Sashe 60
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya sosai tayi ta fitar mishi da cooler shinkafa da miya da salad,
kamar mayuwancin zaki ya fara cin abincin da ya dade baici irinshi ba,
saida yaci yayi katt sannan ya fara dawowa cikin hayyacinshi,
Dakinshi da ya shiga ne ya sake sanya nutsuwa a tattare dashi saboda irin gyaran da Nadeeyah tayi mishi,
da takalmin kafarshi ya mike a gadon ya fara kwasar bacci hankali Kwance.....
*TUN RAN GINI*
Mrs Tijjani Shattimah......
[01/04 9:50 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*
*EMIR PALACE SASSOUN BOROUM*
Sarkin sassoun boroum ne tsugune a gaban sarki "TIDJANI YALLO" yana mika gaisuwa kamar yadda sarakuna keyi wa na gaba dasu,
bayan sun gama gaisawa aka cika kayayyakin abinci da sha a gabansu saboda girmamawa,
babu abinda Sarki Tidjani da Shareefah suka kalla, bare har su kai ga cin shi,
cikin nutsuwa da kasaita suka gabatar da dalilin zuwansu,
nan da nan aka wakilta dogarai dan suje can rugar Haldo su nemo Hajja yar Ruga su taho da ita,
da yake rugar bata da nisa da gidan sarki sai gasu sun dawo,
cikin girmamawa suka ce bata da lafiyar da zata iya zuwa,
daka musu tsawa sarkin sassoun burum yayi yace "maza su koma su dauko ta,
dakatar dasu Shareefah tayi hade da mikewa tace "su barta kawai, su zasu isa zuwa gidanta,
Duk yadda sarkin sassoun burum yaso nuna musu kaskancin zuwa rugar Haldo hakan bai hanasu zuwa ba,
a cewarsu su suke nema a gurin ta,
ya zame musu dole su ganta yau kota halin kaka.....
Wani irin wari dakin Hajja ke fitarwa,
warin ma marar misaltuwa,
tana kwance a kan tabarmar da takai rabi saboda cinyewa,
dakyar aka iya dagota ta jingina da wani sudadden pillow,
"wani dan kara tayi saboda wani ciwo da yayi mata rami a mazaunanta,
yaron dake kula da ita ne ya sa mata wani pillow a gurin ciwon,
saboda tausayin halin da Hajja ke ciki ya sanya Shareefah sharar kwalla,
Dakyar muryar Hajja ta iya fita tace "sannunku da zuwa,
da kai suka amsa hade da gyara zama akan daddumar da dogarai suka shimfida musu,
saboda son jin abun da ya kawosu ko kyankyamin dakin basu ji ba,
"Daga ina ranka ya dade?
Hajja ta fadi baki na rawa,
Shareefah ce ta fada mata sunanta da dalilin da yasa suka zo gurinta,
bude ido Hajja tayi sosai ta kure shareefa da ido,
*SHAREEFAH YALLO*
kece?
murmushi Shareefah tayi tace "nice,
ashe ma kin sanni,
kuka Hajja ta fashe dashi tace "farin sani,
ni na raineki tun kina tsumma,
nafi shekara ashirin a gidanku tun kafin a haifeki,
ashe zan sake ganinki,
rabona da ke inaga in banyi karya ba yakai shekara arbain, dan tun kina shekara goma sha biyu na bar agadez,
ashe ina da rabon sake ganinki ta karashe da kuka hade da tari,
Cike da kosawa sarki Tidjani yace "sai hakuri Baba,
dama haka rayuwa take,
kuma duniya fadi gareta, wata rana in da rai dole a hadu,
yanzu gashi sanadiyar mutuwar UMMU AYYU Allah ya kawo mu gurinki,
yanzu bamu da isashen lokaci zuwa mukayi ki fada mana labarin da Ummu tace ke kadai ce kika san dashi,
labarin YARIMA,
wani kukan ne ya kufcewa Hajja a zuciyarta tace
"yau labarin da yayi shekara da shekaru a kunshe, hali yasa zata bayyana shi,
labarin da ya zame mata tamkar kwai a cikin zuciyarta saboda riritarshi,
ajiyar zuciya tayi tace
"babu mamaki fitar labarin nan ya zama silar samun warakarta,
Nuni tayi ma yaron dake kula da ita wani gurin dake cike da kaya,
mikewa yayi ya dauko wata jakar saka ya mika mata,
hannu na rawa ta karbi jakar ta dauko wani ginin mutum mutumi wanda yake kewaye da kawunan mutane babu adadi,
Saboda tsananin tsorata saida shareefah ta rungumi kafardar mijinta,
abun ba karamin tsoro ya bata ba kuma ya daga tsigar jikinta matuka,
yadda aka yanyame shi da wasu abubuwa kamar kwari yasanya har sarki jin tsoro amma kadan,
wani guri ta daga a gefenta, inda take ajiyar abubuwa,
nan ta mike dayar ruwa nabin bayanta ta fita tsakar gidan ta daki wani dakali dake kofar dakinta,
nan take gurin yayi rami, hannu tasa ta ciro layu masu tarin yawa,
daga can kasa ta hango kurciyar da suka binne shekara da shekaru kwance babu rai ga layu kewaye da ita,
a gigice ta ciro kurciyar da duk wata sai ta bata ruwa ta mayar ta rufe,
tun da ta kwanta ciwo kusan watanni takwas bata kara bi takanta ba domin itama ba lafiyar gareta ba,
girgiza kurciyar tayi tana kuka tana fadin
*YARIMA ADAMU*
wayyo Allah Kunzo a kurarren lokaci,
nasan duk inda Yareema yake a yanzu to kasa ta rufe idonshi,
wannan kurciyar rayuwar Yareema ce,
Allah na tuba,
wayyo ni Allah,
haka ta dinga fadi hankali tashe,
Da karfi ta saki mutum mutumin hanunta ya tarwatse a tsakar gidan,
nan tabi kowane kai ta cire dabaibaiyin da aka mishi,
runtse ido Sarki Tidjani yayi saboda juyawa da yaji kanshi nayi,
dakyar Shareefah ta tallabe shi ya zauna a kasa ba tare da duban dattin gurin ba,
itama hakan ce ta kasance da ita, saidai ita ta kasa fahimtar komai,
sabanin Sarki Tidjani da komai ya shiga yawo a kanshi,
yadda abubuwa suka faru ya dinga tunowa kamar yanzu ake yinsu,
kusa dasu Hajja taje dan itama wani karfi taji a jikinta,
burinta ta sanar dasu komai da suka sani da wanda basu da masaniya...
"Nasan yanzu wasu abubuwan sun fara dawowa a kanku da kuma daukacin mutanen da suka san Yareema a Agadez,
to saidai abin da baku sani ba shine dalilin da yasa ya kaurace muku ya tafi can wani guri inda babu wanda zai ganshi bare har yasa shi waiwayen gida,
"Adamu Yallo... sarki ya dinga maimaitawa a bakinshi,
fuskarshi yake kallo kamar yanzu suka rabu cikin lambun *Shehrah Agadez*,
ina dan uwanshi ya tafi har tsawon wannan lokacin,
yana kallon fitarshi daga lambun lokacin bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa kiranshi bare har ya tambayeshi inda zashi,
sai yau yaji tunanin ya dawo sabo dal game dashi,
Da sauri ya maida idonshi kan Hajja yace
"ina Adamu?
Me ya sami Adamu?
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me ya shiga kaina har na manta da dan uwa kuma aminina,
Ya salam ya fadi hade da dafe kai..
"Ba laifinka bane Yallabai,
Laifin namu ne,
bakai ba ma kowa a garin Agadez a yau sai ya tambayin dalilin da yasa ya manta da Yareeman da suke matukar so fiye da sarkin Kanshi...
har ke ma Shareefah,
a karancin shekarunki zaki iya tunawa da
*Yeeman ki* ,
*Yeeman Pappalinto*
nan take mafarkinta ya dawo mata sabo,
sunan Yeema take yawan fadi cikin mafarkinta,
wani irin kuka ne ya kufce ma Shareefah ta dinga nanata sunan a ranta,
tabbas ta tuno kuruciyarsu saboda mafarkinta bai rage mata komai ba,
cikin kuka tace "Bani labarin Yeema nah!
Bani labarin dalilin da yasa yayi nesa dani.....
*TUNA BAYA.......*
**********
Ranki ya dade kici abinci dan Allah,
rashin cin abinci zai iya zame miki illa,
kuma kin sani sarki bazai fasa abun da yayi niyya ba,
cikin Kuka Fulani Ayyu tace "Hajjara yanzu anyi min adalci,
ace sarki ya rasa da wacce zai hadani sai da
*Kuyanga Rosalin* ,
kuyangar da na bawa yarda tasan sirrina fiye da kowa,
tayaya zan iya kallon mutanen gari,
wannan ai cin mutunci ne a gareni da masarauta baki daya,
Gabanta Jakadiyya Hajjara ta dawo tace "ki kwantar da hankalinki,
ki barshi yayi auren,
zamu san yadda zamuyi da ita,
da kalamai masu dadi Hajjara ta kwantar mata hankali har taci abinci....
Wata hudu bayan auren *sarki Abdallah Yallo* da Kuyangarshi mai kula da komai na alamuranshi *Rosalin Mujdaha*
mahaifinta shine mai bawa sarki kariya,
bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta ya bawa sarki ita domin ta zama mai aikinsu ta jikinsu wacce zata kula dasu,
garin binciken shi na rashin haihuwa Rosalin ta fado ciki har malaminshi ya fada mishi alherin da ke tattare da aurenta,
bai damu da kalubalen da ya fuskanta daga yan uwa da matarshi ba aka sanya rana, har Allah yasa ta zamo matarshi,
kyakykyawar gaske ce doguwa sambal,
ga biyayya da hakuri,
hakan yasa yake matukar kaunarta,
babu irin asirin da Fulani Ayyu batayi ba dan taga bayanta amma Allah cikin ikonsa duk ta tsallake,
saboda tsoron Fulani da Rosalin keyi hakan yasa bata fita ko nan da can,
duk abin da zai hadasu tana neman hanyar kaucewa saboda bata san tashin hankali,
mugun hakuri gareta ga kawaici da sanin ya kamata,
Babu wanda keda masaniyar tana dauke da ciki domin tsakaninta da bayinta yar kallon fuska ce,
ko mikewa a gabansu batayi,
A ranar da cikinta ya cika wata tara ranar akayi haihuwa a gidan,
wazirin sarki wanda ya zamo kani ga sarki,
a gurin barka ne kowa ya fahimci ciki gareta,
ranar Fulani mutuwa ne kadai batayi ba,
gaba daya kansu ya kulle ita da Hajjara suka rasa ta inda zata bullowa al'amarin..
Ranar suna Yaro yaci sunan *TIDJANI*,
A daren ranar sunan Rosalin ta tashi da nakuda,
sarki da kanshi ya sa aka kira unguwar zoman gidan ta karbi haihuwar,
yana daga bakin kofa yaji kukan jinjiri,
wani irin kuka ya fashe dashi na murna wanda yaki dauke mishi har saida yaji dumin danshi a jikinshi,
nan gaba daya gari ya dauka Sarki Abdallah Yallo ya samu magaji.....,
kwana goma akayi ana buduri a garin,
gidan kuwa zama yayi kamar gidan gala, domin cike yake tun safe har washe gari,
babu abin da akeyi sai ciye ciye da raye raye,
ko ina ka zaga cikin garin farin ciki ke dauke a fuskar kowa saboda sarki ya zamo mai kyautatawa a garesu....
Shekarar Yareemah Adamu bakwai rikonshi ya koma gurin Fulani Ayyu da tayi sanadiyyar mutuwar Rosalin da karamin ciki bayan barin da ta dinga yi,
sarki yayi kuka yayi bakin cikin mutuwar Rosalin mace mai matukar nuna kula a gareshi....
Duk yadda Ayyu takai ga son kuntatawa Yareemah Adamu hakan yaki yiwuwa saboda sarki yana sanya ido sosai akanshi,
sai kuma matar waziri mahaifiyar Tidjani wacce yake yini a gurinta bacci kadai ke maidashi gida gurin mahaifinshi,