← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 113

Sashe 43

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai ita kadai ta rage mana,
ashe wani farin cikin na tafe zuwa garemu,
ashe ina da rabon ganin Magaji na kafin kasa ta rufe min ido,

Wannan kalma ta *MAGAJI* ita sanya Goggo jin wani dumi tun daga kanta har cikinta,

Ido ta zurawa Baffa da yake ta sambatu a gaban Papy da Anni,
duk yadda taso su hada ido dashi sam yaki dan gaba daya ya manta Allah yayi halittar ta a gurin,

Yasan dai tana makale cikin ranshi amma ganin Papy ya sanyashi mance duk wata soyayya in ba tashi ba,

ji yakeyi ina ma ace da kuruciyarshi da sai yayi zagaye da Papy a bayanshi ba tare da ya gaji ba..

Wani irin kugin taji a cikinta tunda Anni ta fara basu labarin shi dawo mata,
ganin yadda tun yanzu Baffa ya ki koda kallonta ya tabbatar mata da lallai akwai aiki a gaban ta,

Mikewa tayi da niyyar tafiya bayi dan cikin nata jinshi takeyi kamar zata kasayar da ya'yan hanjinta,

Tana mikewa taji kafarta tayi mata nauyi saboda yadda zawon ya taho mata gadan gadan,
dakyar ta daga kafarta,
tana dagawa zanin jikinta ya sabule ta feso shi ba tare da sanin inda zashi ba,

Wani irin ihu Radiya ta saki tana fadin "I'm dead" wayyo Allah na,

"Dariyar Ruwaida ce ta cika gurin tana yi tana fadin
*nyan nyan nya* disgusting!

Papy kagani da kace "in an min abu in dinga hakuri Allah zai saka min, yau gashi naga ni da idona,
wayyo cikina,
she deserve more old lady karo mata,,

Janyota Mami tayi da karfi ta sake maida idonta cikin mayafinta kamar yadda kowa yayi a gurin,

kunnenta taja tace "ke wace irin yarinya ce,
in sake jin kince pim kiga abun da zan miki,

Mummy ce ta tashi da sauri tana tare Goggo tana fadin Goggo lafiya,

Hawayen takaicin da Goggo ke rikewa ya zubo a kuncinta,

cike tsoron ganin hawaye a idon wacce babu abin da ke sata kuka Mummy ta ja hannunta sukayi bayi,

shi kuwa Baffa maida kallonshi gurin Radiya dake kuka tana kyankyame jikinta yayi yace
"je ki wanke jikinki mana,
ko so kikeyi warin ya kashe mu,
baki ganin muna cikin farin ciki ne,

karaff kalamanshi a kunnen Goggo,

wani Kukan ta sake fashewa dashi a zuciyarta tana tambayar kanta ta inda aka samo matsalar,

Damuwa ce karara a fuskar Mummy dan iya rayuwarta bata taba ganin hawaye a idon Goggo ba,
bayan ta gama kimtsa ta suna jiyo muryar Baffa yana basu Labarin Suwaiba da 'yayanta,

ita kanta Radiya cike take da mamakin yadda yake basu labarin suwaiba da 'yayanta dan a da ko labarinsu baya son ji bare ya ba wani,

Kallon Goggo Mummy tayi tace "kiyi ma Baffa uzuri, shekaru sama da arbain rabonshi da dan da ya cire rai da kasancewarsa a duniya,
sannan kuma shi kadai ya zame mishi namiji,
kinga dole yayi farin ciki,
ni kaina cikin farin ciki nake,
dan a yanzu na fita a sahun ni kadai,
mun zama biyu, ďan uwa dadi gareshi Gog----

dogon tsaki taja wanda ya katse mummy da karasa maganar ta,

"Ba tun yau na lura da cewa ke din bakya kishi na da kanki ba,
inama Allah Halima ya bar min ya daukeki Goggo ta fadi cikin gushewar hankali,

Zaro ido Mummy tayi zatayi magana ta jiyo muryar Baffa yana kwala kiranta,
bai bari ta amsa ba cikin doki yace "fito muje gidanki suga Nadeeyah,

ki kira muntari in yana gari shima ya dawo gidan sai su hadu,

Jaka Mummy ta dauka tace ma Goggo "kiyi hakuri, gobe zan dawo,

ko kallonta batayi ba,
idonta na kan kofa tana jiran ganin Baffa ya shigo dan su hada ido ta samu dukkan madafun ikon hanashi zuwa,

Anni da Mami ne kadai suka leko suka yi mata sannu da jiki, sannan suka wuce,,

Shurun da taji a tsakar gidan ne ya bata damar lekowa,
babu kowa a gidan sai Radiya dake tsaye daga ita sai undies, tana ganin Goggo taja mata tsaki tace
"walhy kin cuceni, sam bazan iya cin abinci ba yau,

gashi Mummy ta tafi ta barni, nidai gaskiya baki kyauta min ba,
kuma ga kashin ki nan walhi bazan kwashe ba,

Hadiye miyau mai daci Goggo tayi ta wuce daki tana saka abubuwa marasa kyau da zata aikata,

saken da tayi na ganin cewa babu wanda zai shigo rayuwarta shi ya janyo mata wannan matsalar......

♡♡♡♡♡♡!
♡♡♡♡♡♡♡♡!
♡♡♡♡♡♡♡♡♡!

Nayi kyau Momma!!

Kallonshi tayi sama da kasa,

jan wando ne a jikinshi ya dan matse daga kasa sai green riga ta dafe a jikin tayi mishi kyau sosai..

Murmushi tayi ta gyara mishi kwalar rigar tace "First class kyau ma,
kaima kasan u are excellent!

Rungumeta yayi hade da yi mata peck yace
"zan fita ur ---
prayer is needed ta karashe hade da cewa "kana da bukatar tuna min ne,
dariya yayi ya dauki keyn motarshi,
har ya kai kofar fita daga dakin tace
"baka fa fada min sunan diyar tawa ba,

waigowa yayi yana dariya yace "tooo expensive, nawa zaki siya?,

Dariya tayi sosai tace "abun da yafi komai tsada a gurina zan biya,

*TEE NA*

Murmushi yayi yace "luv yhu Momma,

*Umm Nadeeyah* is the special one.. my Omri...

Ya karashe hade da fita da dan gudu gudu,

zama tayi tana maimaita sunan farin ciki na ratsa ko ina na jikinta.....

A kofar gida yaga Raliya tsaye tana tsaki tana kallon drivernta yana duba mota,

tsayawa yayi yace "Maman fadeel fita zakiyi?

"Eh Taheer motar kuma ta samu matsala,

Ayya,
shigo muje in kaiki mana, Taheer ya fadi yana fitowa a mota,

Girgiza kai tayi tace "bazan matsa maka ba,
jeka kawai walhy,

Babu wani matsi Allah,
saidai in motar ta miki karama ya fadi cikin tsokana,

Dariya sosai tayi ta bude ta shiga ta cema drivern ya kai motar gurin mechanic...

Dadin da yaji baya misaltuwa na sanin gida zataje...

kwatance ta fara mishi taga yana ta kai kanshi tun kafin ta fada mishi,
murmushin jin dadi tayi ta kasa tsokanarshi saboda kar tasa yaji kunya....

*******

Tun karfe biyu ya sauka a airpot din Abuja,
bai tsaya jiran wata wata ba ya dauki drop har kaduna,

zuwan nashi na aike ne a ganin Anty Reemah,
bata san shi zuwan nashi ya wuce aiken da tayi mishi ba,

Musaddiq ne kadai yasan da zuwanshi dan shima ya matsa a kawo mishi wasu takardun makarantarshi,

saboda go slow basu iso kaduna ba sai to 5,

A daidai gonin gora Musaddiq ya tsaya ya daukoshi cike da farin cikin sake haduwarsu bayan watanni,
hira sosai sukeyi a motar kamar wadanda suka shekara goma basu hadu ba,
ko wanne a cikinsu yayi kyau sosai,
musamman Hilal da ya fara practicing karatun da yayi ta hanyar yin zanen da ya doke na dubban mutane a cyprus,

Ba kananan kudi yake rikewa ba,

shiko Musaddiq bautar kasa yakeyi,
shima yana samun kudi sosai tunda yana taya Daddy wasu yan ayyukan, saboda tsabar kaguwar da Hilal yayi ya sanyata a ido shi ya sanya shi ganin kamar Musaddiq baya gudu, tsayar dashi yayi hade da karbar tukin ya taka motar a 140....

Tsayawa yayi da ya sauke Anty Raly a kofar gidan,
ganin da tayi bai tafi ba yasa ta dawo tana murmushi tace
"ko in kira maka ita ne?,

Murmushi ya sakar mata mai kyau wanda ya bata amsar manufarshi,

shigewa ciki tayi tana adduar Allah yasa Daddy baya gida,
dan tasan a gidan basa zance sai sun gama secondary school,
ita kuma bazata iya hana Taheer ba domin nauyinshi take ji sosai...

A parlor ta samesu zaune suna kallo,
saboda akwai Badar a parlon shi ya sanya Nadeeyah zama daga lungun Husnah tana gyara kumbarta da tasha jan lallen da ya rinu sosai ya koma maroon,

zama tayi ta kalli Nadeeyah da take ta mata murmushi,

"ina wuni Anty, ta fadi hade da mikewa ta dauki Fadeel,

hannunta ta kama tace "wow waye ya muku lalle,

Nuno mata hannu Husna tayi tace "Sadiya,
jiya tayi mana,

shafawa Anty Raly tayi tace "kaii gaskiya yayi kyau,
kwa kirata tamin in Abban Fadeel zai dawo,

kallon Badar tayi tace "Rasa kunya ina wuni,
bata kalli inda take ba ta mike tana fadin lfy lau ta wuce daki,

girgiza kai tayi tace "Allah ya shirya,

Nadeeyah jeki waje ki karbo min sako pls,

ajiye Fadeel tayi ta dauko dark purple hijab din islamiyya har kasa tasa ta yi hanyar waje,

tsayar da ita Anty Raly tayi ta taso tazo inda take,
gyara mata Hijab din tayi dan ya karbeta sosai bata ga dalilin sata ta canza ba,

"karki bani kunya kadai ta fadi hade da tura ta waje,

Tafiya ta fara yi tana maimaita "karki bani kunya a cikin zuciyarta,

sharewa tayi kawai ta fita dan ganin sakon da zata amso mata,

Tana fita idanuwansu suka sarkafu cikin na juna,

tsayawa tayi a bakin gate din ta kasa karasawa gurin da yake,

Tunanin juyawa tayi sai ta tuno kalaman Anty Raly,

Kamar zatayi kuka ta makale a jikin gate din gidan,

karasowa yayi yana murmushi,
yanayin tsoronta na matukar burgeshi,

gab da ita ya tsaya yana kallon yadda take wasa da yatsun hannunta,

Hankalinshi kacokan ya tattaro ya maida kan yatsun hannunta da kafa,
ya ilahi ya fadi a cikin ranshi,
"Son yarinyar nan dada narkar da zuciyarshi take,

Saida suka dauki minti uku babu wanda yayi magana,
ganin shurun yayi yawa yasa ta dago kai ta kalleshi,

saida ta gwammaci da bata dago ba saboda wani irin mayataccen kallon da yake mata,

maida kanta tayi da sauri murya na rawa tace
"ina wuni, wai ka bani sako inji Anty!

Dariya yayi hade da sauke ajiyar zuciya,

"sakon zuciyata zan baki,

ki taimakeni ki amsheta hannu biyu,

kinsan ita zuciya sakarya ce akan abin da take so,

Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari,
duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe.

Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata.

Ki taimaki wannan zuciyar da bata taba furta so ba sai akanki

*Umm Nadeeyah*.
Chapter 43 · 0% Book details