← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 113

Sashe 11

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mrs tijjani shattima.....
[04/12 09:49] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣6⃣

A yau ne malam Adamu ya cika kwana bakwai da mutuwa,

in kaga Nadeeyah da mamanta a wannan lokacin sai ka matukar tausaya musu,
duk da irin wadatar abincin da suke samu baisa su walwala ba bare har su kai ga cinshi cikin jin dadi,

A cikin kwanakin Mummy tayi bajinta matuka, ta manta duk wani girman kai nata,
sai ma tsananin tausayin yar uwarta,

A wannan lokacin ne Daddy da Musaddiq da duk wasu makusantansu suka san lallai jini daya ya wuce wasa,

yaran mummy ma sunyi bajinta matuka daga su har mazajensu, sam mummy bata ba kowa kofar da zaiyi complain ba..

A cikin kwanakin kullum ta koma gida a tsorace take,
Jikinta na bata kamar  zata iya rasa wani makusancinta lokaci daya, ( Nidai nace Allah yasa wannan canjin ya daure)..

Bayan an watse adduar bakwai kowa na shirin tafiya gida,
mummy ce ta shigo daki ta zauna gefen gadon da mama suwaiba take,

cikin Nasiha tace "suwaiba ki kwantar da Hankalinki,
kiyi tawakkali,
Allah ya fiki san Adamu, kuma ya karbi abinshi,
dan Allah kar kiyi abin da zai sa ya'yanki su cutu, domin yanzu ke kadai kika rage musu,
dan Allah suwaiba ki rage tunani,
ga kayan abinci nan na hadesu guri daya, na bawa Nadeeyah mukullin,

gyada kai mamma tayi idon nan yayi ciki ciki, tace "Mun gode mummy Allah ya bada lada,
Allah ya biyaku da gidan aljann----- bata karashe ba kuka mai karfi ya kwace mata,
Hakuri su mummy da sauran matan dakin suka shiga bata suna tayata sharar kwalla,

nan fa kuka ya rikide ya zama tari mai karfi,

tun tana tarin da sauran karfinta har takai ga ta fara tarin jini,

a gigice mummy ta fito tana kiran sunan Hafeez..

Hafeez na kofar gida yana sallamar baki shi da musaddiq suka jiyo ihun mummy,
suka ruga cikin gidan a guje,

a rude mummy tace "maza ka fito da mota Hafeezu mu tafi asibiti Suwaiba Aman jini takeyi,

fito da ido waje Hafeez yayi cikin firgici yace "aman jini?
eh mummy ta fadi tana turashi cikin dakin,

Daukota yayi cakk ya fito da ita waje yana fadin dan Allah mamma kiyi hakuri,
karki tafi ki barmu,
gurin motarshi ya nufa da ita musaddiq ya bude baya aka shimfideta,

gefe Nadeeyah ta shiga idon nan a kafe babu ko digon hawaye,

zafin da kirjinta yakeyi ba mai kwatantuwa bane a wannan lokacin,

motar Hafeez yaja da karfi suka nufi Asibiti mafi kusa.

Da isarsu Hafeez ya sauka ko key bai cire ba ya fara kiran nurses,
gadon emergency aka gunguro aka shimfideta a kai,

gungurashi ciki suka fara yi da sauri sauri,
da kyar kalmar salati ke fita a bakin mamma,
babu wani sauran karfi a tattare da ita,
komai nata ya riga ya gama sakewa,
da karfi ta cakumo hannun Nadeeyah wacce take tayata salati ta hada da na Hafeez,
idanuwan nan nata dakyar take iya budesu,

"Ka rike min su Amana Hafeez,
dan Allah ka rikesu, nasani kai me rauni ne Hafizu,
abu kadan ke juya kwakwalwarka,
na rokeka kar ka barsu suyi kukan rashin mu,
na yafe maka, kuma mahaifinka ma ya yafe maka,
ta juyo da kallanta gurin Nadeeyah da idonta ya kada sosai tace "Nasani Zainab nada nagartacciyar uwa,
basai nace komai ba!
Allah ya albarkaci rayuwarki,
kiyi Hakuri da rayuwa Nadeeyah,
ina matukar alfahari dake tun daga haihuwarki har kawo yau,
Allah ya cigaba da taimakonki a duk halin da kika tsinci kanki,
hannu Nadeeya tasa ta rufe mata baki tace "mamma babu abin da zai sameki in shaa Allah..

Dakin emergency aka shiga da ita aka ce su jira a nan likita zai shiga ya duba ta,

kuka sosai Hafeez da Musaddiq keyi, Nadeeyah ce kadai tayi karfin halin yin addu'a,
minti talatin da shigar doctor su mummy suka shigo,
kafin su karaso doctor ya fito fuskar nan cike da damuwa,

Kallon Hafeez yayi nan take zuciyarshi ta karye yace "am sorry, she is no more!!
zuciyarta ta kai awa daya da yin collapse,
yanzu ta daina aiki kwata kwata..

wani irin ihu Mummy ta saka wanda ya razanar da daukacin mutanen asibitin...

Juyayi kwakwalwar Nadeeya ta shiga yi,
a can cikin kanta take jin kalmar "she is no more,
baya ta fara ja tana ganin mutane biyu biyu,
kukansu sai juya kwakwalwarta yakeyi,
batayi aune ba sai jinta tayi jikinta ya saki bata da wani sauran karfin da jikinta zai dauketa,
sulalewa tayi saura kadan ta kai kasa,

Cikin zafin nama ya karaso gurin ya riketa,
babu wanda hankalinshi yake kanta,
kowa kuka yakeyi babu kakkautawa,

suma shigowarsu gurin kenan don daga airport asibitin suka wuto saboda Raliya ta fada musu halin da ake ciki..

Sunan Doctor HILAL ya fara kira da karfi hade da dagata ya rike a jikinshi, nan take hankalin masu kukan ya dawo kansu,

wani daki aka shigar da Nadeeyah aka kwantar da ita a kan gado,
hannunta Hilal ya rike yana murzashi da karfi yana kiran sunanta,

koda doctor ya shigo Hilal na zaune a gefen gadon yanata bubbuga hannun,
magana doctor yayi mishi yace ya tashi ya dubata,
mikewa Hilal yayi ya koma kusa da su Papa ya harde hannunshi hade da jingine kanshi a bango,

zuciyarshi ta karye matuka,
da ya iya yi ma damuwa kuka da irin kukan da zaiyi ba mai misaltuwa bane,
sai dai shi sam kuka baya daga cikin jerin abinda ya dauka me yaye damuwa,
dan in yaga mutum na kuka har mamaki abun yake bashi.

Minti kalilan doctor yayi a kan Nadeeyah ya fita bayan ya sanar musu shock ne yasa ta faduwa, amma in shaa Allah nan da awa daya zuwa biyu zata farka...

Dakin gawar suka koma, kuka ya dawo musu sabo,

   Zuwan Daddy ne ya sanyasu cikin hankalinsu da nasihar da yayi musu, sannan yasa aka dauki gawar a ambulance suka wuce dan yi mata sutura....

( *ALLAHU AKBAAR*    Haka rayuwar ta gada, mutuwa na daya daga cikin abubuwan da muka debo na daga rayuwarmu,
akwai masu rasa biyar lokaci daya, kuma badan Allah baya sansu bane, sai dai dan musan mutuwa ta zama dole,
dukkanmu zamu dandanata komin daren dadewa,
Allah ya kara mana hakurin rashin da mukayi dukkaninmu,
kuma yasa mu cika da kyau da imani) Ameen ya Allah

Mrs Tijjani shattima...
[04/12 09:50] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣7⃣

Ba gidan mutuwar ba, har unguwar su Nadeeyah sai da ta sake hargitsewa da koke koke,
duk rashin imanin mutum sai ya zubar da hawaye saboda tausayin rai... ana sauke gawar, kofar gidan ya sake dinkewa da mutane..

A sanyaye Zainab ta shigo gidan,
dama dakyar taje islamiyya a ranar, Hafeezu da kanshi ya kaita saboda tirjiyar da tayi, sai da ya sai mata sweets sanan ta yarda suka tafi..

mummy ta tarar a zaune tana kuka kamar ranta zai fita,
duk sauran yaran na kanta suma suna sharar kwalla,
dakin mamma tazo shiga da sauri,
bin bayanta Husna tayi dan ta hana ta shiga,
kafin Husna ta karasa zainab ta isa cikin dakin,
kwance ta samu Mamma a rufe cikin likkafani,

a gigice ta karasa jikinta,
girgizata ta shiga yi tana fadin Mamma me ya sameki?
meyasa naga suna ta kuka a waje,
duk da karancin shekarunta tasan menene mutuwa domin tun rasuwar mahaifinta tasan mecece kalmar, kuma ta fahimci in mutum ya mutu to fa bazai dawo ba,
kuma taga yadda akayi wa babanta haka akama mamanta, domin kafin a
fitar da gawarshi saida aka kaita kanshi,

wani irin kuka ta saki hade dayin wurgi da sweets din da Hafeez ya sai mata bata sha su a makaranta ba,

Mamma ki tashi, dan Allah ki tashi, wallahi bazamu sake barinki kiyi kuka ba,
ga yaya Hafeez ma zance kar ya sake tafiya ya barmu,
dan Allah ki tashi,
hannun wacce tayi mata wanka ta kamo tace "dan Allah ki tasheta, kice tayi hakuri karta tafi yanda Baba ya tafi, wallahi muna santa ni da Anty Nadeeyah,
kowa baya santa, tasani mu kadai ne muke santa,
rungumeta Husnah tayi hawaye na bin idanuwanta, ta dauketa ta fitar da ita a dakin dakyar,,
babu wanda bai zubda hawaye a gidan ba..

Bayan an gama shiryata kowa yayi mata addu'ar samun dacewa da rahama..

Baffa na zaune a kofar gida, idon nan nashi kamar gauta,
jikinshi babu inda baya rawa,
dakyar aka dagashi ya shiga dan yiwa diyarshi addu'a,
ki yafe min suwaiba,
ki yafe min,
ubangiji Allah yayi ma abin da kika bari albarka,
na cutar dake matuka,
tun kuruciyarki har kawo yau,

kuka sosai yakeyi kamar karamin yaro,

tabbas mutuwa tayi mishi gaggawa,
ina hankalinshi yake lokacin da yake azabtar da marainiyar Allah,
babu abin da yasani nata tun tasowarta,
bashi da masaniyar damuwarta,
duk rashi irin nata bata taba gajiyawa gurin kyautata musu shi da matarshi ba,
wani irin kunci yakeji a cikin ranshi da ya tuno bai taba barinta ta samu abinda take so ba,
kallon gefenshi yayi ya hango Daddy tsaye shima hawayen ne ke zubar mishi babu kakkautawa,
dukkansu biyun abubuwa masu zafi suke tunowa da faruwarsu shekaru da dama da suka shude,
share hawaye Daddy yayi ya fita daga dakin zuciyarshi a karye...

************

****Kalli sararin samaniya ki fada min abun da kika gani,
sauke idonta tayi bayan ta kalla, tace "Naga abubuwa da yawa, wasu taurari masu kayatar da duhun daren samaniya,
saidai Mamma, ga wani tauraro can, yafi kowanne haske,
ga kuma wasu masu haskawa biyu a kewaye dashi,
sannan ga wasu can sun disashe su biyu ba'a ko iya hangosu,

murmushi Mamma tayi ta dafa Nadeeyah tace "Tauraron da yafi ko wanne haske 'Kece Nadeeyah',
sannan biyun dake kewaye dake bani da masaniyarsu,
amma tabbas alkhairai ne masu karfi da yalwa a kewaye dake,

sannan sai biyun da suka disashe----- sai tayi shuru tana kara kallon sama,
tace "bar batun biyun nan Nadeeyah Allah kadai ya barwa kanshi sani,

saidai a gefen tauraronki baki hangen wani wanda yake turo kai karfi da yaji yana san doke hasken naki,
Chapter 11 · 0% Book details