← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 113

Sashe 75

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Little ka kwanta ne,
tsaki ya ja hade da nade daddumar da suka idar da Sallah akai,
bude kofar yayi yace "lafiya Anty?

dan tsaki tayi tace
"wallahi na kasa bacci ne,
ga gidan yayi min girma in kwana ni kadai a daki,
turo min Nadeeyah mu kwanta tare,

"Nima gidan yayi min girma, kinsanni da tsoro,
har gara ke, ya fadi on a serious nt,

"to sai mu kwana mu uku,
in a nan ne in shigo in can ne kuma ku dawo,

"Da kai kawai ya amsa mata hade da rufo kofar,

Juyowa yayi yaga Nadeeyah a bayanshi,

"ina zaki?

zanje can dakin,
tunda tana jin tsoro bai kamata mu barta ita kadai ba..

Hannunta ya riko haďe da janyota gab dashi,
a dan shagwabe yace
"nima tsoro nakeji,

kokarin kwace hannunta tayi tace
"ai tace muje mu uku mu kwana, dan Allah zo muje kar ranta ya baci...

Hade jikinshi yayi da nata yana shinshinar daddan kamshin kanta hade da lumshe yace

"ni dai tare da matata zan kwana,
plss ki rabu da ita,
kwana nawa rabona dake,
kinsan irin wahalar da kika ba zuciyata,

"Tsugunawa yayi dan saita tsayinsu haďe da sake narke mata,

"pls,
pls,
pls,
wata yar dariya tayi wacce ta sashi sake rikice mata,

"dariya kike min ko?

"Dan Allah maida bakin, ta fadi tana tura bakin da hannu.

yadda ya sake turo bakin yasata sakin dariya mai dan sauti,

abun da yake so kenan dama,
nan yayi mata wata irin runguma mai dauke da shaukin so,

wasu rikirkitattun sakonni ya shiga aika mata masu wuyar fassaruwa wanda ya sanya jikinta kyarma matuka,

"kuka sosai ta sanya mishi na rashin sabo tana tureshi,

shi din ma kanin kukan yakeyi wanda ya sanyashi daukarta ya ajiyeta a tsakiyan gado,

Daga shi har ita basu taba shiga cikin yanayin da suke a yanzu ba,

ba kamar Musaddiq da yake namiji mai jini a jiki wanda yake tashe da kuruciya da kudi,
ga madarar kyau,
amma Allah ya tsare shi da mu'amala da ko wace irin mace,

Nadeeyar dai kadai yake gani mace a duk matan da yayi arangama dasu,
bai taba sanin feelings din kasantuwa da mace haka yake ba shiyasa yayi matukar gigita fiye da tunani,
babu abin da yake iya saurare a wannan lokacin sai kukan Nadeeyah da ya kasance abin so a gurinshi,
duk irin bugun da Anty Radiya kewa kofar baiji ba saboda a inda Musaddiq yake guri ne wanda bayajin kira komin karfin kiran kuwa.....

Mrs Tijjani Shattimah......
[17/04 8:22 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣9⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Anty ya akayi?

Raudha ta faďi bayan ta ďaga wayar Radiya rai a bace,
"ba karamin faďa sukayi da Abbati ba akan dadewar da tayi,
kuma ya tabbatar mata da yasan an gama jeren Nadeeyah tun kwana uku da suka wuce,
bayan ya gama kwance mata kwandon masifarshi ya bugo mata kofa yaje ya kwanta cikin 'yayanshi,

daga ďaya bangaren Radiya ta zauna akan gado tace

"Hmmmm Raudha,
ai ni yau naga jaraba,
wallahi yaron nan ya haike mata,
samm baya ko jin bugun da nakewa kofarshi,
dan wani kayan takaicin ma muryarshi ce ta karaďe ko'ina a gidan babu ko kunyar ina gidan,

wannan aikin yafi karfi na,
gobe zanbi first flight in koma gidana,

"Ki kwanta Anty,
da safe zanzo sai musan abun yi,
nima yanzu haka raina a bace yake,
Abbati ya gama bata min rai, wallahi sai yayi paying for ci min mutunci da yayi,

Allah ya kaimu gobe zan san abun yi, Raudha ta karashe hade da kashe wayar...

Kwanciya Radiya tayi zuciyarta na tukuki tana dana sanin tsayawarta a gidan,
tunanin yadda zata fara haďa ido dashi takeyi,
tasan yasan taji komai da ya wakana a tsakaninsu da Nadeeyah,

wannan kayan kunyar bada ita ba,
domin Musaddiq kaninta ne sosai bawai immediate ba,

da tunane tunane marasa dadi hade da kara jin tsanar Nadeeyah a cikin ranta bacci mai cike da mafarkai yayi gaba da ita.....

Cikin sanďa Marakisiyya ta lallabo cikin dakin tana taku a hankali dan kar a farga da shigowarta,

"Nasan da zuwanki hatsabibiya, ta jiyo muryarshi kamar daga sama,
makewa tayi tana waige waige dan ganin ta inda yake mata maganar,

Badariyya da baccinta baiyi nisa ba tayi saurin mikewa hade da lalube saboda duhun dake cikin ďakin,
"wacece,
"wacece a nan gurin,
dan Allah kizo ki taimakeni,

jin da Marakisiyya tayi ba wata muryar dake sake fitowa daga bayanta ya sanya ta karasawa kusa da Badar hade da toshe mata baki,
ihu marar fita Badariyya takeyi tana mutsu mutsun neman kwatar kanta,

"shhhhh,
taimakonki zanyi,
zauna ki kuma yi shuru,
ni mutum ce yar uwarki,
kamar yadda aka kawoki nan, nima haka aka kawo ni,
shekarata ta biyu kenan a gidan nan,
haihuwata ďaya talll,
sunana Marakisiyya,
a garin katsina nake,
zanso jin labarinki sannan mu haďu mu nema wa kanmu mafita,
gobe da safe kizo bayan Bukkar yara zanyi zaman jiranki..
tana kaiwa nan ta saki bakin Badar ta mike ta fita da sauri,
tayi mamakin da taji muryarshi kuma bata ga bayyanarshi ba,
har ta karasa bukkarta tana addu'ar Allah yasa bai jita ba..

Gimbiya Sailuba.. ita ta dauke hankalinshi daga isa gurin su Marakisiyya,
yadai san dalilin zuwanta bai wuce dan neman mafita ba,

wata dariya yayi haďe da maida kanshi jikin Sailuba,
"yaro bai san wuta ba sai ya taka....

Badar kuwa tun zuwanta gidan bata taba jin abin da ya faranta ranta kamar maganar Marakisiyya ba,

juyawa tayi ta tsinci kanta da murmushin jin dadin ta kusa barin gidan ta koma ta samu Masoyinta, abin kaunarta Musaddiq,
tunanowa da tayi Nadeeyah na cikin rayuwarshi ya sanya zuciyarta tafasa haďe da sake saken muggan abubuwan da zatayi mata bayan ta kubuta a gurin.....
(wasa farin girki)

Jakar kayanta ta janyo ta sauko parlon haďe da sake kiran Raudha karo na uku,
daukar wayar Raudha tayi haďe da latsa hon,

"Gani a gate,

kashe wayar Radiya tayi ta mike ta nufi kofar fita daga parlon,

Da sauri Raudha ta kashe motarta ta fito ta nufi inda Radiya ke tsaye,

"Anty dan Allah mu koma, wallahi bazaki tafi yau ba,
sai kinyi wannan sati biyun da muka ce,
wallahi sai mun cika burin mu,
in kika tafi ma ai dadi zata ji ta samu damar juyashi san ranta,
nayi waya da Mummy tun asuba na shirya mata maganganu,
tace zata turo Faida gobe ko jibi, sannan tace zata nemi Badariyya tasa ta dawo daga makaranta,
gara duk mu hadu mu kauda wadannan dangin tsiyan cikin zuri'armu,

Ita kuma Husna mu zuba mata ido,
tunda ita taji ta gani babu wanda zai tursasa ta,
in taji wuya ta nemawa kanta mafita,
bata bar Radiya tayi magana ba ta dauki jakarta ta bude kofar ta jata suka koma ciki,

kafaďunta Radiya ta dafa tace
"Raudha,
bakiji abinda naji bane,
wallahi yanzu haka kunyar ganin Little nake,
nidai bazan iya ba,
in zauna gidan yaro kullum yana zuba rawar kafa akan yarinya karama, ni kuma su barni da saurare,
kuyi keda su Badariyyan kawai,
ni kam na girma da wannan,,,

"Ohhhh Anty,
kunya ai shi zai jita,
ke kam zama zakiyi a cikin gidan dan ki dinga lura da movements dinsu,
ni kuma zanyi duk wasu kullin da suka dace,
sannan Faida da Badariyyah sune zasuyi completing aikin in shaa Allah,

zaunar da ita tayi ta gama tsarata tayi convincing dinta har ta yarda zata kara sati ďaya a gidan,
cike da farin ciki Raudha tace

"ko kefa,
ai mu ya kamata mu maidashi hanya,
in muka barshi ya cigaba da haukar kuruciyya ai sai ya bata rayuwarshi kan wannan yarinyar marar asali,

cire hijab dinta tayi ta nufi sama tace
"ina zuwa Anty,
ita dai Radiya bata ce komai ba sai gyaďa kai kawai da tayi....

Bugu da Murda kofar da Raudha tayi yayi daidai da fitowar su daga bayi,
sake gyara towel din da ya naďota yayi ya sake rungumeta cikin kirjinshi haďe da cewa

"ina kwana Anty,
plss come nd help me sai kuka takeyi,

yadda yayi maganar shima kamar zaiyi kukan ya sanya Raudha yi mishi wani irin mugun kallo,

"Me na faďa maka jiya?
yanzu dan rashin kunya little bazaka iya jiran Anty ta bar gidan nan ba,
bansan ranar da ka lalace har haka ba wallahi,
kai da kayi barnar sai ka gyara da kanka,
sakarai kawai...
tana kaiwa nan ta fita daga dakin haďe da buga kofar da karfin gaske,

kwantar da ita yayi yana share mata hawayen da yayi kaca kaca a fuskarta,

"sorry plss,
bari insa miki kaya muje asibiti,
hannunshi ta kama haďe da girgiza kanta tace
"ka barshi,
ba sai naje asibiti ba zan sami sauki,
rike hannunta yayi sosai yace "Noo ki bari muje,
banasan wannan kukan da kikeyi plss,
kanta ta juyar gefe tace

"um um, ka bari kawai,
ďago kan yayi ya zauna haďe maidota jikinshi yace
"dan Allah ki tashi mu tafi,
kinga jikinki yayi zafi,

"Ni bazani ba,
in naje kace musu meke damuna?

hawayen da ya gangaro bayan ta gama maganar ya share mata ya rasa yadda zaiyi,
murya a raunane shima kukan yake shirin farawa yace

"To me kike so inyi miki ki daina kuka,

"ka kyaleni,
zan taimaki kaina,

wayarshi ya mika hannu ya dauko ya latsa number Anty Reemah,

"Little ango,
an tashi lafiya?,

"lafiya kalau Anty,

yadda taji muryarshi yasata mikama Zainab plate din arish tace
"maza kije ki karya kafin su Adeel su fito..

"Lafiya Diku?
ya naji muryarka haka?

Cikin Muryar shagwaba yayi mata bayanin komai,

dariya tayi tace
"To ni me zanyi,
kai kayi barnarka ni kuma sai in maka magani,

"Ni dan Allah Anty ki faďa min,

bata tsaida dariyarta ba tace "bani Nadeeyah,
da sauri ya kara mata a kunne yana cewa
"kiyi magana,
Anty Reemah ce,

A kunyace ta gaisheta,
cike da zolaya Anty Reemah tace "Allah yasa na samu ďa, kuma jika,

rufe ido Nadeeyah tayi kamar tana gabanta,
Chapter 75 · 0% Book details