← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 113

Sashe 79

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya yayi sosai yana duban ta inda zaiga rabin rayuwarshi,
hangota yayi cikin dogon hijab tana sakkowa daga sama fuskar nan dauke da murmushinta mai kyau,

Gaban Mummy tazo ta tsuguna ta gaida ta,
dagota tayi cike da kissa ta rungumeta tace

"mun sameku lafiya?,

"lafiya lau Mummy,
ya hanya?

"Hanya ba daďi,
muje in huta sai inci abinci,

"Ki fara cin abincin Mummy,
Faidah ta faďi tana rike mata hannu,
kyafta mata Anty Radiya tayi wanda hakan yasa ta nufi gurin dining din ta zauna,

Zama Musaddiq yayi a gefenta ranshi wasai dan yasan Mummy zata ji daďin girkin matarshi wanda saida aka kai ruwa rana kafin su barta ta shiga tayi,

Kamshin da ya karaďe gurin ya sanya Mummy faďin

"Mmmm Masha Allah,
nayi missing abincinki Nadeeyah,

Murmushin jin dadin kalaman Mummy tayi,
duk wani bacin rai taji ya gushe cikin zuciyarta,

"Shinkafa zakici ko tuwo?
Faida ta tambaya tana bude warmers din,

"Saka min tuwon,

Malmala biyu ta zuba mata sannan ta bude miyar ta fara karto kasan da serving spoon tana zubawa,

Kallon kallo Radiya da Raudha sukayi wa juna,

Kafin suyi magana Mummy tace
"samin naman mana,

"Babu a cikin nan,
saidai ko a stew,
bude stew din Faidah tayi ta fara zakulowa nan ma ba nama,

Hankalin Nadeeyah ba karamin tashi yayi ba, dan tasan tayi miya da naman saniya, ganda da na kaza,

Wata siririyar ganda Faida ta dauko cikin stew din tace
"luckily an samu bpomo...

Jan kujerar Mummy tayi ta mike haďe da cewa
"Nagode, yunwar ma bata dameni ba,

Faidah zo ki siyo min Nama a waje,
tana kaiwa nan tace
"ina ne dakin da zan kwana?

Ko akwai BQ,
in akwai a kaini can in yaso da safe sai in nemi hotel kar in takura ma little da Amaryarshi... ta karashe dauke da murmushi a kan fuskarta,

"Wallahi ke da gidan danki babu abinda zaisa ki kama hotel,
Raudha ta faďi tana hararar Nadeeyah da Musaddiq,

"In ba rashin sanin darajar na gaba ba, ki dauko tafiya tun daga kaduna har nan amma ki tarar da abinci lami,
tsiyar ýaýan talakawa kenan, basu san inda suke nuna makonsu da tattalinsu ba,
Allah ya kyauta,

Hannun Mummy Radiya ta kama tace
"yi hakuri Mummy,
muje sama ki huta,
yanzu zan miki farfesu,

"a'a karku damu,
kuyi mata uzuri,
inaga ko taga naman ba yawa ne,

Gaban Nadeeyah taje wacce tuni hawaye ya jika gaban hijab dinta tace
"daina kuka yar albarka,
in banci nama yau ba gobe zanci,

Sake sunkuyar da kai Nadeeyah tayi tana jin wani irin zafi a cikin ranta kamar zata mutu,
tana jin su sunata maganganu har suka haura sama..

Kallon Musaddiq tayi wanda shi din ma ita yake kallo idanuwanshi jajur,
ya rasa inda zaisa abun da idonshi ya gane mishi yau,
ya jira ta kare kanta amma baiji ko kalma ďaya daga gareta ba,

Ashe haka kike?
Shine tambayar da zuciyarshi takewa tata,

Bai taba tunanin rashin girmama mahaifiyarshi har ya kai haka a gurinta ba,

ganin irin kallon tuhumar da yake mata ne ya sanyata takowa inda yake,
tsananta kukanta tayi wanda a lokacin ya ke ganinshi kamar na raini,
dan tasan baya son yaga hawayenta,

"ka yar-----

"Plss Nadeeyah ya katseta haďe da ďaga mata hannu,

juyawa tayi ta ruga daki da gudu tana kuka mai sauti sosai,
tana ganin sanda suka arta ciki a guje suna dariya...

Waiii...
lallai Faidah akwai kaifin tunani,
dama tace ke kadai ce zaiga an taba ya hassala,

Shhhhh....
Faida tace haďe da rage murya,

"bazamu taba kuskuren maida maganar nan ba sai ranar da aiki ya cika,
mistake kadan na iya watsa efforts din mu,

Bakinsu suka kama sukayi gumm suka cigaba da zaman tagumi suna jiran shigowar Musaddiq....

Sosai suka ingiza zuciyarshi, Mummy na tausarsu tana hawayen munafurci tace

"Ni ban san me nayi ma Nadeeyah ba,
iya kauna na nuna mata,
kowa yasan ajizancin dan adam ai, da sai tazo ta bani hakuri....

Naman da ya siyo ya ajiye mata ya tashi ya fita rai a bace najin har lokacin bata je ta bawa Mummy hakuri ba...

Koda ya shiga dakin kasa yi mata magana yayi ya faďa bayi dan watsa ruwa,

Kukan ta da yake ji har cikin bayin shi ya sake dungunzuma zuciyarshi,
"ita dadi ne ma yayi mata yawa,
ita ce tayi laifi kuma itace ta ke kuka,
yana fitowa ya sanya kaya ya dauki pillow ya kwanta akan kujera haďe da toshe kunnuwanshi,

Tafi awa tana kuka bai kulata ba, shima yin na zuci yake,

Ita kadai ce a duk duniya zatayi mishi abin da tayi ya kyaleta,
duk rashin fushinshi yakan yi action akan mahaifiyarshi dan yana matukar kaunarta kamar yadda take kaunarshi,,

Da yaji kukan yaki karewa ya mike ya dawo inda take,

"Ko zaki je daga waje kiyi kukan?
kinsan in dadi yayi maka yawa babu abinda bazakayi ba!

Kalamanshi sun sosa mata rai sosai tace

"Ka sakeni sai in tafi can wani guri inyi kuka na,

Kanshi ya juyar gefe zuciyar mai hakuri ta baci matuka,
murya a kausashe yace

"Sau biyu kenan kina furta min wannan kalmar,
dan kinga ina sonki, kuma kina ganin bazan iya rabuwa dake ba shiyasa kike threatnn dina da ita ko?

Cikin kuka sosai tace

"Ni dai bazan iya ba,
gara kawai mu rabu ko----

Wani mugun mari ya ďauketa dashi haďe da shake wuyanta,

"Gara in kashe ki nima in mutu da kalmar da kike son kasheni da ita,
samm baya ko ganin yadda ta rike hannunshi tana kakari saboda yadda idonshi ya rufe da bacin rai da hawaye,

Saida yaji tana wani irin kuka kamar mage tasha damka sannan ne jikinshi yayi sanyi ya saketa ya zauna a gurin yana rusa kuka,

"why did u want to lv me,
why?
Meyasa kike son gasgata mafarkina?

Duk da wuyanta na mata makaki hakan bai hanata sakkowa inda yake ba,

Tasan bata kyauta ba,
duk dan halak hakan zaiyi in yaga abun da ya faru yau,

wani ma zaiyi fin hakan,

Cikin jikinshi ta shige kamar mage ta kwanta haďe da rungumo wuyanshi tace
"am so sorry,
dan Allah ka yafe min,

Wata irin runguma yayi mata kamar zai maida ita cikinshi yace

"Dan Allah karki rabu dani,
no matter how hard tins are plss my love,

bata bashi amsa ba tayi kokarin sanya bakinta cikin nashi dan ta kwantar mishi da hankali...

A wannan daren da su Mummy ke kwance cikin farin cikin fara samun nasara,
a wannan daren su kuma ma'auratan suka sake samun shakuwa mai karfi a tsakaninsu,
wanda suke ganin in har wani abu yayi sanadiyyar rabuwarsu to fa zasu iya rasa rayuwarsu.......

Washe gari tun shida na asuba Nadeeyah ta shirya ma Mummy breakfast mai rai da lafiya haďe da farfesun kaza,

A kofar kitchen din ya tsaya yana kallonta cike da shauki,
sai a lokacin ya sake tabbatar da jiya matsala aka samu,

Haďe komai tayi cikin warmers, tana wanke hannunta taji ya kwanto ta bayanta,
murmushi tayi tace

"yauwa plss ka siyo kunun tsamiya sai a dama ma Mummy, kasan tana son karyawa dashi,

Lumshe idanuwanshi yayi yace
"nooo muje ki huta,
gobe sai kiyi mata kunun,

gyaďa kanta tayi tace

"ko dai kaima yunwar kake ji?
daukarta yayi yace
"sosai ma,
amma kinsan bana karyawa da wuri,

"Daukata baya maka wuya,
abinci zan fara ci inyi adding weight in ka daukeni kayi ta nishi, dan Allah ka saukeni kar wani ya fito ya ganmu,
tafiya ya fara yi yace
"in an ganmu ai da matata aka ganni,
ni bacci nakeji,
muje ki tayani,

Sun kusa step din karshe Mummy ta fito daga ďakin da ta kwana,
kokarin sauka Nadeeyah tayi ya sake riketa yana dariya,

"Wai kunyar ki take ji!

runtse ido Nadeeyah tayi tace

"Dan Allah ka saukeni,
a hankali ya sauketa yace
"Good morning maa,

Cike da danniyar maida danta bawa da taga Nadeeyah tayi tace "morning my dear,

"Ina kwana Mummy,
Nadeeyah ta faďi bayan ta tsuguna kasa,

"lafiya kalau Nadeeyah, ya gajiyarki,

"babu gajiya Mummy,
ga breakfast can ko nan zan hawo miki dashi,

"a'a barshi a can,
zan fi jin dadin karin a can,

Gefe suka matsa dan bata guri, ta wuce tana tunanin ta inda zata sake bullo musu,

ya zame mata dole tayi abun da zatayi yau zuwa gobe dan jibi zata wuce......

Ranar throughout Nadeeyah bata basu wata kofar da zasuyi complain ba,
kome zatayi a tsantsane take yinshi saboda bata san abin da zai kara sanya mijinta cikin bacin rai,
duk yadda Faida taso provoking dinta taki yarda ta kulata dan bata da lokacinta,

Cikin dare suka tashi suka shirya kulle kullensu,
sannan daga can wani bangaren da basu masaniya ana taimaka wa aikinsu.....

*(Kana Bacci ana maka nasari)*

Mrs Tijjani Shattima.....
[22/04 8:08 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣2⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Kamar kullum yau ma tun uku saura ta farka dan yin sallar Nafila,
wata iriyar kasala ce ta sauko mata wacce ta hanata barin kan gadon,
zaune tayi tana gyangyadi har huďu ta gota,
da ta gaji da gyangyaďin sai ta ja pillow ta kwanta riris,
bacci mai nauyi yayi gaba da ita...

A kunnenta aka sallame sallah a masallacin kusa dasu,
mikewa tayi jiki ba kwari ta nufi bayi dan yin alwala,

sai da tayi minti goma akan toilet tana bacci sannan ta buďe ido da kyar tayi tsarki ta mike ta kunna pampo tayi alwala kamar me tsoron taba ruwan,
koda ta fito daga bayin zama tayi a kan kujera tana tuno mafarkin da tayi wanda ya kashe mata jiki matuka,
mafarkin ya taba ta sosai dan a iya saninta mafarkin dariya bai taba zama alkhairi ga mai yinshi, bare ita da taga dukkan wadanda suke nuna mata kiyayya kewaye da ita suna kuka ita kuma tana tsakiya tana kyakyata musu dariya mai sauti harda kaiwa kasa,
gefe kuma Musaddiq na zaune shima dariyar yakeyi yana kurbar juice,
dariyar da sukayi a cikin mafarkin kamar wadanda aka saukar musu da wahayin yinta, haka kukan da su Mummy keyi kamar wadanda suka rasa wani sashi na jikinsu,
Chapter 79 · 0% Book details