← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 113

Sashe 103

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kinsan sunce kar mu bari tayi labour,
c.s zasuyi mata,

hararashi tayi ta kamo Nadeeyah domin tasan ciwon nakuda bazata taba barinta cikinshi ba,
amma tabbas lokacin barinta gidanta yayi.....

Suna isa asibitin babu bata lokaci suka karbeta sukayi aune aunensu,
bayan sun gama suka yankata suka ciro santalellen yaro wanda ya shiga cikin zuciyar Anty saude a ganin farko,
farin ciki a gurin Taheer da Amal ba'a cewa komai,
tun daga nan yaro ya fara ganin gata ta musamman domin yini yakeyi a hannu...

Ranar Suna yaro yaci suna Mukhtar.. Hilal,
shima dakyar Nadeeyah ta faďi dan da cewa tayi su sa da kansu,

duk yadda Anty Saude taso ta nuna ma Nadeeyah bata kaunarta Taheer ya hana domin ya nusar da ita cewar ba laifinta bane...

Akwai wani dare da tace mishi

"Kar dai so kakeyi ka koma gurin bazawarar yarinyar nan,
to wallahy Taheer in har tunaninka kenan gara ka janye dan bazan taba yarda su kashe min kai ba,
karka yarda kace zaka dawo da ita cikin rayuwarka in ba haka ba sai nayi mugun saba maka,

Shidai kwantar mata da hankali yayi bai bata amsa ba....

Watanta biyu da haihuwa Taheer ya fara lallabata su tafi gida,
cikin kankanin lokaci ta yarda cike farin cikin sake ganin Musaddiq,
tasan in yaga gudan jininshi zai dawo da ita su cigaba da rayuwarsu cikin kaunar juna,

Saboda tsabar sonshi da takeyi ta manta da irin wulakancin da yayi mata shi da su Anty Raudha,
tayi musu uzuri na ajizancin dan adam...

Ganin yadda take farin ciki ya sanya Taheer soma shirin tafiyarta,
ranar da suka tafi tare dasu Amal saida Anty saude tayi kewa,
tayi matukar sabawa da Junior, komai ita ke mishi,
tsanar da tayi wa Nadeeyah sam bata shafi danta ba,
domin sau daya takk a rayuwarta ta taba samun opportunity din raino,
sai gashi Allah ya kawo mata wani wanda kaddarashi tazo da ta tsani mahaifiyarshi,

Soyayyar Taheer ce kadai tasa ta yarda Nadeeyah ta zauna har wadannan kwanaki,
sai kuma soyayyar dan mala'ikan Allah.....

Lagos Nigeria..

Da murnarta ta sauko a cikin motar haďe da lumshe idonta,
memories din baya ya shiga yi mata yawo,
kofar gate din ta kama ta tura,

Mummunan gamon da tayi shi ya sanyata sakin kofar Garammmmmm.... ta koma motar su Taheer da sauri tana sheshshekar kuka...

"Lafiya Nadeeyah? Menene,

"Muje kawai uncle,
zanyi maka bayani,
tada motar yayi yajata ya fita daga layin ya wuce hotel din da ya sauka kwanakin baya,
daki biyu ya kama da parlor,
saida suka gama kimtsawa sannan ne ya tambayi Nadeeyah da har lokacin bata bar kuka ba...

"Babu amfanin komawa garesu Uncle,
sun manta dani,
Musaddiq ya riga yayi aure,
ya auri Faida wacce tayi sanadiyyar rabuwarmu,

Dan Allah uncle karka matsamin in koma gurinsu,
domin rayuwata bazata taba inganta ba,
bazasu taba barina na zama independent ba,
kowa a cikinsu ya manta dani,
bani da sauran gatan da ya wuce in nemi ilimi,
ku tafi kawai,
zan shiga duniya neman ilimi har Allah yasa in dace da tsayuwa da kafafuwata...

Tissue ya mika mata yace ta share hawayenta,
wayarshi ya dauka ya kira number mai gadin gidansu ya sashi ya duba ko Raliya na nan..

saida yayi kusan minti goma sannan ya kirashi yace bata nan amma ya samu number da take aiki dashi yanzu,
cike da murna ya umurceshi da ya turo mishi,
bayan ya turo mishi ya wuce daki dan kiranta,
yana kira ta daga kamar dama tana jiran wayar,

"Hello salamu alaikum,
ameen wa alaiki salam mummyn Fadeel, ya gida?

Cikin rashin sanin muryar tace "lafiya kalau ya harkoki,

fine alhamdulillah ya faďi yana gyara zama,

Taheer ne,
in bazaki damu ba dan Allah ina son ganinki,

Ayya Taheer ya su Anty saude,
shikenan sai kuyi zamanku haka akeyi..

dariya yayi yace
"Ba haka bane karatu ne ya rikeni,
ina Fadeel?
Gashi can yana wasa,
yaushe zaka zo?

Gobe da safe in shaa Allah,
to Allah ya kaimu Taheer, sai kazo.....

Washe gari suka hau jirgi zuwa kaduna,
saida ya fara sauke su Amal a gida suka ci abinci suka huta sannan suka wuce gidan Anty Raliya...

Basu sameta a gida ba saida suka jirata har na tsawon minti goma..

Ayi min afuwa Taheer, na kusa fara exams ne walhy,
ban cika samun zam----
muryarta ta kakare saboda yin tozali da Nadeeyah da tayi,

Mutsitstsika ido tayi haďe da sakin hannun Fadeel,

Na---dee--yahh....
ta faďi cikin rawar murya,
rau rau idon Nadeeyah yayi tace
"Na'am Anty,
kirji Raliya ta rike itama idanuwan nata suka kawo ruwa,

"Nadeeyah,
dama kina nan a raye?

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina kika shiga?

Kasa bata amsa tayi sai kuka mai karfi da ta fashe mata da shi,
zama Anty Raliya tayi ta rungumo Nadeeya tana share hawayen farin cikin,

Taheer ina ka nemo mana Nadeeyah,
shekara ďaya da watanni kenan muna nemanta,
an shiga matsaloli sosai na rashin ta,
ashe tana nan da rai..

Alhamdulillah,
Allah nagode maka da ka dawo mana da Nadeeyah cikin koshin lafiya,
kankame Nadeeyah tayi tana shafa bayanta haďe da kukan farin ciki....

kushun kushun din yaro taji yana shirin fara kuka,
hannun Taheer ta kalla taga ya daurashi a kafadarshi yana jijjigashi,

kallon mamaki ta bishi dashi tace "Taheer kayi aure ne?
Babynka ne?
ina Mamanshi?
Duk wadannan tambayoyin tayi su ne cike da zullumin kar yace mata Nadeeyah ya aura,
tasan in hakan ne tabbas rayuwar kaninta na cikin hatsari..

Jin Babyn tayi a kusa da ita tayi saurin kallon Nadeeyah da ta fara kokarin bashi nono,
dago kai tayi da sauri taga Taheer har ya fita daga dakin saboda ya bar Nadeeyah ta shayar da Babynta...

Nadeeyah yaushe kukayi aure?

Ya salam ta faďi haďe da dafe kai hawaye ya sauko a idonta...

Daura mata babyn tayi a hannunta tace
"Danki ne,
jininki ne Anty, dan yaya Musaddiq---neeee..
ta karashe cikin kukan tunanin Musaddiq yayi mata nisa...

Wata irin runguma Raliya tayi ma Junior ta dinga sumbatarshi tana zubar hawayen farin ciki,
tabbas wannan jininta ne,
komai nashi na mahaifinshi ne,

wayyo Allah,
wannan ita ake kira

*Zazzafar Kaddara*,
ina ma Musaddiq zai iya zuwa yanzu yaga gudan jininshi...
kuka sosai ta dinga yi tana sambatu a fuskar Junior....

Mrs Tijjani Shattima.....
[12/06 7:55 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣8⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

A tare suka waigo dan ganin wanda yayi wa kofar gidan haka kamar dama yanada haushin gidan,
horn din da zubair yayi ne ya sanyasu manta batun kofar Hilal yaje ya bude mishi gate din....

Daya bayan daya sheik ya kalli su Papy da su Baffa,
ganin har ya gama kallonshi bai dire idonshi kan yayarshi ba ya sanya shi tambayar inda take,

Baffa da tun shigowarshi gurin ya ke kallon Sheik yana hasashen da ya tabbatar gaskiya ne,

Daddy ne yayi karaff ya fara ma sheik nasiha da sigar tunatarwa sannan ya nuna Baffa yace wannan shine mijinta,
wannan kuma danta ne,
Allah yayi ma twin sis dinshi rasuwa,
introducing kowa na gurin Daddy yayi mishi sannan ya karashe da cewa Nadeeyah is no were to be found,
bamu samu gawarta ba shiyasa muka yarda da cewa she is alive,

Baffa ne ya cigaba da magana bayan Daddy ya dire ya ba sheik labarin yadda rayuwar Atika ta kasance da yadda kullum bata da magana sai tashi,
har ranar da zata koma ga mahallincinta saida ta ambaci sunanshi....

Kukan da sheik yakeyi mai sauti shi ya katse Baffa daga bashi labarin Atika,
babu wanda ya hanashi zubda hawaye saima wadanda ke tayashi irin su Papy, Baffa da Maleekah,
saida sukayi mai isarsu sannan suka fara tsagaitashi saboda nasihar da Daddy ya cigaba dayi,

Labarin gararin rayuwar da Papy ya gani suka bashi wanda ya sake jefashi cikin mamaki da tsananin tsoron Allah,
sosai Sheik yayi bakin cikin rashin sake ganin yayarshi,
amma yayi murna matuka da ganin yadda zuri'ata ta yaďu gwanin ban sha'awa duk da baiga mutum biyu ciki ba,
daya bayan daya ya shiga rungumarsu kamar zai maidasu ciki,
farin cikin kasantuwa da yan uwa baya misaltuwa,
a wannan rana sheik ya kira Hilal da alherin rayuwarshi,
dan a sanadiyyarshi ne ya haďu da yan uwanshi na kusa,
zuri'ar yar uwarshi da tasoshi matuka......

Masauki na musamman Daddy ya kamama Sheik da iyalanshi,
a can ma saida suka raba dare suna hira kamar babu gobe....

Jamal da Ruwaida ne zaune kusa da Maleekah suna faďa mata yadda suka daďe suna kallon films dinta,
cike da jindadi tayi musu alkawarin tafiya tare dasu domin kallon sabon film ďinta Saheebul qalbee,
sun dade suna hira haďe da daukar hotuna,
sai kusan 12 na dare suka fara shirin zuwa masaukinsu suma..

Har waje ta rakasu tana karewa kasar da bata taba zuwa ba kallo,

Har motar su Papy ta bacewa ganinta bata koma ciki ba saima waje da ta fito tana zagayawa dan karewa arear kallo sannan ta jira ganin fitowar Hilal da ke can kasa yana ma Abbunta order irin coffeen da yakeso duk dare....

"Omoo see fine girl..
wani dan bayerabe ya faďi bakinshi kunshe da wiwi,
dayan da gaba ďaya a buge yake yana kallonta dishi dishi yace

"O boy i no see anything,

kamo hannunshi yayi suka nufi inda take takunta day day hannunta rungume da kirjinta,

rigar dake jikinta girmanta duka bai wuce gwiwa ba,
sai dan karamin mayafi da ta ďaura shi akanta,

Suna karasowa kusa da ita taji wani mugun warin da bata taba jin irinshi ba duk rayuwarta,
da sauri ta matsa baya tana faďin

"Ya subhanallah,

sake matsota sukayi gadan gadan har suka samu sa'ar cafke hannunta,
gaba daya yanayinsu kyama ya bata hakan yasa ta fara masifa cikin harcen larabci tana kokarin kwatar kanta,
da taga sunfi karfinta kuma suna janta iya karfinsu ta saki wani ihu tana neman ceto,

Shurun unguwar ya sa babu wani mataimaki a gurin sai Allah,
kara karfin ihunta tayi lokacin da taga sun nufi wani lungu da ita,

"Ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagithu....
hakan ta dinga faďi hawaye na fita sharrr daga cikin idonta...
Chapter 103 · 0% Book details