← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 102

Sashe 98

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gabaki aya. A.m da ya ji kiran salla zubbur ya mi e ya kalle ta wadda tsoro ya sa ta baccin dole. Ji ya yi kamar ya sha eta da sauri ya haye sama ko tashin ta bai yi ba,saboda takaicin gani girkin da ya yi mata ko guda uku ba ta ci ba. Ya tura akin ya shiga har yanzu bacci take yi saboda bayan kukan da ta sha bacci ya auke ta ba don ta so ba. " Zainab ki tashi kiyi sallah." Sai ta yi tsuru tana kallon sa yayin da hawaye yake bin gefen fuskarta. " Na rasa ta yadda zan fito na yi miki bayani ki yarda da ni Zainab."Ya fa a muryar kaukausa domin shi yana ganin bai kamata ta aga hankali a kan yarinyar da baya jin sonta a cikin ransa ba. " Na gaya miki ba so a cikin auren nan na yi shi ne don kawai mu samu a,kuma na yi miki al awarin da zarar ta haihu zan cika miki al awarin da na aukar ma ki ba ta saki uku." " Zuciya ce take ar amma tun da haka ka ce shikenan ka yi ma Abba magana ta koma gidanku."Ta ce mishi lokacin da ta yi hanyar bayi. " Wannan ba zai yiwu ba domin Abba ya ce dole sai na zauna da ita,amma ni ba zan iya zama da wata mace ba bayan ke,ki yi ha uri har ta haihu sai mu bar garin bayan na saketa mu koma London sai mun auki tsawon shekaru kowa ya manta mu dawo." Rungume shi ta yi tare da manna mi shi kis ta ce."Na yadda da kai mijina na san duk wannan matsalar ni na kawo shi,domin da ban biye wa son zuciya ta ba,da son gayu da yali na haihu ko da aya ne, da baka janyo Juwairiya cikin rayuwarmu ba,na yi takaici sosai ban san cewa kana son yara haka ba,sannan ba za ka iya rayuwa dole sai ka so ka ga anka." Sai kuma ta sake shi ta sa kuka ta ci gaba da cewa." Kaicona da na bi ru in duniya na i bari na haihu ko sau aya ne,ina ma matan da suke shan maganin hana haihuwa don wani buri na su,ko mazan suka umurce su za su daina duba ga irin yadda na tsinci kaina cikin nadama.Don Allah A.m karka karya al awarin da ka yi mini,saboda kishin ka zan ije aikina har Juwairiya ta haihu na osa ta fita daga cikin rayuwarmu ba zan iya barin ka kai da ita ba,wallahi jiya da na gan ta hauka ne kawai ban yi ba,saboda duk kyan da na ke da shi na tsorata da ganinta.Ashe haka mata suke canzawa in suna da ciki." e ta gam ya yi har cikin ran sa yana jin tausayinta don in ya kalli cikin Juwairiya ji yake yi kamar zai sume,to ina ga ranar da ya fito duniya ya ga an mutum ace na shi. " Na yi miki wannan al awarin ba ki da matsala." Duk wani abun da A.m zai yi ya kwantar da hankalin Zainab yana yi,abu aya ne ya ji sam ba zai iya ba yadda ta hana shi ko da kallon Juwairiya,domin ko motsi ya yi idanunta na kan sa. Gabaki aya ta ije duk wani yawonta da take nadamar yin sa da ta yi,tana zaman gida sai ta yi kwanaki ba ta fito ba. Duk sadda ta ga cikin Juwairiya da ya ara girma, sai ta shiga aki ta yi kuka ta yi kuka har ta ji babu da i,watarana sai ta yi ta buga kanta a bango tana nadamar ri on sakainar kashin da ta yi masa. Ba ta ara shiga tashin hankali ba sai da Juwairiya ta fara kubburi duk da alokacin cikinta wata shidda da sati biyu,hankalinsa ya yi dubu ya tashi kamar zai yi hauka,wanda Zainab ta ka sa gane akan baby yake yi ko uwar baby. Da suka je asibiti likita ya ara tura su scanning sannan jini za a ara mata,saboda jininta ya yi asa,take A.m ya ce a iba na shi a saka mata. Zainab ta tada hankalinta matu a tsiya sosai suka yi akan ya siya jini a saka. Sai dai ba ta yi nasara a kan sa ba, don kwana biyu ya yi ana iban jinin sa wanda aka sakawa Juwairiya,da yanzu ta fara raina kanta ganin yadda take komawa har kammanninta sun fara canzawa,ga afafuwanta da suke kubbura. Bayan an saka mata jini suka dawo gida Allah ya auki wani irin tausayin Juwairiya ya saka a zuciyar A.m,wanda ko juya idanunta ta yi sai ya ji wani madarar tausayinta a cikin ransa. In yana gida sam ba ya iya zama a ko ina sai falon asa,daga baya arya ya yi wa Zainab cewa Momi ta ba shi umurnin ta koma sama,in ya so a ba ta aki aya ta zauna madadin zaman ta a asa. Zainab hankalinta ya ara tashi saboda tun da ta dawo ta ga duk sun canza mata suna wani nan-nan da ita. Kullum suna sintiri gurin kawo mata abinci na ayi,haka Momi da Abba kullum sai sun kirata sun ji lafiyarta. Ta raina kanta matu ar gaske kullum cikin nadamar abin da ta aikata take.Ga tarin dukiyar da take buri ta samu ta samu don yanzu asar ingila take son ta ha a hannu da asibinta,ku i kam ba ta da matsalar su amma babu kwanciyar hankali,saboda ta lura yanzu sam hankalin A.m ba shi a jikinsa,da ta yi masa magana ya ce zuwan baby ne. A.m da Zainab suka shirya zuwa waje suka yo siyaryar kayan baby,wanda ita kanta Zainab ba ta san iya yawan ku in da ta kashe ba. A.m sai ha a tarin dukiya yake yi ma Juwairiya har da wasu share in sa na waje yake son ya bar mata,saboda kar in suka rabuya rage mata jin zafin rabuwa da baby. Ita kanta Zainab ta yi masa al awarin za ta ba ta dukiya masu yawa, ita dai burin ta ta bar mata A.m da babyn da yanzu take jin ta fara son sa a cikin ranta,don son da za ta nuna masa shi kawai zai wato mata martabarta a gurinsa. Bayan Juwairiya ta dawo sama wata aryar ya shirga ma Zainab akan dole yanzu ya rin a kwana da ita saboda cikinta da ya shiga wata na bakwai. Da fari in amincewa ta yi amma daga baya sai ta yarda akan za su dun ga kwana dukansu tare. Sai dai A.m ya i mata ya an nuna mata hakan ba zai yiwu ba ta amince,don ta san yanzu in dai ba rashin tausayi ba bazai kalle ta ya bu aci wani abu daga gareta ba,duba ga yadda ta koma. Juwairiya na ana ku arta duk wani wahala da take ba ma mutanen gidan,da tsiwa kan dole ta watsar domin yanzu ta kanta take yi,kusan kullum cikin wahala take domin cikin na matu ar ba ta wahala sosai,kamar za ta mutu ko nishi ta yi sai ta ji wani azaba,ita kam ta sheda mutuwa za ta yi,shi ya sa kullum take kuka sosai akan ya kai ta gurin Mama,saboda ta san mutuwa za ta yi. Ranar wata daren Alhamis A.m hankalin sa ya tashi matu a ganin yadda take sauke numfashi sama-sama. A lokacin cikin wata takwas ya shiga amma duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata,saboda ta yi wata irin atuwa a yadda kamanninta suka canza ina tunanin ko Mama ta ganta sai ta yi da gaske za ta gane ta. A.m hankalin sa ya tashi warai tun da ya fara kwana da ita ya shiga tashin hankali,ganin irin wahalar da take ji sam ba ta samun bacci. Hannunsa ya sa da nufin ya kamata cikin tausaya,amma sai ta ture shi ta ri e kwankwasonta tare da rintse idanunta,tana jin wani irin azabar ra in mutuwa yana shigar ta. " Wayyo Allah na!Mama ki yafe mini dama haka kika ji kika haife ni! Wayyo Mama ba laifina ba ne halin da kike ciki ya sa na amince da abin da mugu azzalimi ya zo mini da ita.Baba Sani Allah sai ya saka wa mahaifina sam baka ri e maraicin da mahaifinmu ya baka amana ba." Sai ta cige baki ta mi e da nufin ta tashi,amma ta kasa da sauri ta koma ta zauna, tare da jingina kanta a kan gadon don ji take kamar an dake cikinta zai fito ta bakinta. A.m da yake jin wani tashin hankali kusan haka suke kwana duk da sun je asibiti,amma sai a ce musu lokaci bai yi ba,sannan (E.D.D) inta bai yi ba balle ayi mata aiki,don haka su jira lokaci. Duk iya juriyar sa in ya ganta cikin wannan tashin hankalin sai ya ji hawaye da nadama na shigar sa. Bai san cewa ya sha u da ita ba musamamman lokacin da ta fara masa tsiwa, tana nuna ba ta son sa da tsoron sa. Hunnunsa ta kama ta ri e ta kalle shi da fararan idanunta wanda yanzu suka koma suka rine saboda ruwan azabar da take kwankwa " Bazan yafe maka ba kai da Baba Sani, kai harma da A.k duk da na san ka tilasta shi ne,amma wata ila da ya jajirce bai amsa ba da ba ku zo gurina tun da kana jin maganar sa b...." " Juwairiya ki yi shiru za ki haihu lafiya ki koma gurin Mama in sha Allahu Mama za ta ara tozal..." Katse shi da arfi ta yi." Ka yi shiru don Allah mutuwa zan yi! Jikina ya ba ni bazan ara ganin Mama ba a rayuwata,ka raba ni da Mama don kawai burinka na ka samu a.Ka tuna ni ma a ce wacce uwa ta haifa take sonta, kamar yadda kake son an da za ka haifa,saboda burinka na haihu ka ba wa matarka ka nisanta ni da Mama A.m ba ka yi mini adalci ba,na tsane ka bana sonka.Dubi irin wahalar da nake sha amma fatan ka na haihu ka rabani da ana,saboda ka faranta ma matarka.Wai shin ita ce mace ka ai a duni..." Wani irin hajijiya da take yi ya hana ta arashe maganar sai da ta auki tsawon lokaci
Chapter 98 · 0% Book details