Sashe 2
Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zainab da ke kwance Kan cinyar Nadiya tace "anty Madara ta, Nadiya tayi dariya tace "kiyi hakuri yanzu za'ayi abinci muci,
mamma na jinsu tayi kamar bata ji ba tace,
"au Hafizu na manta ka siyo ma auta Madara kaji, Nadiya tayi murmushi tace kamar kinsan maganar da takeyi kenan, Mamma tace au haba, taho auta ta kinsan ni namiki alkawari kuma bazan manta ba,, haka suka kasance cikin farin ciki a ranar, ji sukeyi kamar babu kamar su a doron duniyar Allah SWT, Allah sarki, kud'in da bai wuce kudin naman wani gida ba shi ya Sanya bayin Allahn nan murna har suke Jin babu kamarsu......
Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:42] Meela Adeel: 3⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
BY Aysha Ya'u Kurah
*******10:56pm******
Zaune yake cikin motarshi kafafunshi duk biyun na waje yana latsa wayarshi da ko minti uku baiyi da kunnata ba,
text din mummy ya karanta yayi d'an murmushi had'e da shafa kwantaccen sajenshi,
rufe wayar yayi ya sake duba agogo,…
gyara zamanshi yayi ya rufe motar yace
"na tabbata yanzu mummy ta isa k'asar Singapore ita da k'awanta cikin mafarki,
tada motar yayi ya karaso kofar gida,
kiran mai gadin su yayi a waya dan ya bud'e mishi gate, yana tsoron latsa hon ya dawo da mummy cikin kasar Nigeria,
da sauri Mai gadin ya bud'e mishi, ya shiga yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye Motoci,
Kiran waya ya shiga yi kafin ya karasa kofar parlon..
Badariyya na zaune tana buga game taji land line din dakinsu na Kara,
pause ta danna ta Mik'e tana tsaki,
"hello.. ta fadi cikin muryarta Mai cike da izza da isgili,
"hey Badar zo ki bude min kofa kuma kiyi a hankali Kar mummy ta jiki kin gane ko,
katse wayar tayi ba tare da ta amsa shi ba ta juya ta fita daga d'akin,
d'akin mummy ta nufa, bud'e kofar tayi ta shiga ba tare da tayi sallama ba, dan a ganin Badariyya sallama ta talakawa ce,,
hasken da ya gauraye d'akin ne ya farkar da mummy daga bacci,
Mikewa tayi hade da mik'a tace "BADAR lafiya,
yaya Musaddiq ne ya kira ni wai in bud'e mishi kofa....
Bawan Allah yana waje yana jiran Badariyya ta bud'e mishi kofa,
ganin da yayi har minti 5 ta wuce bata bude ba ya fara mita cikin zuciyarshi, d'aga wayar yayi da niyyar sake kira yaji ana tab'a kofar,
tura wayar yayi cikin aljihu ya k'arasa kusa da kofar fuskarshi d'auke da murmushi,
"ina kika tsaya ne haka, har hakuri na ya fa---- maganar ta makale mishi a mak'oshi sakamakon ido hud'u da sukayi da mummy,
zaro ido yayi ya had'iye wani mugun miyau,
dariya ya fara yi yana fad'in mummy baki kwanta ba,
tun d'azu Ina nan k'ofar gida a zaune ni da Tinau Mai gadi yana bani Labarin k'auye,
sannan malam--- juyawa tayi ta barshi a tsaye,
shigowa yayi ya rufe kofar ya bi bayanta da gudu,
can gefe ya hango Badariyya tsaye tana mishi kallon raini,
harara ya jefe ta dashi yace "tun kina yar ficiciya kin iya munafurci da makirci Ina ga in kin girma, wallhy kinji haushin rayuwar ki idiot,,
tsaki taja ta wuce d'akinsu,,
Kofar dakin mummy ya karasa,
a hankali ya murd'a kofar ya shiga had'e da sallama,
kusa da ita yaje yayi kneel down ya kamo hannunta yace
"kiyi hakuri mummy, wallahi ba party na je ba, ina gidan su Mahmud tun da na fita daga gida,
sai dare na bar gidansu na dawo kofar gida na zauna,
Dan Allah kiyi hakuri banason wannan fushin please ya karashe a shagwabe,,
bata tanka mishi ba ta zame hannunta cikin nashi tace "bani,,
zuciyarshi na dukan uku uku yace "me zan baki?,
K'ara tamke fuskarta tayi tace kud'in Baffa da na aike ka dashi,
dakewa yayi yace "ni gidan mama suwaiba kika aikeni saidai ko driver kika aika gidan Baffa,
"karka raina min hankali Musaddiq,
kalleni da kyau banyi girman da zan fara mantuwa ba,
dubu biyar na baka ka kaima "SUWAIBA"
dubu d'ari biyu na Baffa, sai dubu Hamsin na k'anwar k'awata "Hajiya Nafeesa dake layin su suwaiba,
bud'e baki yayi yace "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun,
mummy ai banji duk lissafin da kika min ba, ni dai sunan mama suwaiba kad'ai naji, na bata dubu dari biyu da biyar,
ga dubu hamsin nan a aljihuna na manta inda kika aikeni dashi,
karki damu gobe in shaa Allah da wuri zan kai mata, kika ce gidanta na kusa da gidan mama suwaiba ko?
Wani mugun kallo ta bishi dashi had'e da taune leb'enta,
matsawa baya ya fara yi dan yasan in mummy ta fara taune leb'e to abin da zai biyo baya bazaiyi kyau ba,
dai dai kofa ya tsaya kamar zaiyi kuka "yace mummy kiyi hakuri dan Allah,
cike da takaici tace "Musaddiq Anya rayuwar da ka daukarwa kanka Mai b'illewa ce,
ka zama almubazzari Wanda baisan darajar kudi ba,
in ba iskanci ba me suwaiba zatayi da dubu dari biyu harda d'oriya, wallhy tun muna mu biyu da kai gobe kafin goma na safe kaje ka amso min kudi na, kuma ka tabbatar ka kaima Hadiza kanwar Hajiya Nafeesa kana ji na ko,
gyad'a kanshi yayi fuskarshi da bata cika nuna fushi ba ta canza launi saboda tsananin b'acin rai,
Takalmin kafarshi ya cire ya kwanta yayi ruf da ciki yana tunanin yadda zaiyi ya samu dubu d'ari biyu gobe ba tare da yaje gidan mama suwaiba ba,
Sai karfe daya ya yanke shawarar Kiran yayyenshi mata ya fad'a musu komai yasan a cikinsu bazai rasa Mai bashi ba.....
Mrs Tijjani shattima....
[04/12 09:43] Meela Adeel: 4⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah
Kamar a mafarki yaji ana bugun kofar dakinshi, mikewa yayi akan dardumar da bacci ya dauke shi bayan sallar asuba,
mik'a ya fara yi hade da addu'ar tashi daga bacci,
kara buga kofar da akayi ne ya sashi kallon agogo,
goma saura kwata ya fadi da karfi yana mai karasawa kofar dakin,
murda kofar yayi a hankali ya ja da baya hade da runtse idanuwanshi saboda tsoron irin kallon da zaiyi Karo dashi...
*HAPPY 17TH BIRTHDAY BROO*
Muryoyin su ya daki dodon kunnenshi,
bude idonshi yayi da sauri ya bisu da kallo daya bayan daya,
wani murmushi ya saki mai matukar kyau, take ya manta da damuwar da ta hanashi bacci ya fara rungumarsu yana fadin "thank u so much sweeries,,
" Happy womb escape uncle"
ya jiyo cikin siririyar murya,
''omg HINAD!! ya fadi da karfi,
murmushi tayi mishi hade da yi mishi nuni da hanyar shigowa dakinshi da idanuwanta,,
Ta madubin console din dake kallon dakinshi ya hangota tsaye cikin shigar jallabiya ta alfarma kanta yane da jan mayafi ta nade hannayenta a kirjinta tana murmushi,
ihu ya saki hade da kwasawa a guje ya nufi gurinta,
bude hannuwanta tayi ya fada kirjinta,
"Best birthday gift eva luvly sis, I love u so much,
dago fuskarshi tayi ta cire farin glass din Idonta tace
''Happy birthday little Diku nah, love you more,,
karasowa suka yi cike da mamaki suka ce ''saukar yaushe ANTY REEMA,
''yanzun nan!, ko gida banje ba, ta fadi tana maida glass dinta,
waigawa musaddiq yayi gurin Hinad ya lakace hancinta yace ''cutie pie ina handsome?
yamutsa fuska tayi tace yana mota wai bazai shigo ba,
dalili? Musaddiq ya tambaya yana kallon Anty Reema,
''don't ask me kasan halin d'an naka,
kallon Sauran kannenta tayi tace mummy fa?,
RADIYA ce ta fara magana, ''muma zuwan mu gidan kenan, ina ga bata tashi ba,
hannun RAUDHA ta kama tace ''ina kika baro WALEED,?
''yana gidan Anty RALLY can yayi sallah, nasan suna hanya yanzu,, Raudha ta bata amsa cike da girmamawa,
falo suka koma dukkansu banda musaddiq da tuni ya fita gurin HILAL....
Maganata ta karshe kenan babu wanda ya isa ya sake dawo da ita farko,
bazan mishi party ba wannan shekarar FAKAT!!! mummy ta karashe fadi tana hararar musaddiq dake zaune kanshi a sunkuye,
but mummy why,? RALIYA da shigowarta kenan ta tambaya tana karasowa parlon,
tsaki mummy taja ta tashi ta wuce kitchen,
Radiya da Raudha kuwa mamaki ne ya hanasu magana dan a iya rayuwarsu sunsan babu abin da mahaifiyarsu ke so sai bidi'a,
haka nan ma kirkirar party takeyi in kudi yayi mata yawa, babu d'a, ko jikan da shekara ta taba wucewa ba ayi mishi kwarya kwarya ba,
barin ma danta d'aya namiji tilo wanda partynshi ke banbanta da na kowa, shiyasa sukayi sammako dan ayi komai dasu,
''wow MIRACLE ya sakko kenan,
yau mummy ce da kanta take cewa bazata yi ma little birthday ba,
iko sai Allah Anty Reemah ta fadi tana mai mikewa,
Raliya tace ''kedai bari anty na Kasa ajiye jaka saboda mamaki,,
'''Ba abun mamaki bane laifi yayi ma mummy'''
waigowa sukayi suna kallon ta inda maganar ta fito,
karasowa tayi rike da cup a hannunta tace
''kwarai kuwa, almubazzaranci yayi da kudin mummy,
ta aikeshi ya kaiwa Baffa shine ya kai gidansu Nadiya Roba Roba,
kuma kudin da yawa har 200k,
mikewa musaddiq yayi a fusace yayi kanta,
rikeshi Anty Reemah tayi da sauri ta girgiza mishi kai alamar ya kyaleta,
Badariyya ta rike kugu tace da kin kyaleshi anty,
karya akayi maka, mtswww wanda bais----''shut up'' Anty Reemah ta katseta da karfi,,
''yaushe yarinyar nan ta fitsare haka,
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun,
duka nawa kike Badar?, Musaddiq sa'an ki,
''Ba sa'a na bane amma abin da zaiyi ni bazanyi ba, dan Sam bashi da hanka-----
wucewar walkiya da tsayuwar ji na wucin gadi ne ya hanata karasa maganar,
rike kuncinta tayi ta Sanya kara mai firgitarwa,
cike da firgici su Radiya suka karaso gurin,
kallo anty Reemah ta bishi dashi yana huci hade da zazzaro ido,