Sashe 31
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nadeeyah bata kula ta ba ta juya ta cigaba da fito da kodaddun kayanta tana cigaba da jerawa,
a harzuke Badar ta fincikota tayi wurgi da ita,
"ke har kin isa ina miki magana kiyi banza dani,
leda ta dauko tasa a hannunta ta fara fito da kayan tana fadin "bazan iya taba dirty kayan nan da hannuna ba,
ke in banda ma shegen tsaurin ido har kina da confidence din shigo mana daki ki fara jera kayanki,
baki ma da hankali tunda har baki iya bijirewa kice dakin yafi karfinki ba,
rufe drawer tayi bayan ta gama fito da kayan tace "oya oya maza hada tsummar roba robarki ki kara gaba, nan dakin yafi karfin kazamai irinki,
Nadeeyah bata amsata ba ta tattara kayanta cikin jaka ta sa a can wani lungu ta yi hanya fita parlor,
da karfi Badar ta janyo mata hijab har yana shaketa,
harararta tayi tace "uban wa kika barwa kayanki?
dalla wuce ki dauke mana su ko dakin mu zai samu saukin wari,
cikin sanyin Murya Nadeeya tace "Badariyya sake min Hijab kin kama min wuya,
"bazan sake ki ba, Badar ta fadi tana girgiza jiki,
Kwacewa Nadeeyah tayi da kyar, ta dauko jakarta ta bude kofar palon,
dankwalinta da ya fado kasa Badar ta dauko tayi saurin binta dashi ta wurga mata tace "dauki kayan war---- bata karasa fadi ba saboda hada ido da tayi dasu Hilal da Mummy a palon,
sakin kofar tayi ta koma ciki ta fada bayi da sauri,
a yanayin da taga Hilal tasan zai iya yi ma jikinta lahani,
tsaki tayi tace "shigowar yarinyar nan rayuwata babbar matsala ce wallahi,
hankalina bazai taba kwanciya ba har sai ta bar gidan nan,
tunowa da tayi an kusa komawa school yasa ta sakin murmushi tasan in ta tafi school zasu dan sarara....
A tare Musaddiq da Hilal suka mike suka isa gurin Nadeeya, jakar Musaddiq ya karba Hilal ya bude dakin yana kwala ma Badariyya kira,
farkawa Husnah tayi a tsorace tace "ya Hilal lafiya,
"ina Badariyya?, ya tambaya yana huci,
bargonta Husna taja tace "anan take kwance sai dai ko in tana toilet,
hanyar toilet din yayi mummy tayi saurin tare shi, tace "kwantar da hankalinka,
barni da ita,
Nadeeyah dauki kayan ki sa a drawer,
jin muryar mummy yasa Badariyya fitowa a bayin tana kukan da ba hawaye,
"Mummy fa ba wani abu na mata ba,
cewa nayi kayan sunyi datti kuma sun kode ta fitar mana dasu kar ta kawo mana kudin cizo, kuma mummy ki kalli gadon yayi mana kadan mu uku, dan Allah ki barta ta koma dakin da ta sauka,
Dunkule hannu Hilal yayi zuciyarshi na tafasa,
baya son kai mata duka saboda kunyar idon mummy da suka fara dasawa yau,
jiran hukuncin da zata yanke yakeyi,
in baiyi mishi yaje ya roki Papa kawai a hada Nadeeyah da zainab su tafi tare,
Murya a kausashe Mummy tace " Nadeeyah a dakin nan zata zauna cikin yan uwanta, dukkanku 'ya'ya na ne,
babu wanda yake bare a cikinku,
ya zama dole ku koyi zama tare saboda zumuncinku yayi karfi,
kallon Husna tayi tace "maza matso ki tayata ku jera kayan,
ke kuma Badar, bana son tashin hankali,
Nadeeyah yar uwarki ce, kaddara ce ta sanya kukayi nesa da juna, yanzu kuma Allah ya hada ku, kuma kinsan baki da yadda zakiyi da hadin Allah...
Ajiyar zuciya Hilal yayi a ranshi yace "Allah yasa Mummy ta daure a haka,
yanzu ne zai tafi hankalinshi a kwance,
yafi son yayi nesa da ita ta samu damar yin karatunta ta zama cikakkiyar mace,
yasan in har yana ganinta kullum bazai iya controlling kanshi ba, dole yayi abin da zata gane halin da yake ciki,
shi kuma ba yanzu yake son furta mata ba,
yana matukar tattalin kalmar har sai ta cimma lokacin ta.....
Karfe 5pm suka dawo gida hannunsu rike da ledoji,
kalolin jallabiya guda shida Hilal ya siyo ma Nadeeyah, sai flat shoes guda biyu milk nd brown, dayar ledar kuma jallabiya ce guda biyu,
kwala kiran Husna yayi,
da sauri ta fito daga kitchen tana tsane hannunta tace "ya Hilal gani,
"ledar ya mika mata yace "wannan naki ne,
kinsan yanzu mun fara dasawa, tsalle tayi tana ihu tace "Thank u *bro Son* , bai damu da sunan da ta kirashi ba yace "wannan ki kaima Nadeeyah,
kinga kayanta duk sun kode,
zan ma Anty Rally magana sai kuje kasuwa a samo mata yan atamfofi,
karbar ledar tayi tace "ummm ya Hilal ashe dai kana da kirki, gaskiya thank u,
kamar kasan in tasa kaya abin na dan taba ni,
wasu ma sun mata kadan,
Murmushi jin dadi yayi yace "yauwa gaskiya i love u, u will be my personal person daga yanzu,
dariya tayi tace "godiya nake, gashi gobe zaka tafi, gaskiya zanyi missing dinka, bari naje na kai mata, nasan zata ji dadi....
Bude kayan Husna tayi ta dinga yaba kyawunsu tana gwadawa a jikinta,
tana cikin gwada wata ja a cikin na Nadeeyah Badar ta shigo dakin,
zama tayi a gefen gado ta dauki daya a ciki tace "waye ya kawo mana jallabiya, shine har kika fara zaba baki jirani ba ko ta fadi a gadarance,
kwacewa Husna tayi tace "to Mummy kiyi hakuri,
ya Hilal ne siyan ma Nadeeyah,
ta dauko nata tace 'kinga nawa nima,
wayyo, ai kamar Husna ta watsa mata ruwan zafi haka taji,
dama duk yau cikin kunci ta wuni saboda yadda Mummy tayi wata wuzu wuzu akan Nadeeyah,
mikewa tayi idonta ya ciko da kwalla zata bar dakin,
tausayi taba Husnah tace "sis zo wasa nake miki,
guda biyu ya kawo mana ni da ke fa,
sauran ne na Nadeeyah saboda bata a kaya,
bata saurareta ba ta fita daga dakin dan tasan Hilal bazai taba yi mata kyauta ba,
ninke kayan Husna tayi ta maidasu cikin ledar ta wuce kitchen ta kira Nadeeya,
A tsorace Nadeeya ke daga kayan tace "duka nawa ne?
gyada mata kai Husna tayi tace "u are very lucky, yaya Hilal bai taba kyautar ko da naira dari biyar ba, yaushe ma kaga fuska a gurinshi bare ya baka,
sai gashi yau har ni ya hada,
dark blue din ta dauko a ciki tace "gwada wannan nasan zata miki kyau,
bayi taje ta sa a jikinta,
fadin rigar yayi mata cibb saboda tana da dan jiki,
sai dai tsawon ya so yayi mata yawa,
madubin bayin ta kalla hade da gyara gashin da ya kwanto a goshinta,
ita kanta ta yarda a zuciyarta rigar ta mata kyau,
dakyar ta iya fitowa daga bayin saboda kunyar Husna,
wooooww..
Husnah ta fadi a fili,
a cikin ranta kuma tace "see beauty, oh Gosh, Allah baya bawa mai wuka nama,
"kinga yadda yayi miki kyau kuwa,
kunya ce ta ishi Nadeeyah tace " nagode,
bari inje in cire,
tareta Husna tayi tace "godiya dai zamu je kiyi ma "ya Hilal, daburcewa Nadeeyah tayi tace "a'a dan Allah bari in canza kaya sai muje, dagewa Husna tayi tace lallai sai dai suje a haka,
dakyar ta yarda ta yafa gyalen a kanta,
murda kofar dakin suka ji anyi,
a tare suka waigo,
daburcewa Nadeeyah tayi ganin Musaddiq da Hilal tsaye a bakin kofar,
karasowa ciki Musaddiq yayi cikin zolaya yace "a'a iyye, kaga kanwata,
ashe dai kina da kyau haka,
to juyo ki nuna mana kwalliyar mana,
janyo hijab tayi ta cukwikwiye kanta tace "ba kwalliya nayi ba, Husna ce tace in gwada ko zai min daidai,
dariya yayi yace "kuma ya miki kyau, ashe dai mun iya zabe,
to babu ko yar godiya,
kara rufe fuskarta tayi tace "yanzu dama zamu je muyi, kuyi hakuri, Nagode Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen Ameen, muma mun gode da addu'ar da muka roka,
gurin Hilal Husna ta matsa tace "ya Hilal kaga yadda kayan suka karbemu,
thank u once again,
murmushi yayi yace "never mind, kinga mukullin motata cikin kayan nan,
zazzage kayan ta koma tayi,
babu komai a cikin su, dago kai tayi tace "baya ciki, ko ka barshi a jikin motar?
Tunani ya fara yi yace "eh to bari inje in duba,
ta gefen ido yake satar kallonta tun shigowarshi dakin,
sai da zai fita ne ya kalli yadda ta matse kanta,
murmushin shauki yayi ya fita zuciyarshi wasai saboda yadda yaga ta fara samun sakewa a gidan.....