← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 113

Sashe 36

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A da zuwa aji yana mishi wuya saboda samm teaching ba layin shi bane,
matsa mishi mahaifiyarshi tayi akan lallai sai ya kula da makarantar,
ganin ya raina turancin malaman yasa shi daukar literature dan yara su samu ingantaccen turanci da kuma sannin yadda zasu kirkiri wani abu kamar labari domin dogaro da kansu,
goma saura minti biyar ya cire medicated glass dinshi ya goge shi sosai, ya maida idonshi, kwantaccen sajenshi ya shafa da hannu hade da gyara zaman hularshi,
danyen voile ne a jikinshi baki wanda ya amshi farar kyakykyawar fatarshi,
fuskar nan tashi sai kyalli takeyi, Allah ya bashi wani irin sirrin kyau da ido mai narkar da zuciyar mata,
duk wanda ya ganshi zai iya sanyashi a jerin yan 30's saboda jikinshi yayi daidai da shekarunshi,
har ya kusa fita ya juyo ya dauki script dinsu na second term c.a test,
arranging dinsu yayi, yasa nata ya zama na karshe,
da gangan yayi failing dinta a script domin yaga yadda zatayi, amma a record dinta ya bata full marks din da taci,  yana dosar class dinsu  hanyoyin sadarwa na jikinshi suka fara charge,
ganin fuskarta kadai kan sanyashi manta ko shi wanene,

wani irin so yake mata marar fasaltuwa,
tun daga nesa Sabrinah ta hangoshi ta fito da sauri ta karbi takardun hannunshi,
gaisheshi tayi cike da kwarkwasa tana shishshige mishi,
dan sauri ya kara yi yana amsata cike da basarwa,

Bayan ya amsa gaisuwar yan ajin idonshi ya sauka gurin sit dinta,
ba yadda ya saba ganin ta ya ganta ba,
nan zuciyarshi ta shiga damuwa, yaso ta'allaka yanayinta da lokacin sanyi ne ya sanyata labta mai a fuska, ta kuma kunshe kanta kamar mara lafiya,
a gurguje ya dan yi musu bayani akan topic din da yazo musu dashi,
yana gamawa ya fito da script din ya fara rabawa,
wasu suyi murna wasu su kunshe abin su,
saida ya gama da kowa sannan ya kira sunan Nadeeyah,
kamar mai tausayin kasa ta fito ta karba,
tana budewa taga 10 duk sauran zeros,
kallon shi tayi idonta ya fada cikin nashi saboda tunda ya bata bai dauke idonshi a kanta ba,
kauda idonta da yayi narai narai tayi,
nan take kwalla suka ciko su, kafin ta karasa gurin zamanta ta fashe da kuka marar sauti,
har lokacin idonshi na kanta, ganin hawayenta ne ya sanyashi daburcewa,
A dan ya fara magana yana yabawa da kokarinsu,
sannan yace duk wanda yaga ba'a mishi marking daidai ba ya sameshi a office,
yana cikin class din aka buga karrawar break,
permission ya basu na kowa ya je yai break,
takardu ya fara hadawa yana kallon su ta cikin glass dinshi, Amal na karbar script din tana fisgewa,
fita yayi a ajin yasan dole in ta duba ta sameshi a office..

Babu yadda su Amal basuyi da ita akan taje ta nuna mishi baiyi mata marking wasu guri ba tak'i,
tace musu babu mamaki shi din yaga banyi daidai bane shiyasa,
zan dage a exams,
cike da masifa Haifa ta fisge takardar tace "ni bari in kai mishi,
sai shegen hakuri kamar damo, an fada miki ana hakuri da marks ne,
bayanta Amal tabi tace " muje wallahi,
sai ya gyara mata,

kwala musu kira Sabrinah tayi da karfi,
tana haki ta karaso gurinsu da yoghurt da bons a hannunta,

karbar script din tayi tace "ku koma class in kai mishi, may be marking ya mishi yawa ne bai gani ba,
da kamar su karba sai suka ga itace class rep dinsu suka bar mata hade da nuna mata gurin da tayi daidai..

Excuse sir..,
bai dago kanshi daga kasa ba yace yes come in,
da sauri ta shiga ta tsaya a gaban table dinshi,
tsaki yayi a hankali da yayi gamo da Sabrinah, "lafiya, ya tambaya hade da mikewa kamar yana neman abu,
makale murya tayi tace "Sir akwai script din da bakayi marking daidai ba,
yarinyar tana can tana ta kuka, kuma ta san ta amsa daidai,
murtuke fuska yayi yace "script dinki ne?
Girgiza kai tayi tace "nooo na Nadeeyah Adam ne,
zama yayi yace "ajiye takardar anan kije ki kirata tunda she is sure of wat she wrote,
ajiyewa Sabrinah tayi ta fita tana girgiza ko ina na jikinta,
ita dai Allah ya daura mata son Tahir,
kasancewarsu makota yasa tare suke zuwa makaranta,
komawa ne ba tare ba saboda baya tashi da wuri,
ya dade da harbo jirginta shiyasa ya kama kanshi dan samm baya san macce mara kamun kai a cikin maza,
ita kuwa Sabrinah ko wani namiji a school din yasanta saboda tsananin kyawunta da rawar kanta....

Tirjewa Nadeeyah tayi tace ita Allah ya kashe ta baza taje ba, zata dage a exams,
bazata iya zuwa office dinshi yana kallonta dayday yana wulakantar da ita ba,
ga turancinshi ya mata tsauri bama ta gane abin da ya ke cewa,
haka nan su Haifa suka hakura sukayi banza da ita su a dole sunyi fushi,
har aka tashi a gida basu kalleta ba,
kamar bakinsu na ciwo suka ce "Nadeeyah sai gobe Allah ya kara sauki,
share majinar hancinta tayi tace "kuyi hakuri ku fahimceni,
basu ko tsaya saurararta ba suka fita,
school bag dinta ta rataya ta fito itama,
a gurin sauka kasa ta hadu da Husna,
riko hannunta tayi tace "ya muran kin dan ji saukinta,
gyada kai Nadeeya tayi tace "da sauki,

muje mu jira malam Ali ya dawo daga kai Badar,
walhi yau muna zuwa gida zan fadawa mummy duk abin da Badar ke miki,
yanzu ki dubi yadda sanyi yayi miki mugun kamu,
saboda tsabar bakin hali duk ta jike bargon da kike rufa,
ni na rasa irin halinta, yanzu dole saboda mugunta kullum sai mun jira an kaita a dawo a dauke mu,
ko tausayin malam Ali batayi,

murmushi Nadeeyah tayi tace "kiyi hakuri karki fada, wata rana sai labari,
babu abin da bai wucewa a rayuwa,
muje school shop in samu tom tom insha,
suna isa Husna ta siyan mata tom tom ta hada mata da biscuit da maltina mara sanyi,
nasan baki fita break ba,
muje mu zauna a can in kin gama sai mu koma gate...

Tun yana kallon kofar shigowa har ya gaji ya dubi agogo yaga lokacin tashi yayi,
tsaki yaja ya mike ya kashe komai na office dinshi,
yasan bazata zo ba,
a ganinshi tafi karfin tazo tayi rokon cewa tayi daidai ne,
rai a bace ya dauki mukullin mota hade da rataya jakar laptop dinshi ya fita daga office din,
jiki a sanyaye ya tada motar ya fara tafiya a hankali,
yarinyar nan tane neman zame ma zuciyarshi damuwa,

yana gab da fita gate din ya hangosu,
atishawa take yi a jere masu zafi, nan idonta ya kada yayi jajur hade da fitar ruwa,
daidai inda suke yayi parking, sauke glass yayi yana jiyo Husna na fadin "wani irin lalacewa kuma malam Ali,
haba dan Allah, kasan Nadeeyah ba lafiya gareta ba,
ga rana gashi babu motar haya, dan Allah ka koma gida ka karbi mukullin motar Mummy,
rai a bace ta kashe wayar tana ma Nadeeyah sannu,,
baisan sunan Husna ba saboda bai daukarsu komai,
yadai san Badar saboda rashin mutuncinta ga dalibai ana yawan kawo kararta, kuma yasan gidansu daya,

"Hey Kyari,
babu wanda baisan muryarshi ba kaf cikin makarantar,
da sauri ta iso gurinshi tace "Yes sir, Good afternoon! "Hw u ya fadi yana unlocking motar hade da cewa "baku wuce gida ba?
yamutsa fuska tayi tace "driver yaje kai Badar on his way back motar ta lalace, yanzu dole mu jira shi ya koma gida ya dauko wata, and my sister is very sick,
saida takai aya sannan ya dauke idonshi a kan Nadeeyah yace "ayya sorry, Allah ya bata lafiya, kuzo muje in kaiku gida,
cike da murna Husna ta janyo Nadeeyah,
zasu shiga motar Nadeeya taja Hannun Husna, tace "in wani guri zashi fa,
ki kyaleshi mu jira malam Ali,
fisgewa Husnah tayi tace dalla shiga muje,
anan zaki zauna ciwon ya karu,
baya ta bude ta shiga hade da cewa "ina yini,
bai amsata ba yayi saurin rage A.cn motar hade da tada ta,
sunan unguwar ya tambaya, Husnah ta fada mishi harda adress,
duk yadda Nadeeyah ta kai ga matse atishawa abin yaci tura,
a jere ta dunga sakinsu,
ta mudubin gefe yaketa kallon yadda idonta yayi,

A lokacin in hankalinshi yayi dubu to duk sun tashi,
hanyar dialogue pharmacy ya dauka,
suna zuwa ya kalli Husna yace "ku jirani in siyo magani,
bai jira amsa ba ya fita,
magunguna ya siyo na mura kala kala kamar zai bude shagon su,
bayan ya biya kudin ne ya dubi yawan maganin,
sai a sannan ya fahimci yawansu, murmushi yayi yace "cire min wadanda suka fi kyau, emergency,
karba yaron yayi ya cire mishi masu kyau hade da rubuta yadda za'a sha su,
barin mishi sauran kudin yayi ya fito ya shiga motar,

Mikama Husnah maganin yayi, kafin yayi magana wayarshi ta fara ringing,
tada motar yayi ya daga wayar,
"Sweet heart,
kunya ce ta kama Nadeeyah tayi saurin kunshe bakinta,
hirarshi ya dinga yi yana fada mata yadda yayi missing dinta,
cike da shagwaba kamar bashi bane mai mugun tsare gida yace "yaushe zaki dawo, gidan is empty witout u darling,
basu jin abinda ake cewa a daya bangaren sai ji sukayi yace "Noo i won't accept that from u,
in baki dawo ba this week zan bar school ba kowa in biyo ki,
ita dai Husna burgeta yayi sosai na yadda yake kula da wacce ta kyautata zaton budurwarshi ce ko matarshi,
Chapter 36 · 0% Book details