← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 113

Sashe 29

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan auren ne ta gane yaudararta yayi,
yazo ne kawai dan ya kwashi dukiyarta yayi gaba,
ko da ta fahimci haka bata dauki zafi ba dan ita mai bashi dukiyarta ne,
abin da ya tsiro dashi na shigowa da mata gidane yafi tunzurata har ta kai ga aikata kisa a gareshi cikin rashin sani,

A kotu ne aka fahimci cewar tana dauke da cikinshi na wata hudu, koda ta fahimci hakan saida taci kukan dana sanin zuciyarta marar kyau,
Kotu bata yanke mata hukunci ba har sai ta haifi dan dake cikin ta ta yaye,

haka kuwa akayi har cikinta ya isa watan haihuwa,
kamar hadin baki dukka ukun ya'yan Baffa cikin garesu,

Husna aka fara haifa, washe gari Nadiya ta biyo baya,
haihuwar Badariyya tayi gardama saida aka yanka Leemah,
ba karamar wuya Badariyya ta ba mahaifiyarta ba,
bayan awanni da yi mata aikin aka fahimci jikin nata babu dadi,

cike da kwarewa doctors ke aikinsu amma ina abin yaci tura, aikin mala'ika da na mutun ba daya bane,
Ashe leemah ajalinta ta auro har ta haifo mishi 'ya,
ba karamin tashin hankali duk suka shiga ba na rashin yar uwarsu, musamman Goggo da tayi karamar hauka...
mummy ce ta dauki Badariyya ta hada da Husna ta shayar dasu cike da kulawa...

Tun a karancin shekarun 'yayan suwaiba suka fahimci zumuncin zuri'arsu sai in kana da kumbar susa, marasa wulakantasu aciki kadan ne....

Rayuwa Badariyya tun tana karama ta tashi a sangarce, bata ganin mutunci ko jin kunyar kowa,
Hilal shine wanda tun fil'azal basa shiri, a gurinshi tasan ba mummy bace ta haifeta,
ranar yaci dukan tsiya a gurin mummy,
Tana gama dukanshi ya fita dan ko a jikinshi dama so yakeyi ya nuna mata ita fa ba yar gidansu bace ta daina kusu fi'ili......

Da wannan labarin zumunci ya faro,
sila itace mace,
uwa,
wacce take da daraja,
wacce Allah swt ya bata ragamar tafiyar da zuri'a,
lallai Macce ta gari itace ginshikin alumma,
domin gyara rayuwae ya mace kamar gyara alumma ne,
mu dage tun yanzu gurin yi ma 'yayanmu maza adduar mace ta gari domin wayau ko dabara bazai basu ba,
sukuma yayanmu matan ka sanya su zamto Mar'atus saliha ga mazansu.....

Mrs Tijjani Shattimah....

[08/03 12:28 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

_HAKKI, HAKKI BABBAN ABU NE YAN UWA, KOMIN KANKANTARSHI MU GUJI DAUKARSHI DAN KANANAN ZUNUBBAI SUNFI MANYA ILLAH, DAN ALLAH MU KIYAYE HAKKIN JUNA_

*Cigaban Labari*

Jiki a sanyaye ta dauko sarkar dake cikin akushin tayita juya ta a hannunta,
tasan Baffa ya dade da mantawa da zaman sarkar shiyasa tayi mata muguwar ajiya,
ko da wasa bata taba yunkurin sata ba,
tun da taje ta tambayi kudin sarkar taji kudi ne masu tarin yawa ya sanyata kara yi mata kyakykyawan ajiye,
ajiye sarkar tayi hade da tagumi. ya zame mata dole ta nuna musu gaskiyarta, shiyasa ta fito da sarkar dan bawa su Nadeeyah gadonsu,
tasan wannan ita ce kadai mafita a gareta da diyarta,
tasan in tayi hakan Muntari bazai yi mata zargin muguwar uwa ba,
zaiyi mata kallon mai amanar da ta iya rike abu mai daraja saboda soyayyar uwarsu,
wannan hanyar ita kadai ce abin da zai samar mata mafita...

Rufe akushin tayi bayan ta dauko wasu magunguna a ciki,
inda ta daukoshi nan ta maidashi ta fito parlor ta dauko leda mai kyau ta zuba sarkar a ciki, sannan ta shiga yin amfanin da magungunan domin rufewa su Daddy da sauran baki....

*1:51pm*

Motaci uku ne suka shigo cikin harabar gidan Baffa,
Motar Anty Reemah ce ta fara shigowa, sannan sauran kannenta suka rufa mata baya,

Raliya ce zaune a gaban motar Anty Reemah, sai Zainab (kanwar Nadeeyah) da Hinad,

a motar Radiya aka tara taron marasa mutunci,
Raudha da Badar,
Cikin kunci Badar take saboda Nadeeyah da Husnah sun shiga motar Hilal,
duk yadda taso taja Husna suzo a mota daya taki saboda farin cikin tayin da Hilal yayi mata na shiga motarshi,
ko kallon motarsu batayi ba ta wuce cikin gidan tana huci,
a zaune ta samu Goggo hannu rike da carbi tana ja,
Allah kadai yasan abin da take furtawa domin janshi kawai takeyi,
babban tashin hankalinta bai wuce kar Baffa ya fada musu komai na labarin Atika ba,
burinta su sameta ita kadai ta hada musu kirkirarren labari ta fada musu saboda tseratar da auren yarta,
jikin ta Badar ta fada ta fara zuba mata shagwaba,
gyaran murya Goggo tayi ta mata nuni da carbi alamar ja takeyi,
sauka tayi ta daura kanta a kan cinyarta,
damuwar da Goggo take ciki ta hana ta fahimtar damuwar dake kan fuskar yar lelenta...

Sallamar su Anty Reema ne ya sanya Goggo sakin Murmushi hade da tattara hannu guri daya tana musu gaisuwa dan su gane carbin take ja bata son a katseta,

neman guri sukayi suka zauna suka bude flow din hirarsu ta kasuwanci,

shigowar su Nadeeya ne ya katse musu hirar saboda yadda Goggo ta yafito su da hannu ita da Zainab,
a darare Nadeeyah ta sauke zainab suka matsa kusa da ita suka durkusa zasu gaisar da ita tayi saurin durowa daga kan kujerar ta hadesu ta rungumesu hade da kuka mai karfi,
"Allah sarki Suwaiba,
ganin jininki ya tuno min ke,
inama ni mutuwa ta dauke ta barki cikin 'yayanki,
inama zan juyo da hannun agogo baya da na nuna miki irin muhimmacin da kike dashi a cikin rayuwata,

cike da mamaki daukacin mutanen parlon ke kallon Goggo,

Ciki kuwa harda Baffa da ya sanyo kanshi cikin parlon ya tarar da abun da idanuwanshi basu taba tozali dashi ba,
yaran da ko cikin parlon basa samun albarkacin shiga bare har su samu darajar runguma,

wani dadi ne ya ziyarci zuciyarshi yayi tunanin mutuwar Suwaibar ce ta kadata haka,
da sallama ya katse shurun mamakin yace "yau gidan nawa cike yake da matana kenan,
sai wacce na zaba,
Murmushi dukkansu sukayi suka gaida shi hade da cewa ai dukkan mu zaka hada,

Badariyya ya kalla da ta rike kanta saboda bugeta da Goggo tayi gurin sakkowa daga kujera,
"a'a Amaryata me akayi miki naga kin rike kai?
sakin kan tayi ta turo baki tace "ba Goggo bace ta bigeni, kallonta Goggo tayi tace "yi hakuri Badariyya ban kula bane, hankalina nakan marayun Allah, babu uwa babu uba, kai wannan rayuwa abar tsoro ce,

Anty Reemah da abun ya bar bata mamaki tace "dama haka ne Goggo,
Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,
ta yiwu mutuwar ita kadai Allah ya ga zata zamto hutu a garesu, shiyasa yayi gaggawar daukesu, Allah sarki Mama Suwaiba,,

wani kukan Goggo ta kuma kecewa dashi tana dada kankame zainab,
kallon tsoro zainab din take mata shiyasa ta saki kuka ta fisge kanta ta koma jikin Nadeeya,

share ma juna hawaye sukeyi gunin tausayi,
shigowar su Mummy dakin ne yasa duk suka mike domin bawa Daddy gurin zama,
bayan yan gaishe gaishe Baffa yace " yau gida yayi albarka, dariya Daddy yayi ya tsuguna ya gaishesu,
bayan yan hirarraki Daddy ya gabatarwa da Baffa dalilin zuwansu, ya kuma kara da cewa "kayi hakuri Baffa nayi maka shishigi a cikin alamarin gidanka,
inason sanin dalilin kiyayyar ne saboda yana neman zama min matsala a cikin Zuri'ata...

Kuka Goggo ta saki tace "Babu kiyayya cikin zuri'ata da na gina ta shekara da shekaru,
kasan zumunci yanzu ya zama na yan zamani,
amma ni a gurina kowa daya yake,
bana banbanta su,,
gyara zama Daddy yayi yace "nasan bakya banbanta su, domin dukkansu 'yayanki ne babu bare a ciki, amma ya kamata ku tsawatar akan yadda akayi ma zumunci rikon sakainar kashi,
bana san yadda abubuwa suka kasance a nan gidan su kasance a cikin 'ya'yana,
bazan dauka ba,
inason 'yayana su fahimci muhimmancin mai shi da marar shi,
banason dattin duniya ya zamana sillar yankewar zumuncin 'ya'yana,
shiyasa nazo a warware min komai kuma ayi ma tufkar hanci,

Gyaran Murya Baffa yayi zai fara Magana Anty Reemah tayi saurin cewa "yi hakuri Baffa zan katseka, dan Allah so nakeyi ka fada mana wacece *ATIKA*
a duburce Goggo ta waigo ta harareta ba tare da sun hada ido ba,
a zuciyarta tace "kaji shegiyar yarinya, ana neman kai magana karshe ba tare da an bullo da maganar Atika ba ta sako zancen ciki,
kara gyara zaman carbinta tayi tana kallon Baffa dake shirin basu labarin Atika....

Kuka sosai Nadeeyah da Hafeez sukayi najin ba Goggo bace ta haifi mahaifiyarsu,
ashe dalilin kiyayyar kenan,
sun sani tabbas in har uwa daya suke dasu Mummy bazasu taba wulakanta mahaifiyarsu ba ko da kuwa mijinta yafi *KAMAYE* talauci

Shi kuwa Daddy banda daurewar kai zuciyarshi ce ta tafi tunanin lokutan da ta dinga mishi magiya akan ya janye maganar aurenta,

kalaman Abbakar ya shiga dawo mishi " *Kyari, yarinyar nan tana cikin matsala, anya kuwa mutanen gidannan su suka haifeta? "Ko a makaranta bata hutawa saboda hidimar yar uwarta, yadda kasan baiwa haka suka maida ta, ina tunanin yar riko ce, ka bita a hankali ka lallabata zaka fahimci daga inda matsalar take, walhi ta bani tausayi matuka saboda yadda naji tana kuka kamar ana yankan naman jikinta*
dana sani marar amfani ne yayi mishi dirar mikiya cikin zuciyarshi,

muryar Goggo ce ta katse tunaninshi,
cikin kuka ta fito da sarkar da ta zame mata mafitar karshe da zaisa ta fita a zargi ta damkawa Hafeez a hannu, tace "wannan sarkar Kakarku ce da mahaifiyarku ta gada,
nayi nayi suwaiba ta karba taki, yanzu gashi bata raye dole in sauke nauyin magada a kaina,

kallon sarkar Baffa yayi ya share hawayenshi yace "Samun mace mai rikon Amana irinki sai an tona Ma'u,
nagode da rike min Amana da kikayi,

Anty Reemah dai kallonsu kawai takeyi hawaye yaki tsaya mata,
tuno irin ukubar da mama Suwaiba tasha takeyi,
babu abinda bata sani ba na daga halayyar da kakarsu kewa mama suwaiba da ahalinta,
wannan shine dalilin da sanyata take matukar kauna da tausayinsu...

Labarin halin kirkin Suwaiba Goggo ta dinga fadi saboda dai ta wanke kanta a idon Daddy,
shi kuwa ya gama fahimtar komai tun da yaji cewar ba ita ta haifeta ba,
sai Gab da la'asar suka fara shirin tafiya,
Chapter 29 · 0% Book details