← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 113

Sashe 8

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:47] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣2⃣

A hankali take maimaita kalmar "innalillahi wa Inna ilaihir rajiun" ruwan hawaye na tsere akan kumatunta,

kirjinshi take dannawa tana share kumfar jinin dake fita a bakinshi, nishi yakeyi Sama Sama yana kakari da karfi,

magana yake fisgowa daga can kasan makoshinshi,
muryarshi ta kara karfi tamkar amsa kuwwar loud speaker,

"kiyi Hakuri suwaiba! ,
kiyi Hakuri da rayuwa,
nasani ban jiyar dake dadin duniya ba saboda talauci na,

gashi zan tafi in barki cikin rayuwar talaucin da babu mataimaki,

kiyi hakuri suwaiba, Allah kadai yasan tanadin da yayi mana a lahira,
ki cigaba da hakuri da duk yadda kika tsinci kanki,
nasani kin iya kanki,

ki rike yaran nan,, basu da kowa a duniya sai ke,

ki fadawa Hafizu in ya dawo
na yafe mishi,!
na yafe mishi,!
na yafe mishi,!!!

Idonshi da yake lumshewa ya daga Sama,
ga azabar zafin fitar rai ga kuma radadin barin iyalanshi cikin yanayi na rashin garkuwa,

Ya Allah! ka iya ma zuri'ata abin da bazasu iya yi ma kansu ba,
LA' ILAHAILLALLAH----- kukan mamma ya karu saboda tsabar firgici,

A gigice Nadiya ta farka daga gajeren baccin da ya dauketa saboda jiyo kukan mahaifiyarta,
fitowa tayi daga daki da sauri har tana turgude kafa ta karasa dakin baban su,

kasa shiga tayi saboda hangoshi da tayi  damke da karfen gadon dakin hade da hannun mamma, yana haki da sauri sauri.

Juyawa tayi ta fita a gigice, 

"wake ta takalmi ko mayafi a wannan lokacin",
gudu takeyi da iya karfinta, ita dai tasan jefa kafafuwan ta kawai takeyi, bata ma San akan abinda suke sauka ba,
hanyar gidan Baffa ta dauka,

duk nisan dake tsakanin su bata gani ba, ita dai burinta a taimakesu a ceci rayuwar mahaifinsu,

Da dutse take bugun gate din gidan da iya kurewar karfinta,

Ya salam!!
Baffa ya fadi yana mai mikewa,
yanzu duk samarin dake kofar gida basu ji bugun gate dinnan ba,

mtsww... ya ja tsaki ya dauki torch ya bude kofa,

Wayeeee ne?
Baffa ya tambaya cikin muryar bacci,
Nice,
Nadiya ce,
Dan Allah ka bude Baffa,

Tsaki ya kara ja yace ohh ya Allah,
Ya bude gate din ya kalleta Sama da kasa yace "lafiya da wannan daren?

"Baffa--- baba zai mutu, dan Allah kazo muje ka kaishi asibiti, Dan Allah baffa,

harararta yayi yace "kece kike daukar rayuwa da kikasan zai mutu,

waya ya ciro a aljihunshi yace bari in kira Antyn ku sai kije ta bada driver sai ya kaiku,

dadi taji cikin ranta dan ko ba komai ya kula,

sau uku ya kirata bata dauka ba,

kudi ya ciro a aljihunshi Naira dari biyu,
bai duba duhun dare ba yace
"maza ki samu Mota kije gidan ki buga musu kamar yadda kika buga min,
kinga babu kowa a gidan nan bare ince su kaiki,

tsugunawa tayi ta karba tayi godiya ta juya da sauri ta tafi,
duk motar da ta tara kin tsayawa tayi, gudun ta sake yi har Allah yasa ta samu machine, ta hau ya kaita har kofar gidan,

Tura kofar tayi ta shiga, Mai gadin gidan ta hango a can kofar bayi,
da gudu ta shige ciki,
kofar parlon ta fara bugawa da karfi,

Badariyya dake daki ta jiyo bugun kofa,
bugun zuciyarta ya tsananta, ta fara gyara jikinta,
wannan Karan doguwar riga ce a jikinta silk material,
Tayi kyau ainun,
tafiyarta mai kyau takeyi har ta isa kofar,

Bacin rai ne ya ziyarci zuciyarta ganin Nadiya a tsaye,
waje ta leko a hankali taga babu kowa,
dogon tsaki taja a ranta tace "duk gyaran nan da nayi na wannan banzar ne,

"Badar Ina mummy? Nadiya ta katse mata zancen zucin da takeyi,
Kallon banza badariyya tayi mata tace " ta tafi koyo sallama,

Badar plss is very important in ga mummy, Dan Allah tana ina,

kofa Badar ta kama zata turo Nadiya tayi saurin riketa tace, "plss Bad---- don't u dare, Badar ta katse ta hade da bige hannunta,
dis nyt is very important for me as well, banason abin da zai bata min shi kin gane ko,
ki bar gidannan kafin ki hadu da wulakanci marar iyaka,

da karfi ta turo kofar ta jingina a jikinta tana maida numfashi,
i hate her, wayyo Allah na, ta fadi hade da dafe goshinta, ganinta a daren nan ya kara darsa hassadarta a cikin ranta,

me ya kawota gidan nan cikin daren nan? ,
daren da ta kosa da zuwan shi shekaru da dama, tun bata gama sanin kanta ba, ,

daren da take mafarkin zuwanshi a cikin yan kwanakin nan,

ta window ta leko ta hango Nadiya na tafe tana kuka hade da shashsheka,

zuciyarta ko digon tausayi babu dan a tunaninta wani abun ne ya kawo ta wanda ya danganci taimakon kudin abinci,

parlor ta karasa ta zauna tana saka yadda zata ganshi a zahiri,
tun tafiyarshi basu taba ko da waya ba,

Bayan tafiyarshi ne ta fahimci ya zamo wani bangare na rayuwar ta,

a karancin shekarunta ta fahimci lallai shi din wani sashe ne a cikin labarin rayuwar ta,
hotunanshi da ke kan IG  ta bude ta fara dubawa,

"kyawun gaske" jajayen labbanta suka furta cikin taushi..

Hoton da yayi posting last a jirgi shi tayi zooming, lumshe idonta tayi tana hango yadda zatayi mishi in ya shigo gida....

A gajiya yake saukowa daga matattakalar jirgin,
akwatin shi yake ja yana tafe cikin kasaitarshi da ta kara karuwa saboda gogewa da Ilimi,

Salam alaikum Malam,
Kamar "Little Diku ko"?
kyakykyawan saurayin ya tsaida shi yana tambayarshi,

daga kai Musaddiq yayi alamun nazari sannan ya sauke ya kalleshi yace "noop wannan
"ENG MUSADDIQ M KYARI"  ne duba cikin Sauran mutane may be ka ganshi,

akwatin shi ya cigaba da ja,
saurayin ya biyo shi ya rike akwatin yace "so sorry guy,

kamaninku sun baci, saidai ni Diku na ba haka yake ba,

okk den, je ka nemoshi sauri nakeyi, abokina na jirana a waje musaddiq ya fadi fuskar nan a tamke kamar da gaske,

kallonshi saurayin yayi Sama da Kasa ya juyo shi sosai sannan ya d'aka mishi duka  hade da rungumeshi sosai,
"I miss so much friend,

"missed u more Mahmud, musaddiq ya fadi yana dariya,

kaga yadda ka zama kuwa, omg, KYARI ya zama big guy, Allah yasa ZUCIYAR ma ta girma, Mahmud ya fadi cike da zolaya,,

daure fuska Musaddiq yayi yace bansan iskanci, dama abin da yasa kace kai zaka zo daukata kenan,

dariya sosai Mahmud yayi ya dauki jakarshi yaja hannunshi yace "sorry abokina,

kasan a gida nace musu sai gobe zaka dawo jirgin ku ya tsaya,
BADAR ce kadai tasan yau zaka dawo, yanzu ma ta kirani,

"kace ni yau da yunwa zan kwana, musaddiq ya fadi yana Murmushi,

Mota Mahmud ya bude yace "why? , nasan Badar ta shirya zuwanka tunda tare muka hada plan din nan,

bude motar kawai yayi yace lallai kam,
Badariyya da kanta, ni tunda na tafi ko sau daya bamuyi waya ba,
tada mota Mahmud yayi yace "haba dai,
"am serious musaddiq ya fadi yana zare takalmin kafarshi..

  Hirar yaushe gamo suka shiga yi cike da nishadi wanda ya mantar da musaddiq gajiyar da ya kwaso,,

Karar wayarshi ce ta katse hirar,

da fara'ar shi ya daga yace "my chocolaty bakiyi bacci ba,

daga dayan bangaren tace
"ohhh haba uncle wani irin bacci, bamuji ko kun isa lafiya ba,
Ga mum can sai gyangyadi takeyi ka barmu da jira,

auuchhh,  so sorry, kinsan ko na kira bazai je ba, jira nakeyi inje gida in kiraku,
ina take bani ita?

gaisawa sukayi da anty reema da papa,,
sannan suka cigaba da hira shi da Hinad,

INA ON ELEPHANT ,? (KANGIWA)
dariya sosai Hinad tayi ta kalli gefen da Hilal yake zaune cike taff da tarin takaddu a gaba,
a hankali tace "gashi can as usual rai a bace,,
dariya Musaddiq yayi yace "Me kuma akayi mishi?

Su ADEEL nd dere rashin ji, suka jika mishi sketching dinshi da water gun dinsu,
kaga yadda yayi musu duka, ko kunyar idon MEERAH baiji ba,

kai mishi wayar in mishi magana, kin sanshi da son sktcn dinshi,
ko ni da muke tare ban taba ganin su ba duk tsawon shekarun nan,
su ya akayi suka gani?

oho fa Hinad ta fadi tana karasawa gurin Hilal,

mik'a mishi wayar tayi tace "uncle yace in baka,
kamar bazai karba ba sai kuma ya karba ya kara a kunnenshi....

Kiiiiiiiiiiiiiiiiiiii!!!
ya taka burkin da karfi hade da fadin Inna lillahi wa inna ilaihir,

Tsayar da wayar musaddiq yayi a kunnenshi kamar wanda aka dasa, zufa ta shiga karyo mishi,
kirjinshi kamar zai fado saboda tsabar firgici,

Da sauri Mahmud ya fita cike da masifa ya fara surfa mata zagi jiki na rawa,

dago kanta yayi daidai da hasko fitilar da musaddiq yayi alamun kiran Mahmud dan yazo su tafi tunda ba abun da ya faru,

tsayar da wutar yayi chak a Kan fuskarta da ta kumbura ta jike sharkaf da hawaye,

girman da ta kara bazai sa ya manta fuskarta ba domin ita din jininshi ce, wacce tausayinsu ke karya dukkan sassa na jijiyoyin jikinshi,
Cike da tashin hankali ya furta sunan

NADEEYAH!!! ,,

Tunda ya kara wayar a kunnenshi bai ce uffan ba,
tana nan makale a kunnen yanajin duk abin da sukeyi bai tanka ba, bai kuma damu da sanin abinda ke faruwa ba,

sunan da musaddiq ya fadi ne ya sanyashi kallon takardun dake gabanshi ya maimaita sunan Nadeeyah?

"Me ya Samu Nadiya ya fadi da karfi kamar zai tsaga wayar.....

Mrs Tijjani Shattima....
[04/12 09:48] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣3⃣

WOHN IS 3 TODAY

ALHAMDULILLAH WOHN FAMILY I LOVE YOU FISABILILLAH...

A firgice Hinad ta saki kofin da ta Kai ruwa bakinta ta nufi gurinshi,
ihunshi ba ita kadai Ya firgita ba har papa da fitsari ya farkar dashi,
palon ya nufa da sauri.
tsaye Ya samesu Hinad tana rike dashi tana tambayarshi,
wayar dake kunnenshi papa ya amsa Ya Kara a kunne,

Shuru yaji Ya cireta ya duba,
kallon Hilal yayi yace "lafiya dai?, Kai da wa cikin daren nan,?
Kai komai naka baka yinshi cikin hankali,
Chapter 8 · 0% Book details