← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 113

Sashe 9

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dafa papa hinad tayi tace "shi da uncle ne papa ba fada bane,
Wani abu ke faruwa a can gida naji Ya kira Sunan NADIYA,

ajiye wayar yayi kan stool Ya Kalli hilal da idanuwanshi da farar fuskarshi sukayi jawur Saboda bacin ran rashin amsashin da musaddiq yayi,
burinshi a wannan lokacin ya ganshi a Nigeria,

cikin taushi papa yace "wacece nadiya?

Inajin Nadiyar mamma suwaiba, Hinad ta bashi amsa,,
dafashi papa yayi yace "me Ya sameta?

Kamar jira yake "yace Nima bansani ba papa, Musaddiq Yaki fadamin, kamar accident ne!

subhanallahi papa ya fadi Yana mai daukar wayar da niyyar sake kiran musaddiq,
Ya kira Yafi sau shurin masaki babu amsa,

A bangaren musaddiq kuwa tunda Ya saki wayar a kasa Ko takalmin da Ya cire bai sa ba ya fita Ya nufi inda suke,
masifa Mahmoud ke mata kamar zai duketa,
kuka sosai takeyi tana bashi hakuri,

Nadiya!!!

Ya kira sunanta a can karkashin makoshi, dago kanta tayi ta kalleshi,
bata gane muryarshi ba Kuma bata ganinshi Saboda duhun dake gurin!

a kufule Mahmoud yace ka Santa ne?

Hannunta Ya kamo ya fara tafiya ba tare da Ya ba Mahmoud amsa ba,

kuka mai karfi Nadiya ta saki tana fadin Dan Allah kuyi hakuri wallahi ban san--- shhhh Musaddiq ya katseta hade da daura lallausan hannunshi kan labbanta,
hasken motar da ta gifta Su ne Ya bayyana mata fuskarshi,
langwabar da kanta tayi hade da sakin doguwar ajiyar zuciya mai hade da shashsheka,
hawayen dake fitowa a idanunta Ya shiga share mata da yatsun hannunshi,
daga ina kike??
Ya tambayeta Yana mai bude bayan motar,

cikin kuka tace "Baba, Baba--bashi da lafiya dan Allah yaya Musaddiq ka taimakemu kar Ya mutu,
ba musaddiq ba har Mahmoud dake kufule sai da Ya tausaya mata,
shiga ciki muje da sauri Musaddiq ya fadi yana gyara hannun kofar,
a gaggauce ta shiga,
Gudu Mahmoud keyi kamar zai tashi sama, a dai dai kofar gidan yayi parking,
A tare suka shiga gidan da sauri, dakin da yake suka nufa,
inda ta barshi a nan ta sameshi, sai dai wannan karan idanuwanshi a rufe suke kamar me bacci, murmushi tayi tace "Alhamdullilah kun ga ya samu bacci,

kusa da mamma ta matsa wacce ke jingine jikin gadon kamar mutum mutumi,
"ya samu bacci ko Mamma? Na tsorata sosai na fita babu Ko takalmi,
a hanya na hadu da Su yaya musaddiq, gasu nan ku gaisa sai ki tashi Baba mu kaishi asibiti,

"He is no more fa KYARI, Mahmoud yayi mishi rada a kunne..
Rawa jikin musaddiq ya fara yi Yayi saurin matsawa kusa dasu Nadiya, dafa Mamma yayi hannu na rawa Saboda firgici da tausayin rai,

suuuu suka ga ta fadi kasa babu alamar numfashi,
Innalillahi Wa Inna ilaihir rajiun Mahmoud ke maimatawa Saboda tsananin tashin hankali,
Wani irin kuka Nadiya da musaddiq suka saki a tare,
jijjigata Nadiya keyi tana kiran sunanta, komawa jikin Babansu tayi tana tashinshi, Baba ka tashi kaga Mamma, me Ya sameta,

waje musaddiq ya fita da gudu Yana kuka kamar ba namiji ba,
Mahmoud ne yayi karfin halin dagata Yana mata nasiha,
fisgewa tayi ta kwanta kan mamma tana ihun kuka mai Sosa zuciya, "nasiha bata da muhalli a wannan lokacin, (Allah da Kuma Wanda abun Ya faru dashi ne kadai suka San irin halin radadin da mutum yake ciki a wannan lokacin)..

zubar da ruwan hawayenta keyi a fuskar mamma Ya fara farfado da ita daga doguwar sumar shock din da shiga,
motsin da nadiya taji ne Ya sata mikewa da sauri tana kallonta, dagota tayi tana kiran sunanta da karfi tana dariyar farin ciki,
tsugunawa Mahmoud yayi ya rike kanta yace "jeki maza ki debo ruwa, a guje ta fita ta nufi ma'ajiyar ruwan Su ta dibo cikin kwanon sha,
tare suka dawo da Musaddiq da idanuwanshi sukayi jawur saboda kuka,
a hankali Mahmoud Ya debi ruwan a hannunshi ya shafa mata a fuskarta hade da tofa mata adduo'i,  ajiyar zuciya ta saki Mai karfi ta fara binsu da idanu,
tana sauke idonta kan Nadiya ta fashe da kuka Marar sauti,
kukan da idan ka ga mai yinshi sai dukkan gabban jikinka sun saki saboda tsabar tausayi,
rungumeta Nadiya tayi suka cigaba da kukan tare,
Mahmoud ne kadai yayi karfin halin tashi ya rufe Baba da zani sannan Ya dawo Ya dafa Musaddiq yace "Tashi muje mu sanar da mutane a gaggauta Yi mishi sutura kafin safiya,

Mikewa yayi yana share idonshi da bayan hannunshi kamar karamin yaro sukayi waje suna jiyo kukan Nadeeyah kamar ranta zai fita...

Nayi tarayya da mutane da dama tun tasowa ta har kawo wannan lokacin,
na hadu da mutane masu hali na Kwarai haka na hadu da marasa kirki Kwarai dagaske,
a cikin yawon da nayi kasashen duniya da cikin kasarmu ta Nigeria ban taba haduwa da mutum Marar imani da kirki Wanda babu abinda ya sani Sai kansa ba irinki ki!
dole ne yau in fitar da abin da yake raina, BAKI DA IMANI Badariyya,
ki guji bakin duniya, ke ko babu baki ki guji rayuwar ita kanta, ganinki kikayi a inuwata shiyasa kike yin San ran-------- Tabdijam lahaulu Wa la quwwata,
Alhaji!!!
Ashe da raina zanji batun gori Ya shiga tsakaninka da jinina,
Gori kuma???
Daddy ya furta yana kallon mummy da ta rike hab'a tana mishi kallon raini,
kuka Badariyya ta fashe da shi tayi hanyar da mummy ta fito ta rungumeta, shafa bayanta ta shiga Yi tace "Gori mana Alhaji, har nawa Badariyya take da zaka kira ta da Marar imani? Har kana furta tana zaune a karkashin inuwarka,
wallhy ko a mafarki ban taba kawo zakayi tunanin goranta ma Badariyya ba, Sai gashi yau a zahiri naga wannan bakar rana,

mtswwwwwww...
Daddy yaja dogon tsaki yace "Na goranta mata,
indai Badariyya bazata canza halinta ba wallahi ba gori ba wata rana Kiri Kiri zan nuna ba n------ katse Maganar yayi dan baiga amfanin furta ta ba, Ya cigaba da fadin Kinsan abinda tayi ne, in har kikaji abinda tayi ko ke sai kin kirata da fin kalmar Marar imani,
nan ya kwashe duk yadda ya ji sunyi da Nadiya ya fada mata,
ya cigaba da fadin kafin in sako riga in fito Yarinyar nan ta Koreta Koda na fita banga Hanyar da ta bi ba,
Abin da yafi bani tsananin takaici nayi Allah wadai da ZUMUNCIN ZAMANI bai wuce rashin sanin gidan su Suwaiba ba,
kaii Innalillahi Wa inna ilaihir, Allah Ya rangwanta musu daddy ya karashe hannunsa duk biyu dafe a kanshi,
duk rashin imanin Mummy saida jikinta yayi sanyi saboda Jini ba wasa bane,
sakin Badariyya tayi tace "Baki kyauta ba Badar, Dan Allah Karki sake kinji rashin lafiya yafi gaban wasa kinji, gyada Kai Badariyya tayi tana turo baki,
shafa kanta tayi ta nufi Daddy tace tashi muje in rakaka gidan Sai mu kaishi asibiti,

SAI DAI KU KAISHI MAQABARTA, GIDA, KUMA DAKINSHI NA GASKIYA, DAKIN DA DUK MAI RAI SAI YA SHIGE SHI.... Muryar da basu tsammace ta a daren ba suka jiyo daga bakin kofa....

In shaa Allah koda 700words ne a rana zaku dinga samu, in banyi ba to ayi min uzuri, yau da gobe Sai Allah...
Ina matukar kaunarku Sosai Sosai fa.. Allah Ya hadamu a aljanna firdaus...

My world of hausa novel 1/2 (wohn)  I just can't do without you...

Mrs Tijjani Shattima......
[04/12 09:48] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u kurah
1⃣4⃣

A tare suka waigo da sauri, murmushin farin ciki da shaukin murnar jiyo muryar sanyin idanuwansu ya dauke  saboda ganin yanayinshi,,

mummy ce ta fara isa gareshi ta amshi rigar daya daura a kafada tace "daga ina kake?
Yaushe ka shigo kasar?
Kaga yadda ka zama kuwa!! ta karashe tana mai tallabo fuskarshi,
Hannuwanta Ya cire a fuskarshi Ya fara jan kafarshi a hankali har ya isa gurin mahaifin shi..

"Daddy dan Allah ka taimaka ka dauki liman muje ayi ma Mijin mama Suwaiba sutura..
hannu Daddy yasa Ya share hawaye dake kwance kan fuskar Musaddiq yace "basai ka roke ni ba little yanzu kuwa zamu tafi, Kai dai calm yourself kaje kayi Wanka ka huta Kaji,
girgiza kanshi yayi yace "muje tare daddy bazan iya zama a gida ba daren zaiyi min tsawo,,

Lallausan hannu yaji cikin hannunshi murya can kasa ta marairaice tace "Haba yaya little, dawowarka kenan fa Ya kamata ka huta Kaci abinci sauran abubuwa Sai su biyo baya, kaga Daddy zai tafi Kuma kaima daga can kake,,

yar kara ta saki saboda yadda yayi wurgi da hannunta gefe,
  a da yana tunanin halin Badariyya yarinta ne,
yanzu kam ya tabbatar wa da kanshi Sam Badariyya bata da zuciyar mutane, babu abinda zai iya canza ta, bata da halin gara a cikin halayenta,
tsaki Ya saki Mai karfi hade da galla mata hararar Kyama sannan Ya maida kanshi gurin Daddy yace
"muje Daddy,
mukullin mota daddy zai dauka Musaddiq yace "Mahmoud na waje tare muke dashi muje a motarshi, 
fita sukayi mummy ta Yi Saurin shiga daki ta dauko hijab tabi bayansu...

Limamin massalacin gidanshi suka dauko wanda ya fito da likkafanin da baya rabo dashi, da kuma abin gwajin tsaho..

Koda suka isa babu Kowa a kofar gidan,
a ciki ne suka ga mata hudu makotansu da mazajensu wadanda kukan Nadeeyah ya   iske kunnuwansu  a hanyarsu ta dawowa daga majalisar dare,

Nan take liman yayi gwaje gwajen da zaiyi, Ya baiwa Mahmoud Ya tafi ya kai gurin tela,

malam Sada tela yayi Saurin karbar likkafanin da gwajin yace "bari inyi Saurin dinkawa tunda nan kusa muke,

Cikin awa daya aka Yi ma 'Malam Adamu' sutura aka feshe shi da turaren Musaddiq dake cikin kayanshi na motar Mahmoud,

Adduo'i suka shiga jero mishi na neman yafiyar ubangiji da samun rahama,
Sai da suka idar sannan suka Yi ma mamma gaisuwa da sallama hade da fadin sai zuwa safiya zasu dawo a kaishi,,
gyada Kai Kawai takeyi idanuwanta na ambaliyar hawaye, 
waje suka fita dukkaninsu Mazan, suna fadin halin Kwarai irin na malam Adamu, da irin hakurin da yayi na rayuwar talauci,
Chapter 9 · 0% Book details