← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 113

Sashe 70

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saboda haka shawara ce zan baki,
in dai ba so kikeyi ki mutu ayi ba,
to ki kwantar da hankalinki ayi kina da rai,
bayan an daura sai ki shigeta kuyi mata illa har su rabu,
amma tabbas akwai aure a tsakaninsu,

Ajiyar zuciya mummy tayi hade da share kwallar takaicin da ta ziraro mata tace
"to Hajiya martai nagode kwarai,
in shaa Allahu naji shawararki, kuma zanyi amfani dasu...

shawarwari ta dinga bata marasa amfani na yadda zata kori Nadeeyah cikin kankanin lokaci,

sunfi minti talatin suna waya sannan sukayi sallama,
sai a lokacin Mummy taji wasai ta mike da karfinta ta shirya zuwa kasuwa......

Shirye shiryen biki sukeyi ta ko wani bangare,

Mummy da ahalinta sun danne bakin nufinsu sunata kankajere suna hidima da jikinsu da kudinsu,
kowa ya manta da lamarin Badariyya saboda Mummy tayi musu karyar ta tafi cotonou makaranta,
amma a zuciyarta kullum sai tayi tunanin inda Badar take da har wannan lokacin bata ziyarci gida ba,
in ta tuno kalaman Goggo sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da cigaba da zuba idon ganin dawowarta...

Anni itace ta dauki nauyin su cincin da dublan da sauran tarkacen garar amare,

ita kuwa Goggo ba baki dan mugun tsoron Anni yanzu Allah ya daura mata,
ta kan ce
"ina zata iya da wannan matsafiyar,
saboda duk asirin da ta dunkulo sai dai ya koma mata ko ya wargaje,

ita a ganinta tsafin Anni ne yafi nata,
bata san dogaro da Allah yafi tsafi karfi ba....

Tun ana saura kwana uku daurin aure Anty Reemah da Papy suka iso,
babu yadda basuyi da Hilal ya biyo su ba, yace sai daren daurin auren zai shigo,
hakanan suka kyaleshi sukayi gaba abinsu...

Duk yadda suka so suyi bidi'a Mummy ta hana a cewarta Daddy yace bayason komai sai daurin aure,
kawayenta ma babu wanda ta gayyata sai makota na kusa da ita,

Bikin ya kasance na yan family kawai sai kawayen su Anty Raliya da yan Gombe da yan maiduguri dangin Daddy...

Ranar jumm'a ake kamun amare,
a cikin gidan akayi decoration wanda ya kawatu da kore da kumbo,

Blue kayan kanuri suka sa dukkansu,
fuskar nan tasu ta dau kwalliya gwanin kyau da sha'awa,

kawayen Husna da yan tsirarrun na Nadeeyah sunyi ankonsu wanda ya dace da kayan amaren,
sai su Anty Reemah suma sunyi nasu lafaya mai kyau da tsadar gaske,
babu abin da ke tashi a gidan sai kidan piano da wani kwararren mawaki keyi,
kida ne taushi mai ratsa zuciya,

Ruwaidah da Zainab ne kadai a cikin tsakiyar filin suna rawarsu ta yaran da basu da wata matsala a rayuwarsu,
sai gefe yaran makota suma suna rayawa dan kar a barsu a baya,

Muryar inna Surayya (M.C Surry k mata) ce ta karade gidan da barkwancinta,
nan manya da yara suka hau dariyar labarin da take bayarwa,

Hinad...

Anty Reemah ta kwala kiranta da karfi..
da dan gudu ta karaso gurinta bayan ta amsa tace
"Mum gani,
wata leda ta mika mata tace "maza ki kaima Uncle links dinshi, nasan yana can bai gama shiryawa ba,

cire dankwalin kanta tayi ta karbi links din ta wuce dakin Musaddiq...

A zaune ta sameshi ya tasa kaya a gaba yana tsaki,
ya rasa taka mai mai kayan da zaisa cikin sabbin kayan da ya dinka,
gashi sai kiran wayar Nadeeyah yake taki dauka,
rabonshi da ya sata a ido tun ranar da ya koma lagos,
sai jiya da suka iso daga Gombe, shima daga nesa ya hango ta,
gaba daya ta toshe duk wata kafar da zata hada da shi,
a waya ma saidai in ya kira Hafeez sannan ne zata amsa,
shima bawani maganar kirki, zata kashe...

"Uncle baka shirya ba?

tsaki ya sake yi yace
"Hinad ban shirya ba,
zo ki zabar min kaya,
banason inyi shigar da zata banbanta da ta matata,

"Ummm ta fadi tana dariya hade da janyo wata danyar blue shadda taji aikin dark blue,
tace "wannan is okay uncle,
tun dazu uncle Hafeez ya shirya kai kana zaune,
plss hurry up,

kayan ya kwasa yace
"i hate Hilal,
shi ya kamata yayi min wannan ya wani ki zuwa,

"kunfi kusa ta fadi hade da ajiye links dinshi a kan kayan ta fita waje.....

Laaaaa Ya Hi----
toshe mata baki yayi hade da rungumeta yace
"nasan yayi fushi,
karkiyi magana yaji,
jeki kawai,

sakinshi tayi ta wuce tana dariya..

Makale lnks din yakeyi yana tsaki hade da mita,
shi kanshi in ka matseshi baisan me yake fadi ba,
yadai san rabin mitar akan Hilal da Nadeeyah ne da suka barshi all alone...

karin hular dake ajiye akan gado Hilal ya gyara hade da matsowa cikin sanda ya daura mishi a kanshi...
*Kyari is nw Complete*
ya fadi hade da saita fuskarsu ta kalli mudubin,

wani irin farin ciki Musaddiq yaji wanda a iya rayuwarshi bai taba jin irinshi ba a ganin Hilal sai yau,

Da sauri ya rungumeshi yana fadin
"idiotic being, sai yau kaga daman zuwa,
komai ni kadai nayi,
from lagos to kaduna haka na dinga wahala sai Zubair dake dan tayani,
i hate you banza kawai,
ya karashe yana dukan kirjin Hilal,

dariyar yake Hilal yayi yace
"da haka zaka zama jajirtacce mr Soft,
maza da wahala aka sansu,
kaga yanzu zaka shiga sahun cikakkun maza,
dole komai kayi ma kanka,

"amma akwai support ko? Musaddiq ya fadi yana hararar Hilal,

dukan kafadunshi Hilal yayi yace
"nd here i am,
kasan bazan taba barinka kayi komai kai kadai ba,

"na nawa kuma,,
muje kasa kayanka gasu can a drawer,
Musaddiq ya fadi yana jan hannun Hilal,

Hannunshi Hilal ya rike sosai ya tako har inda yake ya kalli cikin idonshi yace

"Musaddiq promise me one thing,
alkawari daya kawai zakayi min,

"nayi maka alkawari dan uwana,
fada min menene,
nan idon Hilal ya fara kokarin canza kala yayi saurin cewa

"kayi min alkawarin duk runtsi duk wuya bazaka rabu da Nadeeyah ba,
bazaka sata kuka ba,
kuma ba---

malam biyu ka fadi ga na uku na shirin biyowa baya,
Musaddiq ya katse shi yana dariya,
bari in sa maka su a one word,

"Nayi maka alkawarin bazan taba cutar da Nadeeyah ba,
bare har abubuwan da ka ambata su faru,

are u happy?

Ajiyar zuciya Hilal yayi yace "sosai,
muje insa kaya,

shaddar shima yasaka milk tasha cofee aiki sannan ya daura coffe hula mai ratsin milk,
sunyi kyau sosai kamar dukkansu ne zasu angwance,

wani bakin glass Hilal ya kwama a idonshi saboda gudun bacin rana......

Mrs Tijjani Shattimah.......
[12/04 7:01 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣7⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

Ganin ba kowa a parlon sai tsirarrun mutane ya sanya Musaddiq kama Hilal suka nufi dakin su Nadeeyah..

Zaune suke... kowacce an rufe mata kai da mayafi suna jiran azo a kirasu,
kawayensu na gefe suna daukar hotuna hade shewar murnan first kawance a rayuwarsu,

*Amal Mus'ab* na ganin sun shigo tayi saurin isa gurinsu tana murmushi,

kallon Musaddiq tayi ta miko mishi hannu tace "oya sako first step kafin muje second step,
cikin rashin fahimta yayi dariya yace
"ban gane ba,
hannu Hilal yasa a aljihu ya ciro bandir din yan 200nts ya daura a kan hannun Amal,

"Uhmmm nt bad ta fadi tana juya kudin,
lallai ka iya zuwa ghana,
guys bazamu sha wahala gurin abokan ango ba,
but next time mr man a kara hannu ta karashe cikin zolaya..

Dariya yayi yace
"next step?

Haifa ce ta matso tace
"a cikin su biyun nan ango ya dauki matarshi sai su fita kafin dayan angon ya karaso,
nan dakin ya gauraye da ihun yanmata masu zallar kuruciya wadanda suke kan ganiyar shaukin soyayya,

kallon duk su biyun Musaddiq yayi ya rasa kafar da zata sada shi da Nadeeyah,
domin ko ina nasu a rufe yake, hatta yatsun kafarsu a rufe yake da takalmi,
gefen da yake tsaye yabi dan ya gama sadakarwa itace a zaune a gurin saboda yadda gashi yayi tulluku a tsakiyar mayafin,

Hannunshi Hilal ya janyo yace "kar kayi abun kunya Mr soft,
ga matarka can ya nuna inda dayar take
dariya Musaddiq yayi yace
"har yaushe zaka iya tantance abun da bakayi ma kallo fin goma ko ashirin ba a zahiri,
look Hilal,
nasan komai game da Nadeeyah, everything saboda na ganta har ganin nata ya sanya ni na zamo cikin shaukin sonta,
ganeta a haka bazai taba min wuya ba saboda tana makale a cikin zuciyata...

dariya Hilal yayi a zuciyarshi yace
"cikin jinina,
a mafarkina,
in my every breath kamanin ta kawai nake gani,

Allah ya tsare akwai bakin glass a idonshi,
da idanuwanshi sun nuna ma ma'abocin kallonshi irin tarin son dake dawainiya dashi,

Karasawa kusa da ita yayi ya zauna hade da yi mata rada a kunne

"My Young Barr---
bai karashe ba tayi saurin bude fuskarta,
idanuwanta da suka tsaru da make up suka fara tara ruwa,
saurin girgiza mata kai yayi hade da sakar mata murmushin karfin hali,
wannan bakin glashin makafin ba karamin taimakonshi yayi ba dan da babu abinda zai hanasu ganin sirrin dake cikin kwayar idamuwanshi...

"Ashe kina da kyau har haka kanwata?, ya fadi a hankali yana kokarin gyara mata mayafin kanta,

"Nayi maka laifi ko?

Yadda tayi tambayar ba tare da ta dauke ido akanshi ba ya sa shi saurin mikewa dan gab yake da rasa control din raunanannar zuciyarshi,
da dariya Musaddiq ya karaso yace

"na gama jin kunya,
ace na kasa gane muradin raina, lallai ya kamata aci tarata..

Waje Hilal ya fita ko zai samu zuciyarshi ta dan mishi dama daman nauyin da tayi,

Bq ya nufa inda su Hafeez suka Hinad na biye dashi a baya tana tambayarshi kudin liki,

"kunnenta ya kama yace
"baki damu da ki bani abinci ko wani abu ba,
ke kawai kudin liki,
ina Zee?

"yaya sakar min kunne plss,
Mum ce tace tasan zaka ci abinci fa,
shiyasa ban samo maka ba,
kuma Zee nima tunda na dawo saloon ban ganta ba,

sakin kunnenta yayi ya ciro kudi a aljihunshi ya raba gida biyu ya bata,
"yasan zasu bukaci kudin shiyasa yasa Galadanci yayi mishi canji tun kafin ya iso,

Godiya tayi mishi tace bari ta kawo mishi ko nama ne,
Chapter 70 · 0% Book details