Sashe 90
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau ma teba Mummy?
Ko kallon inda take bata yi ba karasa kwashe tebar cikin cooler,
miyar ganyen da sukayi wacce bata samu arzikin nama ko kifi lando ba ta mayar kan gawayin da ta sauke tebar,
na Goggo ta ďauka ta wuce mata dashi ďaki,
Tari ta fara yi sosai cike da faďa tace
"Wai har yanzu bazaki dawo hanya ba Goggo,
kullum Allah na nuna miki abubuwan da kikeyi ba masu kyau bane ya cire hannunshi akanki sai cigaba kikeyi,
da tsufanki kullum sai mugun abu kikeyi yana dada dawo mana,
kai gaskiya da ana canza uwa da tuni na dade da canzaki wallahi,
Ko ni da na faďa cikin wannan jarabawar nasani sarai hakki ne,
hakkin Suwaiba da zuri'arta,
na dade da mikawa Allah lamarina,
nasan wata rana zaizo rescue dina,
Maganin Goggo ta kuma zubawa cikin wutar tace
"Tun kina karama nake shan bakar wahala dake,
badan a gida na haifeki ba da zance daga tsatson Harďejo kika fito su suka canza min ke,
in ke sakara ce to ni bazai yiwu in zama sakarai ba,
ku uku ne a gidan nan dukkanku sakakku,
mazajenku basu ko waiwayarku sannan kice in nemi guri in zauna,
bana tunanin zan mutu nan kusa, nasani sai naga mutuwar zuri'ar Atika da tun shigowarta rayuwata ta tagayyara komai nawa...
*MUSADDIQ...*
jin Raudha tayi ihun sunan gudan jininta da ta shekara har da doriya bata sashi a ido ba yasata fasa bawa Goggo amsar da tayi niyya,
da gudu ta fito waje har tana bugewa da kauren ďakin,
tana shirin karasowa ta rungumeshi yayi saurin ja baya wanda hakan yayi daidai da shigowar su Baffa da Sheik,
Share hawayen da zubo mata tayi ta wuce daki ta dauko hijab,
ďakin Anni da ta bari Baffa ya shiga dasu,
sam baiyi niyyar shigowa da Sheik gidan ba, dan dai Papy ya matsa ne,
Shigowa Mummy tayi da sallama hannunta dauke da tray din pure water,
Papy, Papa da Sheik ne kaďai suka amsa sallamarta,
da ido Papy yabi Musaddiq yana ta kokarin su haďa ido,
kamar ance ya ďago suka haďa ya sakar mishi lafiyayyar harara,
Kauda kanshi yayi ya sake tamke fuska ciki ciki yace
"Ina wuni,
kallon shi kadai tayi ta maida dubanta gurin Sheik wanda tsufa bai hanata ganin Atika cikin fuskarshi ba,
"Ateek right?
Cike da murna Papy yace
"shine,
ashe kin sanshi,
hawayen daya zubo mata ta share tace
"Na fi kowa mu'amala da yayarshi,
lokacin inada karancin shekaru dan zan girme mishi da shekara biyu ko uku,
kullum sai ta ambaci sunanshi fin sau goma a rana,
duk wanda ya santa a cikin yaran gidan Harďejo yasan Ateek,
dan labari nashi take bayarwa Maryam din Harďejo ko mai babban suna su dinga yi mana fassara,
Kuka sosai ta fashe dashi na tuno ukubar da mahaifiyarta ta bawa Atika wanda bata da bakin faďawa wani..
Share hawaye Papy yayi yana matukar jin kewar rashin ganinta bawai dan ya rasa uwa a gurin Anni ba,
shima Sheik kukan ya keyi bayan an fassara mishi abun da tace....
Dakyar Goggo ta iya shigowa dakin,
a tsay tsaye ta gaisa dasu ta fita saboda rashin son ganin fuskar Sheik,
duk ta kalleshi sai gabanta ya faďi...
Hira sosai sukayi da Mummy, Papy da Sheik,
Papy yaso Daddy ya shigo yaga sauyin da matarshi tayi,
haka nan yaji ya kasa tsanarta duk ko irin abun da akace tayi,
bayan fitarta ne ya kewa Musaddiq faďa sosai akan Muhimmancinta duk ko irin laifin da tayi mishi,
ko gezau Musaddiq baiyi ba dan zuciyarshi ta kangare sosai bayajin akwai abinda zai sauya shi daga dawo ma mahaifiyarshi yanda yake da...
Zubo teban Raudha tayi ta zauna a bakin kofa tana ci saboda tsabar yunwar da takeji,
Hilal da ya shigo gidan bayan ya gama order abincin da zasu ci da kuma masaukin da Sheik zai sauka ya kureta da ido,
Karyewa Zuciyarshi tayi yaji abun na yawo a cikin jininshi,
blood is thicker than water,
lallai bature yayi gaskiya,
Bai bari ta ganshi ba ya fita ya je wani store dake kusa dasu ya lodo kayan abinci masu yawa har saida kuďin dake hannunshi suka kare,
yana zuwa kofar gidan yaga
Rilwanu,
kiranshi yayi yasashi ya shiga da kayan yace ya faďa musu inji Daddy,
Basu bama har Papy saida yayi murna sosai ya kuma sake zage damtsen yin addu'a har sai Allah ya daidaita su,
Ita kuwa Goggo cewa tayi hayakin da tayi ne,
ta dinga fankama nan da sati zaizo ya maida Mummy dakinta....
Gidan Anni suka yada zango nan suka ci suka sha sannan suka bararraje anata hira har bayan la'asar,
Anni hana matan tafiya tayi tace saida mazan su tafi,
haka kuwa akayi su Mami suka zauna a gidan suka raba dare suna hira ana fassarawa Anni da ummi....
Kuďi masu yawa Anty Reemah taba Mummy sannan ta je gidan Raliya tayi mata faďa sosai akan rashin taimakama su Mummy,
a sannan ne Raliya take faďa mata Daddy ne ya hanata yace in tayi sai ya saba mata,
dafe kai Reemah tayi tace
"Daddy yayi fushi da yawa, wallahi ko maganar Mummy baya son ayi mishi,
"Addu'a kawai zamu cigaba dayi danni ita kadai ke bani tausayi ba su Anty ba,
dey deserve it... Raliya ta faďi rai a bace...
sun dade suna hira suna nemawa mahaifiyarsu mafita....
Kwanansu Sheik Uku suka shirya komawa gida da yan uwa dan suje suga inda yake,
kyautar ban girma yayi ma su Mummy wacce zata mantar dasu talauci na wucin gadi,
tayi murna sosai da wannan kyauta dan saida tayi kamar zata mishi sujjada,
har suka tafi baisan cewa Mummy matar Daddy bace,
ya dauka kawai a gidan take zaune, ya dai san yayar su Papy ce....
*Cyprus...*
Da yake mansion din Sheik yana da matukar girma hakan yasa ya kwashe dukkansu,
harda Husna da suka taho da ita dan ta haihu,
dadin duniya babu wanda bai jiyar dasu ba,
duk companies dinshi saida ya nuna musu harda na wasu kasashen,
Saboda murna ya cire wani babban companynshi dake Holland ya mallakawa Papy a matsayin gadon mahaifiyarshi,
sannan ya bawa Hafeez wani abun shima,
gaba ďaya ya kasa controlling kanshi akan zuri'ar yayarshi....
Kwanansu biyar a garin akayi ma Husna tiyata aka ciro mata baby girl saboda haihuwar tazo da Matsala,
lokacin su Daddy sun koma Nigeria,
murna a gurinsu ba'a magana saboda dama cikin na yawan bata wahala,
Papy da kanshi ya shiryawa Mummy tafiya dan taje gurin yarta taga jikarta,
Ita dai a kullum haushin kanta takeji na biyewa zuciya tayi wa Suwaiba abubuwa marasa dadi kafin mutuwarta,
gashi yanzu danshin su take raba taji dadi,
lallai da ta hana auren Hafeez da Husna da sai takaici ya kusa ajalinta,
kullum bata da addu'ar da ta wuce Allah ya dawo da Nadeeya cikin koshin lafiya dan danta ya samu farin cikin rayuwa,
a yanzu ko ita bata samu farin ciki ba 'yayanta su samu,
ta fahimci farin cikinsu shine nata,
ďan zaman da tayi da su Radiya ta fahimci cewa ba kowani ďa bane ke sadaukar da farin cikin sa akan iyayenshi,
a nan ta koyi basu farin ciki,
in ta gansu cikinsa tasan itama zata kasance a ciki...
Ranar Suna Daddy ya sanya wa yar suna Suwaiba,
sosai dangi suka nunawa yar gata dan ta samu kaya na gani na faďa,
Mummy ta sake tsorata da ikon Allah da tazo taga daular duniyar da dangin Atika ke ciki,
inama Suwaiba na raye tazo ta dandani arziki,
wayyo,
ita nata dadin a lahira ta ďeboshi.....
Na fa lura da wani abu Anty,
Raliya ta faďi tana sanyawa Nour ďiyar Husna pampers,
"Me fa?
Anty Reemah ta tambaya haďe da gyara zama,
"Na kusa yin siriki, Raliya ta faďi tana murmushi..
"Wa kenan??
"Dadina dake ganewa Anty Raly,
Husna ta faďi tana ajiye kofin shayi,
ni ai tun tuni na sani,
Jamal ya hanani faďi,
"Kaii nifa ban gane ba,
wai me kuke nufi?
Anty Reemah ta tambaya cike da mamaki,
"Y'ata ta wajenki tayi kasuwa, soyayya sukeyi da Jamal,
Mikewa Anty Reemah tayi tace
"to ai ba sai kun faďa min ba, kuma iyaye ne,
in akwai alheri Allah ya tabbatar...
Dariya sukayi haďe da tafawa suka ce Ameen Ameen,
ashe zamu sha biki...
Hinad da ta doso dakin ta juya da sauri ta nufi waje cike da murna,
tasan tunda Anty Raly tasa baki Allah ya kusa cika mata burinta,
soyayyar Jamal ta zame mata tamkar jini da hanta,
bata jin akwai abin da zai cire mata sonshi cikin ranta,
kamar shima yadda Jamal din keji game da ita saboda kyawawan dabi'unta,
zuwanshi kasar yasake sanya shakuwa mai karfi a tsakaninsu, wacce har ta sa aka fara diga ayar tambaya akansu.....
Zaune suke a katafaren parlon sama suna duba ayyukan da gwamnati tayi approving,
Zanen da Hilal yayi wannan karan na musamman ne,
cike da yabawa sheik ya kalli zanen karshe yace
"Bravoo alaika ya Hilal,
Allah ya albarkaci hannunka,
yanzu kaga sai dai kawai mu fidda kudi a hau aiki,
Murmushi Hilal yayi zaiyi magana Irfan ya faďo parlon babu ko sallama,
kusa da Sheik yaje ya zauna haďe da faďin
"Masa'ul khair Aby,
kallonshi yayi sama da kasa yace
"uhummm,
kudin naka sun kare kenan,
sosa keya yayi yana hararar Hilal yace
"Eh,
akwai wani business da nasa kudi na,
inaso inyi clearing ne bani da cikon kudin,
20mill ne kawai,
"I struggle to get 5 thousands aday nd u are calling 20mil only,
it's well dear,
zanyi maka addu'a Allah ya baka,
Lokacin da na kiraka ina farin cikin ganin yan uwana kaima kazo su ganka kazo?
Kayi ignoring dina so yanzu ni bani da abun yi maka,
yana kaiwa nan ya kalli Hilal yace
"My dear gobe ka sameni a office sai mu fara shirye shirye ko?
Cike da girmamawa Hilal yace
"Okay sir, Allah ya kaimu...
A tare suka mike Sheik ya raka Hilal har kasa sannan ya wuce dakin da Husna take dan duba lafiyarsu...