Sashe 100
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya Taheer yayi yace
"Allah ya kaimu,
Pizza Hut or restaurant?
Pizza nd ice cream Dad,
kwanar da zata sadasu da Pizza hut ya shiga suka karasa suna dan taba hira da junior,
ita kuwa Nadeeyah dake zaune a baya gabanta sai faďuwa yakeyi tana Maimaita sunan,
*MMK*
*Musaddiq Mukhtar Kyari*...
No no no,
tayi saurin kauda hakan a ranta haďe da runtse idonta....
Duk da bai kware a zane ba yayi kokarin zana fuskar Musaddiq haďe da kasumbar da ta kawata kayunshi,
saidai zanen samm bai fita ba dan yayi yarinta da yinshi...
daga gefe ya rubuta katon
*MMK Mus*
Bayan ya gama ya zura mishi ido har bacci ya daukeshi a gurin....
Madarar da ta shigo mishi da ita ta ajiye akan madubi ta fara tsince kayan dake kasan dakinshi tana mitar yadda kullum yake bata daki,
"Bai yar a kasa ba,
zuciyarta ta yi mata tuni da hakan,
murmushi tayi bayan ta tuno da Musaddiq a baya kafin soyayya ta shiga tsakaninsu har kaddarar rabuwa ta gifta..
Zanen da yayi ta daga ta ajiye a gefe,
ta maidashi kan gadonshi ta tofeshi da addu'a haďe da rufe mishi jiki da bargo,
warm ta maida a.cn dakin mai hade da room heater saboda sanyin garin,
tana gamawa ta tattara takardun dan maidasu mazaunin su,
tana dauko wanda ya zana tayi saurin wurgi dashi haďe da dafe kirji,
Yaya..Musa...ddiq,
ta faďi a hankali idonta ya ciko da kwalla,
dago takardar tayi ta kare mata kallo,
bata san lokacin da zuciyarta ta ingizata ta haďe hoton da kirjinta ta durkushe a kasa ta fara jero kuka mai taba zuciya,
"Yhu forgt all the love,
all the promises,
Why did u lv me,
dis is nt fair, why will yhu remind me of ur existnce,
Whyyy.....???
Ta karashe cikin silent cry mai cin rai...
saida tayi kukan ta ma'ishi sannan tayi ma takardar buya ta musamman inda junior bazai taba ganinta ba.....
A sanyaye ta fito daga ďakin bayan ta kashe mishi wuta,
hanyar dakinsu ta nufa dan babu abinda take son kasancewa dashi sai gado da pillow,
tana gab da shiga dakin taji iska sosai tana kaďawa,
dama tun yamma hadari ya haďu,
ragowar kayan junior dake veranda tayi saurin fita dan ta kwaso,
Tsaye ta samu Taheer ya na kwasosu,
karasawa tayi kusa dashi ta fara tayashi kwashewa haďe da cewa "Ashe ka rigani,
bani in kai su daki,
"Bakiyi bacci ba?
Eh yanzu zanyi in shaa Allah, ta bashi amsa tana cigaba kwashe kayan saboda yadda ruwan ya fara sakkowa da feshi,
Jallabiyar da ta rage ta karshe ta daura hannunta zata cire shima ya daura kan nata cikin rashin sani saboda sauri,
A firgice ta kalleshi ta fara kokarin cire hannunta,
yanayin da ya shiga ya haneshi cire hannun saima sake damkeshi da yayi..
Cikin rawar murya tace
"Uncle ruwa,
duk irin karfin da ruwan yayi shi bai gani ba saboda yanayin da yake ciki,
ya zame mishi dole yau ya sauke duk wani nauyin dake cikin ranshi ko zai samu sukuni,
a hankali ya ďaga hannun haďe da rikoshi cikin nashi,
cike da kasala ya matso dab da ita har yana iya jiyo numfashinta haďe da bugun zuciyarta,
Runtse idonta tayi ruwan dake fesowa ya dinga gangara akan fuskarta zuwa jikinta,
sajen ta da ruwa ya kwantar ya kalla wanda hakan yayi sanadiyyar tashin tsigar jikinshi yayi saurin kai bakinshi saitin kunnenta,
"U promise to be with me years back,
will u fulfill ur promise?
everything is back Nadeeyah,
ur love is back,
i love yhu alot,
Will u marry me?
Plsss Nadeeyah....
Yadda yake maganar a wahale ya sanya jikinta mutuwa tubuss,
ya zama dole tayi ma Taheer adalci,
ya sota tun kafin ta gama sanin kanta,
saboda ita ya kai matakin tuzuru babu aure,
ya kula da ita da danta ba tare da bijiro mata da soyayya ba,
ita kuwa me ya rage mata a yanzu banda ta yarda da nagartaccen miji irin Taheer wanda zata samu nutsuwa a tare dashi,
"Uhmm answer me plss ya sake faďi kamar zaiyi kuka,
kayan dake hannunta ta saki kasa cikin raunanniyar murya tace
"Yess i will,
am all yours Uncle...
Ko babu shaidan a wannan lokacin dole zuciyar da ta daďe da tsumuwa da soyayya ta aikata ba daidai,
kamar yadda bature yace (Everything is fair in love and war)
Taheer baisan sanda ya haďa jikinshi da na Nadeeyah ba,
"Thank yhu Nadeeyah,
Thank u so much,
itama lupp tayi cikin faffadan kirjinshi tana sakin ajiyar zuciya mai karfi...
duk irin ruwan dake zuba yana jika su basu dubashi ba saboda dukkaninsu sun shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa....
Saida zuciyar Taheer ta samu nutsuwa sannan ne ya nemi tsari daga sharrin zuciya ya raba jikinshi da nata,
da sauri ta wuce ciki tana maida numfashi da sauri sauri.....
Cikin kwanaki uku soyayya mai karfi ta wanzu a cikin gidan wanda har saida duk mutanen gidan suka gane,
Amal da ta sawa ranta auren Taheer tayi gaggawar cirewa dan tasan dama tuni Nadeeyah yake so,
a take tayi wa kanta addu'ar samun duk abin da zai zamo mata alkhairi....
Ga mamakin Nadeeyah sosai Anty Saude ta sake mata ta dinga lallabata tana nuna mata kauna ta musamman..
Hakan ba karamin daďi yayi ma Taheer ba..
A daren ranar alhamis suna zaune dukkansu a parlor Taheer na yanke ma junior farce yana tsoma baki cikin hirar tasu....
Kallon shi Anty Saude tayi tace "Munyi magana dazu da kawu Tidjani,
na faďa mishi maganar zuwa neman aurenka,
na sanar dashi ina son ayi komai cikin sati ďaya dan banasan wata matsala ta biyo baya,
Mikewa Nadeeyah tayi ta wuce ďaki da sauri,
Dariya yayi yace
"Sai su taho ranar sati dan mu haďu tunda gobe zamu tafi,
ni zanso ma a ďaura auren a ranar Mommah tunda babu wani shirin da ya rage..
Buďe baki tayi cikin mamaki haďe da sakar mishi dakuwa,
Dariya yayi sosai ya dauki Junior suka wuce dakin Nadeeyah......
*******
*Kaduna*
Toshe hanci Raudha tayi kamar zatayi amai,
hawayen idonta ta share tace
"Ya Allah ka sassauta mana,
mun wahala iya wahala,
mun gina ramin mugunta mun auka ciki,
wuyar da muka so wata tasha ita muka haďiya har na tsawon shekaru takwas...
Audugar da ta share ruwan ciwon dake fita a jikin Goggo ta yar a bola.. mistakely ya sauka cikin waken da Radiya ke gyarawa,
Wata ashar ta sakar mata haďe da mikewa tace
"wallahi bazan dafa abincin ba,
ni na gaji wallahi,
duk ku kuka jamin,
yanzu ga Shamsu ko waiwayata baya yi,
yana can ya koma Italy da zama shi da yarinyar da tayi min aikatau,
wannan wace irin masifa ce..
Mummy dai jinsu kawai takeyi tana kokarin daga Goggo ta daurata akan pour,
Kafin ta daurata har ta saki kashin a gurin,
a sittin su Raudha sukayi waje dan dama su ba aikin sukeyi ba,
Shekara uku kenan Goggo na fama da ciwon da babu wanda yasan irinshi,
asibiti sun gaji sun maido ta gida,
wani katon rami mazaunanta yayi saboda zama,
ga wasu ramuka da jikinta yayi yana fitar da ruwa mai matukar wari,
Mummy ce kullum ke hidima da ita saboda a yanzu komai ya fice mata a rai,
gara tayi wannan, ta yiwu Allah ya yafe mata sanadiyyar hakan,
Dakyar ta iya wanke mata kashin ta canza mata gurin kwanciya,
saida ta gyara dakin tsaff sannan ta fita dan shan iska..
Tana zama taji sallamar su Papy da ahalinshi da su Anni,
nan fa ta mike ta dinga musu maraba,
yadda ta fita hayyacinta sai wanda dama ya santa shi zai ganeta,
duk da yanzu suna samun gata domin Raliya na taimakonsu sosai..
Bayan sun duba jikin Goggo suka koma dayan dakin suna ta hirar yaushe gamo,
Awan su ďaya sai ga su Hafeez da 'yayanshi uku..
Suwaiba, Adam, da Autan wanda yake hannu mai sunan Papy,
sai Husna da ta zama big madam,
Dakin suka shiga suka gaida su Mummy sannan suma suka zauna akayi hirar dasu....
Daddy ka dawo ne?
akwai abin da nake so mu tattauna..
Raliya ta faďi cikin girmamawa kamar yana gabanta,
"Eh Raliya,
muna kaduna, jibi zan koma lagos kina iya zuwa gida yanzu,
Cike da jin daďi ta mike ta fara shirin zuwa gidan su Goggo dan ta taho dasu Mummy,
dama tun last week ta gindaya ma Anty Reemah karyar Goggo ta shiga coma tazo su dubata..
Anty Reemah ta tabbatar mata yau suna nan tafe,
saida ta kaiwa su Fadeel abinci makaranta sannan ta wuce gidan Goggo...
Taji dadin ganin su Papy,
nan take ta shirya plan din da yasa duk suka shirya tafiya gida..
Goggo kaďai aka bari a gida sai Rilwanu dake zaman jiran zuwan iyayenshi....
Suna isa gidan Mummy ta fara hawayen bakin ciki da dana sani,
lallai in baka godewa Allah ba to tabbas zaka godewa azabarshi,
A darare ta karasa cikin gidan saboda gudun wulakanci a gurin mamallakin gidan...
A lokacin da yaji sallamar su yana parlor yana kallon news,
da sauri ya mike ya taro Papy yana faďin maraba da proff,
bismillah shigo,
bai lura da mutanen bayanshi ba saboda yadda yayi kewar ganinshi shekara da shekaru,
Saida suka nutsu cikin gaisuwa sannan ya kalli sauran mutanen parlon,
yana sauke idonshi kan su Mummy mood dinshi ya canza gaba ďaya,
Cike da masifa ya mike zaiyi magana yaji Sallamar su Anty Reemah,
nan take fuskarshi ta sauya yace "A'a yau gida yayi albarka,
Allah ya sanya alkhairi a wannan taron..
kafin a amsa da Ameen
Muryar little Nadeeyah ta karaďe parlorn,
*HABIBI*,
*YAA OMRI*..
Ta sama Musaddiq ya leko dan jin muryarta kamar amsa kuwwar speaker..
ganin parlon a cike yasashi sakkowa da sauri..
Da ita ya fara tozali rike da kugu tana mishi wani irin kallo,
karasowa yayi ya dagata sama ya dinga juyata tana kyalkyala dariya,
Wani wawan duka Hilal ya kai mishi a baya sai a sannan ya dakata ya rungumeshi,
haka nan ya tsinci kanshi cikin farin cikin da ya rasa na meye,