← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 113

Sashe 107

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar dai yadda na faďa maka Alh Mukhtar,
Taheer ďana ne,
kanina ne ya haifeshi, mahaifinshi Allah yayi masa rasuwa shekarun baya da suka wuce,
to yana zaune tare da mahaifiyarshi acan Canada,
wannan zuwan da mukayi, alkhairi ne ya kawo mu,
a yanzu da na fahimci wacece Nadeeyah sai nakejin kamar yau dinnan a kaddamar da komai a hutar da kowa,
domin ita din 'ya ce ga kowanne a cikin mu,
duk da na fi kowa karfi akanta a al'adarmu da kuma musuluncinmu,
yanzu a gurina nine mutum marar karfi akanta dukkanku nan kun fini karfi,
ku kuka san komai nata tun tasowarta,
Saboda haka Alhaji Mukhtar nazo gareka ina nemawa ďana *Taheer auren ďiyarka Nadeeyah.... *
yana disa aya fadawa suka yi mishi kirari haďe da miko mishi ruwa yasha domin yin magana mai tsayi...

Ya ilahi... haskowa masu karatu halin da daukacin yan uwa da masoyan Musaddiq halin da suke ciki..

A kiďime Musaddiq ya mike da zaman da Papy ya tursasa masa yinsa,
domin yaso bin bayan su Anty Saude da kuma Nadeeyar da ya tabbatar tana kitchen din...

Cikin kaurarrar murya yace

"whatt a jo----
da sauri Hilal ya toshe mishi baki haďe da kokarin maidashi ya zauna,
iya karfinshi yasa ya hankaďa Hilal ya tafi tagaga zai faďi..

Daddy da a ganinshi yafi Musaddiq din shiga tashin hankali yayi saurin mikewa ya rike Musaddiq dake shirin sake magana,

"Da aka fara magana kaji an kira sunanka?
Ko irin tarbiyyar da ka samu kenan?,
a gaban bakin mu wanda yake kamar Mahaifi ga Nadeeyah kake kokarin nuna musu irin rashin mutuncin da ka koya cikin kankanin lokaci ko?,
to bismillah,
in ka gama dasu sai ka dawo kaina.....

'Dago idonshi da ya zama kamar gauta yayi ya kalli gefen da Taheer yake,
da sauri ya kauda kanshi haďe da fara takawa baya a hankali,
cikin rashin sani yayi muguwar buguwa da bangon bayanshi..

Da gudu Hilal ya doso inda yake, kafin Hilal ya karaso ya juya ya haye sama da gudun da taku uku kaďai yayi ya isa ďakin da yake...

Dafe kai Papy yayi cike da tausayi ya kalli Daddy da ya koma ya zauna yana magana cikin karfin hali..

"Mashaa Allah ranka ya daďe,
na baku Nadeeyah,
Allah ya sanya albarka a cikin auren,
karku damu da sakarcin Musaddiq,
yarinta ke damunshi..

Cike da jindadi Sarki yace
"To madallah,
sai a yanke mana sadaki domin muna da nisa,
munfi son ayi komai cikin lokaci...

Wannan karan duk wani kuzari na Daddy ya kare da kyar ya iya cewa

"Da kai da kaya duk mallakan wuya ne,
ranka ya daďe duk hukuncin da ka zartar daidai ne...

Kuka sosai Anty Raliya ta fashe dashi na tausayin dan uwanta da kuma halin da taga mahaifinta,
daki ta wuce da gudu Husna ta rufa mata baya itama kukan takeyi...

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun... shi kaďai take maimaitawa tana faďin duk laifi na ne,
a tunanina in Nadeeyah ta dawo zata komawa Little,
ashe wata kaddarar Allah ya shirya mana daban,

Cikin kuka take bawa Husnah labarin komai da tayi wanda yake neman jefa dan uwanta cikin barazanar rayuwa....

Wani irin wawan mari Anty Reemah da ta biyo bayansu taji komai ta wanka mata..

cikin masifa ta fara zaginta tana kiranta da marar imani,
tasan inda Nadeeyah take tabar kowa cikin zullumi musamman Mahaifiyarta dake fuskantar rayuwar ukuba saboda hakan,
ta inda take shiga bata nan take fita ba..

Durkusawa Anty Raliya tayi cikin kuka ta bata hakuri da kuma amsar laifinta,
ita tayi shi ne in a good faith dan Nadeeyah ta samu ingantacciyar rayuwa,
ashee inganta rayuwarta zaiyi sanadiyyar shigar rayuwar Musaddiq cikin wani rudanin..... ta karashe cikin matsanancin kuka.....

Zama sukayi su ukun suna cikin jimami suna zubarwa da dan uwansu hawaye...

Minti goma kaďai su Sarki suka kara sukayi shirin tafiya,

Kallon Hafeez Shareefah tayi tace anjima suzo shi da iyalanshi su sameta..
cikin ladabi ya amsa mata da "To,

Adress ta karba gurin Taheer ta bashi cike da farin ciki.....

Katse wayar dake shigowa cikin wayar Baffa yayi karo na biyar ya tashi ya tafi yin rakiyar su Sarki shima jikinshi ba kwari,
kawai dai basu da bakin bijire musu ne dan suna da dukkan iko akan Nadeeyah,
ga kuma taimaka mata da sukayi, ya zama dole suma su rama musu halaccin da sukayi mata...

Kallonshi tayi cike da tausayi bayan ya gama nacin Junior yazo gurinshi yaki,

A hankali tace "Bari mu tafi *KYARI*
in shaa Allah gobe da safe zan kawo maka shi,
baka bani phn numbernka ba,
kai dai har yanzu kana nan da miskilancinka akan mace,
to ni na tambaya a bani,

Dariya yayi wacce da gani yake ce, ya fara faďa mata number,

Shafa kan junior yayi yace "Takwarana sai gobe ko,
ka zo da kaya da yawa dan rikeka zanyi....

Saida suka ga fitar motocin sannan suka koma ciki dukkansu babu mai karfin yiwa dan uwanshi magana...

*DADDY*

sunan da ya bayyana a jikin wayar haďe da special ringing tone,

Dauka Husnah tayi ta nufi kitchen da wayar,
can baya ta hangota zaune tana wasa da yatsun kafarta,
dafata tayi haďe da zama a gefenta,

Idonta da sukayi luhu luhu ta dago ta kalli Husnah haďe da kakaro dariya, zatayi magana kenan wayar ta sake kara,

Ajiye mata wayar Husnah tayi akan cinyarta ta kauda kanta can gefe,
ganin sunan ya tabbatar mata da junior ne da aikin nan dan tare suka siyo sim din Nigeria dashi,,

Saida ta kusa katsewa ta dauka,,

"Mamma..
ya faďi kamar karamin yaro..

"Uhmmm Uncle,,
tafiya babu sallama ko?

Kwantar da kanshi yayi a jikin kujerar yace
"Na daga miki kafa ne,
nasan yau baki da lokacin mu ni da junior,
kinga yan uwa bayan dogon lokaci,
just call to tell yhu
"I love yhu alot..

Runtse idonta tayi tace
"Uhum,

"Uhummm, say it plss,
ya faďi cikin kaguwa,

"Same to yhu..

Dariya yayi yace
"Muna nan zuwa anjima bayan isha'i, take care plss...

"Ohk uncle, in shaa Allah bye.. tana kaiwa nan ta katse wayar...

"Husnah kun dawo kaduna ne ko kunzo hutu ne?

Hannayen Nadeeyah Husnah ta kama ta fashe mata da kuka,

"Dan Allah Nadeeyah karki auri Uncle,
dan Allah karkiyi sanadiyyar mutuwar Yaya Musaddiq,
Sake dawo mata da ainihin labarin halin da ya shiga bayan tafiyarta tayi,
sannan ta kara mata da irin halin rashin walwalar da ya ke ciki har yau dinnan da ya ganta..

Da sauri Nadeeyah ta share hawayenta tace

"Walwala?
wacce yakeyi da FAIDA matarshi fa?

"Faida?
Husna ta faďi cike da mamaki,

Faidar da keda 'ya'ya uku?
Faida ai tayi aure bayan rabuwarku da sati biyu,
ta auri abokin yaya Musaddiq Zubair..

Cikin sanyin jiki Nadeeyah tace "Na gansu tare a gidanshi suna tsaye cikin annashuwa da jin dadi..

"Kwarai kuwa zaki gansu,
basu da nisa,
kinsan bayan rabuwarku Daddy ya saki Mummy,
sai ya koma lagos da zama,
duk wanda yaje gidan ita ke kawo mishi abinci,
may be kin samesu ranar da baki a gidan ne.. 

Shuru Nadeeyah zuciyarta ta raunana matuka,
tausayin dan uwanta Musaddiq ya ratsa dukkan sassa na jinin jikinta,
saidai is too late... wata zuciyar ta faďi mata yayin da ta tuno da irin halaccin Taheer a gareta,

Shanye kwallar da ta taso mata tayi tace

"Husnah, Allah ya kaddara zamana da yaya Musaddiq na ďan lokaci ne,
rabon da ya haďa mu gashi nan ya fito duniya,
kinsan an ce Matar mutum kabarinsa,
a yanzu bana tunanin zan iya zama da kowani namiji in ba Uncle ba,
dan All---
da sauri Husnah ta bar gurin tana fitar da kuka mai sauti...

Rufe fuska Nadeeyah tayi itama ta fashe da kukan da ya daďe da tokare makoshinta.....

Tun Hilal na bugun kofar dakin Musaddiq har ya hakura da bugun ya koma ban baki..

"Look Kyari,
don't harm urself,
ka bude min kofar nan, everything will be alright,
trust me....

Kamar da dutse yake magana, dan Musaddiq bai ma san abinda yake fada ba,
tsaye yake gaban madubi hannayenshi dukka biyu ya daurasu kan table din yana fitar da numfarfashi kamar zakin da ya hangi nama,

Kalmar
"Daddy da yaji daga bakin gudan jininshi, da kuma kalamanshi,
har kawo furucin sarki, sai amsa kuwwa sukeyi a kunnenshi,

runtse idanunwanshi yayi saboda wani irin yanayi da yake ji a cikin jikinshi,
kaunar Nadeeyah dake adane a majiya mai tsafta ta taso mishi gadan gadan kamar guguwa mai karfin gaske,
da sauri ya buďe idanuwanshi wanda hakan yasa ya daki glass din mudubin dake dakin saboda yadda yaga idon kamar jini dan tsabar jaaa....  

A firgice Little Nadeeyah ta farka da tsananin ihu tana waigen ta inda karan ya daki kunnenta,
hango Musaddiq tayi yana sake bin glass din yana farfasa su da hannunshi da jini ke zuba..
a tsorace ta nufi kofar fita tana ihu tana kiran sunan Mahaifinta..

Muryar Hilal taji yana magana cikin ihu yana umurtata da buďe kofar,
dakyar ta iya dabarar da ta murďa lock ta buďe da sauri ta faďa jikinshi tana ihun kuka,,,

Mika ma Maleekah da karar glass ya tarkato su zuwa sama yayi ya nufi Musaddiq da gudun gaske,

Hilal na ta'bashi yayi wurgi dashi ya cigaba yin wurgi da kayan gaban madubin yana faďin
"i'm useless,
Daddy is right i'm a fool nd a looser,
bani da amfani a gurin kowa,
gara in mutu kowa ya huta da mutum marar amfani iri na...

Cikin kuka yan uwanshin ke kiran sunanshi suna hanashi ji ma kanshi ciwo,
duk suna tsoron matsawa kusa ya illata su,

Mummy kuwa da tasan duk itace silar hakan zama tayi a bakin kofa tana kuka ririsss,

Cikin zafin nama Daddy ya karaso cikin ďakin ya isa gaban mudubin ya juyo dashi da karfi ya daukeshi da kyawawan mari har guda uku,
yana shirin sake yin na hudu Baffa da Papy suka hanashi..

Cire hannun Papy Musaddiq yayi a jikin Daddy ya kai hannun fuskarshi ya cigaba da marin kanshi,

"Slap me to death Daddy,
Dan Allah ka mareni har sai mutuwa ta riskeni,
i'm dead already,
numfashin ne kadai ya rage,
wallahi ko baka kasheni ba,
ni zan kashe kaina....
Chapter 107 · 0% Book details