← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 113

Sashe 81

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka tambayi zuciyarka in ta yarda zan iya aikata abun da aka faďa maka fine, sai ka dau mataki a kaina,

Rage murya yayi yace

"Yaushe kika canja Nadeeyah,
are u ok?

"very okk, ban canja ba,
saidai in kai ne ka kasa ganin abun da wasu da yawa ke gani a gurina,

"Wallahi Allah na gaji,
kullum cikin sharri,
da nasan hakan ce zata kasance dani wallahi da bazan taba yarda da aur---------

Mari masu zafi har biyu ya sauke mata a fuska haďe da kaita jikin bango da karfin gaske,

"Aaaaaa......

ta faďi tana rike kanta dan ta bugu sosai,

Yanayinshi gaba ďaya ya sauya kamar zaki,
babu abinda da yake iya furtawa sai wasu numfarfashi da yake fitarwa,

komai zai iya sauraronshi daga gareta banda batun rabuwa sai kuma yanzu da ta nuna favours tayi mishi da ta aureshi,
bacin ran da yake ciki a yanzu yafi na kullum,
murya a kausashe kamar wanda ake ingizawa yace

"Wacece ke?

Wacece ke da kike ganin kamar kin taimakeni ne da kika aureni,
badan zuciya me rore rore ba ke kin isa ki zamo matata,

kalleni da kyau,
kinsan nafi karfinki ta ko ina, babu abinda ban kere miki ba a rayuwa,

Wallahi badan tausayinki da ya rikiďe ya zame min soyayya ba da babu abinda zanyi da marar asa----

Cikin kuka ta katseshi a hankali dan kalamanshi sun kashe mata jiki matuka,

"Akwai wadanda suke so na, wadanda basu damu da sanin asalina ba,
me yasa baka barsu sun aureni ba?
meyasa baka bar wanda zai rikeni ya yarda da asalina ya aureni ba?
sai yanzu da ka koyamin sonka zaka bullo da cin mutunci a gareni,
why Yaya Musaddiq?

Hawaye ne ya zubo a idonshi amma zuciyarshi sam bata karaya ba yace

"I will free u,
kije ki auri wanda kike ganin zai fini baki kwanciyar hankali,

Toshe mishi baki tayi da hannunta haďe da shigewa jikinshi tana kuka sosai..

"Dan Allah kayi hakuri,
don't separate urself from me, plss....

Su Mummy dake tsaye a bayanta tun jin kararta na farko suka dawo cikin gidan ta fashe da kukan munafurci,

Shigowa kitchen tayi ta kashe gas din da ruwan ya kusa kafewa tace

"Bana san rabuwarku,
bansan me yasa kika tsaneni ba Nadeeyah,
har kika kai ga zagi da cin mutuncina,
har kina nuna min cewa ke ba son ďana kikeyi ba a idona,
wace uwa ce zata juri wannan,
waye yake zuga ki?
Waye shi inje inji dalili,

Dama harzuka Musaddiq din tazo yi aiko ya harzuka,

nan ya fara zagin Nadeeyah,
zagi na cin mutunci wanda a iya saninshi bai taba yinshi ga wani ba,
da taga ya tabo inda bazata iya jurewa ba ta share hawayenta ta fara maida mishi,
nan kitchen din ya gauraye da tashin hankali,

su Raudha da Radiya suka shigo suka haďu akan Nadeeyah,

Ganin har lokacin Musaddiq yaki furta kalmar saki ya sanya Mummy rike hannun Nadeeyah tace
"A idona kike cin mutuncina da 'yayana,

"a idonki 'yayanki ke cin mutuncin iyayena,
kin hana su?,

Rashin kunya sosai ta zubawa Mummy wanda dama shiryayye ne sun san dashi,

kafin ta rufe baki Musaddiq ya daka mata tsawa haďe da furta kalmar saki cikin rashin sani da tsananin bacin rai,

Yana furtawa Anty Raudah ta jashi waje dan ma kar kukanta ya karya mishi zuciya,
cikin mota ta tura shi tace ma Faida taja shi su tafi......

Tafawa sukayi haďe da sakin tsalle,

"zo "zo "zo
Badariyya,
akwai sauran rina a kaba,
kalli ki gani...

Hoton Faida ta nuno mata suna zaune cikin mota tana rarrashinshi cikin kwarkwasa,

Kallon marakisiyya tayi cikin tashin hankali tace

"Ya zamuyi da wannan?,

"Ina zuwa Marakisiyya ta faďi haďe da mikewa,
da dan gudu tayi dakinta ta dauko wata allura da naďin laya,
duk abun nan da sukeyi a idon Yareemah Suhail,
jiransu yakeyi su gama ya tarwatsa aikin sannan ya kwace duk wani sihiri da Marakisiyya ta mallaka,

Shiryayyen shiri sukayi ma Faida wanda zaisa gaba ďaya taji Musaddiq ya fita a ranta kuma ta faďa mishi duk irin shirin da sukayi dan rabashi da Nadeeyah,

ma'anar hakan shine Badariyyah naso in ta koma ya zamana ita kaďai ce wacce zata dinga kula da shi,
dan tasan zai tsani Mummy da tayi mata zagon kasa da sauran yan uwanshi,
sun fi awa hudu suna aikin kafin su iya samun nasarar aikawa gurin Faida da har lokacin suke tare da Musaddiq,

Wani abu ne taji ya soketa wanda ya sanyata dauke hannunta daga kan kafaďunshi,
a lokacin shi kuma wasu zafafan hawaye suka shiga fitowa da cikin idonshi,
tausayinshi ne ya ratsata taji bata kyauta ba da ta raba shi da matarshi sabon aure,
tasan yadda yakeji saboda tana ganin yadda masoya sukeyi a film,
sannan ta tuna da rabuwarta da masoyinta Zubair wanda iyayenta suka hanata aurenshi saboda bashi da kudi,

"Kayi hakuri Musaddiq,

kwantar da kanshi yayi kan sit ya fara kuka mai sauti,

"kamar wacce aka tsikara ta fara faďa mishi abubuwan da suka shirya tun kafin aurenshi da Nadeeyah, har zuwa na yau bata rage mishi komai ba, har marin da Nadeeyar tayi mata sannan ta karashe da cewa is not late Musaddiq,
Kaje ka dawo da matarka, dan bazan boye maka ba, zaiyi wuya ka samu mace irinta mai kawaici da hakurin shanye abubuwa...

Tunda ta fara magana yake mata wani irin kallo na mamaki,
tana kaiwa aya ya dubi agogon hannunshi, biyar saura ya gani, bai tsaya bata lokaci ba saboda bashi da ishashshen lokaci yayi saurin cewa

"Muje gida plsss,

tada motar da sauri,

Revrse tayi ta ja motar da gudu kamar zata tashi sama,
burinta ta isa akan lokacin domin shirinsu na su koreta ne sai suce ita ta tafi da kanta bayan ta zazzagesu,

wayarshi ya dauka ya dinga kiran Nadeeyah yaji wayar a kashe,

dangwarar da wayar yayi haďe da dafe kanshi yana ta hango wautarshi,
magiyar da ta dinga mishi ya ke tunonowa.,
runtse idonshi yayi sosai hawaye na artabu a cikin kwayar idonshi,

"Me ya sameni,?
ya furta a hankali kamar me koyon magana,

Faidah da itama ta rasa abinda yake mata dadi cikin ranta tace
"Babu,
influence din mu,
plss forgive me,
am going outta ur life yau dinnan....

Suna isa kofar gidan ya buďe kofar tun kafin ta tsayar da motar,

wani irin turi yayi ma gate din ya bude dukkanshi,
gudu gudu yayi ya shiga ciki,

Tun a harabar gidan yake jiyo shewar su Anty Raudha,
bai bi takai ba dan shi burinshi daga ya shiga yayi tozali da Nadeeyah,

suna jin an turo kofar sukayi gumm suka koma gurin Mummy suna danna kafaďunta suna bata hakuri,

Taku uku yayi ya hau sama ya murďa kofar ďakin da karfi,
jin karan ruwa a bayi yasa shi sakin ajiyar zuciya haďe da maida numfashi,
matakin da ya shirya dauka akan yan uwanshi da mahaifiyarshi mai karfi ne,
dan kiriss ya rage su rabashi da abunda yake jin so a yanzu fiye da komai a rayuwarshi,
bayin ya nufa da sauri ya murďa haďe da sakin fuskarshi,
ganin bata cikin bayin yasashi fara dube dube yana kiran sunanta,
kayanta dake cikin dakin ya duba yaga wayam ba komai sai kamshinta dake manne a gurin,
da sauri ya koma daya dakin dan duba ko tana can tana kwashe sauran kayanta,
nan ma babu ita sai tsirarrun kayanta,
faďin irin tashin hankalin da Musaddiq ya shiga a wannan lokacin bata baki ne dan kuwa babu inda a jikinshi baya rawa yana dube duben inda zai ganta,

Kasa ya sauko da sauri yana kwala kiran sunanta,

matsowa kusa dashi Anty Radiya tayi tace

"Ka bar neman wacce ta mari mahai-----

Don't u dare...
ya faďi da karfi wanda ya tsorata dukkaninsu,
wani irin yanayi suka gani akan fuskarshi wanda basu taba sanin akwaishi tattare da kaninsu ba,

bai dauke idonshi a kanta ba yace

"Ina Nadeeyah?
ja da baya Radiya tayi dan ga dukkan alamu Musaddiq na iya dukanta domin yadda idanuwanshi suka canza launi jijiyoyi suka mimmike akanshi,

"Ta tafi Musaddiq,
nasan batayi nisa da gida ba,
zo muje mu nemota kafin lokaci ya kure...

kallon mamaki su Radiya suka bi Faida dashi,
basu iya furta komai ba har suka bar parlon..

Duk inda ya kamata su duba sun duba basu ga Nadeeyah,
gaba ďaya hawaye ma Musaddiq nemanshi yayi ya rasa saboda tashin hankali,
gidan Hajiya Zubaida nan suka je a karshe bata can,
duk tashoshin kusa saida suka duba basu ganta ba,
ko wayarshi dake ta ringing bai duba ba bare yasan wanda ke kiranshi...

Sake kiranshi Hilal yayi a karo na goma sha hudu har lokacin Musaddiq bai dauka ba,

Zubair ya kira a waya yace
"yazo ya daukeshi a airport bazai gane gidan ba,
ya kuma rokeshi da yayi sauri dan tun jiya hankalinshi yaki kwanciya,
Minti talatin ce ta kaishi airport din saboda gudun da yayi, gaisawa sukayi Hilal ya faďa motar suka nufi hanyar gidan Musaddiq....

Wani lungu Nadeeyah ta zauna a nesa da layinsu kusa da 3stars luxury Hotel taci kukanta ma'ishi, wanda har ya saukar mata da zazzabi,

wayarta da zata kira Papy ma sun kwace mata,
haka suka tasota a gaba ba ko sisi tare da sharadin kar ta nemi Daddy tunda ba ubanta bane shi,
akwatinta ta dauka lokacin gari yayi duhu ta fara tafiya tana neman abun hawan da zai taimaketa ya kaita tashar da zata samu a kaita Gombe....

"Kusan fifty seven million Momma,
but zasu cire 5m na workers sai 5m a each shareholders na gwamnati,
yanzu ina driving ne kuma is late gobe da safe zanje bank inyi transferring zuwa acc dina,
hope kina kula da kanki?,

gyara kwanciyarta tayi cike da jindadi tace

"sosai ma,
ga kuma wasu kudin sun shigo na sake kula da kaina da kai,
Allah dai ya jikan Abbanka,

"Ameen Momma,
na kusa karasawa masauki in shaa Allah,
su Aman ma sun shigo lagos gobe zamu taho tare,

"To Mashaa Allah,
sai kun zo Allah yayi maka albarka, take care,

"In shaa Allah bye..
Chapter 81 · 0% Book details