← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 113

Sashe 45

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi shima ya mike yaja kumatunta yace "haka nake so kanwata,
karki kara zubda hawaye kinji?
kai ta gyada mishi ya kashe mata ido daya ya juya zai fita a dakin,

Ganin Badariyya yayi tsaye a bayanshi tana huci,

wani irin kallo yayi mata hade da cewa "lafiya?
Bata iya bashi amsa ba sai hawaye ya ga suna sauka a idanuwanta,

mtswwwww....

dogon tsaki yaja ya bi ta gefenta ya bude kofar dakin ya fita,

wani kololon bakin ciki ne ya turnuke Badariyya tayi ma Nadeeyah wani irin kallo hawaye na cigaba da ambaliya a idonta,

Mikewa Nadeeyah zata wuce Badar ta janyo ta ta hankada ta baya,
"uban me kukeyi a dakin nan ta fadi murya kausashe,

Husnah da shigowarta dakin kenan tace "me ko sukeyi, *Soyayya*
mana,

baki san suna soyayya ba dama?
ta fadi hakan ne dan ta tunzura ta, dan ta gane take takenta da dadewa....

aiko ta tunzuru,
dan hauka ta fara yi, ta cakumi wuyan Nadeeyah iya karfinta tana fadin
"wallahi saina kasheki,

shakar da tayi mata ita ta hana ta ihu mai karfi,
sai hawayen azaba da take fitarwa,

Da Husnah taga ta kasa kwace Nadeeyah a hannunta kuma tana ganin take taken zata iya kashetan da gaske tace

"na shiga uku,
wallahi karya nakeyi,
ki saketa Badar,

inaa kesashshiyar zuciyar Badariyya bata ji bata gani wen it comes to Musaddiq,

Da sauri Husnah ta fita tana ihu tana fadin
"Zata kasheta,
wayyo Allah Anty Raly kizo zata kashe ta,

Wa za'a kashe?

Daddy da ya shigo a lokacin ya tambaya a gigice,

Husnah da kuka ya kufce mata ta nuna dakinsu tace Badariyya zata kashe Nadee----

kafin ta karasa fadi Hilal ya murda kofar da karfi har yana cire handle din kofar,

lokacin da ya shiga kiriss ya rage Nadeeyah ta suma,
dan idonta da ya jike da hawaye ya fara lumshewa,

ita kanta Badar din kukan takeyi, amma zuciyarta ta ki bari ta saketa,
dama wannan damar take jira,
tsanar da tayi ma Nadeeyah mara misaltuwa ce,
gara ta kasheta kowa ya huta,
tasan hukuncinta kadan ne tunda bata kai 18yrs ba "a karancin iliminta na addini",

Iya karfinshi ya sa ya janye Badar, yayi wurgi da ita jikin drawer dakin har saida mudubin drawer ya fashe,

da gudu Musaddiq yayi kan Nadeeyah da ta durkushe tana tari dakyar,
rungumota yayi jikinshi yana jijjigata,
yana kiran sunanta da karfi saboda firgici......

Mrs Tijjani Shattimah......
[24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣2⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Ganin yadda take lumshe ido ya sa Daddy cewa
"kawo ruwa da sauri Husnah,

rige rigen dauko ruwa sukayi ita da Anty Raly,

A kidime Musaddiq ya bude bakinta yana hura mata iskar bakinshi saboda yadda jikinta ya fara saki,

babu wanda a cikinsu ya ji, ko ya saurari irin dukan da Hilal yakewa Badariyya kamar Allah ya aikoshi,

Tun tana ihu anaji har muryarta ta dashe,
da gudu ta rarrafa ta rike kafar Daddy tace

"dan Allah Daddy kace yayi hakuri bazan kara ba wallahi,

finciko Hilal yayi yace "kin san Allah dama,
belt din hannunshi har ya tattare saboda azabar duka,

Badan tausayi ba,
sai dan saboda muryarta ta ishi Daddy yasashi cewa
"kyaleta Muktar!

Badan yaso ba ya kyaleta yana yi mata kallon ban gama dake ba,

a guje ta bar dakin tana ihun azabar haurin da yayi mata a baya,
a kofar shigowa palon taci karo da Su Mummy,

rungumarta tayi a tsorace tace "ke lafiya,
meya faru?

Kankameta Badar tayi tace

"zasu kasheni Mummy,
wayyo Allah bayana,

kallon su Mami da Anni tayi tace "ku shigo ciki ku zauna,

shigowa sukayi suka zauna,

Mummy taja hannun Badar suka shiga dakin,

Tsaye ta samesu dukkansu akan Nadeeyah da ta bude idonta tana maida numfashi,

Belt din hannun Hilal ta kalla rai a bace tace

"uban me tayi maka kayi mata dukan ficewar hayyaci,
abin da ya kawoka gidan nan kenan,

ya ilahi kayi min maganin yaron nan da duk in yazo gidana sai ya tayar min da husuma,
wannan wace irin mas----

dakata min!!

Daddy ya katseta fuskarshi a murtuke babu alamun wasa,

Naji alamar zuwan baki,
muje in samesu,
da kaina zanyi maganin matsalar gidana,
naji duk abin da ke faruwa tun zuwan Nadeeyah gidannan har kawo yau da idona ya gane min,

"Nadeeyah,

Mummy ta fadi a hankali,
ta kalli Nadeeyar dake kwance har lokacin a jikin Musaddiq,

Saida Daddy ya bar dakin ta tambayi Husnah abun da ya faru,

yadda abin ya faru ta fada mata, ta sakaya mata ainihin abun da ya tunzura Badar,

jiki a sanyaye ta fita a daki dan bata da mafita sai jiran hukuncin da Daddy zai yanke....

Ya Musaddiq..
Daddy yana kiranka,
Husnah ta fadi tana ajiye wayar da Daddy yayi kiranta,
maida kan Nadeeyah kan pillo yayi,
ya sauka suka fita a dakin tare da Anty Raly domin kaiwa baki abin ci da sha...

"Baki da karfi dama kika fara *Soyayya*
dagowa tayi ta kalleshi,

tsareta yayi da ido kamar bashi yayi maganar ba,

"ni bana soyayya, ta fadi hade da rufe fuskarta da hijab dinta,
faduwar gabanta ya karu sosai,

nade belt din hannunshi yayi yace
"in ma kinada niyyar farawa gara in tuna miki,
kije ki koyi fada,

dan in baki da karfi zaki cutu a soyayya,

ko tsoron maza bakya ji kin wani tsaya gab dashi,

to da bamu zo gurin ba me zai faru kenan?

Shi---
runtse idonshi yayi maganar ta makale a makoshinshi,
a zuciyarshi yana neman tsari da shedan dake kawata mishi abubuwa marasa kyau,

canza maganar yayi da cewa
"wuyan baya miki zafi,
in yana miki zafi kiyi magana a kaiki asibiti,

"Murya can kasan makoshi tace "zai daina in shaa Allah,
yana yi kadan kadan,

Dauko waya yayi a aljihunshi ya danna number Hinad,
tayi ringing sau biyu, a na uku ta dauka,

"ina Zee,?

jin ya ambaci sunan Zainab yasa ta mikewa zaune,

"bata nan ya Hilal,
sun fita da *Anty Mee*,

kashe wayar yayi ya kira Meerah taki dagawa,

wayar na katsewa tata ta shigo,
video call,
tsaki yaja ya dauka,

"Hi dear,

ta fadi tana daga mishi hannu,

"Hello Meerah kina lafiya?

Kamar yadda ka gani am very ok, but am missing yha, ta fadi a shagwabe,

kauda zancen yayi ta hanyar tambayarta

"where is Zee?

Juya wayar tayi zuwa gurin Su Adeel cikin muryarta mai dadi tace
"say Hi to Ya Hilal,
fitowa tayi a cikin motar wasan yara ta bude hannu hade da cewa "oyoyo!

Murmushi yayi yace

"yawo,

kika fita yawo baki fada min ba, nt good baby,

karbar wayar tayi ta bata fuska tace

"wayau zaka min ko,
dan kaga na hakura bana kuka har yanzu,
ka gudu ka barni baka kaini gurin Adda na ba,

Tun Nadeeyah na rike murnarta najin muryar gudan jininta,
har ta kasa tayi saurin zuwa gurinshi zata karbi wayar,

hada ido sukayi tayi saurin maida hannunta,

dariyar da bata fito fili ba yayi, sannan ya mika mata wayar,

da sauri ta karba sukayi ido da ido da abar kaunarta,

safa da marwa ta shiga yi suna hira cikin farin ciki harda yar kwallarsu,

murnar ganin yadda zainab ta koma ya hanata sukuni ta dinga yi mata tambayoyi,

sun fi minti bakwai suna hira sannan tace "ga Anty Mee ku gaisa,
tana kula damu sosai ni da Ya Hilal,

kallon juna suka yi na seconds kafin Nadeeyah ta saki murmushi tace "ina wuni,
amsawa tayi itama tana mata musayar murmushi,

yadda take jin sunan Nadeeyah a bakin Hilal ya tabbatar mata da lallai ganin da tayi mata yafi jinta,

domin duk kushen mai kushe bai isa ya nemo aibun Nadeeyah ba,

kyawunta na musamman ne,
gashin da yayi kwance a gefen farar fuskarta su sukara kara kawata kyawunta,

gashi in tayi murmushi ko dariya gefen kumatunta daya ke lotsawa can ciki,

haka nan Meerah taji wani abu ya darsu a cikin zuciyarta,

ita kanta Nadeeyah da bata cika lura da abu ko sanyashi a ranta ba taji wani abu kadan game da Meerah,

kallon farko da sukayi wa juna dukkansu suka fahimci jininsu yayi nisa gurin haduwa,

shurun da sukayi suna kallon juna ya sanya Zainab karbar wayar suka cigaba da hira,

Tunanin inda ta taba ganin Nadeeyah meerah ta shiga yi,

dakyar ta iya tunano sketch din da yayi a school as assignment,

duk da wancan da dan yarinta sosai amma ta gane ita ce,

lokacin duk wanda ya tambayeshi sai ya amsa cikin shakiyanci yace

"My dream girl,

a mafarki na na hadu da ita shine kamanninta suka mannu a zuciyata,

nan da nan kamannin Meerah suka canza,
zufa ta fara karyo mata tace "Zee bani wayar nan,

mika mata tayi ta zauna kusa da ita,

"Bani Hilal pls, tace ma Nadeeyah fuskar ta babu yabo babu fallasa,

sai a lokacin Nadeeyah ta waigo ta kalleshi dan ta manta ma yana dakin,

juyar da wayar tayi inda ake iya ganinshi ba tare da ta sani ba ta sunkui da kanta kasa,

wani irin kallo Meerah ta hangoshi yana yi ma Nadeeyah wanda bata taba sanin ya iyashi ba,

lokacin da ta mika mishi wayar bai kalleta ba ya fara kokarin kasheta,

da sauri Meerah tace

"Kangiwa kana ji na?

"Yes Meerah Turaki ina jinki,

yadda ya kirata ya tabbatar mata yana cikin shauki,

"ina kabar Musaddiq,
ta fada tana jin wani mugun kishi a cikin zuciyarta,

sai a lokacin ma ya tuna da Musaddiq yace

"auchh yana daki may be, ko Daddy ya aikeshi,
bari in dubo shi will call u,
ya katse wayar kafin ma ta sake magana,

Yana kashe wayar Husnah ta shigo dakin da gudu tana kiran Sunan Nadeeyah,

Hijab ta mika mata tace "yi sauri kisa,

kallon Hilal tayi tace "my PP,

zo muje kaga wani abun al'ajabi,

Maida wayarshi cikin aljihu yayi ya bi bayansu dan ganin abun da zata nuna mishi...

Ga Nadeeyahn nan....

Daddy ya fadi yana murmushin jin dadi,

Allah kadai yasan irin farin cikin da yake ciki,
gani yakeyi kamar da ita kanta Suwaibar yake zaune,

gefe Nadeeyah ta tsuguna tace "ina wuni,

Hannu Papy ya bude mata alamar ta iso gareshi,
Chapter 45 · 0% Book details