← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 113

Sashe 50

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yakeyi mai dauke da kuka yana fadin Taheer kayi hakuri,
kayi hakuri abokina,
na boye maka ciwo na saboda nasan ba na tashi bane,

Naso sai ka koma makaranta zanyi tafiyar nan amma inaa lokacina yayi,
ban isa kara kwana daya ba koda kuwa ina son kara shi,

"Kukan da Taheer yakeyi a lokacin mai sautine dan bai taba fitar da wannan labarin da yayi mishi karan tsaye cikin rayuwarsa ba sai yau da a karo na biyu yake shirin rasa wacce yake tunanin dawowar farin ciki cikin rayuwarshi,

Ita din ma Nadeeyah kukan takeyi na tausaya mishi da tausayawa kanta,
domin ita ma tayi rashin dukka iyayenta,

"Ban taba kawo mishi mutuwa ba saboda ban yarda zai tafi ya barni a wannan lokacin ba,

kin saurararshi nayi muka daukeshi dan kaishi asibiti,
ina tuno sanda ya shafa fuskata muna gab da fita daga masallacin yace
"Taheer kaki yarda ko?

Dole ka yard---a d------a wann----
nan ya fara kakari har yafi karfin wadanda suka rikeshi,

ka-- kula  da--- kanka da-- da-- mahaifiyarka,

damke hannuna yayi har lokacin idonshi bai gama rufewa yana tayi min murmushin da ya saba,

"A wannan ranar ne na ga abun da ake kira damuwa karara,

a wannan bakar ranar naga kaddarar rabuwa da abin da kakeso,  a wannan daren mahaifina ya mutu tare da duk wani kuzari nawa..

Tun daga ranar na manta farin ciki da yadda akeyinshi,
babu abin da ke burgeni a duniyar nan bare har yasani farin ciki,

Rabuwa da Abbana....

ya ilahi!!
nan da nan Nadeeyah ta rikice saboda yadda yake kuka kamar ana zare ranshi,

kuka sosai yakeyi wanda bai samu damar yinshi ba ranar da ya rasa mahaifinshi,

Abubuwan da suka cunkushe mishi ya fitar yau yake kokawa a kansu,

shakuwar da yayi da mahaifinshi ta wuce ta ďa da uba,
ta zamo shakuwar jini da hanta,

a ko da yaushe ya rufe idonshi murmushinshi kadai yake gani,

bai taba karo da bacin ranshi ba sai dai farin cikin shi,

Gabanshi ta tsuguna itama kukan yaci karfinta tace

"Uncle kayi hakuri,
sau tari abubuwan da muke so basu cika kasancewa tare damu ba,

jarabawar mu kenan,
gara kai kana da wacce in ka juya zakaji dadi,

ni fa babu uwa babu uba,
babu yan uwan uba da zan kirasu nawa saidai na uwa,

ka godewa Allah domin not all are fortunate,

Duk abinda kaga Allah ya dauke maka to yana da dalilin yin hakan,
ta yiwu in ya bar mana su wata rana saboda azabar ciwo mu gwammaci tafiyarsu akan tsayuwarsu cikin ciwon da mu kanmu bamu isa mu magance musu ba,
nasan yadda kakeji domin nima ina jinshi ko ma ince fiye da naka,

Dan Allah a duk lokacin da ka tunashi ka dinga fadin *innalillahi wa inna ilaihir rajiun*
sannan kayi mishi addu'a domin yafi bukatarta a yanzu....

Wata irin nutsuwa ce ta saukar mishi wanda tun kafin rasuwar Abbanshi rabon da ya shiga irin ta,

share hawayen idonshi yayi ya dago ya kalleta,

Sai a lokacin yake tambayar kanshi dalilin dayasa har ya fada mata damuwar da ya dade yana dakonta,

Tabbas zuciyarshi ta gamsu ita ce wacce zai samu nutsuwa da ita,

kalamanta sunyi matukar sanyaya mishi zuciya,

jin zuciyarshi yake wasai kamar an sauke mishi duk wani nauyin da zuciyarshi ke dauke da shi,

Tsugunawa yayi kamar yadda tayi yace

"is ok, kukan ya isa haka,
ni nasa ki kuka,
ni kuma na daina ke kin ki dainawa, sorry kinji,
tashi ki zauna...

Mikewa tayi tace
"zan tafi class ne,

kujera ya ja mata yace
"kice wa ya saki kuka?

Ajiyar zuciya tayi mai karfi sannan ta zauna,

Ji yakeyi kamar ya rungumeta ya hanata wannan kukan da yasan irin ciwonshi,

"nace ya isa ko nima so kikeyi in cigaba,

kinsan in na fara nawa biyu zan hada,

da na rashin mahaifi da kuma rashin farin cikin rayuwata,
ya karashe fadi a raunane cikin damuwa,

Share hawayenta tayi kamar me shagwaba tace

"na daina,

"Kina sona Umm Nadeeyah?

Yadda ya jefo mata tambayar ta sanyata saurin dauke kanta daga kallonshi,

"ummm bani amsa plss,
nd "who is Musaddiq? Ya karashe yana janyo kujera...

"Yaya Musaddiq? Ta fadi tana kallonshi,

gyada kai yayi yace

"yes waye shi, meye alakarku?

"Babu komai,
he is my cousin, 
"nd husband to be, Taheer ya karashe yana kallon cikin idonta,

A razane tace

"whatt,

ba gaskiya bane,

kaga sister na wacce ta karbi hula dazu?

Gyada kai yayi alamar eh,
"to ko zaiyi aure nasan ita zai aura,

wannan hularshi ce

"ya Hilal ya bani shine ta dauka shi ya bani,

"yaya Musaddiq is very nice, bashi da matsala,
yadda ya dauki su Husnah haka ya daukeni,

cike da gamsuwa ya dan samu nutsuwa yace

"Hilal kuma ya kuke dashi?

Murmushi tayi tace
"dan yayata ne,

He is like an angel to me sir,
he wants the best for me,

Bayan yaya Musaddiq da ya nuna tausayinshi ga iyayena,

Yaya Hilal shi yake bani duk wata kulawa lokacin da na rasa iyayena,
he luks after komai nawa,
movements dina da komai,

he wants me to be an independent lady and----

katseta yayi ta hanyar cewa yayarki ce ta haifeshi,

i mean mamanku daya da mamanshi?

"No Anty Reemah yayar Husnah ce,
she is my cousin,

"Okay
kawai yace ya kauda maganar ta hanyar cewa bani amsar farko da na tambayeki,

Ya zame mata dole ta fada mishi gaskiyar yanzu babu soyayya a gabanta,

Danne tausayinshi tayi a can kasan ranta tace

"Uncle,
shhhh nt uncle,
Taheer...
ya fadi yana mata wani narkaken kallon da ya kashe duk wasu gabbai na jikinta,

Call me TAHEER,
ina son jin sunan daga bakinki plss,

marairaicewa tayi tace "no sir i can't,
sorry plss,
"zaki koya with time,

inajinki!

"Kayi hakuri in abun da fada maka yayi maka ciwo,

bance bana sonka ba,

a yanzu ba soyayya bace a gabana,
nasan in kana sona sosai kamar yadda kace zaka girmama ra'ayi na,

Dan Allah sir mu ajiye maganar soyayya yanzu,

kayi hakuri ka taimakeni in taka matakin nasara a rayuwata,

in Allah ya rubuta kai din mijina ne, babu wanda ya isa ya rabamu saidai mutuwa,

Dan Allah uncle kayi hakuri,
mu yarda duk abin da Allah ya rubuta akan mu shine alkhairi,

"Murmushi ya sakar mata mai kyau zuciyarshi ta samu nutsuwa da kalamanta,

dole ya girmama ra'ayinta yayi nesa da ita ya tayata cika burinta,

yasani kamar yadda ta fadi in har kasantuwarsu tare rubutacce ne a lauhil mahfuz, babu makawa duk inda taje dole ta dawo gareshi,

A yanzu jin kanshi yakeyi kamar sabon mutum wanda ya yarda da duk abin da ya faru dashi kaddararshi ce tazo da haka,

"Na amince da bukatarki,
zan kuma girmama ra'ayinki saboda karatu nada matukar muhimmaci a rayuwar mace,
musamman marainiya irinki, naci burin aurenki a cikin kwanakin nan,
nasan inada karfin kaiki bangon duniya kiyi karatu in har anayi,

to nima inaso ki samu abin da kike so,

lokacin da kika mallaki hankalin kanki you decide who u want to settle with,
i pray to Allah nine wanda zuciyarki zata amince dashi a lokacin,

Zan kauracewa ganinki har kiyi achieving goals dinki,
saboda ganinki zai dinga hanani sukuni har in kasa tayaki cika burinki,

Wani zobe ya fito dashi a jakarshi ya mika mata yace
"Aure nufi ne na Allah,
in Allah yayi ni mijinki ne kamar yadda zanyi addu'a ba dare ba rana to babu makawa sai na aureki,

ki rike wannan zoben a matsayin kariya daga gareni,

"Take care of yourself please,
u will always be my omri..

Hawayen da ke makale a idonta ne ya sauko ta kasa dauke idonta akanshi,
hannu yasa a lallausan kuncinta ya share mata hawayen yace

"bana son kuka Omri na,
karki dinga kuka kinji,
duk abin da zai dameki ki tuno *Taheer Haroun Yallo* yana tare dake kuma baya san ganin damuwarki,

Mikewa tayi da sauri ta fita daga office din,

bayan office din ta zauna ta dinga zubar da hawayen tausayin Taheer,

shine mutumin da ya fara furta so a gareta,

badan santa da karatu ba da babu abinda zai hanata amince mishi,

zoben ta kalla ta kankameshi a kirjinta kamar zata maidashi cikinta....

A bangaren Taheer kuma daurewa yayi sosai ya iya yi mata wadannan alkawuran,

ya sani sarai rashin ganin Nadeeyah babban masifa ce a rayuwarshi,

ya zaiyi yana sonta dole yaso farin cikinta,

Waya ya dauka ya kira *Captain Mus'ab* bayan sun gaisa yake ce mishi yasa a shirya mishi visa,
nan da 5days yake son komawa Canada,

"Har zaman nigeria ya isheka kenan *Mus'ab* ya fadi yana dariya,

"Yes uncle Mus'ab, zan koma Phd,

"to makarantar fa?
wa zaka barwa ita,

"Momma na nan,
ya fadi a kasalance yana jajantawa kanshi,

"Jiya Amal ke ce min project dinsu,
Yanzu haka zaka bar mana yara ka tafi,

kaga "Aman baya wani kokari yanzu,
Allah science yafi karfinshi yanzu, yasa wasa,
har Amal ta fishi kokari,

Dariya Taheer yayi yace "karka ma hadasu,

shi da yake science flexibilityn ma ba daya bane,

Amal dake Art wasan yara kawai suke yi,

Dariya Captain Mus'ab yayi yace
"naji wannan nidai kasa a sake samin ido akanshi,
sannan kazo office anjima sai muje in sa a fara shirya maka visa,

yar Hira suka taba sannan sukayi sallama.... 

Tattara takardunshi masu muhimmaci yayi yasa cikin wata jaka,
yana gamawa ya fito da jakar yasa a mota,

Yana hango Amal da Aman daga nesa suna fada akan kudin break, Haifa na tsakiya tana rabasu,

Abin da kullum sai sunyi ne,
shiyasa ma bai bi takai ba ya shiga motarshi,

Ta mudubin gefenshi ya hangota tana lekenshi tana kuka,

nan shima zuciyarshi ta karye sosai,

tada motar yayi da sauri ya bar gurin dan kar ya kasa jure ganin kukanta ya saba alkawarinshi tun kafin aje ko ina.....

Mrs Tijjani Shattimah.......
[27/03 8:42 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣6⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Chapter 50 · 0% Book details