← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 113

Sashe 10

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy da Musaddiq kadai aka bari a cikin gidan,
duk yadda mummy takai ga kyankyamin talaucin yar uwarta Sai da ta tausaya mata saboda yadda rai yake da alfarma,
  A zuciyarta fadi Kawai takeyi "INA MA NA TAIMAKI ADAMU LOKACIN DA YAKE DA RAI" dana sani Marar amfani mummy ta dingayi wanda hakan yake ga Kowa lokacin da zafin mutuwa ke ratsasu... ( MU TAIMAKI YAN UWAN MU KAR MU BARI SU TAFI SU BARMU DA DANA SANIN DA BAZAI AMFANE MU BA, MU KYAUTATA MU'AMALAR MU DA MAKUSANTANMU KAR MU YARDA MU RASA SU MUNA MASU DANA SANI,
MUTUWA BATA BADA NOTICE BARE MUCE ZAMU JIRA LOKACI YAYI MU KYAUTATAWA JAMA'A).

Ana idar da sallar asuba Baffa da Goggo suka iso, tun daren mummy keta neman numbersu a kashe,
tare suka iso da su mummy da suka koma gida tun dare,

A inda mummy ta tafi tabar mamma da Nadiya nan ta samesu,
Nadiya ta tura kanta cikin cinyoyinta hawaye Ya jika rigar jikinta har yana diga,

kuka Baffa ya fashe dashi a can cikin zuciyarsa yana jin tsanar kanshi na rashin taimaka musun da baiyi ba,
cikin muryar kuka yace "Wayyo Adamu ashe mutuwa zakayi,
ina ma jiyan da Nadiya tazo na biyota mun kaika asibitin,
walhi bani da masaniyar ciwon yayi zafi haka, shiyasa na turota gidanku dan Nasan can akwai direbobi komi dare,

wani sabon kukan takaici ne Ya kufce ma Nadiya,

Musaddiq da Daddy kuwa waje suka fita saboda takaici,
anan ne Musaddiq ya kwashe duk yadda Zumuncin nasu Ya kasance wanda sani tun tasowarsa Ya fada wa daddy,
cike da mamaki daddy yace "yanzu duk kudin zakkar da nake bawa Mahaifiyar ku ta bawa Suwaiba bata bata, 
Musaddiq yace "wallahi ba'a bata, na dai San ana bata dubu biyar duk shekara,
Ya Kara da bashi Labarin abinda ya faru kafin Ya tafi Cyprus,
girgiza Kai daddy ya shiga Yi cike da takaicin halin dangin matarshi...

Ohhh Ho Ho!!
wai waye ne keta damunka da wannan sanyin safiyar,

Tsaki taja ta daga kanta a kan kirjinshi ta mika hannu ta miko mishi wayar, 
Sai da ta dauka saboda ganin bakuwar number a zatonta mace ce, 
jin muryar Namiji yasa ta mika mishi wayar ta Mike ta nufi toilet dan yin wanka,
karawa yayi a kunne cikin magagin bacci yace
"Waye ne,
Hafizu ni ne, 'Garba kero' ne,
  Allah yayi ma mahaifinka rasuwa cikin dare,
Nima yanzu labari Ya iske ni,

A gigice Hafiz ya Mike daga luntsumamman gadon da yake kwance,
"kero bansan iskanci kana jina,! in dai so kukeyi kusan inda nake to kuzo ina nan a AYALLA HOTEL Area 11 Abuja,
Kazo yau zan baka kudin da ka tambayeni, amma ka daina Yi min wasan mutuwa akan iyaye na,

Tsaki kero yayi hade da hadiye yawun bakin shi yace "in kaga dama  daga nan ka wuce ROCK VIEW, damuwarka ce, bana bukatar kudinka yanzu, saboda ina neman na kaina Kuma ina tafe da albarkar iyaye,
Kuma kasan, Ni ba mahaukaci bane da zanyi maka karyar rasuwa, mahaifinka Allah Ya karbi abinshi,
kana iya zuwa in kaga dama, in kuma babu dama to kana iya tura mishi da addua dan dama zuwanka bazai maido shi ba, yaja tsaki ya kashe wayar cike da takaicin halin son kai irin na Hafeez, (Dama Halin mutum na Kwarai ko kirki baya bayyana Sai yayi arziki)....

Jiki na rawa Hafeez ya Mike, Ya dauki riga Ya sawa jikinshi, ko jiran farkarshi baiyi ba yayi waje yana jiyo muryarta tana kwala ihun kiranshi,
inaaa bai ko waigo ba bare yayi tunanin komawa dakin Ya sallameta,

Motarshi Henesy ya shiga ya tayar Ya fara gudun fitar hankali,
hanyar Kaduna Ya dauka yana tafe yana kukan dana sani....

Takwas da rabi ya iso gidan lokacin ana kici kicin daukar gawar Malam Adamu,
kuka ya fashe dashi da ya hada ido da mamma,
Kure shi tayi da ido cike da mamaki da takaici, durkushewa yayi a gabanta yana kuka Mai Sosa zuciya,
ganin da yayi za'a fitar da gawar ne Ya sanya shi mikewa da sauri ya nufi gawar,
ya sa hannu zai karbi makarar a hannun Musaddiq yaji wata gigitacciyar tsawa a bayanshi,
" IDAN KA KUSKURA TA TABA MAKARAR NAN BAZAN TABA YAFE MAKA BA,,
Chakkk ya tsaida hannunshi ya waigo ya Kalli cikin idonta,
kau da kanshi yayi da sauri saboda abun da ya gani a kwayar idon,
soyayya mai dishi dishin kiyayyar bacin rai ya gani,

"Kiyi Hakuri Suwaiba, mahaifinshi ne Ya zame mishi dole yayi rakiyar gawarshi,
Sailuba matar malam Sada ta fadi tana share hawaye,
"Ban hanashi rakiya ba, amma kar kazamin hannunshi ya kuskura ya taba min gawar miji, ta karashe hade da mai da kanta jikin bango tana gunshekar kuka,
fitar da gawar akayi nan gidan ya sake gawraye da kukan mutane musamman makusantan gawar.....

Mrs Tijjani Shattima
[04/12 09:49] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣5⃣

Ranar murna, mun cinye gasar BBC, proudly fikrians💃🏻💃🏻💃🏻 Safiyya ciyaledi i ❤ u bebi..... FIKRAH WRITERS Bamu fi kowa ba, Amma da wuya ka samu irinmu, komai namu daban yake... Yin na Allah ne ba namu ba ALHAMDILILLAH.....

"Ita Rayuwar nan da kake ganin ta Hafeezu kamar gari ne kaje wanda ba naka ba,
kaga komai daren dadewa, komin dadin zaman garin nan dole ka barshi, saboda ba garin ka bane, bakunta ne ya kaika...

TALAUCI jarrabawa ce babba wacce cinyeta yana da matukar wahala,
duk karfin imaninka dole wata rana zuciyarka ta raurawa saboda zafin wannan jarabawar,

Haka shima *ARZIKI* Jarabawa ce mai wuya kuma mai sauki ga wanda ya fi karfin zuciyarshi,
ina mai baka shawara da kayi yaki da zuciyarka,
ka tafiyar da arzikin da ya fara ziyartar hannunka ta hanyar da ya dace,
domin akwai ranar da zakayi bayanin hanyar da ka kashe su,
nayi maka farin ciki matuka na samun abin yi Allah ya sanya wannan arzikin ya zama sanadiyyar shigarka aljanna,
Allah ya baka ikon sauke hakkinmu kafin mu bar duniyar nan domin Allah shi kadai yasan gawar fari..........  ****
Durkushewa Hafeez yayi idonshi na hango murmushin fuskar mahaifinshi yayin da yake mishi wannan Nasihar,
Wayyo Allah na, wayyo Baba, kaico na, kaicon rayuwata, ya Allah ka dauki raina nima in huta da wannan bakin cikin, wayyyyo baba...,

dakyar mazan gurin suka iya dagashi saboda yadda ya cije yana buga kanshi a kasa,
ku sakeni Dan Allah rayuwata bata da sauran amfani, dan Allah ku barni in mutu,

Tsawa mai karfi Daddy ya daka mishi hade da ma mutanen alamu da su sake shi,
hannu yasa a bakinshi yace "wallahi zan bata maka rai idan kayi yunkurin sake koda nishi kwakwkwara a gurin nan,
  in har so kakeyi ka nuna mana ka fita a musulunci to kaje daga wajen makabartar nan akwai rijiya ka fada, domin wannan duk haukan banza kakeyi,

  Nutsuwar da daddy yaga ta bayyana jikin Hafeez ne yasa shi ya sakko ya dafa shi yace "zai fi kyautuwa ka tsuguna kayi mishi addu'a domin a wannan gabar ita kadai yafi bukata a gurinka ba kuka ba,

Hannun Daddy Hafeez ya kama yana kuka sosai,
yace "in na rokeshi gafara zai ji ni ya yafe min,
idon Daddy ya ciko da kwallar tausayi domin yana auno shine mahaifinshi ya mutu yana fushi dashi,
rungumeshi yayi yace
"nasan ya yafe maka Hafeez kai dai ka dage mishi da addu'a da sadaka su kadai zasu nuna zallar soyayyarka a gareshi....

limamin da ya jagoranci sallar gawar ne yayi addu'oi hade da nasihohi, sannan duk suka juya suka bar makabartar suna masu yi ma mamacin fatan dacewa......

CYPRUS

Tsaye yake jikin wagegen bud'ad'd'en windon dakinshi,
iska na kada labulen windon yana taba gefen fuskarshi,
hannunshi rike da daya daga cikin zanen, ya kura mishi jajayen idanuwanshi,
zuciyarshi a karye take a wannan lokacin, wayarshi ya dauko ya sake kiran Musaddiq,
wannan karan ma bai daga ba,

wurgi yayi da wayar hade da dafe kanshi yana mai jin radadi a cikin zuciyarshi,
komawa gado yayi ya kwanta ruf da ciki,
shi kanshi a yawancin lokuta yana mamakin yadda Nadeeyah ke makale a cikin dukkan kewayen zuciyarshi,
tun baisan kalmar So ba yake jinta a ranshi,
tun ganin da yayi mata lokacin da ita kanta bata san kanta ba,
yana mamakin da a kullum bashi da zanen da ya wuce nata,
kullum kara auno fuskarta yake da yanayin girmanta,

gyara kwanciya yayi yanata juye juye,
a kunnenshi akayi kiran sallar asuba,
mikewa yayi jiki ba kwari yayi alwala ya fito dan zuwa masallaci,

Anty Reemah da Papa ya hango zaune a parlon kasa sunyi jugum jugum cike da damuwa,
da sauri ya sakko daga sama har yana bige kafarshi a matakalar karshe,
baibi takai ba ya karasa gurinsu,
Mum, Papa, "meya faru na ganku haka? Ya tambaya yana mai tsugunawa kusa da mahaifiyarshi,
uhhmm Anty Reemah tace, sannan ta cigaba da cewa, "mijin Mama Suwaiba ne ya rasu cikin dare,
yanzu Raliya ta kirani ta fadamin,
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kalmar da Hilal keta maimatawa kenan a cikin zuciyarshi, tunanin shi ya tafi gun sanin halin da Nadeeyah take ciki,
zungurinshi Anty Reemah tayi tace "bakaji an tada Sallah bane,
mikewa yayi a firgice ya bi bayan Papa da yake kokarin fita daga kofar palon.....

Kuka sosai Badar takeyi hannunta rike da kanta tana shashsheka,

saboda tsabar kuncin da take ciki bata san gari har ya waye ba,
rana ce ta kyallaro ta jikin dan tsagin labulen ta kashe mata ido,
a daidai lokacin ta mike da niyyar wucewa daki tayi tozali da madubin parlon,
wani irin kamanni ta gani a tattare da ita mai wuyar fassaruwa,

fuskar nan tayi jawur hancin yayi suntum saboda kukan da tasha,

wani kukan ta sake fashewa dashi hade da rugawa cikin daki,

cikin kunan rai ta fada bayi ta kunna pampo tana watsa ruwa a fuskarta tana magana cikin kuka,

"Nadeeyah bazan taba kyaleki ba, kamar yadda kikayi min ruining wannan ranar sai nayi ruining life dinki gaba dayanta,
bazan taba iya tuna rabon da na zubda hawaye ba,
amma yau na zubar sanadiyar ki, 
na tsaneki, na tsaneki Nadeeyah!! ta karashe hade da kifa kanta jikin bangon bayin........
Chapter 10 · 0% Book details