Sashe 74
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shima hakan yakeso saboda tsabar bacin ran da ta haifar mishi na cewa bazata dawo gida ba zasu wuce lagos da safe,
in ba dan ta rainashi ba bazata iya dawowa gida ta yi mishi sallama ba sai ta waya saboda ta isa,
shima zai nuna mata tashi isar........
"Uhumm,
su Nadeeyah anyi kaura da talauci,
irin wannan mansion haka,
to Allah yasa a san yadda za'a tafiyar da gidan,
"ai tare zamu tafiyar da gidan Anty Radiya,
Raudha ta karbe cike da isgili,
yaushe zan barta ta bata gidan da zatayi zaman wucin gadi a cikin sa,
inaa sam bazai yiwu ba,
kullum ina nan,
zan nemi Badariyya a waya daga sun samu hutun makaranta ta dawo nan tayi hutu tunda kusa ne,
barin irin su Nadeeyah su kadai a gidan nan ai hatsari ne,
sai su la'anta shi,
dole insa ido kafin mai guri tazo ta naďe kayanta...
Mikewa Hinad tayi dan ta fara kosawa da maganganun da sukeyi a kunnenta,
kuma dan cin fuska a gaban Nadeeya dake zaune kai a rufe,
barin dakin tayi tana kun kuni ta fita harabar dan madaidaicin duplex din dake cikin lekki,
babu abin da ke kadawa a gidan sai flowers wadanda suke huro da ni'imtaccen sanyi mai dadi,
Hilal kawai take son gani ta bashi labarin abubuwan da ta jiyo tun daga kaduna har zuwa lagos,
duk irin kullin da suke da shirin yi ma Nadeeyah ta nadeshi tsaff,
bata son fadama Mamanta kar ta haddasa musu tashin hankali, amma dole ta fadi ma Hilal, tasan zai iya yin wani abu,
Hango Jamal tayi da su Zainab a can wani lungun gidan kan wasu kujeru,
nufarsu tayi cike da murna dan tasan tare suke yawo da Hilal,
"Sannu ko,
Zee ina Ya Hilal?
"Ya tafi koyo sallama, Jamal ya bata amsa yana kallon cikin idonta,
zama tayi tana dariya tace
"lallai yayi kokari,
bari ya dawo ya koya min,
"Nafi shi iyawa,
in na koya miki zaki fi dauka,
"kuma fa hakane,
to mu fara bita, ta fadi tana ajiye wayar hannunta,
sake sanya idonshi cikin nata yayi yace
"Allah dai yasa kan naja,
dan i hate in koya ma mutum abu sau biyu,
k'in dauke idonta tayi cikin nashi itama saboda wayewar turai tace
"ban taba cin second ba Malam,
fara koya min kagani may be ma in karasa in ka bani hint,
cike da shauki yayi dariya yace
"Anya ba burga bace?
"Ka tambayi yaya Hilal,
ni ai bana karya,
nan fa hira sosai ta barke a tsakaninsu gunin ban sha'awa har sukayi exchanging numbr,
saboda dadin hirar har Hilal ya iso gurin ta manta da abun da ta guntso ta fada mishi.....
Ka kula da yarinyar Dan Allah, nasan harce da hakori suna sabawa,
amma in sun saba suna kokarin sasantawa,,
mu mata sai hakuri,
nasan Nadeeyah ma zatayi avoiding duk wani abun da zai bata maka,
kuma kaima i trust u,
baka da fushi,
da dai ďanka ne to dama tare zamu zauna saboda halinshi,
Yadda ta fadi maganar tana kallon Hilal ya sanya shi mikewa yana dariya,
itama dariyar tayi a ranta tana farin cikin sauyin da take gani a halin ďanta,
cigaba dayi ma Musaddiq Nasiha tayi tana kara nusar dashi zaman aure,
sunfi awa suna zantawa har lokacin tafiyarsu yayi....
Hilal ma ya kara jaddada mishi ya kula sosai ko ba dan komai ba ya kula da maraicinta,
"Yanzu bata da kowa sai kai,
dan Allah ka kula da ita,
in ta bata maka rai, kafin ka yanke hukunci,
ka tuna maraicinta sai ka yanke mata hukuncin daidai da ita,
zaman aure hakuri akeyi,
kadai ji kowa ya fada maka,
sai school,
dan Allah ka nema mata admission as soon as possible,
kafadunshi Musaddiq ya dafa yace
"worry not Daddy,
in shaa Allah tare zamuyi kuka kuma tare zamuyi dariya,
"Dariyan dai Hilal ya fadi yana dariya..
har gurin mota suka kai suna hirarsu cike da barkwanci,
sam bayason ganin Nadeeyah shiyasa ma bai nemi yi mata sallama ba,
yanaso yayi moving on,
bayason sake tunanin ma ya taba son ta a rayuwarshi,
saboda yanzu ta haramta a gareshi gaba daya.....
Kowa ya watse a gidan sai Anty Rauda da Anty Radiya da batasan wainar da ake toyawa a gidan ta ba,
Zaune suke a parlor sun bararraje suna hira suna cin dublan,
ko tunanin mikewa suyi sallar isha'i basuyi ba,
wayar Raudha ce ta fara ringing tayi saurin dauka hade da cewa
"Hello Abbati kayi hakuri,
har yanzu bamu gama jeren bane,
Tsaki.. kawai yayi ya kashe wayar ya dauki *Hanna* da *Hisham* yayi daki dasu,
Ajiye wayar tayi tana dariya tace "ai fa yanzu ba zama sai dai yayi hakuri,
sai naga little ya rabu yarinyar nan sannan ne zan samu nutsuwa,
karbewa Radiya tayi tace "ai nima zan fi sati biyu anan,
gara mu hada karfi da karfe,
wallahi badan imani da kuma zumunci ba da sai nayi abun da zai batar da Nadeeyah a doron kasa,
duk Baffa ne ya cucemu da ya shigo mana da dangin tsiya cikin zuri'armu,
nan fa suka hakikance suna aibata Nadeeyah da iyayenta,
in ka gansu zaka rantse wasu bare suke aibatawa ba yan uwansu na jini ba....
Ajiyar zuciya yayi hade da ajiye ledojin da ya shigo dasu yace
"Har yanzu baku wuce ba?
"Au korarmu ma kakeyi,
to ai da sai ka ce har yanzu ban wuce ba,
dan Anty Radiya a nan zata kwana,
"Kwana kuma?
Ya tambaya haďe da zama akan kujerar dake fuskantarsu,
"eh kwana little,
ko gidan kanwata kakeso inje in kwana,
tun yanzu zaka fara mana iyakw da gidanka, Radiya ta fadi tana rike hab'a,
mikewa yayi yana dariya yace "nan ma gida ne,
bari inje sama,
duk abun da babu a dakin kasa sai ki kirani a waya,
Salati Radiya ta saki wanda yasa shi saurin sakin ledojin da ya fara diba,
"little ni zaka ajiye a dakin baki,
ni bakuwace a gidan ka Diku, tabdijam,
lallai duk inda muke tunanin abun ya wuce nan Raudha,
"Hmmm ai ni abun yafi karfi na Anty,
tashi kawai mu tafi gidana,
dukda da kunya kina babba ki kwana a gidana,
kusa dasu ya karaso a tsorace yace
"haba baku fahimceni bane,
dan Allah kiyi hakuri Anty,
muje saman ki zabi wanda kike so a ciki,
kanne mata ido Raudha tayi sukayi murmushi hade da tashi su nufi saman....
Dakin da Nadeeyah ke ciki suka nufa saboda nan yafi ko ina tsaruwa,
nan ne sukaji Anty Reemah na kira da turaka,
bata cikin dakin hakan ya basu tabbacin tana toilet,
Ajiye ledar Musaddiq yayi a kan gadon ya tsaya kallonsu,
yadda suka nufi bayin gadan gadan ya sashi tunanin ko lalura ce ta kaisu,
Da karfi Raudha ta murda bayin ba tare da bugawa ba, dan dama shammatarta suka so yi,
Saboda tsabar kaduwa Nadeeyah bata san ta zaune a gurin ba,
Tsaki.. suka jaa a tare Radiya tace "dan Allah ji rashin kunya,
in banda rashin ta ido yarinyar nan tasan sarai muna gidan nan kuma ta shiga bayi a haka saboda tasa yaron nan fitsare kafarshi a gabanmu,
Allah ya kyauta matan zamani, mu a da ai sai muyi wata bamu shiga wanka ba sai ance muje,
Kofar bayin Musaddiq ya ja yace "menene laifi dan tayi wanka, ai kowa nasan tsafta,
dan Allah muje ki kwanta,
ke kuma kije gida gurin su Hisham,
"Anan zata kwanta,
Raudha ta fadi alamar da ta fara hassala da kalamanshi,
kafadunshi ya daga yace
"ok fine, bari ta shirya sai muje can dakin,
ai duk daya ne,
bai tsaya kallon reactn dinsu ba ya bude drawer ya ga ba kayanta a ciki sai nashi,
wata rigar baccinshi ya dauko wacce yasan inya sa mata zata wuce mata gwiwa ba tare da wando ba, ya wuce bayin ya barsu da mamakin anya kuwa zasu iya rabasu cikin sati biyun da suke tunani,
basu kara shan mamaki ba bakunansu dake kuskus suka tsaya a haka na ganin yadda ya daukota cakk cikin faffadan kirjinshi,
bai direta ko ina ba sa dakin dake dan nesa da inda suke,
komawa dakin yayi dan dauko mata abin da ya siyo mata ya tarar dasu suna tafa hannu,
kwaso ledojin yayi ya mika ma Anty Radiya daya,
"Diku ko kunyarmu baka ji ba,
"kunyar me?
ya tambaya yana murmushi,
"a gaban idonmu ka dauki matarka har kana kankameta cikin kirjinka,
"Diku waye ya 'bata ka haka?
Dariya yayi yace
"Nadeeyah ko ba matata bace kanwata ce,
zan iya daukarta in lalura ta sameta,
to ya zanyi in barta a bayi tunda ku ba fita zakuyi ba itama kuma tace bazata fito ba,
shiyasa kawai na raba gardama,
"Hmmm yara kanana da makirci ni jikar Ma'u,
to bari kaji in fada maka,
wannan rawar jikin da kakeyi ka rageshi,
ita mace in taga ana sonta sosai nan ne take bude kafar iskanci,
ka hankalta ka dinga jan ajinka, ka zamana kai mai gidan ne gaske,
yawan sake fuska da hira duk suna sanya mace ta raina namiji,
Barshi Raudha
"zo ki zauna muci naman nan zan mishi course anjima,
dan bana jin bacci...
Shi mamaki ma suka bashi,
kowa yana ce mishi matarka itace komai naka,
itace abokiyar wasanka kuma sirrinka,
su kuma ga irin tasu lakcar,
murda kofar yayi yace
"sai da safenku,
"a'a karkayi bacci,
zamu---
"Aiko zanyi bacci ya katseta hade da rufe kofar yana dariya,
shi ya rasa me ke damunsu, bayan Mummy kawai suke bi,
Wanda duk yaso Faida ya bar Nadeeyah a gurinshi baisan me yakeyi ba,
a iya gane ganen yan matanshi bai taba ganin macen da ta hada komai irin matarshi ba,
wayarshi dake kara ya dauka ya kara a kunne hade da cewa,
"Mahmood har kun isa, daga daya bangaren Mahmood yace "yess yanzu na shigo gida,
na manta, akwai wasu kaya da Mama ta bani in ba Nadeeyah,
suna nan boot din *Zubair,* na kirashi zai kawo maka gobe,
"ohk Besty ba matsala,
thank u soo much,
"most welcome Kyari,
a kular mana da kanwa,
nyt, "in shaa Allah, Allah ya tada mu lafiya......
Knock knock knock...