← Book details Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 113

Sashe 1

Zumuncin Mu A Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[04/12 09:41] Meela Adeel: 1⃣
° *ZUMUNCINMU A YAU* °
By Aysha Ya'u Kurah

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

'''BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM'''

Sadaukarwa ga mahaifi na kwarai *LATE ALHAJI YA'U KURAH* Allah SWT ya jikanka ya kai rahama kabarinka..

*SHIMFIDA*

"Assalamu alaikum" Ta faďi karo na uku cikin siririyar muryarta,
cikin ďaga murya taji ance,
"Wai wacece ta ke ta kwaďa mana sallama ne haka?!"
A hankali jikinta na rawa ta amsa.
" Ni ce."
"Tooo!! Sannu NI CE, me ya kawoki?"
Cikin rawar murya ta ce "Mamma ce ta aikoni in kawo muku abinci."

Daga cikin ďakin ta jiyo muryar dattijon wanda ya bata tabbacin shima yana ciki. "Toh ki ce an gode, je ki ďauki naira ashirin a saman tagar ďakina kiyi gaba."
A hankali ta sauke ďankwalin da aka ďaure kayan a ciki ta kwance ta fito da sababbin samirun tuwo da miya ta cire ďankwalinta tace "Nagode BAFFA, Allah ya saka da alkhairi." Ta ďauki ashirin ďin ta fita cikin k'unan rai.

A hanyar da zata sada ta da kofar gida taci karo da su Husna rik'e da manyan kuloli suna tafe suna nishi da kyar, rab'ewa tayi ta basu guri dan su wuce, suna karasowa dab da ita suka kwashe da dariya haďe da faďin "Nadiya roba-roba."
Badariyya ta ajiye kular hannunta ta shafi kayan jikin Nadiya tace
"Kaiii!! Wannan ba roba bace rai fess ce."
Suka sake tintsirawa cikin shakiyanci suka ce "Su Nadiya bana an samu canji, daga atamfar roba zuwa shaddar roba."

Cikin sanyin jiki tayi gaba tana jiyo ihunsu har suka shige cikin gidan.

Tana fita tayi tafiyar minti biyar sannan ta isa titin da zata roki masu mota su ďauketa da naira ashirin ďin da aka bata, dan in tace zata tafi gida a kafa sai ta kai yamma saboda nisa,
zuciyarta cike take da mamakin yadda zumuncin zamani ya koma,
tun tana karama ta ga mahaifiyarta na fuskantar irin waďannan wulakancin saboda kasantuwarsu talakawa, sau tari takan tambayi mahaifiyarta anya Baffa ne ya haifeta kuwa?

Acikin gidan kuwa, su Husna na shiga babu ko sallama suka faďa ďakin,
zabura Baffa yayi ya sakko daga kan gado yana faďin. "Lale da matana, lale-lale."
Badariyya ta faďa jikinshi tana faďin "Kakus, ina barka da Sallah na?"
Cikin rawar jiki yasa hannu a aljihu ya ciro yan ďari biyar-biyar sababbi ya k'irga goma ya bata,
yatsina fuska ta yi tace "Haba kakus, dubu biyar fa ka bani, ni gaskiya sunyi min kaďan Pizza kaďai zanci da su." Washe baki ya yi yace "To yar lele, an gama." Ya karo mata wasu biyar ďin ta mike a jikinshi babu ko godiya sai ma faďin "Ko kaifa, ai da na sake ka yanzun nan,,,
Husna ta matsa kusa dashi tace " Saura ni kakus."
Dubu goman itama ya bata saboda yasan sakon barka da sallan shi na tafe don tun safe y'arshi mafi soyuwa a gareshi ta kirashi tace zata aiko MUSADDIQ da sak'o, yasan sakon bai wuce na kuďi.
"Ina yayanku? Ko ba tare kuka zo ba?" Baffa ya tambaya yana gyara aljihu.
Badariyya tace "Ka ji kakus a kofar gidannan fa muka sameshi, yana fita muna shigowa dan ya riga Nadiya fita ma." Kallon mamaki yayi musu yace "Aiko bai shigo ba."
Goggo ta rufe kular da ta bude ta ce "Kasani ko ya manta da wani abu ne?"
"Hakane kuma." Ya faďi tare da basar da maganar.
Nan suka hau hira da ciye ciye, sun ma manta da samirun tuwon da Nadiya ta kawo saboda sunsan babu wani abun arziki a ciki.

Zaune take tayi tagumi tana jiran shigowar Nadiya dan tasan in Allah Ya yarda zata samu ko ďari biyar ce a gurin su Baffa na barka da sallah,
Zainab ce ta taso rike da robar abinci tace "Mamma zan kara abinci." Janyota ta yi jikinta tace "Yi hakuri auta, yanzu Anti zata dawo har madara ma sai kisha in kinaso kinji?"
Gyaďa kanta tayi cikin murna ta kurawa kofar gidan ido tana jiran b'ullowar yayarta.

A gajiye ta shigo gidan ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi,
da sauri Zainab ta mike ta ďauko mata ruwa, karb'ar ruwan tayi haďe da janyota jikinta tace " Kin ci abinci?"
D'aga mata kai tayi, "Eh naci amma ban koshi ba. Mamma ta ce zaki kawo kuďi a siyo min madara."
A hankali ta ďago jajayen idanuwanta ta sauke kan mahaifiyarta, kallon tausawa juna sukayi sannan suka kau da kawunansu, cikin sark'ak'ak'k'iyar murya Nadiya tace "Mamma na kai musu, Baffa ya bani naira ashirin, ki tayani yi mishi godiya dan ya taimakamin, da a kafa zan dawo gida."
Cikin b'oye b'acin rai Mamma tace "Kai madallah!! Allah ya biyashi da aljanna, gaskiya naji daďi, tashi maza kije kiyi sallah."
Tana kokarin mikewa taji anyi sallama, juyowa tayi haďe da amsa sallamar, suna haďa ido tayi saurin kau da kanta,
Mamma ta mike cike da murna tace "Maraba da Musaddiq, yanzu kake tafe?"
"Eh Mamma ina wuni."
"Haba dai daga tsaye?" Ta faďi haďe da shimfiďa dadduma.
Zama yayi yana sosa k'eya suka gaisa sosai,
kuďi ya zaro a aljihunshi kusan dubu dari biyu yace;

"gashi inji mummy tace a kawo muku" bai jira jin me zata ce ba ya ajiye kuďin ya fice daga gidan da sauri dan yasan in ya daďe a gidan to asirinshi zai tonu..

Kasa tab'a kuďin tayi saboda firgici Kai anya Musaddiq yaji inda aka aikeshi da kyau kuwa?
Wannan kyautar tayi yawa dan tsakanin ta da yar uwarta bai wuce kyautar dubu biyar,

"Nadiya mik'o min wayar can" tace tana mai nuna ma nadiya wayar,
da sauri ta ďauko ta mik'a mata. Hannu na rawa ta fara neman lambar yar uwarta, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ďaga cikin isa da tak'ama,
murya na rawa Mamma tace "ina yini Hajiya"

"lafiya" kadai tace murya can k'asa, bata damu da amsawar ba dan in da sabo ta Saba, sai ta cigaba "yanzu Musaddiq Ya kawo min sak'o shine nace bar..."

Dakatar da ita tayi ta hanyar cewa "ina da abin yi Suwaiba nasan godiya kika kira kiyi, bakomai yiwa kai ne" tayi saurin kashe wayar, cikin mamaki ta ajiye wayar tana duban kuďin zuciyarta cike da farin cikin yar uwarta ta fara sanin muhimmancin zumunci....

Musaddiq na fita ya nufi motarshi ya kashe wayoyinshi ya ta da motar yayi gaba yana nazarin yadda zaiyi ya fahimtar da mahaifiyarshi da kakanninshi muhimmancin zumunci,

A kullum yana mamakin yadda zumuncin zamanin yanzu ya zama sai in kana da kuďi,
yana takaici matuka saboda irin wulak'ancin da Mamma suwaiba da ya'yanta ke fuskanta saboda kawai basu dashi, bashi da wani burin da ya wuce yaga kan zuri'arsu ya haďu, Mai shi ya taimaki mara shi, amma kullum abun k'ara lalacewa yakeyi saboda masu shi ďin basa taimakawa na jikinsu saidai na neman suna..

Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:42] Meela Adeel: 2⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
BY Aysha Ya'u Kurah               

"Nadiya amshi maza kira min yayanku,
cike da murna ta karbi wayar ta latso number,

Yana zaune ya kifa kanshi a wheel barrow yana tunanin ta inda zai fara,
'Dan kudin dakon da ya samu na Sallah shi ya had'a yayi ma kannenshi kayan sallah, ragowar ya ba mahaifiyarshi tayi abincin sallah,
karar da wayarshi keyi ne ya dawo dashi cikin duniyar tunanin da ya tafi,
hannu ya zira cikin aljihunshi ba tare da ya d'ago ba ya danna ya Kara a kunnenshi,
Assalamu alai-- "hello Ya Hafiz ta katse shi cikin kaguwa,
dago kanshi yayi  cikin firgici yace "Nadiya Lafiya,?
fizge wayar mamma tayi tace "Hafizu kana Ina ne, duk abunda kakeyi ka barshi ka dawo gida, mikewa yayi da sauri ya Sanya silifas dinshi, ya kalli abokin aikinshi yace "Haladu dan Allah ka Mik'a min baron nan gidan oga lukman in har ban dawo da wuri ba,  Haladu yace "lafiya dai ko, "walhy ban sani ba mamma ke kira na, ya karasa fadi yana tafiya da sauri ,
"Allah yasa lafiya haladu ya fadi da karfi dan Hafiz ya kusa karya kwana,
zuciyarshi cike take da fargabar abinda zai je ya tarar a gida...

Hello Baffah, an yini lafiya,
baki har kunne baffah "yace lafiya lau ya sallar,
"sallah alhamdulillah,
"Dan Allah Baffa kace ma su Husnah su biyo MUSADDIQ na aiki Haruna driver,
to bakomai daga ya karaso zansa su taho saboda dare,
"kana nufin har yanzu bai zo ba baffah,
baffah yace "eh to sunce min sun ganshi d'azu amma ni har yanzu bansa shi a idona ba,
ikon Allah ta fadi hade da gyara zama,
ya rigasu fita gida fa, kuma saida na mishi kashedi akan yawo, Yanzu haka yana can gurin abokan banza, amma dai ya basu sak'onka ko? ,

"ko kusa bai basu ba, baffah ya fadi had'e da yak'e wanda yafi kuka ciwo dan ya kosa yaji makwafin kudin da ya ba jikokinshi da Karin wasu a aljihunshi,
"karka damu baffah bari in kirashi inji inda ya tsaya,
"too bakomai Kar dai ki matsa mishi kin San yaran yanzu saida lallami,
haka ne baffah nagode a gaida Goggo,"to zata ji Nima na gode,....

Kiran Musaddiq ta shiga yi, abin ya d'aure mata kai da taji wayoyin shi a kashe, lallai yau zan bala'in sab'a ma Yaron nan, duk fadan da na mishi akan shirman partyn nan baiji ba ko, Allah ya kawo shi gida wallhy Mai rabani dashi sai Allah ta wurga wayar cikin jaka ta d'auki gyale da mukullin mota ta fita...

"ji nake kamar a mafarki mamma, shafar kudin ya sake yi yace
"ban taba tunanin zan rike irin wadannan kudin ba a rayuwata,
Mamma da farin ciki ya mantar da ita damuwa da yunwa tace
"kaidai bari, Allah kenan maji rokon bawa, duk yadda mutum ya kasance cikin kunci da bakin ciki to in ya dogara da Allah sai ya samar mishi mafita,,
Hafiz yace "haka ne mamma, to yanzu ya zamuyi da kudinnan,
"shi nake tunani hafizu,
mu jira babanku ya dawo sai musan abin yi dashi,
  dubu biyu ta ciro cikin kudin tace je kayo mana cefane da wannan muyi abinci kafin ya dawo,
Chapter 1 · 0% Book details