← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 113

Sashe 69

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mrs Tijjani Shattimah........
[11/04 12:07 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣6⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Mikewa Mummy tayi zuciyarta ta fara sanyi na yadda taga Badar ta harzuko, tasan tabbas Badar bazata taba bari auren nan ya tabbata ba koda kuwa zai zama ajalin Nadeeyah...

Hannunta ta kamo tace "Musaddiq dinki Badar,
mun gama magana da wani malamina akan halascin aurenku, da murnata nazo na fadawa Daddy,
shine yake cemin wai ai Papy Saif yazo mishi da maganar yanason hadin auren Nadeeyah da Musaddiq,
shi kuma nan take ya amsa mishi saboda kinsan yadda Daddynku yake da s-any-in haaa--li,
ni yanzu bansan yadda zanyi da raina ba,
ta karashe da kuka sosai wanda yake nuni da tabbas tana bukatar taimakon Badar...

Furzar da huci Badar tayi murya a kausashe tace
"Wallahi bazai yiwu ba,
na dauki alwashin saidai Musaddiq ya zauna babu aure in har ban halasta a gareshi ba a baya lokacin da kika ce ba aure a tsakanin mu,,
bare kuma yanzu da na tabbatar na halasta a gareshi zan yarda ya auri wata,
watar ma Nadeeyah,

wallahi Mummy saidai ayi auren nan babu raina,
bazan ma mutu ba,
sai dai ita ta mutu,
hannu ta daura kan kafadun Mummy tace
"ki kwantar da hankalinki,
kima daina kuka,
kisa ma ranki salama yau zuwa gobe zakiji sabon labari,

zaunar da ita Mummy tayi cikin tsorota da yanayin kalamanta tace
"Badai kauce hanya zakiyi ba?

Dariya Badar tayi tace "karki damu nace,
badai kin yarda da batun aurena da Yaya Musaddiq ba?

Gyada kai Mummy tayi tace
"eh,
a zuciyarta kuwa tana jin tsoron karyar da tayi ma Badariyya, tasan sarai in auren nan ya lalace wata rigimar ce zata sake bullowa,
kauda zancen tayi a zuciyarta, dan tasan yadda zata tafiyar da Badar bayan maganar auren Nadeeyah ta lalace......

*KUNGAMAR GARZAR*

Washhhhh....,
na taka qaya,
duba min kigani Lawisa Lawal,
hannunta Lawisa ta kama tace "sauri fa zamuyi Badar,
kina ganin har la'asar tayi bamu karasa ba,
dajin nan is very dangerous, nima Anty Laurah ta taba kawo ni, ban taba tunanin ma zan gane ba,
dan Allah ki dago kafa,

"dingisawa Badar tayi ta sake yin ihu hade da tsugunawa ta cizge kayar,
bata damu da jinin da ke bin kafarta ba tabi Lawisa suka dinga sauri cikin dajin,

minti talatin suka kara suka isa gaban wata katuwar bukkar fulani,
almajirai ne kewaye da ita suna kara kaini da alluna,
sai gungun kyawawan yaran fulani daga can nesa suna wasan kasa, matan na yar gala gala...

Suna shiga gidan suka bangaji wata yar budurwa da ta arto a guje tana ihun kuka,

wata katuwar farar mace fuska duk kalangu na biye da ita da bulala a hannu tana zaginta da fulatanci,
ramawa budurwar takeyi tana fadin

"Allah ya isa muguwa, azzaluma, bazan yi wanke wanken ba,
in kinga dama ki kashe ni,
ganin su Badar ya sanya matar yar da bulala tana fadin "marabanku,
ku shigo daga ciki,
a darare Badar ta kalli matar sannan ta kalli Lawisa dake kokarin janta zuwa ciki,
zatayi magana kenan Lawisa tayi mata alama da tayi shuru su shiga daga ciki,
a tsorace ta fara bin Lawisa da matar har suka isa wata lafiyayyar bukka dake kawace da adon fulawoyi,

"babu abin da ke fitowa a bukkar sai hayaki mai karfin kamshi wanda ka iya buga kan mutum in ya shakeshi na tsawon minti goma,
da sauri Badar taja gyalenta ta rufe hancinta gabanta na tsananta faduwa,
a zuciyarta tana dana sanin biyo Lawisa gurin nan da tayi..

" *Lawisa ta dade tana bata shawara akan tazo suje inda zata karkato da hankalin Musaddiq da Mummy su yarda da aurensu koda kuwa bai halasta ba Badar taki, saboda a ganinta zata iya shawo kan komai saboda irin soyayyar da Mummy ke mata, jin batun auren Nadeeyah da Musaddiq shi ya harzukota ta nemi Lawisa suka taho ba bata lokaci, bata san azal ke kiranta ba*

katse mata tunani Lawisa tayi tace
"ance mu shiga Badar,
firgigit Badar tayi ta cire takalmanta suka fada cikin bukkar,

Suna suka saka kafarsu a ciki hankalinsu ya gushe suka manta inda suke,
sai ganin kansu sukayi a cikin wani kayataccen parlon da duk iya maitar mutum bazai san ta inda yabi ya shigeshi ba,
jiki na rawa Badar ta damki hannun Lawisa suka zauna a gaban wanda Badar tafi zaton shine bokan,
gefenshi kuma saurayi ne dan shekarun da basu fi talatin da biyar ba yana zaune shima da kayan tsubbun a gabanshi,
dago kai saurayin yayi ya kallesu yace

"Badariyya da Lawisa barkanku da zuwa,

nan cikin Badar ya duri ruwa saboda tsabar tsoron da taji,
a ina yasan sunan su?
Tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan,

"Nasanki tun ranar da kika duro duniya Badariyya,
babu motsinki da ban sani ba,
har wannan zuwan da kikayi na sani,
dan ni na shiryashi,
gefen da Lawisa take ta kalla nan da nan ta saki hannunta saboda wata iriyar dariyar da takeyi mata mai cike da ban tsoro,

mikewa lawisa tayi tana dariyar da ta ke amsawa a cikin dakin, sannan ta Kalli Badar tace

"ke matar dan sarkin mu ce, wannan shine

*Sarkin bokaye Shahalu*

sai danshi
*Yareemah Suhailu*
karki damu Badariyya,
ni kawarki ce kamar yadda kika dauka,
amma ki sani na zo gareki ne saboda wannan ranar da zan cikawa Sarkin mu burinshi,

"ni ba mutum bace,
amma sarki da yareemah mutane ne kamar ke,
kyakykyawar mu'amalar dake tsakaninmu dasu ita ta janyo har na taimakeshi,
ki kwantar da hankalinki yau kinzo inda kaddararki take,
zaki ji dadin zama dashi da yan uwanshi,
bissalam kawata Badariyya....
ta karashe tana daga mata hannu tana dariya har ta bacewa ganinta,

wani irin ihuu Badar ta saki tana bin gurin da lawisa tabi,

"wayyo Allah Mummy ki taimakeni,
wayyo Allah Daddy,
na shiga uku na lalace,
wayyyyyo Allah na,

keeeeeeee!!!

Wata irin tsawa taji daga bayanta wacce ta sanyata dunkulewa guri daya,

murya a kausashe Sarkin bokaye yace
"Karki sake yi min ihu anan,
kin san Allah dama?
In kika sake kiramin sunan Allah anan zan cire idon ganinki,
na rantse da abun bautarmu *GARGAZ*,

Kee... *Kande*
ya kwala kiran katuwar matar da ta shigo dasu,
Da sauri ta karaso ta tsuguna a gabanshi tace
"Ranka ya dade gani,

"Maza ki dauketa ki kaita cikin gida dakin da *Halyo* ya gyara jiya,
an sa gado da katifa dama,
jiran zuwanta kawai akeyi, sannan ki jawa
*Gimbiya Sailuba* kunne,
babu ruwanta da kishi da ita,
domin wannan itace matar Suhailu ta farko,
tun kafin tazo duniya Mahaifiyarta ta bashi,
sai yau *Garzar* ya bamu ikon dawo da ita gurin mijinta,

cike da girmamawa Kande tace "to ranka ya dade,
an gama,
nan ta damki hannun Badariyya tana janta a hankali Badar na turjewa tana ihun neman dauki a inda babu mai jinta sai Sarkin sarakunan da biyayyarshi bata dameta ba,
sarkin da a sati baifi ta gaisheshi sau daya ba,
sarkin da ya hore mata lafiya da kuma abun da lafiyar zata ji dadi...
*ALLAH AZZA WA JALLAH*

shi kadai zai fidda Badar daga kangin da take ciki......
*SHIN INA BADAR TA FADO*

_(fadan da yafi karfin ka ya kai dan uwa, bar wa Allah yayi maka shi, domin shine mai dukkan karfi.......)_

Tun Mummy na jiran Badariyya a daki, har ta koma leke ta window da kofa,

karfe 11 agogon parlon ya buga,
a tsorace ta sake kiran Badar karo na ba adadi,
har lokacin wayar a kashe take,

zama tayi akan kujera ta Shiga jero salati,

"Ina Badariyya ta Shiga har wannan lokacin,
ya ilahi kasa ba wani abun bane ya same ta,
tagumi tayi tanata sambatu dan hankalinta Sam yaki kwanciya,

Har karfe 1 na dare babu labarin Badar,
sai a sannan ne ta fara kiraye kiraye waya tana kuka Dan gaba daya ta gama tsurewa,
duk wanda ta kira wayarshi a kashe,
wayar Daddy ce kadai ta shiga,
shi kuma bai dauka ba saboda gajiya da yayi,

yar da wayar tayi ta fashe da kuka tana dana sanin barin Badar ta fita,
gaba daya idonta ya rufe burinta kawai a fasa auren Nadeeyah da Musaddiq,
Sam bata hango matsala a fitar da Badar tayi ba,

sai gurin hudu bacci barawo yayi gaba da ita,
ana idar da sallar asuba Daddy ya kira ta saboda ganin misd calls dinta da yayi,

firgigit...
ta farka tana fadin Badariyya,
"Hello Badariyya kina ina?,
gyaran murya Daddy yayi yace "ina Badariyyar ta tafi?

Wani irin kuka Mummy ta fashe dashi tace
"Badariyya bata kwana a gida ba,
na rasa inda ta tafi,
na kira wayarta har naji ba dadi na kasa samunta,

cikin halin ko in kula Daddy yace
"kinsan duk inda take zata dawo, ki kwantar da hankalinki, ai ba yarinya bace, big girl ce..
na turo miki kudin kayan kitchen,
zuwa anjima kuje ku siyo,
bana son muyi abubuwa cikin kurarren lokaci,
yana kaiwa nan ya kashe wayar,

Ajiye wayar tayi ta cigaba da rero kuka,
"da wani baki zata fada musu cewa tana da masaniyar inda Badar taje,
wa zata fadama ya fahimceta har ya taimaketa,

Goggo ce ta fado mata a rai tayi saurin kiranta,
saida wayar ta kusa katsewa sannan ta daga dakyar,
yanayin muryarsu daya ko wannensu cikin kunci yake,

Mummy ce ta fara fada mata damuwarta,
nan take Goggo tace
"rabu da ita zata dawo da kafarta,
kin manta haka uwarta ma tayi,
kina zaune zata dawo,
ke dai kije kisan yadda zakiyi wadannan matsiyatan kar su shigo cikin zuriarki, dan babu alkhairi a duk inda suka sa kafa..
da kalaman Goggo hankalin Mummy ya kwanta ta mike tayi wanka tayi sallah sannan ta zauna tana tunanin ta inda zata bullo,

kawarta Hajiya Martai ce ta fado mata,
nan ta kirata ta kora mata matsalolinta,

minti talatin Hajiya Martai ta bata tace ta sake kiranta zata sa wani malami yayi bincike akai,

ko minti daya bata kara akan minti talatin din ba ta kirata,

a sanyaye Hajiya Martai tace

"Hajiya zainab wannan auren babu abinda zai hana shi sai mutuwa,
akwai rabo mai karfi a tsakani,
kuma akwai wani babban al'amari da zai taso marar dadi wanda Allah ne kadai ya barwa kansa sani,
Chapter 69 · 0% Book details