← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 113

Sashe 77

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gara in kashe kaina da irin kisar da kake shirin yi min Taheer,
gara in mutu kafin ka kashe kanka kasa min mutuwar ko'ina na jikina,
bani da wani muhimmanci a cikin rayuwarka,
akan mace kake so ka kashe kanka har kake kiran rayuwa ba komai bace in babu ita,
gara ka barni in fara mutuwa sai ka biyoni,
bazan iya jurar ganin gawarka ba Tee...
. bazan iya ba....
ta karashe tana kuka sosaiiii....

Kanshi ya daga sama da niyyar haďiye kukan da ya tokare makokwaronshi,

inaa sam ya kasa,
wanda yake kokarin haďiyewa ya fito da karfinshi,

Zaman dirshan yayi a gurin yana kuka sosai kamar karamin yaro,
bata hanashi ba dan itama kukan takeyi,
wallahi da zatayi arangama da yarinyar da tayi wa ďanta haka sai ta shake wuyanta ta kusa kaita lahira,
ita duk tunaninta cin amanar ďanta tayi,
domin ita tace ya jirata,
sai kuma yaji labarin aurenta,
duk da bata san wacece Nadeeyah ba taji a duniya bata ko san karo da mai sunan a rayuwarta,

Saida sukayi kukansu ma'ishi sannan Taheer ya rarrasheta ya kuma yi mata alkawarin daina tunani akan wacce ta zamto matar wani,
sannan ya roketa da Allah kar ta yi mishi maganar aure nan kusa har sai yayi niyya dan kanshi,

Badan taso ba ta yarda da kudurinshi,
tasa ma ranta nemo mishi yarinyar da zata maye mishi gurbin cin amanar da akayi mishi......

Lafiyayyen abinci ta shirya mishi ta dinga mishi hira,

"auu kaga damuwa ta dauke min hankali,
jiya *Mus'ab* ya kirani,
wai su *Aman* sun samu gurbin karatu anan university of Toronto,
ina ganin gobe ma suna hanya, bakaji daďi da naji ba,
dan zasu rage min kaďaici in ka tafi makaranta,
nuna mata jin dadinshi yayi yace

"mantawa nayi ban faďa miki ba, ni na nema musu admission din, Anty Nuwairah duk ta damu wai sunyi nisa,
saida taji a gida zasu zauna shine hankalinta ya kwanta,
naman karshe Anty Saude tasa a bakinshi tace
"Haka tace min,
ai naji dadi sosai, Allah ya kawo su lafiya, "Ameen ya faďi haďe da mikewa yace
"bari in watsa ruwa,
inaga gobe zani lagos,
Kudin Abba na companyn coffee ya fito,
sunce in je inyi signing.....

cike da jin dadi tace

"Kaii mashaa Allah, Allah ya kaimu goben......

**********

Tagumi tayi akan dadduma bayan ta idar da Nafila tana jiran a kira sallar asuba ta tashi tayi,
tunanin irin rayuwar da takeyi a gidan aurenta takeyi,
tunda tazo gidan ta auri zaman ďaki,
bata san kalar kitchen dinta ba domin yadda su Radiya suka kanainaye komai,
babu inda take fita kullum daga bayi sai ďaki,
bata da matsala sam da Musaddiq domin yana kula da ita sosai,
abinci ma in ya siyo da kanshi zai bata kuma ya kwashe kayan da kanshi dan shima tsoron tashin hankali yakeyi,
a da bata jin son Musaddiq a matsayin abokin rayuwarta, amma kwanaki shidan nan da sukayi tare,
halayyarshi ta samar mishi matsayi mai girma a zuciyarta,

Mutum ne mai gudun zuciya,
yadda bazai bata maka ba,
kaima karka bata mishi,
samm baya kwana da wani a ranshi,
sanyin halinshi shine abu mafi soyuwa a gareta,
tun ranar da ya kusanceta yaga irin kukan da tayi,
bai sake koda kwatantawa ba, duk ko da tsabar dannewar da yakeyi,
samm bayasan abin da zai sata cikin damuwa,
ya gwammaci matsuwar ta dameshi akan yasata cikin damuwa...

kiran assalatu ne ya katse mata tunanin da takeyi ta mike dan ta tashe shi ta kuma sabunta alwawarta,

Bargon da ya dukunkune ta yaye a hankali,
zufar da ta gani a fuskarshi ce ta sanyata zaunawa kusa dashi da sauri haďe sa hannu a goshinshi ta fara share mishi,
hawayen da ya jika saman idonshi shi yafi komai daga mata hankali,
a rude ta fara kokarin ďago kanshi ta kasa saboda har lokacin cikin bacci yakeyi,
gefen kunnenta ta kwantar a saitin kirjinshi taji yadda zuciyarshi ke bugawa da sauri da sauri,
ajiyar zuciya ya saki haďe da shashesheka ya sanya hannu ya rungumeta sosai a jikinshi,

"plss don't lv me,
i can't lv without u....

yadda yake maganar ido a rufe ya bata tabbacin mafarki yakeyi,
duk wata kunyarta ta nema ta rasa ta rungumo kanshi haďe da share mishi hawayen da yakeyi tace
"bazamu rabu ba,
in shaa Allahu babu abinda zai rabamu,
Allah ne ya haďamu,
shine kadai zai iya rabamu in yaso, "bazan barka ba!

Jin kalaman da yake a zahiri ba'a mafarki ba yasa shi buďe idonshi haďe da kwantar da ita sosai a jikinshi yace
"promise?

gyaďa kanta tayi haďe da cewa "Ummm,

"umm me?
Ya fadi yana daďa narke mata,

turo bakinta tayi a shagwabe tace
"um um,

dariya yayi yace
"kinsan nafiki iya shagwaba,
in na fara nawa gari zai waye mana ba muyi sallah ba,
kinji an tada kabbara, tashi muyi sallah mu roki Allah kar ya tabbatar mana da mafarkin da nayi,

juyo fuskarta yayi ya daura hancinshi kan nata numfashinsu ya gauraya da na juna yace

"i don't want to loose you,

hannunta tasa ta toshe mishi baki cikin zolaya tace

"hmmm...
muje kayi brush,

"bakina wari ko,

"ni dai ban faďa ba!

"laifin ki ne,
baki sani nayi rinsing baki na ba,

nidai ba ruwana,
kaji anyi sallama ko,
dan Allah muje muyi sallah,

"zakiyi bayani bari mu idar da Sallah,
ya faďi yana dariya haďe da nufar bayin......

Wai Mummy Faida bazata zo bane,
babu wani improvement fa,
kullum daďa like ma yarinyar nan yake,
can u believe that ko gaisheni bata fitowa tayi,
ni kam in bazaki turo Faida ba zan shirya in koma gurin 'yayana,

Daddyn Ra'ees ko daga wayata baya yi,
wannan bai dameni ba, dan nasan ina komawa gida zai huce,
burina inga munyi winning yarinyar nan ta bar rayuwar little,
Radiya na dire aya Mummy tace

"Karki damu,
Faida na nan tafe anjima,
mun gama magana da Hajiya Aliya,
in shaa Allahu komai ya kusa zuwa karshe,
kudai ku cigaba da taka tsan tsan kar Daddynku ya gano kina can, dan wallahi in ya gane ba zamuji daďi ba,
gyara zama Radiya tayi tace "bazai ji ba in shaa Allah,
ai kwana kaďan ya rage,

"To Allah ya nuna mana,

"Ameen Mummy, sai anjima....

Ki shirya zamu fita bayan la'asar, maida pillow mazauninshi tayi tace
"To Allah ya kaimu,

"Ameen Habeebty....

Karfe huďu da yan mintina suka fito a shirye tsaff gunin sha'awa,

Allah ya taimaka su Raudha sun tafi sama yin Sallah,
shiyasa taji dadin fita daga parlon...

Banana island suka fara zuwa gidan oganshi wanda suka saba sosai da matarshi, dan yawancin duk wasu muhimman aike Musaddiq ke zuwa,

Tarba mai kyau suka samu daga gurin Hajiya Zubaida,
mace mai mutunci da fara'a, ga sanin ya kamata,
wayayyar mace ce yar birnin kebbi,
yaranta uku duka maza,
babban cikinsu bai wuce shekara 18 ba,

Sai wanda take kira auta dan shekara 9,

Bayan sun gama dan taba kayan da ta kawo musu suka dan yi hira kadan sai Musaddiq ya bukaci da su tafi,
hana su tafiya tayi tace
"ku jira shi,
yanzun nan zai dawo,
tana rufe baki suka ji an murda kofar,

Alhaji Kamal Gumel ne ya shigo tare da ďanshi na biyu,
faďaďa murmushinshi yayi yace

"Ango kasha kamshi,
tare muke da Zubairu,
yanzu ya tafi siyomin kifi,
ai da nasan kana ciki da na tsaida shi,

cike da girmamawa suka tsuguna suka gaida shi,
amsawa yayi ta sigar mayar musu da girman haďe da zama yace

"masha Allah,
gaskiya Musaddiq ka iya zabe, Allah ya baku zaman lafiya,
nan hirar aiki ta kacame musu,
"ba karamin wahala suke sha ba na hutun da Musaddiq ya dauka, dan in yana nan aiki bai musu yawa haka,
akwaishi da azamar aikin office,
samm bashi da kasala a nan, saboda yanda mahaifinshi ya nuna mishi muhimmancin aikin da kuma inda suke fatan ya kaishi nan gaba,

Da Hajiya Zubaida ta gaji da hirar aikin tace ma Nadeeyah ta tashi suje karamin parlon,
ba musu ta mike tabi bayanta,

"Wannan hirar tasu ba mai karewa bace,
gara muyi tamu anan wacce zata amfane mu,
tambayoyi Hajiya Zubaida ta fara yi ma Nadeeyah,
kasa bata amsar su Nadeeyah tayi domin wasu bata san yadda zata sa mata ba,
dariyar manya Hajiya Zubaida tayi ta fara bata shawarwari kama daga kitchen har kwanciyar aure,
da irin ladan da mace ke samu a gidan aurenta,
sosai shawarwarin suka shiga Nadeeyah saboda haďawa da tayi da ayoyin Allah da kuma tarihan magabata,

Saida suka kara kusan minti 30 sannan suka fara shirin tafiya,

Sha tara ta arziki Nadeeyah ta fita dashi daga gidan,
sunyi matukar farin cikin haďuwa da juna......

Sai bayan isha'i suka koma gida,
fitar tayi ma Nadeeyah daďi dan dama zama guri daya ya isheta,

Tun daga waje suke jiyo shewar su Raudha kamar wadanda akayi ma albishir da gidan aljanna,

A darare Nadeeyah tabi bayan Musaddiq dake rike da ledojin da suka dawo dasu,

"oyoyo my dear broo,
Faida ta faďi haďe da nufo inda Musaddiq yake,

Sakin fuskarshi yayi yace

"Manyan baki ne a gidan, welcome,
ya kike?

Ledojin hannunshi ta amsa tace

"am fine, bari in rage maka nauyi,

Wani miyau mai ďaci Nadeeyah ta haďiye wanda bata san daga inda ya taru zuwa bakinta ba,

Tana kallon yadda Faida keyi ma Musaddiq fari da idanuwa tans kwarkwasa jikinta,

Hanyar sama ta nufa a hankali kamar mai koyon tafiya,

ďaga Murya Faida tayi tace

"Ina wuni Amarya...

cakk.. Nadeeyah tayi a gurin ta kasa juyowa ta bata amsa,

Cike da kirsa Radiya tace

"uhmm, kaji inda ake girmama na gaba,
a duk zaman da nayi a gidan nan Nadeeyah bata taba yunkurin gaida ni ba,

"Hmmmm naga deal Anty,
gashi yanzu ma ta wuce ba tare da kallon inda muke ba,
ai ko ba komai mu yan uwanta ne na jini,

amshewa Radiya tayi da cewa
"nifa ban ga laifinta ba,
dan taga little na rawar jiki akanta ne,
shiyasa bata damu dayi ma yan uwanshi biyayya ba,

yo ko Mummy ma bata gaisar wa bare ni,
jiya Mummy 10missed call tayi mata bata dauka ba,
amma ina jiyo muryarta da Hafeezu suna waya...

"Kinga laifinta, Raudha ta faďi tana hararar Musaddiq,
Chapter 77 · 0% Book details