Sashe 63
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Good, take care kinji,
naji dadi sosai da naji muryar da na dade banji ba,
Ina fatan ganinki soon in shaa Allah...
love yhu bye,
Bata bashi ba ta kashe wayar hade da mika ma sabrinah,
karba tayi ta wuce ba tare da ta kawo komai a ranta ba...
"Kin gama?
ya fadi yana murda key,
"ta gama mana yaya,
muje plss,
tada motar yayi ya figeta da wani irin mahaukacin gudu,
ya rasa dalilin da ya sanya wani abu yayi mishi karan tsaye a cikin kahon zuciyarshi,
menene yake shirin faruwa dashi,
tun tafiyarshi lagos kome yakeyi ita ke fado mishi,
har sabawa yayi da tashin da take mishi da asuba,
komi nisan baccin da ya tafi in yaji karar wayarshi yasan ita ce,
dan ita kadai ke kula da tashin shi,
in ko yaje cin abinci babu wanda yake a gani a gabanshi in ba ita da daddan girkinta ba,
yana matukar kaunar ganin yanayinta a duk lokacin da ya tsokaneta,
wannan dawowar da yayi week end domin ta yayi shi saboda a matukar takure yake,
kewarta na addabar shi,
Tufka ya dingayi da warwara akan abun dake shirin faruwa dashi game da Nadeeyah,
har ya isa gida bai tufka komai ba bare ya warware...
Bakin motoci ya gani a harabar gidan shiyasa yayi parking daga can baya,
da sauri duk su biyun suka karasa ciki saboda lalurar dake tare dasu,
wasu lafiyayyun mutane suka gani su uku,
manyan mata biyu sai wata tsaleliyar budurwa black beauty, hannunta rike da katuwar waya mai fadi tana ta latsata tana taunar cingam,
gaishesu sukayi matan suka amsa da murmushi,
yafito Husnah Mummy tayi da hannu tace "zo ki gaida Anty Aliya,
takalmi ta cire ta karaso kusa dasu ta gaida su,
shafa kanta Anty Aliya tayi tana murmushi tace
"Husnah ta girma,
waccen fa ban gane ta ba?
daidai lokacin Musaddiq ya shigo parlon,
"Yar step sis dina ce wacce ta rasu,
Ayya,
yar me kyau da ita,
Allah ya jikanta,
Ameen Mummy tace hade dayi ma Nadeeyah nuni da ido da ta wuce daki,
juyawa tayi ta murda kofar dakin nasu ta shiga,
kan gado ta kwanta tana mikar gajiya,
karar shigowar sakon da taji a wayarta shi ya sanyata sakin wani irin Murmushi hade da daukar wayar,
a yanzu shakuwar da tayi da Hilal ta wuce misali,
har ta kanyi mamakin yadda ta saki jiki dashi sosai haka,
saboda dadin da sakon yayi mata har saida hakoranta suka bayyana...
*Congrats to my young Barrister, bigger yhu i pray, i'm very Happy, more grads are coming in shaa Allah....*
Kiranta barrister da yayi shi yafi komai yi mata dadi cikin sakon, tunda ta fada mishi abun da take son karanta shikenan kullum sakonsu ya koma akan lawyers,
_Thank you yayana, Allah ya biya maka bukatunka duniya da lahira, yhu are an angel......_
Wani irin juyi yayi a kan makeken gadonshi,
"will be ur life soon Nadeeyah,
ya Allah, i can't resist it,
i have to tell her,
wani irin faduwar gaba yaji da sauri sauri,
Soyayyar Nadeeyah kullum kamar kara hurata akeyi a cikin qalbinshi,
baya tunanin akwai abin da zaizo ya rabashi da ita sai dai ko mutuwa,
a kasalance hannunshi ya rubuta.
*Akwai wani sakon da zan baki zuwa anjima, kiyi ma sakon tanadi, domin yanada matukar tsada da kuma muhimmanci, take ur time daga yanzu zuwa dare dan sakon yana bukatar nutsuwa, domin a nutse za'a isar dashi, 10pm dot...*
Kokawa ya fara yi da zuciyarshi,
wannan tana ka tura wancan tana karka saba alkawarin da ka dauka na saita gama makaranta zaka isar mata,
wata tana fadin karka bari ya huce domin zai iya kawo rabon wani,
tunanin shi na karshe ne ya sanyashi saurin turawa,
kashe wayar yayi gaba daya dan gani yakeyi kamar in a kunne take zata iya ganinshi,
wani irin nishadi ya yake ji,
ya tashi ya fita parlor gurin su zainab,
wasan da bai saba yi dasu ba ya shiga yi har Anty Reemah na tsokarshi..
Ita kuwa juya wayarta ta dinga yi ta rasa wani irin sako ne wannan dake bukatar nutsuwa,
ita dinma zuciyar sai bugawa take da sauri sauri,
abu daya ta kawo a ranta kuma tayi saurin kawar dashi dan tasan ba mai yiwuwa bane,
Hilal yayi mata zarra ta kowani bangare,
nan take ta kauda tunaninta ta ajiye wayar ta shiga bayi,
wanka tayi ta fito ta sanya wani plain material lemon green da jar flower a jiki,
ta sanya jar hula a kanta ta gyara dakin ta fita dan zuwa yi ma Musaddiq abinci,
karo sukayi da Husnah a kofar dakin tana kokarin shigewa ciki,
"Har kinyi wanka, kaii kin huta, ni su Mummy sun hanani katabus,
bari inyi wanka zan sameki a kitchen,
dariya Nadeeyah tayi na ganin yadda jikin Husnah ke rawa ta karasa fitowa a parlon,
wannan karon ba kowa a parlon sai Musaddiq da budurwar,
hada ido sukayi tayi mishi Murmushin da ya sanyashi sukurkurcewa ya bita da ido,
saida ya daina ganinta sannan ya dawo da hankalinshi gurin wacce ta kira kanta da *FAIDA*,
"kana jina ko,
ta fadi tana kallon cikin idonshi,
"Eh yauwa, inaji,
kikace wani level ma?
"200l ta fadi tana murmushi, ta cigaba da cewa
"dama Mum tace min i will like u,
gashi daga farkon haduwarmu i like everything about u,
i love you!,
wani irin murmushi yayi ya shafo sajenshi hade da jan hancinshi yace
"dats nice,
i like u too,
saidai anya zaki iya kuwa? liability ne ni,
komai yi min akeyi,
komai fa, infact ko toilet zani sai an rakani,
dariya yayi wacce bai san ta fito ba yace "Kuma gash---
wata dariya yaji wacce ta sanyashi kasa karasawa,
bata kalleshi ba ta bude drawer gurin dining ta dauki abun da tazo dauka,
shima dariyar ya cigaba dayi yace "yauwa Nadeeyah zo,
matse dariyarta tayi ta karaso inda suke,
"Gani,
"zauna ki bata labari na,
zama tayi tace
"Karki ce dan yana yayana ko dan yana zaune anan,
gaskiyar kawai zan fada miki,
"yaya Musaddiq a cikin dubu kafin ki samu daya irinshi sai kin tona,
he is very nice,
bashi da fushi sam,
baima iya shi ba,
yanada kyautawa fiye da tunani, sannan yana son a kula dashi da kuma cikinshi, gaskiya kinyi dacen samun yayana,
yhu are very lucky...
Tana kaiwa nan ta mike hade da kallon yadda ya kureta da ido,
dariyar tsokana tayi mishi ta wuce kitchen,
Dan tabashi yaji anyi nan ya dawo cikin hayyacinshi,
ya salam ya fadi a zuciyarshi,
abubuwan nan dake faruwa dashi game da Nadeeyah ba lafiya bane,
ya kasa tantance menene shi,
"Ko a ya kake kayi min!
muryarta ta sake maidoshi cikin tunanin da zuciyarshi ta tafi,
hankalinshi kacokan ya dawo dashi kanta yace
"Menene So?
Ya akayi kikaji kina sona daga ganin farko?
Menene kikaji game dani har kika gane kina sona,
Nan Faida ta gyara zama domin kwararrace a wannan fanin, bata san adadin samarin da tayi a rayuwarta ba,
yadda ta maida kudi take watsarwa ko ina haka ta maida namiji
*SO*
Gamon jini ne,
so wata halittace wace take kwance a cikin zuciya,
Halittar na iya daukar mutane da yawa,
saidai kowa da muhallinshi,
Soyayyar iyaye tanada gurinta,
soyayyar yan uwa, aboki da sauransu suma akwai muhallinshi,
sai kuma main the main,
soyayyar Abokin rayuwa,
wannan soyayya ce wacce ke faruwa a lokacin da mutum bai shirya ba,
Tausayi siga ce ta soyayya,
duk wanda kake tausayinshi to tabbas soyayya ce ta jawo haka,
damuwa,
yawan damuwa da mutum wannan ma alama ce ta soyayya,
Tsayuwa cikin rai,
mutum ya zauna a ranka babu dare babu rana ko yaushe tunaninshi kakeyi wannan shine kankat, domin ko shakka babu soyayya ce mai karfi ta shigo lamarin,
kamar yadda yanzu ina sanyaka a idona naji my heart beats for u,
ban taba jin wani abu game da wani da namiji ba sai akanka,
Surutanta take tayi shi kuwa ya tafi can wata duniyar,
murmushi kawai kake gani a kan bakar kyakyawar fuskarsa mai cike da annuri,
komai na Nadeeyah ke mishi yawo akanshi,
"I'm in love ya furta a hankali,
kallonshi Faida tayi hade da mikewa tace wawww, alhamdulillah,
sama tayi da gudu dan kaiwa maman ta albishir,
bai ma san tanayi ba ya shafa kanshi har lokacin yana furta kalmar
"I'm in love,
bayanshi ya jingina jikin kujera yana fitar da murmushi mai sauti,
wasu irin numfarfashi yake fitarwa wanda duk fitarsu suke tafe da zazzafan kaunar Nadeeyah,
muryarta keta yin amsa kuwwa cikin kunnenshi,
"Yhu are very lucky,
kasa ya koma ya mike kafarshi yace
"yhu are the lucky one Nadeeyah,
and I'm the luckiest,
Muryarsu ya jiyo a kitchen yayi saurin zuwa kofar kitchen din ya nade hannuwanshi yana kallon duk wani taku da tayi a kitchen din,
da ido Husnah ta nuna mata shi,
saida ta shanye dariyarta ta juyo tace
"mun kusa gamawa,
angon mu,
muma dai mun kusa hutawa,
amma dan Allah a bari mu dawo daga Gombe ko Husnah, ta karashe tana taba kafadar Husnah,
kusa dashi Husnah ta dawo tayi mishi rada a kunne tace
"Yaya nidai bata min ba,
bata da class,
kaji wani ihun da tayi da sunan wayewa,
samm batayi kama da matar yayana ba,
bai dauke idonshi a kan Nadeeyah ba yace
"Tunda ba tayi miki ba sai mu canza wata auta,
yana kaiwa nan ya bar kofar kitchen din,
bazai iya kara kwana daya ba tare da ya sauke wannan nauyin son a zuciyarshi ba,
dakinshi ya shiga ya kwanta a gado hade da dauko wayarshi,
Hilal ne kadai zai tayashi sauke wannan nauyin,
daga bakinshi kadai zataji ta saki jikinta dashi ta kuma amince mishi,
layin Hilal din ya kira,
da farko yaki shiga sai da yayi sau uku, ana ukun ne yayi sa'ar ya kunna wayar,
cike da Annashuwa Hilal ya dauki wayar da bashi da masinayar itace yankewar farin cikinshi na lokaci mai tsaho.....
"A kasalance Musaddiq ya furta kalmar
"I'm in love main man,
cikin shauki Hilal ya jingina jikinshi a karfen balcony ya sauyawa wayar hannunshi mazauni zuwa kunnen dama yace "Wowww,
is this a dream or?
REALITY Musaddiq ya katseshi hade da lumshe manyan idanuwanshi,