Sashe 61
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 24* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM A tare zuciyarta take bugawa da ringing in da wayar take yi.Ta kira sau biyu bai auka ba sai jikinta ya yi sanyi ta ije wayar,ta kalli Hauwa da ta kafe ta da ido. " Na kira shi amma bai auki ba ina tunanin wayar ba ta kusa da shi."Ta fa a cikin karayar zuci. Zama sukai suna jiran kiran wayar ko wannen su zuciyarsa na buguwa tamkar za ta fito. Sun jima a gurin suna jiran kiran sa har suka gaji.Ita ta fara mi ewa ta kalle ta ta ce." Mai zai hana ki fara nuna masa so misali ki din ga nuna mishi kin yi kewar shi ,da kalamai masu zafi kuma ki din ga tura masa,ai shi ba yaro ba ne dole ya fahimta wata ila ya san za ki kamu da son sa shi ya sa ya ce kar maganar so ya shiga tsakanin ku." "Ki na ganin haka shine mafita na riga na aukar wa kaina in har bai ce ya na sona ba ba zan ta a yadda na bar ciki ya fito a jikina ba."Ta gaya mata cikin sassanyar murya. " Allah kawai ya san me ya oye a gaba amma ki dage da addu'a kuma ki din ga nuna masa irin yadda kike son sa a aikace ke fa matar sa ce,kuma tun da ya har ya iya ha a jiki da ke ban ga abin da zai hana ya soki ba,amma ni fa nafi son ki bari ki sami ciki naga irin haukar da zan yi. Maganar ya gundireta fara tafiya ta yi ba tare da ta ce mata komai ba, a ranta sam ba za ta amince da shawarar ta ba, ta yi al awari ba za ta dai na zubar da ciki matu ar ba zai zauna da ita na har abada ba. Kamar yadda suka shirya sai ta fara an sakin layi ta na yi masa wasu irin abubuwa sa anin hankalinsa saboda har mamakin ta yake wai dama haka take! Duk wani abin da take mishi ya biye mata har ma ya na mata fiye da haka. Ranar da suka shirya za ta gaya mishi amma a waya don ba za ta iya taran idanun shi ta furta mishi ba. Da fari text ta ce za ta rubuta mishi sai Hauwa ta ba ta shawarar ta kira shi. Cikin sa'a ringin aya ya auka ta na sanar mishi da ta na son ta yi magana da shi kuma maganar is verry important sannan kuma comfidential. "Ok ba ki da damuwa tun da kina cikin makaranta ki bani an lokaci,ina gidan A.k na je gaida matarsa ni da Zainab bari na shigo cikin makarantar,ba sai kin gaya min a waya ba." Duk yadda ta so ta hana shi zuwa don tafi son su yi a waya amma ya kafe ga shi nan zuwa,daga bisani kashe wayar ya yi ganin za ta yi masa gaddama. "Ya ce ga shi nan zuwa ya i yadda na gaya masa a waya." Ta fa a yayin da zuciyarta take bugawa."Gaskiya ya na girmama lamarinki bari na oye yau ina son na ga A.m, a zahirin gaskiya da ya sace zuciyar rabin raina ya hana ma awata sukuni." Dariya ta yi ta kauda kanta ba ta ce komai ba saboda irjinta yake bugawa. A lokacin da motarsa ta shigo sai Hauwa ta mi e da sauri ta la e,ta yadda za ta din ga kallon duk abin da ke faruwa ba tare da ya ganta ba. Har kusan in da take ya araso da motar sa sannan ya yi parking ya fito ya taho in da take. Kallonta ya yi lokacin da ya zauna akan aya daga cikin kujerun, da suke a gurin tare da sakin wani wawan ajiyar zuciya. "Kin tsorata ni fa wallahi na auka ko babu lafiya,amma tun da na gan ki lafiya lau fa a min matsalar ki." Ya fa a ya na kallonta tare da ri e mata hannu suna kallon juna ido cikin ido. Sun auki tsawon lokaci suna kallon junan su ba tare da sun ifta ba. Da sauri A.m ya mi e tare da juya mata baya domin ko ba ta fa i abin da take son fa i ba,idanunta sun bayyana tsa on su dama ba tun yau ba yake ganin ta na sakin layi,wanda yake biye mata don ya faranta mata. In ko ta na son ta fa a masa son shi take, kamar yadda ya gani a wayar idanunta, ya kamata ya yi maza ya dakatar da ita, don ba zai ta a son wata mace ba bayan Zainab in sa. Juyo wa ya yi ya kalleta ta da take ta in da inda ta in da za ta fara."Juwairaah kar ki ce ki na sona don ni ba na sonki." A zabure ta tsaya gaban sa ta fara hawaye kamar an bu e famfo. A hankali ta nuna kanta da yatsa ta ce."Ba ka sona A.m da gaske ba ka sona kake yi min abubuwa irin na wacce ake so?" ara masowa ya yi kusa da ita."Yes ni fa ban ta a jin ina son ki ba,kawai ina girmama lamarin ki kamar yadda na sha gaya miki.Saunawa kike son na gaya miki ba na sonki ko kafin na aure ki na fa a miki,Zainab ita ce macen da nake so kuma na aure ki da sanin ki akan ki haifa min yaro na bata.Wai mai ya sa kike dawo da hannun agogo baya ne?" Ya fa a cikin aga murya duk da babu mutane sosai a gurin sai aya biyu,amma har an fara taruwa ganin ya na magana da arfi. "Ina sonka ba zan fasa sonka ba!Na fara sonka tun kafin ka bijiro mini da aurenka, kuma na san kai ma ka na sona sau nawa kasha fa a mini ka na son surar jikina da halina,mai ya sa ba za ka so zuciyata ba?" Ta fa a cikin muryar da tafi nasa amo don ji take kamar za ta yi hauka. "Ni fa ban ta a ce wa ina sonki ba sai surar jikinki,kuma ta ya ya zan yi na saka son macen da na san ban ba mu dace ba.Ki tuna mahaifinki har ya mutu bai bar muku komai ba,sanin kan ki ne mahaifina ya yi fice a duniya." A.m ya fa a ran sa na suya ganin ta na son ta tara mutane, wannan kamar cin mutunci ne mai ya sa ba ta gaya masa a gida ba. Cikin jin zafin ta ya fara tafiya zuwa motar shi, da gudu ta bishi ta dur usa a gaban sa ta na hawaye."Tabbas haka ne ka fa i gaskiya mahaifina bai bar mana komai ba sai talauci,amma ka sani ba ku i ba ne kawai Allah yake sawa a so mutum shi ya sa har yanzu na kasa gasganta son Zainab kake yi. Saboda ka na sonta ne don kawai ita ajin ka ce na san watarana za ka fahinci gaskiya, za ka gane a kwai baiwar da Allah ya kan yi ma bayin sa aso su ba wai sai dukiya ba. Ni na san watarana za ka soni kuma sai ka yi nadamar abin da ka gaya mini ko ina raye ko ba ni raye." Ta numfasa ta na jan numfashi ganin ya yi shiru ya na kallonta sai ta ora da ce wa."Ina sonka ba zan fasa sonka ba sai ranar da numfashina ya yi bankwana da gangar jikina." Tafiya ya fara yi bai ce mata komai ba.Kamar wata zararriiya ta mi e ta juya ta na kallon shi ta kira sunan shi. "Ina sonka! Ina sonka!! Ina sonka!!!" Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya na jin kukan ta na yi mishi zafi sai ya ara sauri ya shige motar sa ya fice daga harabar makarantar a guje. ushewa ta yi a gurin tare da saka razanannen kuka. Da sauri Hauwa ta fito ganin motar sa ta ace tare da kama ta ta na son ta mi ar da ita. awa jikinta cikin muryar kuka da sheshshe " Ki taimake ni A.m ba ya sona ya tsane ni na tabbata son shi zai kashe ni domin na fi bu atar na mutu fiye da ina kallon ya na fifita wata a kaina.Wayyo Allah na!Ina ma a ce mutuwa na yi ban ha u da shi a cikin rayuwata ba." Hauwa ta ru e ganin kukan da take ba na wasa ba duk da guy in ya cancanki a so shi,amma ita a ganin ta bai kamata ta so shi haka ba ganin za ta cutar da rayuwarta a banza. yar ta ja ta suka bar gurin domin su kaucewa mutanen da suka fara taruwa. Ruwa ta mi a mata wanda ta kar a tare da alle murfin,ba ta ije gorar ba sai da ta shanye duka. "Ki yi ha uri ban baki shawarar ki fa a masa ba don ya wula anta ki,da ace na san abin da zai faru kenan da ban ce ki gaya masa ba.Kici gaba da addu'a babu abin da ya gagari Allah.Amma da kin bari ki samu ciki wata ila ta nan kawai za mu ci galaba a kan sa." "In har A.m bai amince da soyayyata ba ni kuma ba zan yadda na samu ciki da shi ba, na gwammace na yi ta rayuwa da shi a haka da na haihu da shi ya gujeni." Abin da ta fa i kenan cikin murya kaukausa ta auki jakarta ta tafi. Tun daga ranar A.m ya auke mata fuska wanda sai da ta yi mishi kuka,sannan ta ba shi ha uri ta janye maganar so a tsakanin su sannan suka shirya. ***** Zainab ta yi ku i na ban mamaki mace ce mai aji wadda take son ta zama babbar mace a kan komai. Ta na da ku i da aji da ilmi ta na jin ta a cikin manyan mata masu amsa sunan su. Ita kanta ba za ta iya irga iya dukiyar da take da shi ba.A yanzu sam ba ta yawan zuwa aiki domin ta zamo babba, a asibitin da take aiki ba ta wani zuwa sai dai