← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 113

Sashe 59

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata sabuwar gaisuwa suka sake yi Baffa yace "Har kun shirya tafiya,
"eh Papy yace hade da fito makudan kudi a aljihunshi ya bashi yace koda za'a bukaci wasu abubuwan,
ya cigaba da cewa
"na biya kudin furnitures a *landninterior* Raliya zata kawo matar tazo taga taga yanayin girman kayan da zasuyi,
receipt din na gurinta,

"dan Allah duk abin da ake bukata a kirani,
in shaa Allah ana gama komai zansa ranar da zamu kawo Anni itama tazo tayi zamanta a gidan babana, ya karashe yana dariyar ganin fuskar Anni,

Godiya sosai Baffa yayi mishi hade da sa albarka,

"Ina Goggon take?
Anni ta fadi tana mikewa dan taje su gaisa,
rakata Baffa yayi yace "tana ciki babu lafiya,
jiya saida wata nurse a makota tazo ta kara mata ruwa,
mikewa sukayi gaba dayansu suka shiga dakin da Goggon take kwance tana kallon sama,

koda suka shigo bata waigo ta kallesu ba saboda kar ta karawa kanta bakin ciki,
har suka karaci yi mata sannu bata ce musu ta tafasa ba,
dan tasan yadda takejin tashin kamshinsu in ta kallesu zuciyarta na iya fashewa,

"Tana jiyo Baffa a tsakar gida yana fadin
"zafin ciwo ne, haka takeyi in bata da lafiya,

har bakin mota ya rakasu yana godiya hade da sa musu Albarka......

Cikin yaran shida uku yayan kusoshin gwamnati ne, uku kuma kannen matar GMD ne,
interview din da za'a yi musu ma duk sun dauka camouflage ne,
dan a ganinsu matsayin iyayensu ya wuce su tsaya yin wani interview,
shiyasa basu damu ba sam,

lift suka hau aka nuna musu hanyar office din GMD,

Hira sukeyi sosai saboda sanayyarsu da juna,

shidai Musaddiq Addu'a yayi tayi kamar yadda Nadeeyah ta fada mishi,
suna gab da shiga office din wata mace ta dakatar dasu,
basu samu ganin GMD din ba saboda yana cikin meeting,
yadai bari ayi musu interview din,

Abin da yaran basu sani ba shine ba yan Nigeria bane zasuyi musu interview din,

samun aiki a irin gurin ba sanayya bane, dace ne da kuma kwazo,

Da ďan kanwar matar GMD
*Zubair Ribeh*
aka fara,

yana shiga gabanshi ya fadi saboda irin mutanen da ya gani a gurin,
takardunshi suka bukaci ya miko musu,
nan ya mika musu a mutunce,
dubawa sukayi sam basu damu da ganin takarddun Nysc dinshi ba,
second class lower gareshi a
*Bsc Chemistry* ,
tunda daga nan suka rufe takardunshi suka tambayeshi abubuwan da ya kamata,
yayi iya kokarinshi ya basu amsa har jikinshi ya jike sharkaff,

sallamarshi sukayi hade da tafa mishi dan yayi iya kokarin yake da dashi,
haka ce ta kasance da sauran yaran,
mai first class din cikinsu da suke da hope akanshi shima ya kasa amsa wasu abubuwan,
sarewa sukayi har suka fara tunanin daukar *Zubair* dan shi kam result dinshi ya nuna kwakwalwarshi ce ta bashi,
sauran kuwa duk siyan musu akayi,

shigowar Musaddiq ne ya katse musu tattaunawarsu,
da fari sun ki yi mishi dan ganin mutane shida kadai suka nema,
babban cikinsu ne yace abashi chance may be su sameshi da abubuwan da sukeso,
takardunshi suka bukaci gani, yayi saurin fitowa dashi,

ledar da Nadeeyah ta bashi ce ta fado kasa,
da sauri ya dauketa hade da mika musu takardun cike da girmamawa,

Juya ledar yayi yana murmushi shi kadai,
nan take kalamanta suka shiga yi mishi yawo a kai,
baiyi wata wata ba ya fito da wayarshi, kasa kasa ya sa wayar ya tura ma Mummy da Daddy text din su tayashi addu'a yana cikin gurin,
har zai mayar da wayar aljihu yaji karar shigowar text,
dubawa yayi hade da murmushin ganin sakon Nadeeyah,

kamar tasan yana bukatar irin wannan adduar a wannan lokacin,
maida wayar aljihu yayi ya dago kai ya kallesu,

Saida ya kusa kaiwa kasa saboda yadda suka zuba mishi ido,

"am very sorry pls, ya fadi dan yasan laifinshi,

cike da bacin ran rainuwar yan nigeria wata mata tace

"nan gurin wasan yara ne,
in ba aiki kazo nema ba, chatting kazo yi ka fita dan babu wanda ya zai matsa maka,,

kartawa cikinshi yayi ya fara basu hakuri cikin harshen turanci yace

"ina bukatar addu'ar iyayena, domin addu'a ita kadai ce zata samar min wannan aikin,
shiyasa na tura musu sakwanni saboda su tayani addu'ar samun aikin,

jikinsu ne ya mutu duk sukayi sanyi suka maida fushin da suke da niyyar sauke mishi,

tambayoyi suka shiga yi mishi akan yadda ya kamata a sarrafa gas da karafan gas,

da yake I.T din da yayi a cyprus a companyn gas yayi shi, nan ya basu gamsashiyar amsa mai cike da ilimi,

Saboda tsabar burgesu da yayi basu san suna jefo mishi wasu tambayayoyin ba,

kaca kaca suka fada da lamarin Musaddiq,
ko amsa zai basu saiya russuna,
duk inda bature yake yana matukar san girmamawa,
nan take suka mike suna tafa mishi hade da jinjina mishi,

wata takarda mace tayi signing tace
"congratulations my dear, ta mika mishi takardar,
har kasa ya tsuguna ya karba hade da sujjadar godiya ga ubangiji,

sunan *Zubair* suka kira shima ya shigo da saurin shi,
takardar shima suka mika mishi ya hau musu godiya hade da kukan murna, rasa inda zai kai murnar da yake ciki yayi dan yasan yau mahaifiyarshi bazatayi bacci ba saboda murna,
Allah ya taimakeshi,
yanzu zai tallafi yan uwanshi da mahaifinshi.....

Sauran yaran basu damu ba saboda dama aikin ba damunsu yayi ba,
iyayen keson gina su saboda gaba,

Sosai Dr Barau yayi murnar ganin Zubair yaci,
sam matarshi bata da masaniyar ya amshi takardun yaron,
kannenta wadanda suke ciki daya ta bada takardunsu ta zame na Zubair,
da yake Allah shine ke taimakon bawa, gashi Allah ya bashi sauran kannenta basu samu ba,

Allah kenan mai kyauta a gurin wanda yaso a lokacin da yaso,

Hotel ya kamawa Musaddiq bayan ya gama ture turen takardun su ta computer zuwa lagos,

kwanciya yayi yana mika saboda gajiya,
ga yunwar da ta addabeshi,

wanka ya shiga dakyar saboda tsabar gajiya,
bai taba irin yawon da yayi yau ba,
duk block din cikin Towers saida suka kewaye shi,

da ruwan zafi sosai yayi wanka hade da alwala,

yana idar da sallah ya janyo jakarshi,
ledar da Nadeeyah ta bashi ya fara karo dashi,
da sauri ya bude,
naman da suka soya na walima wanda aka basu suka ajiye cikin microwave shi ta dumama mishi tayi foiling tasa a leda,
zafi har yasa naman ya fara nakewa,

zai fara ci kenan yaji an buga kofar dakin shi,
abinci ne aka kawo mishi wanda ya tabbatar zaiyi wuya ya iya cin shi,
karba yayi hade da mishi godiya,

ajiyewa yayi ya fara juya salad din,
da sauri ya ajiye cokalin ya dauki juice din dake kai,

Naman kadai yaci ya hada tea,

yana idar da Sallar isha'i ya janyo wayarshi da ya soka ta a charge,
23missed calls ya gani ya fara dubawa,
na Daddy da Mummy ne a sama sai Hilal, Badar, Nadeeyah da Husnah,

Daddy ya fara kira sukayi murnarsu sosai sannan ya mikawa Mummy wayar itama tayi murna sosai hade da yi mishi adduo,i,
cike da murna sukayi Sallama ya kira Hilal,

Sunfi minti goma suna hira yana mishi fada akan ya dauki aikinshi serious,
"banda baccin asara dan nasanka, baka cika daukar abu serious ba,
dariya Musaddiq yayi yace "yau ma dakyar na tashi,
saida Nadeeyah toshe min kunne ta kusa kasheni,
yarinyar nan bata jin magana, but ta kyauta fa,
gashi Allah yasa nazo akan lokaci kuma na samu nasara,

saida Hilal ya danji abun a ranshi,
kauda mugun tunanin da shaidan ya kawata mishi yayi saurin yi hade da cigaba da hirarsu....

Game yakeyi yana juyi akan gado bacci na dan fisgarshi kadan kadan,
karar wayarshi ce ta sa ya watstsake ya dauka,

"congrat yayana, Husnah ta fadi da karfi har saida ya cire wayar a kunne,

"Thanks sis, baku kwanta ba?,

"10 fa yaya,
har ka fara bacci ne?

Juyi yayi yace "ummm na fara,
to ga Nadeeyah ku gaisa ta mika mata wayar da sauri,

"Congratulations, Allah yasa ka fara sa'a, ya kaika matakai masu daraja a cikin aikinka,

Sosai yaji dadin da ya rasa ko na meye,
dadin jin muryarta da yayi ko kuma na adduoin da ta jero mishi,

Ameenn My PS, ya fadi ya lumshe ido,

Dariya tayi tace shi PS din meye shi?

"Problem solver,
nayi missing dinki sosai,
furta kalmar yayi cikin gushewar hankalin mai bacci, bude idonshi yayi yace "naman da kika san min ya taimakeni, wani abinci suka bani kamar tsutsa, na kasa ci,

Murmushi tayi mai sauti tace "haka nan zaka koya, aiki fa zaka fara,
dole ka koyi cin abincin waje tunda ba'a gida bane, da haka zaka saba, Shuru yayi yana jin muryarta na ratsa ko ina na jikinshi, saboda tsabar dadin murayarta da yakeji har bacci mai cike da mafarkai ya daukeshi ba tare da ya sani ba......

Washe gari Dr Barau yace su shirya tafiya lagos,
badan yana so ba haka ya daure suka tafi,

A can ya sai kayyaki dan sun ma fada mishi tafiyar kwana bakwai ce,
wahala iya wahala babu irin wace Musaddiq bai sha ba, nuna musu abubuwa akeyi ana koya musu yadda zasuyi ayyukansu,

kwanansu takwas cirr suka dawo gida dauke da takardunsu na offer da komai nasu na accomodatio, wardrobe money da sauransu,
tun a jirgi Musaddiq ke kiran wayar kowa a gidan bata shiga, dakyar ya samu number Malam Ali yace ya fada musu yana hanyar dawowa sannan yazo airport ya daukeshi.......

Wurgar da komai nashi yayi a parlor ya nufi kitchen saboda muguwar yunwar da yake ji,
a tsaye ya tadda ita tana goge gas tana bitar haddar da zata bayar,

a hankali ya karaso inda take ya sanya yatsunshi daya cikin kunnenta,

wani irin ihu ta saki wanda ya sanyashi toshe mata baki yana kyakyata dariya,

rankwafowa yayi daidai kunnenta saboda gajertan da tayi a gabanshi yace "matsoraciya,
irin wannan ihun ai sai ki firgita mutane,

me kika dafa min?

"Ayya bansan zaka dawo ba ai,
kayi hakuri bari in tuka maka tuwo,
kaje ka huta awa biyu ya isa,

"In na kara minti talatin a duniya ki godewa Allah,
kawai kice kaje ka kashe kanka, dan Allah ki daina wasa,
Chapter 59 · 0% Book details