← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 113

Sashe 68

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasan zakayi mamakin dalilin da yasa nace kazo,
to dalilin mai karfi ne,
nan ta labarta mishi abun da taji daga bakin su Mummy da Rauda sannan ta daura da cewa,
a yau ba gobe ba ina son kaje gidan Alhj Muntari domin maganar auren Musaddiq da Nadeeyah,

Alh Muntari ya cancanci ayi mishi fiye da haka domin ďan halas ne,
mutumin kirki ne,
zuciyarshi kamar auduga haka take,

tunda har ya nuna ya son abun nan,
dan Allah mu nuna mishi mun fishi so saboda mu saka alkhairi da mafificin alkhairi,

Cike da jin dadi papy ya gamsu da maganar Anni kuma yayi alkawarin a yau zaije ya sameshi su tsaida maganar auren,
bazai jinkirta ba dan kar shaidan yasa shi jin kunya.....

Tare sukayi Sallar Isha'i a masallacin kofar gidan Daddy,

Cike da murnar sake ganin shi Daddy yaja shi zuwa cikin gidan dan suyi dinner tare...

Suna gama cin abinci suka hau hira Daddy yace

"Yata tana shirin zuwa sai gaka kazo,

dariya Papy yayi yace

"Nima zuwan ďana nayi,
neman auren yarka nazo yi,

Allah yasa ba'a riga mu ba?

Dariyar rashin fahimta Daddy yayi yace wacce yar a ciki??

Nadeeyarka nazo nemawa ďana Musaddiq,

Ajiyar Zuciya Daddy yayi dan gaba daya tunaninshi ya tafi can gurin ďan Papy Jamal,

fadada Murmushinshi yayi yace wannan dan naka sai a hankali,
gaskiya kace ya nemi wata,
ni 'yata sai Governor,

Wata irin dariyar manya Papy yayi yace
"kasan in da rabo shima zai taka wannan matsayin,
mun kawo kokon baranmu,
Allah yasa a cika mana shi,

Duk wanda yaga fuskar Daddy a lokacin yasan yana cikin farin ciki matuka,

"Na baka ita Alhj Abdallah, au Proff Saifullah,

Nadeeyah ta Musaddiq ce,
in shaa Allah,
yanzu sadaki kawai zan yanke muku ku kawo,
sai a sa ranar daurin aure,
kunsan yar tawa mai tsada ce,
ku kawo miliyan goma,

Mikewa Papy yayi yana dariya yace
"zamu kawo fiye da haka,
mun gode kwarai Allah yasa ayi auren nan a sa'a,

Ameeen ya Allah... Daddy ya fadi hade da mikewa,

rakiya yayi mishi suna hira har suka karaso gurin motar,

Motar Musaddiq ce ta kunno kai cikin gidan,
yana yin parking suka fito suka karaso gurin su Daddy,
cike da girmamawa Musaddiq ya gaida Papy,
dagoshi yayi ya amsa hade da cewa
"kana lafiya Ango,
sunkui da kai Musaddiq yayi yana sosa keya,
dariya Papy yayi yace

"Allah ya tabbatar mana da alkhairi,

Ameen Papy...
Musaddiq yace ya ja baya ya tsaya,

kallon Nadeeyah da Husna Papy yayi yace
"baku tambayi mutuniyar taku ba,
da sauri Husnah tace

"Ay gobe zamu je Gombe in shaa Allah,

"aaa to masha Allah sai ku shirya goben sai mu tafi tare karfe sha biyu,
da Murnarsu suka amsa da

"To zamu shirya da wuri,

Gurin Hafeez suka zaga suka cikashi da Hira,
saida suka fi 30mints a gurin sannan duk suka shiga cikin motar,

Hafeez na kokarin tada motar Husnah tayi saurin dakatar dashi,
number wayarshi ta bukata nan take ya karanto mata sannan yayi musu sallama suka wuce.......

Tashin Husna Nadeeya ta dinga yi akan taje ta tada Musaddiq kar ya makara dan jirgin 6 zaibi zuwa lagos,

mikewa tayi tana turo baki tace "kije ki tasheshi mana,
ni bazan iya ba,
hakuri ta shiga bata har ta samu ta yarda ta wuce dakinshi,

kamshin turarenshi da taji ne ya bata tabbacin ya tashi,
a tsaye ta sameshi yana gyara links din hannun rigarshi,

"ashe ka tashi?,
alhamdulillah na huta,

dariya yayi yace aikin Mummy ne,
tun dazu ta tasheni,
ina matata?

Hamma Husnah tayi tace "tana daki ita ta matsa min inzo in tasheka karka makara,
sosai yaji dadi har cikin ranshi yace
"muje in ganta kafin in wuce,

A kofar shigowa suka kusa karo da Mummy rike da plate din indomie da kwai,

Cup din hot choco kadai ya karba ya yi hanyar dakin su Nadeeyah,

"Ina zaka je?
Mummy ta fadi tana bin bayanshi,

"amm zan je.... zan ----
dawo nan ka zauna kaci abinci,

ko jirgin na ubanka ne in lokaci yayi bazasu jiraka ba,

"Mummy,
Nadeeyah bata da lafiya ne zai duba ta....

wani mugun kallo tabi Husnah dashi wanda yasa ta saurin murda kofa,

"zo nan sakarya wacce bata san ciwon kanta ba,

sum sum Husnah ta dawo inda Mummy take,
kunnenta ta kama tace

"wallahi kinji na rantse,
wannan rawar kafar da kikeyi akan Nadeeyah in baki daina ba sai na ci miki mutunci,
kuma in sake jin maganar tafiya Gombe a bakinki sai na tattaka ki, marar mutunci kawai..
ta karashe hade da dungure mata kai,

kafa Husnah ta fara bugawa a kasa tana fadin

"ni wallahi sai naje,
hanyar dakin Daddy tayi Mummy tayi saurin tareta dan karansu na daren jiya baiyi mata dadi ba,
yanzu in ta bari Husnah ta kai kararta tofah tasan bazai mata da kyau ba,

"Ina matsayin mahaifiyarki kike kokarin bijire min har kike yunkurin kaini kara,

ni zakuyi ma tawaye?

Babu komai kuyi abin da kuka ga dama ta karashe tana matso kwalla,

kewayeta sukayi suka shiga rarrashinta,
dakyar ta hakura ta tasa keyar Musaddiq har mota sannan ne ta samu kwanciyar hankali.....

Dubu dari biyu Papy ya bada kudin sadakin Nadeeyah,
sai dubu dari na gaisuwa...

cike da farin ciki Daddy da abokinshi Alh Abubakar suka karbi kudin,
nan Daddy yasa biki wata biyu dan yana so ya samar musu gida a can lagos dan suyi nesa da duk wani tashin hankalin gida.....

*(Shaff ya manta Raudha na lagos kuma duk tafi kowa matsala cikin 'yayan nashi,)...*

*******

Woww mashaa Allah my little brother ya girma,
yaushe aka sa bikin Daddy?

"June amma bamu cire date ba,

Maganar shirye shirye na kira inyi miki,
inaga zan turo miki kudi ku shiga Dubai kuyi mishi siyayya,
sannan zan bawa su Raliya su siyo wasu anan dan mahaifiyarku tace babu hannunta,

dariya Anty Reemah tayi tace
"ko sisinka karka kashe Daddy,
zamu hadu mu hada mishi lefe na gani na fada,

"wallhy naji dadin wannan hadin dan dama bana son Nadeeyah ta kufce mana,
kullum cikin tunaninta nake..

"Ajiye kofin zobon dake hannunshi yayi ya dafe kanshi da ke sara mishi,

"shikenan ya rasa Nadeeyah, tunda har akasa ranar auren ya fidda ranshi da tunanin ko Allah zai taimakeshi ta zamo tashi,

maida kwallar da ke kokarin fito mishi yayi da sauri yace

"wish u all the best Nadeeyah,
Allah ya dawwamar dake cikin farin ciki...

yasan Musaddiq na can yana nemanshi,
haka itama Nadeeyar,
bashi da karfin kunna waya yayi magana da ko daya daga cikinsu,
dan raunin da yake ciki bazai barshi ya danne zuciyarshi ba,
dole ya koka musu har su gane yana cikin damuwa,

Yana cikin wannan tunanin yaji Anty Reemah ta dafashi tace
"shine baka fadamin wannan abun dadin ba,
yanzu sai mu fara shiri daga bangarenmu,
dan bazan bar kowa yayi mishi kayan lefe ba,
kai kuma sai ka shir----

Mum kinsan ina Msc,
kuma mun kusa fara exams, dakyar zan samu zuwa,

"cike da Mamaki tace

"Hilal...

Musaddiq ne fa,

kada kanshi yayi cike da damuwa yace
"Mum bance bazani ba,
amma for nw banda karfin shirye shirye,
plsss ku barni inyi karatu...

Mikewa tayi cike da tausayin danta tace
"take ur time dear,
Allah ya bada sa'a...
tana kaiwa nan ta wuce kitchen ranta duk a dagule.....

Gaba daya Nadeeyah ta mance damuwarta tunda tazo garin gombe, gidan karamci,

wani irin ji dasu Mami takeyi kamar ita ta tsuguna ta haifesu,

Yawo kuwa babu gurin da basu je ba a cikin Gombe,
ga wani shiri na musamman da Mami tasa akewa Nadeeyah wanda ya kara fitar da kyawunta ta ciko tayi bulbul,

fatar jikinta sai sheki takeyi ga santsi kamar tarwada...

Husnah da Hafeez kuwa wata shakuwa mai kama da soyayya ce ta musamman ta shiga tsakaninsu,
tun Hafeez na dari dari har ya saki jikinshi sosai da ita,
raba dare sukeyi suna tsaftattaciyar hirarsu mai ban sha'awa,
da Papy ya lura da hakan ya kirasu duk su biyun ya tambayesu,

Husna ce ta fara amsawa da tana sonshi,
sannan ne Hafeez ya samu karfin gwiwar bada tashi amsar,

farin ciki marar misaltuwa Papy ya shiga..

sallamarsu yayi hade da kiran Daddy ya labarta mishi,

Daddy cike da jindadi yace to ai bazamu jira ba,
gara a hade bikin ayi shi rana daya,
nan suka gama tsara yadda zasuyi sannan sukayi sallama cike da jindadi....

Kwanciya Daddy yayi yana kabbara da girmama hukuncin ubangiji,
wato ubangiji ya hanashi auren Suwaiba saboda wannan ranar da auratayya zata bullo a tsakanin jinin da suka yi tsaftattaciyar soyayya ta tsakani da Allah,

lallai
*kaddara*
itace jigon rayuwar dan Adam,
domin da ita yake yawo duk inda zashi....
ina ma Suwaiba zata dawo taga hukuncin ubangiji,
taga yadda rayukan 'yayanta suka canza,

wata yar kwallar murna ya share yayi adduoinshi hade da runtse idanuwanshi......

Hauka ne kadai Mummy bata yi ba da taji labarin hade auren harda na Husnah da suka gama maganarta da kawarta Hajiya Safara'u,
babu irin masifar da batayi ba,
shiko Daddy ko a jikinshi kudin kayan kitchen ma yayi mata transfer zuwa account dinta dan sauran da kanshi zaiyi su,

Sa kai yayi ya fita ya bar gidan dan lagos ma zai tafi da daddare akan maganar gidan da aka samu...

Kuka ta zauna a parlor tana yi sosai kamar an mata mutuwa,
bakin cikin da take ciki yau har gwammaci dama bata taba sanin Daddy a rayuwarta ba,

Badar ce ta fito tana hamma,
duk wainar da ake toyawa a gidan bata da masaniyarsu dan ba zaman gidan takeyi ba,
da sauri ta isa gurin Mummy tana tambayar abun da yasa ta kuka,

Ganin da tayi wa Badariyya ya sa hankalinta dan kwanciya,
dan wani abu da ya darsu a ranta,
tasan Badariyya ce kadai zata iya yi mata maganin damuwarta...

Hannunta ta rike ta sake rushewa da kuka tace

"Badar na shiga uku,
Musaddiq zai auri Nadeeyah, Hafeez kuma Husnah,

kinji a inda zan kare a ya'yan da basu da asali,

yayan mai gadi ni zainab.....

Wani irin ihu Badar ta saki tace

"Whattt?

Nadeeyah zata auri Musaddiq dina....
ta fadi hannu na rawa tana dafe kirji.......
Chapter 68 · 0% Book details