,

Hilal ke tuka motar yana sauraron duk murnar da su Jamal sukeyi na yin kallo cikin cinemas din turawa....

Ya rasa asalin abun da yake ji a cikin ranshi,
duk tunanin da ya dauko sai yayi saurin kaudashi dan ba'a cikin muhallinshi yake ba,
soyayyar da yayi a baya bayason sake yin makamanciyarta dan zata iya buga zuciyarshi,
ya samu dakyar ya maida soyayyar Nadeeyah wani muhallin daban,
baya kaunar sake tsintar kanshi cikin mawuyacin halin da ya shiga a baya,
suna isa airport din yayi parking haďe da runtse idanuwanshi yana tuno abubuwa da dama,

"Ur problem is lving!

Buďe idonshi yayi yaganta tsaye jikin windon gefenshi,
bai dago kanshi daga kwanciyar da yayi ba ya zuba mata manyan lumshashun idanuwanshi,
ita din ma cikin idonshi take kallo babu ko kiftawa,
maida idonshi yayi ya rufe dan a rayuwarshi ya tsani mace a tsaytsaye,
abubuwa da dama kan sashi ya ragawa Maleekah,
kofar ta buďe tasa hannu ta buďe idonshi duka biyun,
nata idon ta gwalo ta turo fuskarta kusa da tashi,

Ya Allah... ya fadi haďe da kauda fuskarta,

"Maleekah kin tabbatar kina da lafiyar....... kanta ya nuna da hannunshi,

haďe rai tayi kamar zatayi kuka tace

"Dan ina kulaka shine zaka ce bani da hankali,
laifi na ne,

"Heyy tambaya ce,
ya faďi da ďan sakin fuska..

bata tsaya sauraronshi ba taja hannun Ruwaidah suka wuce ciki,

Murmushi yayi bayan yaga kurewarsu yaja motar yayi gaba.....

Mrs Tijjani Shattimah........
[13/06 10:15 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Mamaki sam ya hana mutanen parlon yin magana sai Badariyya data dawo kusa da mijinta ta rokeshi da yayi shuru,
in gaskiya ne zasu fahimci hakan da kansu...

Jin da sukayi jiniyar taki tsayawa yasa Hilal da Daddy yin waje,

Shi kuwa Musaddiq sama yayi da little Nadeeyah dan ya bata chocolates,
samm bai tausayawa Badariyya ba domin ta sanyashi cikin ukubar da bata da magani...

Suna fita sukayi karo da motoci takwas,
huďu daga gidan sarkin Zaria, biyu daga gidan gwamnati sai biyu tasu Taheer,

Dukkan motocin numfashi kawai sukeyi,
saboda tsabar haďuwa babu wanda a unguwar bai bisu da kallo ba,

Dogarai ne suka fito da sauri suka tattare kofafin fitowar kowacce mota,

Sarki Tidjani ne ya fara fitowa shi da Shareefah,

Sai ďayar motar Sarkin Sassounburom da mutanenshi,

Cikin kasaita Anty Saude ta fito cikin wani kasaitaccen lace irin na jikin Shareefa,
wuyoyinsu da hayyensu sai kyallin zinari yakeyi..

Samm idon Anty saude bai kai mata kan Daddy dake tsaye a kofar shiga parlon ba..

Motar karshe wacce Kamal ya tuko ita wani dogari ya buďe,

Junior ne ya fara fitowa yana rawar wakar *Issa goal* da Kamal yasa mishi,

Dariya Anty saude tayi tana kara jin kaunar yaron a cikin ranta...

A hankali yake mata magana cike da kauna yana lallabata ta fito,

karfin gwiwa ya bata akan babu abinda zai faru,
ta fito su tafi,
he will not lv her here,

Dakyar ya samu ta ziro kyakykyawar kafarta wacce take cikin wani lafiyayyen jan flat shoe mai beza..

Numfashin Hilal neman daukewa yayi saboda ganin yatsun da ko cikin magagi ya tashi zai gane maishi...

*NADEEYAH....*

ya furta a hankali gabanshi na dukan uku uku..

Bayyana kanta tayi fatar nan sai kyalli takeyi,

Ash jallabiya ce a jikinta wacce akayi ma ado da jajayen duwatsu,

gyalen kanta bata samu nutsuwar yane shi ba sai nadashi da tayi akan jelar suka sakko a dukka kafadunta..

Rufe kofar Taheer yayi yace

"Calm down Baby,
babu abinda zai faru,

ďaga idon da zatayi dan bashi amsa ta saukesu cikin na Hilal wanda ke tsaye kamar wanda aka dasa...

Wani irin sanyi taji ya ratsata ta fara gudu a hankali dan isa gurinshi,

"Ya Hilal..
ta faďi cikin muryar kuka,

Kauda kanshi yayi dan baya so sam taga hawayen da ya taru a cikin idonshi..

Ganin hakan yasa ta shigewa cikin jikinshi ta fashe da matsanancin kuka,

kukan da yake boyewa dole ya sakeshi ya rungumeta shima yana fadin

"Kina nan da ranki all this while Nadeeyah,
ina kika shiga?

Alhamdulillah ya Allah...

"Barrister Nadeeyah!
ur Nadeeyah is now a Barrister Ya Hilal,
i missed u alot...

Dago fuskarta yayi yana dariya mai dauke da kuka,

"Missed u more,
dis is tears of joy,
Alhamdulillah...

"Nadeeyah...

da sauri ta waigo ta kalli Daddy dake tsaye idonshi jajur,

'Kasa ta tsuguna yayi saurin dagota ya haďata da jikinshi...

"Kin nuna min ban haifeki ba Nadeeyah,
meyasa kikayi min haka?
Daddy ya faďi yana mai jin zafi a cikin ranshi na rashin ta cikin wadannan shekarun..

"Kayi hakuri Daddy,
kaddara ce,
dan Allah kayi hakuri..

"Bana fushi dake Nadeeyah samm banyi fushi ba,
Nadai gode ma Allah da yasa zan sake ganinki kafin na mutu.....

  " *MG Kyari*
cike da mamaki Daddy ya dago ya kalli me maganar...

" *SAUDATU HALLIRU*...
ya faďi yana zaro ido....

"Ikon Allah....
Anty Saude tace tana rike haba,
ashe rai kan ga rai?,

"Saudatu kina nan abinki,
lallai duniya tanada faďi,
shekara kusan nawa rabon da mu haďu,

Kaii mashaa Allah Nourun ala nourun ya faďi cike da farin ciki..

Ga kawu na can ka barshi a tsaye...

Cikin daburcewa Daddy ya karasa kusa dasu ya tsuguna har kasa ya kwashi gaisuwa sannan yace su shigo ciki...

Cikin takun kasaita suka fara takawa har cikin parlon...
Chapter 104 · 0% Book details