← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 113

Sashe 58

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallama sukayi ma Hafeez da kunya ta hanashi katabus saboda irin kallon da Husnah take mishi, 
dalilin da yasa ya sanya Ruwaida a tsakaninsu kenan da ya fito yi musu rakiya,
ko a da lokacin da yayi wauta da rudin kudi mata ke kawo kansu,

ita kuwa Husnah ganin irin gidan da ta fito ya sanyashi jin kunyarta da taka tsantsan,
dan yasan tafi karfinshi, shi da bashi da cikakken asali kamar yadda Goggo ke yawan fada,

wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa,
gara ya nemi saffa saffa dai dai shi....

Mrs Tijjani Shattimah......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Kasa tabuka komai Nadeeyah tayi ta dauki wayarta ta latsa number Hilal,
sai tayi kamar zata shiga sai tayi saurin kashewà,
tun daren jiya take abu daya,
tasan yadda ya saba da yi mata text haka nan bazai ki turowa ba sai da dalili,

Abin da bata sani ba shine, duk latsin da zatayi ma numbershi tana shiga kadan sai ta katse,
da haka ya fahimci ta damu da rashin tura mata sakon wanda yayi shi domin fahimtar wani abu daga gareta,

Yana gama shiryawa ya dauki wayar ya latso ta,

ajiye kwan da take kadawa tayi da sauri ta dauka ringing na farko,
"ajiyar Zuciya yayi a hankali,

ita din ma hakan tayi amma nata ya dan fito kadan,

shuru ne ya ratsa wayar na yan sakwanni,

shi ya fara katse shurun ta hanyar cewa

"ina kwana Anty,

saura kiris wayar ta fado a hannunta tayi saurin riketa tace "kayi Hakuri,
ina kwana,

"a'a ai ni ya kamata in fara gaisuwar,
kina nan lafiya?

bata amsa ba ta sake cewa

"ina kwana, yasu Anty?

dariya yayi mara sauti yace "kowa lafiya,

"harda k---

shuru tayi ta kasa karasawa,

"Harda ni Nadeeyah,
lafiyata kalau,

alhamdulillah ta fadi a zuciyarta,

a fili kuma tace
"to Masha Allah,

gyara tsayuwarshi yayi yace "jiya kuma bakiga sakona ba,
ke kuma baki damu ki turo ba,
shikenan da mutuwa nayi haka zaki manta dani bare har in sa ran addu'a,

cikin rawar Muryar da take nuni da alamun tayi matukar missing sakonnin shi tace
"Dan Allah kayi hakuri,
na rubuta sai na kasa turowa,

"ehen me kika rubuta?
fada min da baki,

toshe bakin tayi da hannu taki sakinshi dan bata san abun da zata ce mishi ba,
tana jiyo Muryar Hinad na cewa "Papa na kiranka,

muryarshi taji bayan fitar Hinad yace "ina jiran ganin sakon irin na jiya sakk,
zan gane rubutun na jiya da na yau,
sai na jiki ya karashe hade da kashe wayar ya sauka kasa gurin Papa....

*******

Karfe goma na dare Mummy ta shigo dakin su Nadeeyah bayan ta gama kashe kayan kallon parlon,
kallon Nadeeyah tayi wacce ke zaune da blue riga da wando na bacci,
tasan Nadeeyah ce kadai a gidan zata iya yi mata aikin tashin asuba,

"Nadeeyah,
dan Allah da asuba ki tashi Musaddiq,
ki hada mishi break fast dan jirgin 6 zai bi zuwa abuja,

Yaye bargo Badariyyah tayi da sauri tace
"zan tasheshi Mummy,

"a'a Badar kar kisa ya makara,
9 ake son ganinsu,

"Allah Mummy zan sa alarm ta fadi tana hararar Nadeeyah,

to shikenan Allah ya kaimu,
dan Allah kar ki bari ya makara,

"karki damu Mummy ta fadi hade da dauko wayarta ta sanya alarm karfe biyar da rabi dan tsabar kwancewar noti,
yaushe har ya tashi yayi wanka ya ci abinci,
al'amuran Musaddiq lokaci suke bukata,
mutumin da sai afi awa ana tashinshi a bacci,

Badar kuwa cike da murnar zata kasance da abin kaunarta ta ja bargo ta rufe kanta....

Karfe hudu saura Nadeeyah ta tashi,
kallon yadda Badariyya ke bacci ba tare da motsi ba tayi,
a zuciyarta tana tsoron tashinta kar ta jama kanta zagi,
"dakyar ta fara tashinta tana fada mata lokaci yayi,

inaaaa Badar bacci yaci karfinta ta juya ta cigaba da baccinta,

Hudu da yan mintuna Nadeeyah ta fita dan tasan in dai aka biyewa Badar tofa babu abin da zai hana Musaddiq kaiwa tara a gidannan,

Murda kofar dakinshi tayi taji karar alarm a gefenshi amma ko gezau baiyi ba,

karasawa tayi tana murmushi ta dauki wayar ta kara mishi karan a kunne,

"ummmmmm kawai ya fàdi hade da toshe kunnenshi da pillow,

ajiye wayar tayi a kan gadon ta yaye bargon jikinshi ta fara zare pillon,

kara kankame pillon yayi yana sambatun dadin bacci,
dan a wannan lokacin wani irin rarrashi shaidan yakeyi ma mutum mai sanya bacci dadi,

babu lokacin da yakai karshen dare dadin bacci,
dakyar ta iya fisge pillon wanda hakan yayi sanadiyar fadawanta jikinshi da karfi,

cikin bacci ya kankameta ba tare da yasan yayi ba,

kici kicin kwace kanta ta shiga yi wanda hakan yaki yuwuwa saboda girma da tsawon Musaddiq,
gaba daya jinta tayi kamar wata babyn roba a jikinshi saboda tsabar kankantar da ta mishi,

ganin ta kasa kwatar kanta ya sata sanya hannu a hancinshi ta toshe,
tasan dole ya bude ido saboda babu hanyar numfashi,

wani irin numfashi ya saki ta baki hade da bude idonshi ya sanya su cikin nata,

kara runtsesu yayi dan ya dauka duk cikin mafarkin da yakeyi ne,
yana kara rufesu ta kara rufe hancin,

bude idon yayi gaba daya kamar zaiyi kuka yace

"menene?

dariya tayi maganarshi ta mantar da ita a inda take tace
"ka tashi karfe shida har da rabi, ga Daddy can ya je dauko bulala,
*Haka Mummy ke ce mishi in yaki tashi ya tafi makaranta*,
Husnah ta bata labarin jiya kafin su kwanta,

"uhmmm ni zan kara minti biyar ya fadi yana sake runtse idonshi,

"Hello Daddy yaki tashi wai bazai je inter-----

da sauri ya mike har yana bige mata hannu,
dariya ta saki tace
" kayi sauri kayi wanka,
lokaci ya kusa,
bari inyi saurin hada maka break fast,
bayi ya fada yana lumshe ido kamar zaiyi kuka,
daurewa yayi ya shiga shower ya wanke jikinshi tass,

A bayin ya shafa mai bayan yayi alwala,
saida ya idar da Sallah ya shirya cikin kananan kaya masu kyau cool colour,
dakin ta kawo mishi kayan kari lokacin biyar da minti goma,

"Bana karyawa da wuri,
dan Allah ki maida, in naje can zanci abinci,

"noo gara kaci tun yanzu in kaje can babu time,
hada mishi tea tayi ta bashi bread guda biyu ta mika mishi plate din kwai,

ka canza wadannan kayan,
kai da zaka shiga cikin manyan mutane sai a ganka kamar area boy,

"dauko min wasu kawai ya fadi yana mai jin kuncin tashi daga daddadan baccin da yakeyi,

Drawershi ta bude tana dariya ta fito da golden brown shadda mai kyau da yauki,

yana gama karyawa ta fita tabarshi,
kayan jikinshi ya canza hade da feshe su da turare,

milk takalmi yasaka sannan ya ratayo jakar takardunshi da laptop dinshi ya fito parlon,

"ina hular fa?

ta tambaya tana karasowa inda yake da leda a hannunta,
shi yama manta da wata hula yace
"ta dauko mishi,
"gefen jakar hannunshi ta bude ta saka ledar hannunta,
taba gurin yayi yace
"meye wannan?

"zaka gode min in kaje can,
karka bude,
zama yayi akan kujera yana jiran ta kawo mishi hular,

Hular data dace da kayan ta dauko ta mika mishi,
kanshi ya miko mata a cewarshi bashi da karfin daga hannu,
gyara karin hular tayi ta sanya mishi ita akai,
yayi kyau matuka kamar wani babban mutum mai cike da haiba da kwarjini,
sakkowa Daddy yayi yana dariya yace

"Saaaadiq ne yau da tashin asuba,
baki ya turo gaba yace bakai kasa ta dameni ba,
dariya Nadeeyah tayi ta tsuguna tace
"ina kwana Daddy,

"lafiya kalau yar albarka,
kin samu ladan yayanki,
Allah ya biyaki,
murmushi tayi taja da baya ta barsu suna zantawa,
kudi masu yawa Daddy ya bashi sannan yayi mishi fatan alkhairi,

"har bakin mota Nadeeyah ta rakashi da addu'a sannan ta fada mishi in zai shiga ya karanta suratun Nasr kafa uku,

Har Malam Ali ya tada motar tayi saurin cewa ka kira Mummy da Daddy lokacin da zaka shiga gurin,
adduarsu mai karfi ce a gareka,

gyada kai yayi yana murmushi ya daga mata hannu,
itama hannun ta daga mishi tana fadin Allah ya bada sa'a,
saida motar ta fita a gate din sannan ta koma ciki ta gyaro mishi dakinshi da kyau,
lokacin biyar harda minti arbain,

Dakinsu ta shiga ta ji karar alarm din Badar,
tana hangenta tayi tsaki ta kashe wayar gaba daya,
samm baccin asara yasata ta mance abin da kudiri niyyar yi,

" bayi Nadeeyah ta shiga tayi wanka ta canza pad saboda tana hutun sallah,

komawa tayi ta kwanta tana sauraron karatun qu'rani har bacci yayi gaba da ita,

Badar bata tashi ba sai karfe tara da minti ashirin,
da sauri ta duro a gado tana fadin "na shiga uku,

kallon agogo tayi taga lokaci,
jiki na rawa ta fito parlor taga ba kowa,
dakin Musaddiq ta fada ta ganshi a gyare kamshi mai dadi hade da sanyi na tashi a ciki,
tsaki taja mai nuni da tsanar irin lalurar baccin dake dawainiya da ita.......

Karfe takwas na safiyar ranar Papy da iyalanshi sukayi shirin komawa Gombe,
gidan Baffa suka wuce dan suyi Sallama dashi,

A kofar gida suka tadda shi yana gaisawa da makota,
fara'arshi ce ta karu da ya hangosu,
Suna karasowa ya gabatar musu da danshi, jikokinshi, da amaryarshi,

Gaisawa sukayi da su,
Alh Jogana ya kalli Hafeez yace
"wannan ba sai an fada min ba,
dan marigayi Adamu buzu ne,
kamanin sun nuna kansu,
dariya Baffa yayi yace
"kwarai kuwa babban danshi ne,
Allah sarki...
Alh Jogana ya fadi cike da tausayi,
har yanzu dai ba'a samu labarin danginsa ba,
mutumin kirki,
ko yaushe na tambayeshi sai yace min daga Agadez yake,
amma sunan garin da yake a agadez ya bace mishi,
ba mamaki maraya ne,
Allah yayi musu rahama,

Ameen... dukka mutanen gurin suka ce sannan Baffa ya sallamesu ya shige gida,
Chapter 58 · 0% Book details