← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 113

Sashe 82

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiye wayar yayi ya cigaba da tuki hankali kwance,
yana karya sharp bend din da zai sadashi da hotel din ya fara latsa hon saboda ganin mace na tafiya a saitin inda yake bata waige bare taga abunda ke bayanta,

Duk irin kokarin da yayi brake din ya taku ya kasa dan ya kure da yawa,
sai da yayi mata mummunan buguwa ya daki ginin gabanta kaďan sannan motar ta tsaya,

kwantar da kanshi kan sitiyari yayi yana maida numfashi sannan ne hankalinshi ya dawo inda mutane ke ihu suna tururuwa,
buďe motar yayi ya fito a gigice ya nufi inda ya buge matar,

dakyar ya iya kutsawa yana faďin ku taimakeni in kaita asibiti dan Allah,
sam bai kula da fuskar ba shidai ya kinkimeta iya karfinshi ya nufi motar da wani mutum ya bude da niyyar taimakawa.....

Subhanallah....
me ya faru a can gurin?
Hilal ya faďi haďe da lekowa ta window,
wani saurayi ya tambaya abinda ke faruwa,

"Wallahi wani ne ya yayi accident har ya buge wata yarinya,
kaii abun ba kyau yarinyar ta bugu, dakyar in zata rayu,

"Ayya, Hilal ya faďi haďe da maida kanshi cikin motar,
Allah ya kyauta gaba,
muje Zubair,

jan motar Zubair yayi suna addu'ar Allah ya tsare dukkan musulmin duniya....

Mrs Tijjani Shattima....
[25/04 9:12 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣3⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Ohhh Musaddiq...
pick my call,
Abbati ya faďi haďe da buga hannunshi jikin siyitiyari...

Wayar Raudha dake cikin motarshi ya gani bayan ya idar da Sallar magriba, abubuwan da ya gani a wayar su suka razana shi matuka,

"How can some1 be so selfish, meye laifin Nadeeyah da suke shirin tarwatsa rayuwarta haka,
dama tun jiya da daddare yaga take takenta, in aka kirata a waya sai tace text me,
duk iya hangenshi bai hango abinda suke kullawa har ya kai haka ba,
in har Raudha zata iya kulla irin wannan abun ga ďan uwanta da matarshi wacce itama ta zamto yar uwa a gareta, to wa zatayi sparing,

wani irin kyamarta yake ji a cikin zuciyarshi,
bazai taba son 'yayanshi su kasance tare da ita da wannan mugun halin nata ba,
da yaga Musaddiq baida niyyar daukar wayarshi sai ya kira wani abokinshi akan su ajiye mishi ticket din zuwa katsina,
gara ya dauke 'yayanshi ya maida su gurin iyayenshi,
ita kuma Raudha ya riga ya gama yanke hukuncin da zai zartar akanta,
duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba to tasa ko huruwa bazata yi ba,
kafin Musaddiq ya saki Nadeeyah shi zai rigashi sakinta,
may be ta shiga hankalinta,

Shi laifin Daddy ma yake gani,
ya za'ayi ya bar 'yaya haka sakaka babu kwaba ba komai,
har mahaiifiyarsu nada ikon zuwa a haďu a bata rayuwar wata da ita,

"tirrr.. ya zama dole ya rabu da 'yar mace domin dama mugun hakuri yakeyi da ita....

Tada motarshi yayi ya nufi gidan Musaddiq dan ya sameshi ya fita hakkinshi akan abun da ya sani kafin hak'an su ya cimma ruwa....

*its too late....*

Da..dd..y......,
ya faďi cikin shashshekar kuka haďe da zuwan wani kukan mai karfin gaske...

Gaban Daddy ne ya faďi ya mike daga kan daddumar da yake haďe da fita a masallacin gaba daya,

"Me ya faru Saaaadiq,

Musaddiq bai bashi amsa ba sai kukan da yake tayi karamar yaron goye,
kuka ne mai cin zuciya wanda ya karya zuciyar Daddy ya sanya shi neman guri a dakalin masallacin ya zauna,
saida ya barshi yayi kukan sosai ba tare da ya katseshi ba sannan yace

"Bana san sakarcin banza,
ya isheni haka,
i have heard enough,
faďa min abin da yake damunka?

"Nadeeyah...
sun raba ni da Nadeeyah..

Mummy da su Anty Radiya sun rabamu Daddy,
na saketa da bakina Daddy,
dan Allah Daddy ka dawo min da ita,
i can't live...
i can't...
ya karashe cikin kuka mai tsanani...

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai Daddy yake faďi cikin zuciyarshi,
ko a mafarki bai taba kawo abun da zai kai Mummy lagos kenan ba,
duk tunaninshi bai kai nan ba,
tunaninshi kawai taje ta zuga danta ya auri wacce take so ne,
ya barta tayi kidanta ne in maganar tazo gurinshi tunda shine wakili ya barta ta taka rawarta,

Ajiyar zuciya yayi yace

"Kar ka bar Nadeeyah ta je ko ina,
ku shirya gobe tun safe taho gida,
nasan matakin da zan dauka...

"Sun koreta Daddy,
ban san inda zan ganta ba,
na duba ko ina ban ganta ba..

Duk da Daddy bai iya fushi da Musaddiq,
a wannan lokacin saida yayi mishi gigitacciyar tsawa haďe da mishi kashedin lallai duk inda take ya nemota, in ba haka ba wallahi sai yayi mummunan saba mishi,

kalmar da Daddy ya faďa mishi a karshe ita ta sake assasasa hawayen idonshi,

"YOU A LOOSER,
U DOS'NT DESERVE A SPECIAL SOUL LIKE NADEEYAH....

Yana jiyo kalaman da Daddy ke faďa mishi wanda yasan shima ba'a cikin hayyacinshi yake faďinsu,
bai iya furta mishi komai ba dan yasan ya tafka babban kuskuren da ya cancanci fin wannan zagin...

Kasa tashi a gurin Daddy yayi har aka gama wa'azin bayan sallar isha'i wanda suke saurara a kullum,
mutanen dake fitowa a cikin masallacin ma daidai yake kallonsu,
yana ganin kamar duk matsalolin duniya a gidanshi aka tarasu,
bai san lokacin da hawaye ke bin idonshi ba,

"Yaso Suwaiba saboda komai nata ya zamo abun so ga kowani da namiji,
yana ganin rashinta shine mafarin shigar rayuwarshi cikin kowani irin kalubale...

Ya nemawa danshi auren yar da yake jin sonta fiye da 'yayan da ya haifa a cikinsa, saboda danshi ya samu zuri'a daga gareta kuma rayuwarshi ta inganta,
sun rabashi da ita, same mutanen da dalilinsu ya hanashi samun abun da yakeso a baya sune dai har yanzu dalilinsu zai kuma hana danshi abun da yake so,

*Tarihi ya maimaita kanshi*...

Hukuncin da zuciyarshi ta gamsu dashi shi ya yanke ba tare da duba tsufa da tarin yaran da suka tara dashi ba,
dakyar ya iya mikewa ya nufi gida zuciyarshi kamar ana soyata saboda gashin kumar da yakeji a cikinta......

Kashe motar Zubair yayi yace

"Muje dai tunda ka matsa,
dama amarya tamin gorin ban taba cin abincinta ba..

Dariya Hilal yayi ya saba jakarshi a baya suka wuce cikin gidan,

Tun kafin su karasa suke jiyo muryoyi ana maida magana kamar karnuka,

kalmar da ta da ta doki kunnen Hilal ita ta sashi yar da jakar hannunshi haďe da murďa kofar parlon...

*Da ya saketa ai ku kuka koreta, ku kuka ce zaku koreta kuma kuka ce mata kar ta sake shigowa cikin rayuwarku, saboda haka ku zaku nemota ko in tona muku asiri wallahi...*

Cikin rashin sani yake kallon wacce tayi maganar dan bai santa ba,

shakar da Raudha ta kai mata ita tasata sakin ihu sosai tana neman ceto,
dukkansu basu san Hilal da Zubair sun shigo parlon ba..

"Dan ubanki saboda wa mukayi?

Saboda ki aureshi muka sanyashi ya saketa kuma muka koreta a gidan,

Fisgewa Faida tayi tace
"Saboda kwaďayi dai,
kwadayin abin duniya da kuma kuna ganin Nadeeyah babu wani nata zai zame muku gata,
ni kuma kunsan waye mahaifina,
in banda son abun duniya waye zai ki Nadeeyah ya daukeni,
ta fini komai na dan adam,
ciki harda halin kwarai,
ranar da muka kwashe naman miya muka boye batayi yunkurin kare kanta ba saboda girmamawa kuma tasan ku kuka dauke dan ta ganshi daga baya,
hakan baisa tayi yunkurin tonaku ba,
ku kukayi ma kanku dan ni ko Musaddiq kadai ya rage namiji a duniya bazan aureshi ba, banason zama da mijin da baya sona,
gara in nemi wanda zai soni in soshi...

"Dan bakya son Musaddiq yanzu shine zaki faďa mishi duk abun da mukayi dan ki haďa ni da ďana?

Mummy ce tayi maganar cikin kunan rai da nadama,

"Gara in faďa mishi yasan lallai fa uwar da ta haifeshi bata kaunar farin cikinsa,
domin da kina kaunarsa bazaki rabashi da matar da ko sati biyu batayi a gidanshi ba,
kuma kinsan irin son da yake mata,

uhmm ni am out of this trash ku karata can,
gida zan wuce,
tana kaiwa nan tayi gaba abinta,

Bin bayanta Radiya tayi ta janyota haďe da ďaga hannu zata kwaďa mata mari,

kammm... taji hannunta alamun an rikeshi,

waigawa tayi dan ganin wanda ya rike hannun tayi tozali da Hilal wanda idanuwanshi suka zama kamar jini saboda tsabar jaa da sukayi,

wurgi yayi da hannunta wanda ya sanyata yin baya tagaga zata faďi,

Buďe fuska Faida tayi saboda rashin jin saukar marin a fuskarta,

ganin Hilal ya nufota yasata yin baya da sauri,

kamo hannunta yayi da karfi har ta kusa missing step zata faďi,

parlon ya dawo da ita ya zaunar da ita dabass kamar wanda yayi wurgi da kaya,
nan idanuwanta suka firfito waje tayi saurin cewa

"Waye kai?
In kaji min ciwo fa?
Akan me zak----

Shut up.... ya faďi da karfi har saida kirjin Mummy ya buga,

Zama yayi yana facing dinta haďe da daukar waya dan kiran Musaddiq yaji inda yake,
karar wayar yaji a parlor haďe da sakkowarshi daga sama a hankali kamar wanda aka zarewa laka...

Maida kallonshi gurin Faida yayi yace
"Bance ki rage min ko kalma daya ba,
bance ki mance komai ba dan in kin mance u will be in for it, komai da ya faru nakeson ji nd lastly...
ina Nadeeyah?

Kamar jira takeyi ya rufe baki tace
"cikin sauki ya kamata ka tambayeni ba sai ka kusa yi min lahani ba,
in dai wannan ne zan baka labarinshi, harda shirin gaba da mukayi....

"Ba kai ba,
uwarka ma bata isa ta shigo gidannan a yanzu tasan abun da ke faruwa ba,
Musaddiq ďana ne,
ni ke da ikon zaba mishi abin da nasan zai fi dacewa da rayuwarshi,
kai waye da kake tunanin zaka iya interfering cikin rayuwarshi a koda yaushe...

Runste ido Hilal yayi dan bashi da wani kuzarin da zai iya amsata,
sake duban Faida yayi zaiyi magana yaji sautin Muryar Musaddiq
Chapter 82 · 0% Book details