← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 113

Sashe 65

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*A rayuwa kowa yana tafe da kaddararsa, duk wanda Allah ya rubuta kaddararka ta zama tare dashi ne, to baka da dabara sai ka zauna dashi, naso kiyi zurfin karatu ta yadda zaki kere wasu matan kema a sanyaki cikin jerin masu ilimi sannan kiyi aure... amma hakan bazai yiwu ba saboda kaddararki batazo a haka ba, _I love Nadeeyah_ .... wannan itace kalmar da dan uwana yace in isar miki, Musaddiq na matukar kaunarki Nadeeyah, da fatan zaki amshi soyayyarshi, domin kun dace matuka, kuma nasan bazai barki ki zubda da hawaye ba, Allah ya barku tare kanwata take care.....*

Tana kaiwa karshe taji wani irin jirin da Allah ya taimaketa a zaune take, dan ta fadi,

Ya Musaddiq ke sonta,
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun,

ya zama dole gobe tayi shirin tafiya Gombe kuma ta zauna a can,
ina zata iya da bala'in Badar,
su Anty Raudha,
uwa uba Mummy da ta dau burin duniya tasa a kan shi,

inaaa samm bazama ta taba nuna taga text dinnan ba,
da sauri ta kashe wayarta ta dukunkune cikin bargo....

*MAFARKI*

_Hannu tasa ta cire akan farar fuskarshi da ta koma jaaa saboda kukan da yaci, "rau rau idonta yayi murya ta fara rawa tace "Yaa Hilal, me ya sameka, wanene? Hannunta kawai ya rike dan kukan yaci karfinshi ya kasa magana, hawayen dake makale cikin idonta ya fara zuba kamar fanfo, a shagwabe tace "Dan Allah ka fada min, menene? Zaiyi magana kenan ya hango wani farin haske dan karami ya doso inda suke, hannun Nadeeyah ya rike yana janta yana fadin ta kyaleshi tazo su tafi, mikewa tayi duk da kankantar haske haka ya rinjayeta ta dinga binshi tana waigen Hilal da ya sunkuyar da kanshi kasa sautin kukanshi ne kadai ke tashi a gurin....

A firgice ta tashi zufaa duk ta jikata,
janyo wayarta tayi da sauri ta kunnata,
bata bari ta gama settling ba ta latsa number Hilal,
lokacin karfe 1 a nigeria,
tasan dakyar yanzu in bai yi bacci ba,
saida ta kira sau uku bai daga ba,

kwanciya tayi taji duk babu dadi dan so takeyi taji ko lafiyarshi kalau,

yana idar da Sallah ya bi bayan kiran da tayi mishi,

hannu na rawa ta dauka tace
"ina wuni?

"Kwana dai Nadeeyah ya fadi murya a dashe,

"umm haka ne,
ba kayi bacci ba?
dama bacci ne ya daukeni kuma bani da charge shiyasa na kiraka saboda tunin sakon..

"yasani sarai ta gani,
danne zuciyarshi yayi yace "mantawa nayi kanwata kuma surukata,
bari in fada miki da baki amaryar Small uncle,
yadda ya fadi murya na rawa ya sanyata kashe wayar da sauri,
dana sani ta dinga yi dan yanzu ya tabbatar mata a kunnenta,
Allah ya sani bata kin Musaddiq amma koda wasa bazata taba iya aurenshi ba,
komawa tayi ta kwanta tunane tunane marasa dadi suka dinga zuwan mata har wani baccin ya dauketa....

A parlor ta zauna da asuba tana jiran ganin Daddy ya dawo daga Salla,
ga mamakinta tare suka shigo da Musaddiq,
dama ita ke tashinshi Sallar asuba to yau taki zuwa,
tasan Daddy ne ya tasheshi,

Har kasa ta tsuguna ta gaida Daddy,
amsawa yayi hade da cewa baki koma bacci ba,
"gyada kai tayi tace
"eh Daddy dama ina son in tambayeka ne,
cikin palon ya shiga ya zauna yace

"zo zauna inji,

kusa dashi taje ta durkusa tace
"Daddy mun gama jarabawa,
dan Allah ina son inje Gombe,
tare zamu tafi da Husna,

fadada Murmushinshi yayi yace "jiya muka gama magana da mamanku,
ku shirya jibi Malam Ali zai kaiku,

godiya sosai tayi mishi ta mike ta shiga kitchen,
shima sama ya wuce dan bacci zai koma saboda lahadi ce babu aiki..

Saida yaji Daddy ya rufe kofar dakinshi sannan yayi saurin zuwa kitchen din,
tsaye ya sameta a kofar shiga kitchen din tana jiran su shiga daki itama ta fito ta shige daki,

Tana ganinshi tayi saurin juyawa zata koma ciki,
shan gabanta yayi da sauri tsayinshi yayi mata rumfa babu abin da take gani a gabanta sai shi,
jan hijab dinta tayi ta rufe bakinta tace
"zanyi aiki ne,

"nima shi zanyi ya fadi yana kwaikwayonta..

Gefenshi tabi zata wuce taga yasa hannu ya tare gurin,
marairaicewa tayi tace "dan Allah ka matsa,
ko baka san Daddy ya karya da wuri?
nade hannuwanshi yayi yana murmushi yace
"sai kin yarda muyi tare,
gyada mishi kai tayi alamar amincewa,

yauwa ya fadi hade da jan hannun jallabiyar shi,
dankali ta debo ta dauko abin ferewa guda 2 ta mika mishi daya,

karba yayi yana dariya yace
"Allah sa dai kar in yanke,

"in ka yanke zaka hakura ai ta fadi itama tana dariyar,

"har so kikeyi in yanke ko?

"Kai ka fada nidai bance ba!

"Kin ce mana,
ya fadi a shagwabe kamar karamin yaro,

dariya tayi hade da tattara dankalin ta juya mishi baya ta cigaba da aikinta,

"An fada miki sakona??

Wani irin faduwar Gaba taji da ya jefo mata tambayar,
bata samu bakin amsashi ba ta cigaba da aikinta hannunta na rawa,

Gabanta ya dawo yasa hannu ya dago fuskarta,
da sauri ta runtse idonta tace

"wani sako?
In abinci ne kasan yanzu zan gama,

"uhm ga acici ko?
To wannan sakon yafi cikina muhimmaci,

Hilal bai fada miki komai ba?
Ya karashe tambayar cike da kasalar da soyayyarta ta sakar mishi,

turo baki tayi hade da ture hannunshi tace
"ni bai fada min komai ba,
hannu yasa a aljihu ya dauko waya ya fara latsata,
da sauri ta daura hannunta kan wayar tace

"Dan Allah yaya Musaddiq ka bar wannan maganar,

yin soyayya ni da kai ba abu bane mai yiwuwa,

"dalili??

Ya tambaya fuskarshi ta nuna alamun damuwa,
rasa abun ce mishi tayi kawai tace

"saboda inada wanda nake so, zoben dake makale a hannunta ta nuna mishi tace wannan zoben alkawari ne,
kuma kasan babu kyau karya alkawari,

Hannunta ya rike a hankali yana shafa zoben zuciyarshi kamar zata soye saboda azabar radadin da take yi,

iya karfinshi yasa ya fincike zoben a hannunta,
tana kallonshi ya sa hakori ya karyashi yayi wurgi dashi ta window,

kallonta yayi da wani irin yanayin da bata taba gani a tare dashi ba yace
"koma waye saidai yayi hakuri dan ba samunki zaiyi ba,
ke tawa ce ni kadai,
kin gane ko?

Kasa tayi da kanta hawaye ya fara zubo mata tace
"kayi hakuri, ina sonshi sos----

*Nadeeeyah....*
ya fadi da karfi rai a bace kamar namijin gaske,
sautin kukanta da yaji ne ya sa jikinshi mutuwa,
hannu na rawa ya dago fuskarta ya fara share mata hawayen,

"kiyi hakuri ki daina kuka,
bazan iya jin bakinki ya furta san wani bayan ni ba,
bazan jure ba,
rage murya yayi yace
"dan Allah ki soni ni kadai,

kamar dada ingizo kukanta yayi saboda bata son ya matsa su shiga cikin matsala tare,
ganin yayi mata tsawo sosai ya sanyashi rage tsawonshi daidai fuskarta,

"Nadeeyah----
"dan Allah kayi hakuri ta katseshi cikin kuka,

"wai dame zan hakura ne?
ya za'ayi in hakura da abun da nake so,
kin san bazai yiwuwu ba,
ya karashe yana daura hannunshi a saman idonta,

"ki daina min kuka, bana so,
in ba so kikeyi inyi ba nima,
kiyi hakuri kinji?
ki manta dashi ga dan uwanki,
kinsan nafi sonki,
kuma kema kina sona,
zaki fi kula dani,
abinci na, komai na,

"Ni bana sanka ta fadi tana goge fuska da hannunta,

saboda shaukin so dake dibarshi baisan sanda ya hada jikinshi da nata ba ya kankameta hade cewa

"zaki soni sosai,

Fiye ma da kanki Ma...

Fiye da komai a duniya...

lumshe idanuwanshi yayi ya cigaba da fadin

*I love yhu Nadeeyah, more than life it self......*

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.....
maimata Kalmar Mummy tayi sau uku tana tafa hannun cike da mamaki da takaici.......

Mrs Tijjani Shattimah......
[05/04 10:42 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Na shiga uku ni Zainab!
yau me zan gani a cikin gidana,

Da sauri Musaddiq ya mike har takalminshi daya na fita a kafarshi yace
"me kika gani Mummy?

"Ubanka na gani ta fadi a harzuke,
abin da kukeyi kenan Musaddiq?

yau ni na shiga uku na lalace,

Oooh wato shiyasa kullum kike hanyar dakinshi da nufin tashinshi a bacci,
ashe zuwa kikeyi ki koya mishi yadda mace da namiji suke jiyewa kansu dadi,
yanzu Nadeeyah har kinyi girman da zaki koyawa namiji yadda zai dinga yi miki kiji dadi,

*DANKARI!*

lallai wannan abun babba ne,

"Wai Mummy me ya faru ne? babu abin da mukayi fa,
kawai ina taya----

zan ci maka mutunci in ka sake yi min magana,
wallahi kana cewa takk zan kwada maka mari,
sakarai wanda bai san inda yake mishi ciwo ba,
maza ka biyoni....

kallon Nadeeyah dake tsaye tana share hawaye tayi tace

"To munafuka maza ki wuce daki ki jirayi hukuncin da zan miki, yar iska mara mutunci,

Rai a bace Musaddiq yace
"ki daina zaginta Mummy,
me tayi miki da zafi har haka kike kiranta da munanan kalamai,
haba....

"Bance karka sake samin baki ba, zo ka fita ka wuce sama gani nan zuwa,

Saida ya bari Nadeeyah ta fita sannan shima ya fita ya haye sama yana kunkuni dan shi samm baiga abin da sukayi ba.....

"Ashe yarannan Iskancinsu sukeyi,
wallahi da wani ne yazo ya bani labarin cewa yaga Musaddiq da mace a yadda na gansu wallahi bazan yarda ba,
dan rashin kunya a cikin gida,

ita kuma dan ta gama zama yar iska harda kankame wuyanshi....

*Zainab....*

Daddy ya daka mata tsawa da karfi dan yaga tana neman wuce gona da iri,

shuru tayi tana hucin bacin ran kalaman da ta jiyo danta da ta gama shirin kece raini dashi yana fadawa Nadeeyah,
Nadeeyar Adamu mai gadi!
da sauri ta runtse idonta dan wallahi tuno abun ma mugun taba zuciyarta yakeyi,

kallon Musaddiq Daddy yayi fuska babu alamun wasa yace

"ka fada min gaskiya,
menene tsakaninka da Nadeeyah?

Nasan ko kai zaka iya rungumar mace Nadeeyah bazata taba kusantar namiji ba saboda i have full faith in Suwaiba's upbringing,

Shin me mahaifiyarka ta gani wanda ya sanyata yin wannan tunanin,

kamar jira yakeyi mahaifinshi ya kai aya yace
Chapter 65 · 0% Book details