Sashe 16
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hello Reemah,
daga daya bangaren Anty Reemah ta bude idonta hankali tashe cikin muryar bacci tace "Na'am, ina kwana Mummy,
''lfy kadai mummý tace, ta cigaba, "kizo gida yanzu ina nemanki, bata jira amsarta ba ta kashe wayar..
Mikewa Anty Reemah tayi jiki a sanyaye,
tasan akan matsalar Hilal akayi kiranta da safen nan,
cikin zafi tace "wai wannan wani irin yaro ne da yakeson kashe ni tun lokaci na baiyi ba,
wallhy yau, ko gobe zamu bar kasar nan kar ya jaza min bala'i,
ina kokarin gamawa da mahaifiyata lafiya yana neman janyo min tsinuwa,
Papa tashi plss ka fara mana shirye shiryen tafiya bari inje gida in dawo,
Ajiyar zuciya kawai Papa yayi ya juya ya kara jan bargo,
samm bayason abinda zai matsawa matarshi da ta zamo jigo kuma garkuwa cikin rayuwarshi,
"Papa kara rufe kanka kayi?
ta fadi kamar zatayi kuka,
yayewa yayi da sauri yana murmushi yace "its too early my omri,
kije ki dawo sai muyi shirye shiryen tare, gyada kanta tayi tasa hijab har kasa ta dauki mukullin mota ta fita...
********
"Waye ya sa ki aiki da wannan safiyar?
Tambayar da Hilal ya jefo mata kenan idonshi na kallon titi,
Tana zaune a kaikaice a baya, saboda kar ta bata musu mota,
cike da jin tsoronshi tace "babu kowa,
naga kayan sunyi datti ne,
Are u an au pair girl??
Musaddiq ya kara jefo mata wata tambayar,
shuru tayi idonta yayi narai narai zai fara zubar hawaye,
juyowa baya yayi ya kalli yadda ta zauna yace "to ruwa ruwa,
zauna dakyau sai kiji dadin yin kukan,
kara kaikaicewa tayi ta kife kanta jikin sit din da yake zaune,
"hey wasa nake miki zauna yadda kike so,
ya fadi hade da maida fuskarshi gaba,
Daidai wani babban shago dake bakin layin Hilal yayi parking,
kallonshi Musaddiq yayi yace "me zaka siya,
hannu Hilal yasa a aljihunshi yaji ba kudi, bai amsa musaddiq ba yace "akwai kudi a jikinka,
taba aljihunshi yayi yace i don't think akwai,
ko akwai ma basu da yawa,
dauko wallet dinshi da ya bari cikin motar yayi ya cire atm din da PAPA ya bashi ya shige shagon,
"Kunada pos?
ya tambayi wani yaron shagon,
eh akwai sir, yaron ya amsa shi cikin girmamawa,
wucewa ciki yayi ya dauko "pad" guda uku,
"Tunda suka isa Asibiti ya lura ta kasa zama har aka gama yi mata allurori,
kuma yaga alamar digon jini a jikin rigarta,
babu inda bai karewa kallo a jikinta ba,
hatta yatsun kafarta wadanda suka fi tafiya da imanin zuciyarshi,
siyayya yayi mata na turaruka da mayuka da sabulai masu kyau da dan tsada,
yadda ya barta haka ya fito ya sameta,
Hira musaddiq ke janta dashi tana amsa wasu, wasu kuma tayi shuru tana murmushi ba tare da ta dago kanta ba,
gefen da take zaune Hilal ya bude,
a tsorace ta dago saboda ta kusa fadi dan ta jingina da kofar,
Ganin Hilal ne ya sanya ta gyara zama ta nutsu sosai,
wani sanyayyen kallo yayi wa nutsuwar da tayi, sannan ya mika mata kayan ya rufe kofar ya shiga suka wuce..
Rike kayan tayi a darare,
ta gefen idonta ta hango pad,
gabanta ne ya yanke ya fadi a zuciyarta tace Allah yasa ba staining tayi ba,
tsoro da kunya duk suka kara dagula lissafinta a cikin motar,
suna isa cikin gidan tayi saurin bude motar ta fita ba tare da ta dauki kayan ba,
kashe motar yayi ya bita da shagalallen kallo har ta kusa shiga cikin gidan,
"yarinyar nan bata dauki kayan nan ba,
musaddiq ya fadi hade da bude baya ya dauko su,
motar Anty Reemah ya gani yace
"ur momma is here,
kallonshi Hilal yayi yace "a haba,
ina take?
"Tayarta na gani ba ita ba ya karashe yana murmushi hade da nuna mishi motar,
fitowa yayi suka karasa cikin gidan a tare...
"Ga munafukar nan ma ta shigo, Mummy ta fadi a kausashe tana kallon Nadeeyah,
tsayawa Nadeeyah tayi a bakin kofar ta kasa daga kafarta, nan take jikinta ya fara rawa,
karaso ciki algunguma,
daga zuwanki jiya zaki yi min setting gida on fire da farar safiya,
to walhy bazan dauka ba,
Nadeeyah saboda tsoro hakoranta suka fara kara kainin haduwa da junansu,
har lokacin bata iya karasowa ba dan kafarta ta gaza dagawa,
ba dake nake magana ba?
Mummy ta kara fadi cikin daga murya,
kuka mai karfi ne ya kufce ma Nadeeyah,
"laaaa ha ila ha illahu!!
uban me aka miki zaki tsaya a bakin kofa ki sake ma mutane kuka,
kaii nikam na bani,
na dauko makirar yarinya da hannuna na kawo cikin gida na,
Mikewa Badariyya tayi ta kamo hannunta out of anger, ta fara janta tana fadin zo ki wuce munafuka dangin tsiya,
yau sai kin bar gidannan tunda ba gidan ubanki bane, tayi wurgi da ita a tsakiyar parlon tana maida numfashi kamar bakin kumurci,
zuciyarta mugun zafi take yi na ganin Musaddiq na petting Nadeeyah kuma harda rike hannunta..
Antyn Reemah dai bata ce uffan tana zaune idonta yayi jawur saboda irin tashin hankalin da mummy ta sata na furucinta a kanta,
tana tsoron sake magana kar ta kara harzuka mummy,
Hannu Badar tasa zata fisge karamin hijab din jikin Nadeeyah,
Hilal ya rike hannun ya dauketa da mari kwarara guda biyu,
ke din gidan ubanki ne?
Nace gidan ubanki ne?
Yanda kike a gidan nan haka take!
Ihunta ne ya gauraye gidan ta shiga zaginshi tana fadin Allah ya isa mugu azzalumi kawai,
wani dukan zai sake kai mata Anty Reemah ta rike hannunshi ta kwada mishi mari,
wani irin kallo yayi mata na mamaki yace "Mum------ shut up ta katseshi rai a bace,
kana hauka ne,
wace irin zuciya gareka da zata dinga saka dukan mace,
ko ka sami jakar ka ne?
tun safe kake jibgarta,
Koma me tayi maka ai da sai ka fadawa mummy ba wai kai ka yanke hukunci da kanka ba,
beside ma ina ruwanka dan tasa Nadeeyah wanke wanke,
meye naka a ciki,
kullum ni kenan in nazo gida bani da kwanciyar hankali saboda kai,
duk sona da yin zumunci haka nake hakura saboda bakar zuciya irin taka,
yanzu rashin kunyar taka akan mahaifiyata ya kai har ka kusa zaginta, saboda dai ka nuna wa duniya mu bamu baka tarbiyar girmama na gaba da kai ba,
To bari kaji, yadda na haifeka itama haka ta haifeni,
walhy duk ranar da ka yarda tayi min baki akanka babu ni babu k------- da sauri Musaddiq ya rufe mata baki,
subhanallah!!!
Anty me ya kawo wadannan magangannun?
Me yayi zafi haka?
Kallonshi Anty Reemah tayi tace "barni da yaron nan little,
so yake yi ya kashe ni,
baya san zaman lafiya ko kadan,
tun jiya da daddare mummy ta fada min irin rashin kunyar da yayi mata, sannan yau da safe ya sauke dukkan fushinshi kan Badariyya,
me tayi mishi har takai ga duka sai kace " *SHAGON MADA* "
in ma da gaske Badar tasa Nadeeyah wanke wanke wat is the big deal in it?
ai mace ce, kuma kowace mace da aikin gida aka santa,
most he sai ya nuna karfinshi jikin 'ya mace sai kace ya samu jaka,
Rage sautin kuka Badariyya tayi saboda taji asirinta na gab da tonuwa,
zatayi magana Musaddiq yayi saurin cewa waitt Anty,
waye ya fada miki Hilal ya daki Badariyya?
Hararshi Mummy tayi tace
"Nice!
Ko karya nayi, bai daketa din bane, fada mishi da bakinki Badar,
ya daketa saboda wannan munafukar ta hada tuggu da karya saboda kawai ta shiga tsakanin ya'yana suyi ta fada kamar karnunka,
to ta Allah ba taki ba walhy. .
Ni fa ban gane ba?
Musaddiq ya fadi hade da kai idonshi kan Badariyya dake rike da kuncinta,
Me Nadeeyah tace game da ke,
kuma da yaushe Hilal ya dake ki?
"Uhmmm uhmm--- uhmn--- ka fita lokacin yace in-- in ya dawo zai min dukan tsiya,
ina tsoron kar ya dake ni shiyasa na fadi ma mummy ya dake ni dan ayi wa tufkar hanci,
kallon Mummy Musaddiq yayi yace "kinji abinda tace ko in maimaita miki?
A kunyace mummy tace "to meye nashi na mata barazana,
ai dole in gasgata saboda nasan bashi da aiki sai duka da zagin na kasa dashi,
Anty Reemah kuwa idonta na kan Hilal dake rike da kunci har lokacin, shi din ma ita yake kallo idonshi jajur,
karyar da kanta tayi zata mishi magana yayi hanyar dakin Musaddiq da sauri,
ajiyar zuciya tayi ta kalli Musaddiq dake ta ma Mummy magana cikin fada,
"Nadeeyah da kika kira munafuka babu abinda tace game da kowa, hasali ma wannan bakar dagar bata san meke faruwa ba har saida muka zo kaita asibiti,
ita ce ma tayi ma Hilal rashin kunya ina jinta bai tanka ba,
walhy in dai baki daina biyewa yarinyar nan ba wata rana sai kinyi dana sani marar amfani,
haba dan Allah ya karashe rai a bace hade da gallawa Badar harara,
Durkusawa yayi kusa da Nadeeyah dake kuka yace "tashi kije daki kisha magani ki kwanta,
mikewa tayi tana share hawaye ta fara tafiya,
kayan da Hilal ya sai mata ya dauko ya bi bayanta,
Dakin Delu yaga tana kokarin shiga yace "ba nan bane dakin gashi nan,
ya nuna dakin su Badar,
Husnah da tun ihun Badar ta farka, tayi hamma tace "a dakin Delu ta kwana kayanta na can,
jinginar da kanshi yayi jigin bango yace "Hasbunallah,
dakin ya bita ya mika mata kayan ya fito da sauri yayi hanyar Sama,
A tsaye yaga Daddy yayi folding arms dinshi fuskar nan tashi a murtuke, asalin Kanuri ya bayyana a tare dashi,
"Daddy kana gan----- naga komai *Saaaaaadiq* " haka yake kiranshi har sai yaja sunan!
kasa ya sauko ya kalli Mummy da duk ta sukurkurce yace
"bana san jin komai,
anjima karfe biyu na rana bayan jumm'a duk mu hallara a gidan Baffa,
"i want to clear all my mystifications, dole ne ku fitar dani cikin duhu,
dan alamu sun nuna min ba Goggo bace ta haifi SUWAIBA,
sannan ba talaucin su bane ya sanya ku tsanarsu a matsayinsu na jininku, akwai dai wani abun a kasa,