← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 113

Sashe 91

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rike gaban rigarshi yayi saboda jin shakun da akayi mishi ta baya, yana da tabbacin Irfan ne dan irin kamshin turarenshi ne ya cika gurin,
ganin yana daďa tamke shakan yasa Hilal yanka rigarshi ta gaba saboda ta kama wuyanshi sosai,

iya karfinshi ya sanya ya cire hannun Irfan haďe da hankaďa shi baya.

Taba wuyanshi yayi yana tari kaďan,

saurin rike hannunshi yayi dan kare kanshi murya a kausashe yace

"Wai menene?

Fisge hannun Irfan yayi ya nuna shi da yatsa..
warning mai karfi ya karta mishi na kar ya sake taka kafarshi cikin gidannan in ba haka ba wallahi sai yayi ajalinsa,

Dariya Hilal yayi yana gyara singlet dinshi zaiyi magana yaji muryar Maleekah a bayanshi,

"Hey akan ka yake?
In yazo gidan nan gurinka yazo?

Kayi aikin gabanka ka bar kowa yayi nashi tunda gidan ba naka bane kai kaďai!

Cikin zafin nama ya shako wuyanta dama yana da cikinta na yadda yake ganin an barta tana facaka da kuďi ba tare da an sa mata ido ba,

sakin keyn motarta tayi saboda azaba tasa hannu tana kakari,

Hannu Hilal yasa ya banbareshi a jikinta haďe da shake mishi nashi wuyan da karfi,

naushi mai karfi Irfan ya sakarwa Hilal a ciki da gwiwar hannunshi,

da sauri ya sakeshi ya durkushe rike da cikin saboda azaba,
gaba daya jikinshi ya dau rawa dan jin ciwon yake har tsakiyar kanshi,

ihuu Maleekah ta saki tayo kanshi ta hankaďe Irfan dake kara tattaka cikin Hilal,
girman gidan baisa kowa yaji ihun ba sai maigadi,
lokacin da ya iso har Hilal ya gama fita hayyacinshi,
cikin kuka tace ma mai gadin ya kira Abbu,
a ruďe ya nufi cikin gidan,
a parlon kasa ya samu Abbu ya fito daga ďakin da Husna take, yana ganinshi yasan ba lafiya,

Nufar gurinshi yayi a tsorace yana tambayarshi abun da ya faru,
bai jira ya gama faďa mishi ba ya fita tsakar gidan da sauri,

daga can gate ya hango motar Irfan sai horn yakeyi yana shirin fita,
inda yake jiyo kukan Maleekah ya nufa,
ganin Hilal a kwance yasashi yin gudu gudu dan ganin abinda ke faruwa,
cikin kuka Maleekah tace

"Abbu Hilal zai mutu,
plss help him,
daukarshi Sheik yayi cikin tashin hankali yana tambayarta abinda ya faru,
bata iya bashi amsa ba ta bude mishi motarta ya sa Hilal a ciki shima ya shiga,
rufe motar tayi ta shiga mazaunin driver ta figeta da gudun gaske...

Asibiti mafi kusa suka je,
lokacin da suka isa Hilal na fitar da numfashi dakyar,

Saboda gigita Sheik baisan takalmin kafarshi ya fita ba,
suna shigar dashi nurses suka shigar dashi emergency,
da sauri likita ya iso gurinshi da taimakon gaggawa,
Allurar pain relief sukayi mishi kafin su gano abun da ya sameshi...

Rungumeta yayi a jikinshi yana rarrashinta,
labarin abinda ya faru take bashi cikin kuka tana zagin Irfan,

Cike da tashin hankali ya zaro wayarshi ya latsa number Irfan,
a kashe yaji ta yayi kwafa haďe da saka abubuwan da zai mishi in Hilal yaji sauki....

Allah ya taimaka babu abin da ya samu Hilal,
zafin buguwar ce ta sanyashi fita hayyacinshi,

Hamdalah Sheik yayi suka nufi ciki gurin Hilal, bacci suka sameshi yana yi hankali kwance,

Zama kusa dashi Maleekah tayi ta kama hannunshi tana murzawa a hankali,
sai a lokacin sukayi tunanin kiran su Papa faďa musu....

Hakuri sosai sheik ya bawa su Papa ya kuma yi musu alkawarin hukunta Irfan hukunci mai tsanani,

"Ah haba,
yarinta ne,
dan Allah ka kyaleshi,
wata rana bazai yi ba,
Allah ya rubuta sai yayi ciwo,
Irfan sanadi ne kawai,
mu dai cigaba da addu'a Allah ya shirya mana su,
Papa ya karashe fuskarshi dauke da murmushi...

Jin shi kawai sheik yayi dan ya riga ya kuduri niyyar hukunta Irfan,
yadda yake jin Hilal a cikin ranshi baya san wani abun da zai taba shi.......

Karfe uku na dare Hilal ya farka daga baccin da ya samu,
Hinad dake zaune a gefenshi ta sakar mishi murmushi haďe da kamo hannunshi,

"Sannu Yaya, ya jikinka,
gyada kanshi yayi ya kalli Anty Reemah dake kokarin ďagashi zaune,
Karfi yayi da jikinshi dan kar ta wahala ya mike zaune haďe da jingina da pillow,

"Me zaka ci in kawo maka?

"Bana jin yunwa Mum,
ya bata amsa yana yamutsa fuska,

"Ai ba dan yunwa zaka sha ba, haďa mishi tea,
papa ya faďi yana miko mata flask...

Tea mai kauri ta haďa ta mika mishi ya fara sipping a hankali,

Buďe kofar su Sheik sukayi, hannun Maleekah rike da wata leda,

"Alhamdulillah, Sheik ya faďi yana nufar inda Hilal yake,

"Are u okk My son?
Murmushi Hilal yayi yace

"yess sir, karka damu, da kun tafi gida dare yayi...

"Nooo dole mu zauna muga yanayin jikinka,
kayi hakuri Hilal, in shaa Allah sai na dau mataki akan Irf---

Plss sir,
Hilal ya katseshi haďe da rike hannunshi
"wallahi na yafe duniya da lahira, kaddara ce,
tana kan kowa, haushina yake ji yanzu, with time komai zai zama normal..

Cike da so da kauna Sheik ya dinga yi ma Hilal godiya da fatan samun lafiya dawwamamma...

Kofin dake hannunshi yake kokarin ajiyewa saboda yadda Maleekah ta kureshi da ido,

kallon Anty Reemah yayi yace "Kuje gida i will be fine here, karku damu,
ina zee dina?

"Tana gidan Mimi Turaki,
can na sauketa dan kar ta haukace mana,
Meerah ma sai kira takeyi kasan dazu ta tafi Malaysia..
Anty Reemah ta bashi amsa tana gyara zaman hijab dinta..

"Yess ta faďa min,
Allah ya maidota lafiya,
plss kuje gida,

Maida dubanshi gurin Sheik yayi shima ya rokeshi da su tafi kar su matsawa kansu,
haka duk suka shirya tafiya dan sunga lafiya ta samu a gareshi...

Chips da chicken salad Maleekah ta buďe ta ajiye a gabanshi ba tare da tace komai ba,
bin bayan Sheik tayi dan tasa shi ya jirata,
tana ganin motar su Anty Reemah ta bacewa ganinta ta fito cikin motar tace mishi tana zuwa,
da yake su larabawa babu ruwansu da bin diddigin 'yayansu in suka yarda dasu sai ya kwantar da sit cikin rashin damuwa ya lumshe idonshi....

A rufe ta samu chips din ta sake budeshi har lokacin da zafinshi,
gefen gadon da yake zaune ta zauna ta buďe tana kallonshi,
ita yadda yake rufe ido ma dariya yake bata,
shi a dole bai san haďa ido da ita,

"Ya Hilal,
ta faďi a saitin kunnenshi,

da sauri ya buďe idonshi dan muryar Nadeeyah yaji,
bashi da dabarar dauke idonshi cikin nata domin kallon da yake mata na daban ne,
yadda ruwa ya kwanta a cikin idanun suka sake kayata kyawun idanun su suka tsuma Maleekah ta ajiye chips din ta kamo hannunshi,
wannan wace irin masifa ce,
a yanzu gaba daya zuciyarta da gangar jikinta sun gama na'am da cewar tana son Hilal kuma tana son karasa rayuwarta tare dashi,

" *I LOVE YOU*

cikin narkakkiyar murya kalmar ta fito ba tare da shiri ba,

Runtse idonshi yayi hawayen dake kwance cikin idanuwanshi suka bayyana kan yalwataccen gashin idonshi..

zuciyoyinshi ne suka shiga kara kainin bashi shawara,
wannan tace
"Allah ne ya dawo maka da Nadeeyah ta wata siga,
wannan yace
"Duk wanda yaso Nadeeyah to ko bazai ki Maleekah ba,
haka nan sukayi ta rikirkitashi...

Bai ankara ba yaji kwanciyar fuskarta kan tafukan hannunshi,
hawayen da ya ďigo a kansu shi ya sanyashi buďe ido da sauri haďe da ďago fuskarta,

Share mata hawayen ya shiga yi zaiyi magana tayi saurin shigewa cikin jikinshi,

"Plss don't say a word Hilal,
plss....
daureshi tayi da jijiyoyinshi kamar tasan abinda yake shirin faďa,
har ga Allah baya kin Maleekah domin wani sashi na zuciyarshi yayi na'am da ita,
saidai sashin da ya mutu da wata soyayyar daban yaki aminta ya farfaďo,
baya tunanin har ya mutu zai iya son wata 'ya Mace kamar yadda yaso Nadeeyah,
ya zame mishi dole ya amincewa Maleekah domin ya daina jin abinda a kullum yake yunkurin mantawa dashi,

Hawayen dake cikin idonshi ya ďigo a kan fuskarta yace

"I love you too Maleekah......

Mrs Tijjani Shattimah.....
[09/06 11:14 AM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Eidukum mubaarak wa aiyyamakum Sa'eedah taqabbalallaahu minnaa wa minkum,wa kullu aamin wa antum bi khair. Eid-el Fitr Mubarak.

Allah ya maimaita mana Ameen.....

Sake kankameshi tayi cike da jindadi tace
"nt too,
i want u to love mee more nd more,

Murmushi yayi haďe da dago fuskarta yace
"Will u teach me how to love u more more more?

Hannayenta ta makalkale a wuyanshi  tace
"we will love each oda more than life itself,

ďaura kanshi yayi kan goshinta yace
"Dare yayi,
go home hoping to see yhu first thing in the morning..
narke mishi tayi tace

"Yaci abinci ko itama taki ci in ta koma gida,
hannu yasa ya ďauko chips din yace suci tare..

gyara zama tayi a kan gadon ya dinga bata a baki itama tana bashi,
duk wani nauyin da Hilal yake ji a cikin zuciyarshi ya ragu,
jinshi yakeyi kamar sabon mutum...

Saida suka gama ci sannan tayi mishi sallama haďe yi mishi alkawarin zuwa da sassafe.....

Cikin wata ďaya soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Maleekah da Hilal,
tun yana jin sonta kaďan kaďan har Allah ya jarbceshi da muguwar soyayyarta, domin ita ďin gwana ce gurin sace zuciya,

Wannan soyayyar da sukeyi Sheik jinta yake duniya Allah ya gama mishi komai da ya bawa yarshi mutum irin Hilal,
jira kawai yake yaji ta bakinsu ya shirya komai cikin kankanin lokaci dan bazaiso yajashi ba saboda masu kawo mata hari kar su hure mata kunne,
shi ko yanzu ne yake jin dadi saboda zai samu surukin da zai iya barwa ragamar dukiyarshi ba tare da tunanin komai ba,

Su Papa kuwa gani sukayi tafi karfinshi saboda Sheik ba karamin mutum bane,
sai da Sheik ya nuna musu bacin ranshi sosai saboda banbanta kansu dashi da sukeyi....

A ranar da Maleekah taje mishi da maganar yayi matukar farin ciki,
nan take ya kira Daddy da Papy ya sanar dasu sannan yace basai kowa yazo neman aure ba domin Hilal nashi ne,
sati biyu ya sanya bikin saboda bashi da wani shirin da yake dashi,
Chapter 91 · 0% Book details