Sashe 37
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallon ledar tayi taga magungunan mura,
murmushi tayi ta kalleshi bayan ya gama wayar tace "Sir kaima mura kakeyi,
bai kalleta ba yace "ni lafiyata kalau,
na siyo miki ne in mura ta kamaki kisha,
murmushi tayi dan ta gane Nadeeyah ya siyo mawa tace "bana fatan Mura, saidai nagode sosai zan bawa yar uwata ita murar ta kamata,
gyada kanshi yayi yace "kin kyauta,
daganan bai kara magana ba har ya kai kofar gidan da ta nuna mishi,
godiya Husnah tayi mishi ya amsa yana dan mata murmushi,
cikin sanyin murya Nadeeyah tace "Mun gode Allah ya saka da alkhairi, Ameen yace a cikin zuciyarshi,
a fili kuma murya can kasa yace "baki da matsala in kinyi failing test ko? It's well, na lura ai karatun bai dameki ba,
yadda yayi maganar ba tare da ya kalleta ba ya dan bata mata rai,
murda kofar tayi ta dauki school bag dinta tace "nasan bazakayi failing dina ba, ni nayi failing, shiyasa zan duba mistakes dina in gyara a exams,
tana kaiwa nan ta rufe kofar ta fara tafiya,
murmushi Husna tayi tace "haka take sir, ko cutarta akayi zata dauki kaddara tace haka Allah ya rubuta,
mun gode sosai, itama ta bude kofar ta fita,
kallo yabi Nadeeyah dashi,
ji yayi kara samar mata special guri a cikin zuciyarshi,
zai tada motar kenan yaga sun tsaya jikin motar da tazo shiga gidansu,
dariyarta mai kyau ya hango, nan ya shagala da kallonta,
bai kula da maganin da Husna ta manta dashi ba saida ya tada motar,
yana gani yayi saurin kashewa ya fito da maganin yayi hanyar shiga gidan,
da yake gate din a bude yake ya hangosu tsaye da wanda ya shiga da motar,
sanye yake da uniform din Nysc,
akwatinshi Nadeeyah ta dauka yayi saurin matsowa kusa da ita yace "bani yayi miki nauyi,
kin bashi tayi tace "a'a yaya Musaddiq babu wani nauyi,
kama gefen yayi yace "to mu kama,
ni kaina yayi min nauyi bare ke,
har sun kusa shigewa parlon mai gadin ya kwala ma Husna kira,
a tare suka waigo suka ga Uncle Tahir a tsaye a wajen gate,
ledar ya mikawa mai gadin yace ya ba Husna ya juya ya tafi gurin motarshi,
haka kawai yaji zuciyarshi ta rike Musaddiq,
ya rasa dalilin da yaki alakanta mu'amalarsu a matsayin yaya da kanwa,
shiga motar yayi ya fara tukata a hankali kamar baya san barin layin.....
Mrs Tijjani Shattima.....
[13/03 9:58 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣6⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
Magungunan Musaddiq ya karba yace "waye baida lafiya, "Nadeeyah ce yaya, Husnah ta fada tana tura kanta cikin parlon,
kallon Nadeeyah yayi yace "yaushe kika fara ciwo,
cikin muryar mura tace "jiya, akwatin ya kwace a hannunta yace "shan ruwan sanyi da kuma A.c, sam bakwa kula da lafiyarku, ga hancinki nan duk ya zuge yayi ja,
Husna da ta ji me yace tace "walhy yaya laifin Badar ne, kasan a kasa Nadeeyah take kwana,
kuma Badar ta kure a.c,
bargon da take rufa kuma ta jikashi,
da ta gane ina matsa ma Nadeeyah ta kwanta sai ta fara kwanciya tana cike gurin ta barmin guri kadan,
kasan ko school zamu bata hada mota damu,
saidai aje akaita a dawo a dauke mu,
cike da mamaki Musaddiq yace "kuma Mummy ta sani,
a'a bata san tana kwana a kasa ba,
amma tasan ba tare muke zuwa school ba,
ajiye akwatin yayi a kasa fuskarshi ta bayyanar da bacin ranshi,
kallonshi Nadeeyah tayi tace "dan Allah kar kayi ma mummy magana,
zaman lafiya yafi komai, wata rana zaka ga kamar ba'ayi ba,
tausayi ta bashi matuka na yadda take magana,
maganin ya mika mata yace "je ki ci abinci kisha maganin sai ki kwanta, sorry kinji,
gyada kai tayi ta wuce dakinsu, tun daga kofa tayi karo da takalmin Badariyya,
tattaresu tayi ta ajiyesu a mazauninsu,
sannan ta dauke jakar makarantar itama ta ajiyeta a gurin zamanta,
tana cire kaya ta hada da na Badar ta zuba a washing machine, sannan ta fito ta karbi na Husna, bayin Husnah ta bita ta tayata zuba ruwa da sabulu ta murda tace "suje suci abinci,
duk abinda sukeyi Badar na kallonsu tana game a waya,
tsaki taja tayi juyi ta cigaba da abin da takeyi, sam bata da masaniyar dawowar Musaddiq,
duk zatonta motar malam Ali ce ta shigo, shiyasa bata fito parlon ba,
Abinci suka zuba suka ci sannan tasha magani,
a parlon suka kwanta Husna ta kunna tv,
tun suna hira sama sama har bacci yayi gaba da Nadeeyah..
Yana gama shiryawa shima ya fito parlon,
bai nemi abinci ba saboda baya jin yunwa,
zama yayi kusa da Husnah yana tambayarta abubuwan da suka faru bayan tafiyarshi service,
labarai ta dinga bashi na yadda Badar da su Anty Raudha suka sa Nadeeyah a gaba,
ba kamar ma idan Anty Radiya tazo, ta dinga kakalo aiki kenan tana sata kuma mummy tayi ta kallonsu bata cewa komai,
Allah yaya abin da akeyi ba'a kyautawa,
abin haushin ma shine in mukaje gidan Goggo,
in kaga yadda suke mata sai kayi mata kuka,
sai fa in Daddy na nan ne take samun sauki,
Anty Rally ce kadai in tazo zata fita yawo damu ta siyan mana abu iri daya da Nadeeyah, yawancin kayan sawanta ma Anty Rally ke dinka mata,
jinjina kanshi yayi yace "ashe dai har yanzu wannan zumununcin namu bai daidaita ba,
ashe har yanzu bamu zama daya ba,
kallon Nadeeyah yayi cikin tausayawa yace "Ya Allah ka kawo ranar sauyi cikin rayuwar wannan baiwar taka,
taga jarabawa iri iri kuma duk ta dangana, ya Allah ka rangwanta mata...
Suna zaune a gurin har aka kira la'asar,
kin tashinta sukayi saboda kar kanta yayi ciwo,
masallaci ya fita dan zuwa yayi sallah,
ita kuma Husnah ta wuce dakinsu,
tana shiga Badar ta fito parlon, jin kamshin turarenshi ya tabbatar mata da dawowarshi, shekeke ta kalli Nadeeyah tana baccinta hankali kwance,
kitchen ta shiga ta dauko swan mai sanyin gaske a fridge,
ko dar bata ji a zuciyarta ba ta bude ruwan taje saitin kunnen Nadeeyah ta kwarara iya karfinta,
wani irin ihu ta saki wanda ya janyo hankalin Musaddiq dake dawowa daukar wayarshi da ya manta,
da sauri ya karaso parlon ya tadda Badariyya tsaye a kanta, tana ganin shi ta ajiye gorar ta fara cewa "ni bansan tana gurin ba,
ruwa nake sha ya zubar mata a fuska,
karasowa kusa da ita yayi yaga fuskar Nadeeyan a jike tana ta murza kunnenta ruwan ciki ya fito,
bai tsaya tambayarta ba ya dago kanshi hade da daga hannu zai mari Badariyya,
da sauri Nadeeyah ta shiga tsakiya hade da rike hannunshi tace "kayi hakuri dan Allah, bata san ta zuba min ba,
wani irin kishi ne ya tokare wuyan Badariyya ganin hannun Nadeeyah a jikin Musaddiq din da ta ke kira da nata ita kadai,
cikin bacin rai ta cire hannunta a jikin shi tace "karki sake taba shi, ina ruwanki,
ke zai mara da zaki wani rike mishi hannu,
turata tayi tace "dalla fita a tsakanin mu,
dankwalinta ta dauka zata wuce daki Musaddiq yaja tsaki yabi bayanta yace "in ruwan ya shiga kunnenki muje kiga yadda zakiyi, murmushi tayi tace "bai shiga ba, ina goge gefen ne,
bata san ta nuna mishi ya shiga dan kar ta kara janyo matsala a tsakaninsu,
daki ta shiga ta tarar da Husnah na sallah,
bayi ta wuce ta bude pampo ta zuba ruwa cikin kunnen ta karkata, nan take duk suka biyo sauran ruwan suka fito,
alwala ta dauro itama ta fito dan yin Sallah...
A parlor kuwa bin bayan Musaddiq Badar tayi tana cewa "nifa ba da gangan na zuba mata ruwa ba,
kasan sharri irin na matsi--- katseta yayi ta hanyar nunata da hannu,
yace "wallhi zagi daya kikayi ma Nadeeyah sai nayi miki dukan da ban taba yi ma wani irinshi ba,
Sosai ta tsorata da yanayinshi, dan bata taba ganin bacin ranshi ba sai sanyinshi,
baya taja tana kallonshi har ya karasa gurin motarshi,
wani irin sonshi takeji yana ratsa dukkan sassan jikinta,
kaff fadin duniya ita har yanzu bata ci karo da namijin da yayi mata 100% ba irin Musaddiq,
ganin yanayinshi na yau ya kara dasa mata soyayyarshi a jinin jikinta,
ko wani yanayi yana da shi kenan,
sanyi da zafi, saidai sanyin yafi yawa dan sam baya da saurin fushi,
zai dade yana tara laifi yana ma mutum uzuri, amma duk ranar da ka kureshi shima yanada nashi zafin,
bai taba gano hakan a tare dashi ba saida ya hadu da wasu yan rainin wayau a gurin service.....
Kasancewar lahadi ranar hutu ce ya sanya su shiryawa zuwa gidan Anty Rally,
dama tun friday ta nemi suzo domin su tayata aikin kwalema, basu wani yi kwalliya ba suka sanya dogayen riguna kimono da gyalensu kalar kayan,
babu yadda Mummy batayi da Badar ba taki binsu dan sam basa shiri da Anty Rally,
sallama sukayi ma Mummy suka fita gurin Malam Ali da kafin su fito ya juyar da kan motar,
shiga sukayi ya jasu suka wuce..
A tsaye suka samu Anty Rally a kitchen tana hade haden girki,
tana ganinsu taji dadi sosai tace "yauwa maza ku zo ku karasa, turo baki Husnah tayi tace "ai sai ki bari mu huta,
"iyyyeee Anty Rally tace tana kallonta,
Dariya Nadeeyah tayi ta daura gyalen a kanta ta cigaba da aikin,
cike da jin dadin yadda take komai tsaf tsaf yasa Anty Rally cewa "kai Allah yayi miki albarka, Allah ya kaiki gidan hutu inda zaki huta babu wanda zai sa miki ido,
Ameen Husnah tace hade da cewa tare dani,
rankwashinta Anty Rally tayi tace "Dalla can zo ki hada kayan cikin wancen basket din,
ki jerasu tsaff bari in dauko hijab,
jerasu ta fara yi tace "ina zamu,
liquid anty Rally ta tsiyaya a hannunta ta wanke hannunta tace "gidan Anty Saude,
jiya da daddare ta dawo daga Holland,
shine zan shiga gaisheta,
wacce Anty sauden,
Anty sauden Legacy?
Husnah ta tambaya,