← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 113

Sashe 21

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan tsaki yayi yace "Gambo ke kike ta aure,
bakya ganin halin da nake ciki,
ko bacci bana iya yi,
daga na runtsa fuskar saurayin da na kashe nake gani yana matsowa kusa dani zai illata ni,
mafitar halin da nake ciki zaki nema, ba wai maganar aure ba,

cike da alajabi tace "yau ka fara kashe mutum?
a kiyasin da nayi ka kashe ya kai talatin banda dabbobi,
meyasa zaka sa wannan a ranka,

Katseta yayi yace "wannan na daban ne Gambo,
duk sauran kisan da nayi musu akwai kwakwkwarar hujjar yin hakan ya karashe ido yayi mishi jajur,
kasa daure damuwarta tayi tace "tashi muje gurin Hardejo,
tashi maza,
bazan juri rashinka ba Shaho,
mikewa yayi jiki babu kwari suka kama hanyar gidan Hardejo....

Allah gafurur rahim,
lallai "Bala Shaho" Allah yana sanka da rahama,
wannan abin da kakeji Allah ne ya fara nuna maka illolin abinda da kake aikatawa,
lallai jinin Habibu jini ne na mu'imini,
Adduoin da iyaye da yan uwanshi sukeyi akanka bazai taba barinka kayi sukuni ba,

A farkon zuwan musulunci kauyen nan, naso mu rugumeshi cikin tsaftatacciyar hanya,
amma sam kuka ki,
kuka amsheshi sama sama,
ku ka dinga aikata sabo saboda ance muku ko an aikata Allah na yafewa,

cike da kunan zuci shaho yace "maleee, (sunan da suke ce mishi kenan cikin isgili) yanzu ka fada min abinda zanyi in daina jin wadannan abubuwan da nake ji,
gyara zama malam yayi ya mishi bayanin addinin Allah da duk abinda Allah bayaso,
sannan ya daura mishi da cewa "ta yiwu Allah ya yafe maka saboda kayi abubuwan da kayi a baya cikin rashin sani,

kasan Allah baya kama mutum da laifin da baida masaniya akai,
sannan sharadin tuba,
sai ka tabbatar in ka daina ji da ganin abin da kake gani bazaka sake komawa cikin aikata sabo ba,
'""Bazan sake ba malee"" ya fadi da sauri,
ni kadai nasan irin wahalar da nasha,

to Alhamdulillah Hardejo ya fadi yana murmushi,
sannan ya fara koyar dashi kalmar shahada da kuma istigfari,
ya horeshi da yin istigfari kafa dubu a kullum saboda yana kankare zunubai,
sun dade tare yana koya mishi abubuwa zuciyarshi na samun nutsuwa,

ita dai Gambo zama tayi kamar gunki tana kallon sabon mutum a gurin danta,
da yake ita din mace ce mai son danta, da duk abin da yake so nan take itama tayi mubaya'a,
malam Hardejo ya cigaba da fadakar dasu akan abubuwan da Allah keso da wanda baya so.....

Rayuwar Atika a gidan Baffa, Rayuwace da ta fara yinta kadaran kadaham,
sam ma'u bata kishi da ita saboda sanin yanayin da sukayi auren,

da fari ta fara bijirowa da cewa tunda yanzu Shaho yayi nadama ya shiryu mai zai hana Baffa ya saketa ta koma ta auri shahon,

a lokacin taga ainihin Fillo Hardejo,
dan saida yayi mata wuzu wuzu sannan ta maida hankalinta,
da yaga ta nutsu ne yasa shi ya koma lallashi,
ya cemata ta sani ko tuban muzuru Shaho yayi,
irinsu ba'a gane tubansu har sai an musu gwaji mai karfin gaske,

cikin hikima ya kwantar mata da hankali,
samm baya ko kaunar hango rabuwar Atika da Muhammadu saboda yasan ko babu rayuwarshi Atika zata zame ma dan uwanshi alkhairi.....

****

Ashe dai ma'u baki da hankali ban sani ba kuma ban gama tabbatarwa ba sai yau,
yanzu har wannan tsaleliyar budurwar Baffa zaice baze kusanceta ba kuma ki yarda,

naman zomon da ta gasa takai bakinta tace " Haire am niko nake da hankali,
an fada miki hakanan na sakankance,
ai ba sakarai nake ba,
nasan yadda Baffa yake da sakarcin nan akan mace wata rana zai iya kusantarta a bayan ido na,
shiyasa na aika can garinmu gurin "Iyan gida" ta amso min gadalin mu na ukari,
sannan ta hada da duk wata mallakar maida mace namiji a idon Baffa,
yaushe zanyi wannan wawancin a barni in zama yar kallo,
ai dole na mike tsaye ko dan yadda Hardejo ke nuna min ita din kamar yarshi take ta jini,

shewaaa sosai sukayi hade da tafawa,
dariya Bingel tasanya itama ganin mahaifiyarta na dariyar babu kakkautawa,
dariyar tata ta sake sasu wata dariyar hade da kai naman zomon na karshe cikin bakinsu....

Kallonsu Atika tayi itama tayi murmushin saboda bata san abun da suke fadi ba,
kara gyara goyon boddo tayi tana jijjigata tana mata wakensu na larabawa,
tunanin Ateek ta tafi wanda ya zame mata tamkar shan ruwa dan kullum,

Ya Allah ka dubamin Ateek.. kalmar kadai take ta maimatawa cikin harshenta na larabci......

Mrs Tijjani Shattima......
[02/03 9:59 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣5⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*

*RUBUTACCEN AL'AMARI*

Sauri sauri yake yi dan samun sahun gaba a cikin masallacin kofar gidan Hardejo wanda Barde da Gambo iyayen shaho suka gama gininshi,
dabe ne na kasa suka bada kudi aka hada karfi da karfe aka ginashi cikin gaggawa,

Shaho ne tsaye a kofar shiga yana sallama ga duk wanda yazo shiga, sanin muhimmacin Sallama da yayi, da kuma irin ladan da ake samu ya sanyashi a koda yaushe fara yin ta ga duk wanda yayi tozali dashi..

Bayan idar da Sallah Malam Hardejo ya zauna a tsakiyarsu ya fara janyo musu wa'azi mai kashe jiki,
kowa a cikin massalacin saida ya nutsu,
zuciyoyinsu suka narke matuka da tsoron Allah,
a cikin wa'azin ya sako musu muhimmacin aure da kuma hakkin da mace take dashi akan mijinta,

"Hakkin duk wani namiji ne ya ciyar da matar shi,
Hakkinshi ne ya tufatar da ita, sannan Hakkinshi ne ya sauke duk wata bukata tata,
lissafo bukatun yayi cikin hikima, sannan ya tunatar dasu azabar da mutum zaisha a gurin ubangiji in bai sauke wannan hakkin ba, wa'azi sosai yayi mai cike da tausayi da al'ajabi...
jikin kowa a sanyaye suka tashi suka fita daga masallacin,
matsowa Bala (shaho) yayi kusa da malam yace "Assalamu Alaikum, a sanyaye Malam ya miko mishi hannu suka gaisa hade da yiwa juna murmushi, kayi hakuri Bala,
yau jikina baya min dadi, bazamu samu damar yin karatu ba, murmushi Bala yayi yace "Babu matsala Malam, Allahn Hardejo ya kare ka da lafiya,
dariya malam yayi yace "Allahn mu gaba daya, gatan mu, kuma gatan zuri'armu....

●●●●●●●●●●

A hankali ya tura kofar gidan ya shiga,
wa'azin Hardejo keta kai komo cikin kwakwalwarshi, zama yayi a tsakar gidan kan wani dakali, tunani ya dingayi na yadda zai sauke hakkin marainiyar Allah akanshi,
ga kuma alkawarin da yayi wa ma'u shima kuma Allah baya son mai saba shi,
yana cikin wannan tunanin ne ruwa ya kece a kanshi,
mikewa yayi da niyyar wucewa daki sukayi karo da Atika ta fito ta kwashe kayan da ta wanke a kan duwatsun shanyar gidan,
matsawa baya yayi da sauri yana mayar da numfashi,
rab'awa tayi ta wuce ta kwaso kayan,
kafin ta gama kwashe kayan gaba daya ta jike sharkaff,
kallonta Baffa ya tsaya yi shima ruwan ya jikashi sosai,
saida ta gama kwashewa tazo wucewa yaji ta dan gogeshi da kaya sannan yayi firgigit ya gane ta wuce,
yasan ma'u bata gidan,
tana can gidan inna wuro tare da yara,
da jan kafa ya bita dakin,
cikin kudurar ubangiji ya fara jin wani abu na fusgarshi game da ita,
shaukin da bai taba jin irinshi ba ya shiga,
a hankali ya kusanceta ya taimaka mata ta rabu da jikakun kayan jikinta,
tuni labarin ya canza zuwa wani sabon babi na shafin labarin....

Mikewa yayi jiki a sanyaye zuciyarshi kamar an sauke nauyin da yakai girman dutsen mambila,
ita kuwa azaba ta hanata yin kuka, dakyar ta iya tashi,
abinka da mutumin "da" shi ficewa yayi yaje bayi ya wanke jikinshi ya barta a cikin dakin,

A daddafe ta fito tsakar gidan, tunanin yadda zatayi ta rabu da wannan azabar da take ji take yi, dakyar ta iya ďiban ruwa ta wuce bayi,
tsugunon ma zame mata aiki yayi amma haka ta daure dan dai kawai ta daina jin zafin gurin, tana watsa ruwan sanyin tayi wani irin ihun azaba,
tsakar gidan ta fito tanata safa da marwa tana zubar da hawaye tana kiran sunan Allah,

Azaba kam iya azaba Atika tasha ta a wannan ranar domin ko abincin kirki babu a gidan gashi babu abin da zata iza wuta ta sa ruwan zafi,

A haka tayi tsaye tanata kuka a gurin har dare ya farayi,

surutun Ma'u ta fara ji sama sama a kofar gidan,
nan hankalinta ya fara kwanciya, tasan zata samu ko dan abinci ne taci,

sallamaa dai Amarya,
hannu tasa ta karbi Boddo dake kuka jikinta jike da fitsari,
saboda duhun dake tsakar gidan Ma'u bata lura da yanayin tafiyar Atika ba,
daki ta shiga ta yayo yayi ta fito ta dauko dutsen kyasta wuta, kyasta shi tayi cikin yayi nan take haske ya bayyana,
bata kara bi takan Atika ba ta wuce daki ta dauko ragowar Tuwon da sukaci da rana,
saka iya wanda zai ishesu tayi a tukunyar kasa dan ta dumama,
ta zubawa Atika mai sanyin a cikin roba ta tura mata,
dakyar ta iya dukawa ta mika mata Boddo, sannan ta dauki tuwon,
can baya taje ta zauna dakyar tanajin radadin a can kasanta, tsabar yunwar da takeji yasa bataji sanyin abincin ba ta dinga turashi tana zubar da hawaye,
muryar Bingel taji akanta tana share mata hawaye tana bata hakuri,
wani sabon kukan ne ya kufce mata hade da rungume Bingel wacce itama kukan takeyi....

11:34pm●●●●
Chapter 21 · 0% Book details