← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 113

Sashe 35

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaye yake gaban class yana kallonsu daya bayan daya,
cikin harcen turanci yace "Ba tambayarku nakeyi ba,
kun shirya ma presentation and drama?,
groups biyu suka mike suka ce sun shirya,
sauran kuwa sukayi kwala kwala da ido,
group 3 and group 6 meye topics dinku, ya tambaya fuska a murtuke, "*PLAGIARISM* "Khalifa ya fadi hade da mika mishi printed papers din da suka hada,
kallon dayan group din yayi yace and you?
Cike da rawar jiki Sabrinah tace *DRAMA, FICTION AND IMITATION*,
hannu ya mika ya karbi nasu takardar sannan ya kalli sauran yan class din yace "Kowa yasan dis is your first CA test,
to yanzu saboda kun nuna you are not serious na maida shi first nd second and is over 40 no attendance marks,
yana kaiwa nan yace duk class din su tafi school Hall su jirashi yazo su fara presenting,
cike da tsoro sauran suka fara ihu suna fadin sorry sir,
wasu a cikinsu kuma suka tafi cafe dan shirya nasu ko baiyi yawan na sauran ba....

Karfe goma daidai group 3 suka fara presenting nasu,
cike da kwarewar turancinsu mai dadi na butters suka gabatar dashi,
saida suka gama tsaff kowa ya tafa musu harda observers,
Shirye shiryen na dramar group 6 suka fara,
saida suka kammala komai sannan suka fara presenting, definition din drama sukayi sai dan short fiction story of Beggars da illolin da irin wulakancin da mabarata ke fuskanta,
a karshen labarin ne suka ce "Yanzu zamu yi muku drama akan labarin da muka gabatar...

Nan jikin Nadeeyah ya fara rawa saboda tsoron turancinta ba irin nasu bane,

Sabrinah da Ishaq sune masu kudi,
sai Nadeeyah, Haifa, da Abdulhameed sune maroka,

Nadeeyah itace Makauniya tana rike da sanda,
sai Haifah kurmah,
Abdulhameed kuma gurgu,
cike da burgewa suka fara dramar akan stage,
da fari Nadeeya taji tsoro,
sai da Haifa tayi mata wuzuwuzu ta tunasar da ita marks din da zasu samu sannan ta saki jikinta,
da sanda take shafa kasa tana fadin "a taimaki almajira saboda Allah da Annabi,
cikin harshen turanci take magana ta karasa daidai inda Sabrinah da Ishaq suke zaune kan dadduma suna shan fruits ta tsaya,
"Hajiya a taimaka min da sadaka saboda Allah..
tsaki sabrinah tayi hade da daukar ayaba tace "Mabaratan nan sunyi yawa a kasar nan honey,
kuma mostly hausawa, kallon Nadeeyah tayi hade da watsa mata bawon ayaba ta cigaba da cewa "ku ko kunya ma bakwaji, da wannan barar da kukeyi ba gara kuje ku zauna a gida ku jira ranar mutuwarku ba tunda baku da amfani,
katseta Ishaq yayi yana murmushi ya daga malunmalun ya fito da dari biyar yace "sweetie,
in ba irinsu ta yaya zamu samu kudin,
Allah na bamu kudin ne dan ya turo su suzo su amsa,
yana mika mata kudin Abdulhameed da Haifa suka fito daga mabanbantan guri suna kokawar kwacewa,
ana haka har suka tura Nadeeyah jikin Sabrinah kamar yadda suka tsara a labarin,
Sabrinah na ganin haka ta mike hade da manta drama sukeyi ta tura Nadeeyah da iya karfinta,

ihu Nadeeya ta saki saboda kafarta daya ta sauka akan stage ta rinjayi dayar,
ga tsakanin stage da kasa akwai yar tazara,
runtse idonta tayi ta sadakar ko kafarta ta karye ko kuma ta samu mummunan rauni,

Bude idonta tayi da sauri saboda jinta hannun mutum da kuma jin bugun zuciyarshi alamar tsoro,

kallonshi tayi ta hango manyan idanuwanshi cikin farin glass sunki daukewa a kanta,
ajiyar zuciya tayi ta fara kokarin raba jikinta da nashi,
sai a sannan ya sauketa ya koma gurin da yake tsaye har lokacin zuciyarshi bugawa takeyi,

Husnah da Haifa ne sukayi saurin isowa gurinta suna mata sannu hade da hawa kan stage din inda Abdulhameed da Ishaq suke ta ma Sabrinah masifa,
itama jikinta yayi sanyi dan bata taba tunanin Nadeeyah zata fadi kasa ba,
hakuri Nadeeyah tabawa su Ishaq tace "mistake aka samu kun sani, kuma faduwar is part of the drama dan a nuna yadda mabaraci ke wulakanta,
in Allah yayi muna da rabon marks zamu samu koda 30 ne,

kalaman Nadeeyah sunyi matukar yin tasiri a zuciyar sabrinah,
nan take taji ta shiga ranta,
a zuciyarta tana auno da ita akayi wa haka da sai ta kusa yi ma mutum illa,
nan dai sauran groups din suka fara presenting nasu..

Kallonsu kawai yakeyi ba tare da yasan me suke cewa ba,
duk kakalen shi na lura da yadda suke fadin words a wannan lokacin bai bi ta kai ba,
hankalinshi kacokan ya tafi can wani guri na daban,
"Sir here is our presentation, Amal ta fadi hade da mika mishi papers din,
glass din idonshi ya cire ya share zufar fuskarshi yace "ku je ku kara shiryawa zuwa next week,
ki fada ma sauran groups din,
wani tsalle Amal tayi ta wuce da gudu tana announcing,
nan Hall din ya kaure da ihun maza da mata,
da ganin haka observers suka miko mishi takardu hade da mishi sallama suka fita...

"Uncle dafatan munci 40/40,
dago kanshi yayi da jin muryar Sabrinah,
papers ya fara hadawa yace "ko 20 baku kai ba bare kusa ran 30,
Nadeeyah da Haifah dake can nesa dashi gabansu ya fadi,
nan Haifa ta taho gurinshi da sauri tace "plss sir karka mana haka, plsss ta karashe kamar zatayi kuka,
gurin da Nadeeyah take tsaye ya kalla ya kula da yanayinta yace "minus 5,
hada baki sukayi suka ce "wayyo uncle,
"minus 2 ya sake fadi har lokacin idonshi na kan Nadeeyah,
a hankali ta fita daga Hall din dan kar ta cigaba da jin kayan takaici,
tasan kaddararsu ce haka,
in ba dagewa sukayi a exams ba dakyar zasu samu C,
ganin ta fita yasa shi fara tafiya yana fadin ko A kuka kara cewa sai nayi minusing,
yanzu dai kuna da 15/40,
gum sukayi suna binshi a baya fuska dauke da kukan shagwaba,
Bai ko kallesu har suka fita yayi hanyar office dinshi,
jin zuciyarshi yake ta mishi nauyi,
duk inda ya wuce yan mata sai sun gaishe shi cike da yanga,
ko kallansu bayayi bare ya amsa, shiyasa suka mishi lakabi da mai girman kai....

Kallon kwallon sukeyi Ruwaida na ihu tana fadin "wayyyo zata fita waje,
bin kwallon tayi da gudu tana nishin murna ganin ta sakko kasa, tana karasowa gurin taga kwallon a hannun Hafeez,
gurinshi ta iso cikin command tace "bani abuna!
Dariya yayi ya mika mata,
har ta fara tafiya ta waigo tace "gurin Yaya Jamal kazo ko,
to bayanan,
kaje can farm house ka sameshi,
yau dai bai zauna a gida ba bare ku hadu ku hanani mosti a gidanmu,
tana karashewa ta murguda mishi baki ta wuce,
bayanta ya bi yana dariya har taa kai inda Papy da mami suke zaune,
tun daga nesa Papy ya hangoshi suka sakarwa juna murmushi,
har kasa Hafeez ya tsuguna ya gaishesu,
cikin sakin fuska Mami ta amsa sannan ta mike dan bude musu parlon baki...

Hafeez ya ga karamci a gidan Alh Abdallah,
saida suka gama yar hira yaje ya gaida Anni sannan suka dawo parlon,
kallonshi Alh Abdallah yayi yace "Dafatan dai lafiya, naji kace kullum sai kazo office,
sosa keya Hafeez yayi yace "lafy kalau sir, kawai dama dan in gaisheka ne,
dadi Alhj Abdallah yaji yace "gaskiya ka kyauta, nima tun ranar da fara ganinka naji kamar akwai bond da ya hadamu,
saidai kuma ni---- katse maganar yayi hade da cewa Allah ne kadai ya hada jinina da naka,
dafatan zaka dunga zuwa kana gaishemu,
in shaa Allah Hafeez ya fadi bakinshi dake dauke da maganar da tayi mishi nauyin tambaya,

"a ina ka sauka ne? Papy ya kara jefo mishi tambaya,
cikin girmamawa Hafeez yace "ina hotel nan kusa da school, har yanzu ban samu daki ba, wadanda aka samu nesa da school ne sai kuma 2 bedroom ni kuma yayi min tsada da girma, amma ana cigaba da dubawa in an samu zan koma can,
gyara zama Alhj Abdallah yayi yace "zama a hotel ai kashe kudi ne,
in zaka yarda kuma zaka iya ka dawo nan gida akwai dakuna sai ka zauna har ka gama karatu,
cike da farin cikin karamcinsu yace "Nagode sosai sir,
Allah ya kara daukaka,
Ameen papy yace yana kokarin mikewa,
tabe baki Ruwaida tayi tace Papy ka fada mishi ni ce princess a gidan nan,
in yana son ya dawo sai ya yarda da bazai dinga min fada ba, kuma zai dinga kaini yawo kullum,
dariya sukayi Papy yace "ai shima ya sani, karki damu ranki ya dade,

sallama yayi ma su Mamy sannan ya wuce cike da farin ciki,
yasan yanzu ya zama kusa dasu zai samu cikakken labarinsu,
dan shi al'amarin kamannin suna rikita kwakwalwrshi, ace kamanni har a cikin 'ya'ya, abun yayi yawa.....

Mrs Tijjani Shattima....

[13/03 9:18 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣5⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Watanni biyar kenan ina dakon soyayyar dalibata,
dalibar da a kullum take kuka dani saboda tsauri na a gareta,
juyi yayi akan kujerar da yake zaune bayan ya gama furta wadannan kalaman,
agogon office dinshi ya kalla yaga sam baya mishi gudu,
ya kosa goma tayi yaje ajinsu,
Chapter 35 · 0% Book details