← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 102

Sashe 11

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *SHAFI NA TAKWAS* Tun daga wannan ranar Juwairiya ta ga canji a tattare da shi,ya sakin mata sosai kuma ya na matu ar kyautata mata,ko hira yake da matar shi sai kiji ya tsoma ta ciki yace"Wai haka aka yi Juwairiya ita za ta fa i gaskiya." Ranar da ya fara mata hakan ta yi matu ar razana ta kalli Anty Naja ta ga ko me za tace amma sai taga sai dariya take ta na jin da i har ta na ara tambayar Juwairiya,wani tsabar takaici ka a kanta kawai ta yi ta shige kicin in wanda dama shi ya wala mata kira don kawai ya tambaye ta. Bayan sati aya sai gashi ya dawo gidan da wuri da yake a ranar matar sa na gurin akin ta na night duty acan za ta kwana.Bayan ya yi sallar magariba ya kulle ko ina na gidan ya shigo,tun da taga ya dawo da motar sa ya wuce masallacin kofar gidan sa gabanta ya fa i hankalinta ya tashi,domin ita canjin da ta gani a gurin sa ya na tsorata. Bai fito ba ya na karatun kur'ani har kiran sallar isha ya tafi masallaci,sannan bayan ya yi sallah ya dawo ya zauna a falo shi da yaransa suna kallo shi kuma ya na aiki a laptop in sa. "Abnaj je ka kira min Antyn ka Juwairiya kace ta zo ta bani abinci."Yace mishi ba tare da ya kalle shi ba,burin sa ya ganta ya san ta oye kanta a aki don kar ya ganta. Yaron ya ruga da gudu zuwa can ya dawo yace."Ga ta nan zuwa."Ya ci gaba da kallon sa bata jima ba ta fito da dogon hijabin ta har asa.Ita sai yanzu dake matu ar dana sanin gadin mijin wata da yaran ta da take,don a a kwai haramcin haka a cikin addini mace baliga da namiji ba muharramai ba dama na ukun su she an ne. Nesa da shi ta tsaya kamar za ta yi mishi magana sai kuma ta juya ta shige kicin ta auko abincin shi ta ije mishi za ta juya."Ba kiji ba Juwairiya."Yace da ita ganin za ta shige akin da take kwana har ta na ha awa da gudu-dugu. Tsayawa ta yi bata re da ta juyo ba ta na watsa da yatsun hannunta gani take kamar zai hai e mata kamar yadda anin mahaifinta ya yi mata,amma sai ta ga ya araso ya tsaya an nesa da ita ya mi a mata sabuwar waya mai kyau a kwali ya an daure fuska."Ga shi na ji Antynki tace Abnaj ya saka miki waya a ruwa ta lalace shine na hutar da ku in ta,amma fa ki kiyaye ki dai na basu don nan gaba in kika bari suka lalata sai na ha a da bulala kafin na canza miki wata."Yace ya na kashe mata ido. Zare ido ta yi ganin wayar da ya siya mata irin wanda take gani a hannun su masu kyau da tsada,ina ita ina wannan wayar ta na ar gidan Malam Shehu kuma me za ta ce ma Anty Naja." Kamar ya san me take tunani sai ya ka a kansa yace."Karki damu na san me kike tunani zan yi mata bayani.Kuma ba ni da nufin na cutar dake alkhairi ne zuciyata,don Allah ki kar a kin san babu kyau mai da hannun kyauta baya."Yace da ita ya na wani marairaice fuska sai kace maraya. "Gaskiya ka bar shi bana so ina gani a matsayina na ar aiki bai kama ta na ri e irin wayar nan ba,don daga ganin ta na san za ta yi tsada kuma in Anty Naja ta gani me zan ce mata?"Sai ta tsinci kanta da furta hakan yayin da takai aya ta tsare shi da ido ta na tambayarsa. Shi ma ya an razana jin tambayar da ta yi mishi kansa ya an sosa ya kafe ta da idanunsa yace."Haba Juwairiya kina abu kamar ba mace ba,kice mata saurayin ki ya baki mana." "Ka yi ha uri don Allah ba na son kyakykyawar ala ar mu da matarka ya ace,kai sheda ne mace ce na warai kuma ta yi min halacci."Tace dashi da murya raunanniya yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta. Ganin haka sai jikinsa ya yi sanyi ya an yi shiru ya na nazarin maganar ta zuwa can ya ja numfashi yace."Laifi ne don nace ina sonki ni fa bani da nufin na cutar dake,kawai ina son ki zamo uwar ana ne."Tsananin tsoron da ta nuna ta na me gwalo ido sai abin ya ba shi dariya. Tafe take cikin sauri bayan ta tashi daga aikin zuciyarta tunanin sabon halin da mijin madan in ta ya fito dashi,yake damun ta har ta fara tunanin ko ta aje aikin ila in Anty Naja ta gane ba lalle-lalle ne ta fahimce ta ba.Kallon tsadaddiyar wayar dake ri e a hannunta da ya bata take kallo wanda ya rantse ya maya in har ba ta auka ba to zai ba wa Antynna ta da take tsoron sani ta bata da kanta. Abin mamaki dai-dai za ta shiga gida ta ji an dameta da hon,kamar ba za ta juya ba sai kuma ta juya in da ta ga mijin Anty Naja a cikin mota ya na aga mata hannu,wato biyo ta ya yi ba tare da sanin ta ba ya ga gidan su.Tsabar takaici ba ta kula shi ba ta shige cikin gida. Koda ta gaya ma Mama abin da ke faruwa hankalin Mama ya tashi warai ta yi shuru kawai ta na jinjina abin a ranta,ta auki tsawon lokaci ba tare da tace komai ba zuwa can ta nisa tace."Ina ga ko ha ura da aikin nan tunna mun sami jari Juwairiya,ni nafi son kiyi aure shine mutuncin ki.Kin san maza basu da ta ido zai iya furtawa hakan ya jawo miki matsala gara mu yi rabuwar mutunci,in ban da shi ma ina ke ina kishi da Anty Naja mace me mutunci." "Nima haka na gani Mama hankalina ya tashi warai."Tace da ita ta na juya wayar da ya ba ta."Kinga gobe ki mayar mishi da wayar shi,kice ni na ce ki mayar masa na tabbata ya tsorata ki ne amma ba zai yi gigin bata wayar ta baki ba,in dai ba ya na so ya kira ma kansa ruwa bane." "To Mama in sha Allahu zan mayar masa,ni ma bana son na ri e irin wayar nan don Allah ka ai ya san abin da Baba Sani zai fa awa jama'a." "Haka ne Allah ya fishi."Ta bata amsa tare da mi ewa don auro alwalar kiran sallar magariba da ke ta kwa awa masallacin kusa dasu. Washegari da ta je gidan bayan fitar matarsa ya dawo kamar yadda an kwanakin yake mata,ta na ganin shi ta ara tamke fuska kamar ba ta ganshi ba ta ji gaba da aikin ta. Ta yi tunanin zai yi mata magana amma sai ta ji shiru na tsawon lokaci,da sauri ta waigo sai ta ga ita yake kallo kamar bai ta a ganin ta ba.Mi a masa wayar ta yi tace."Mahaifiyata tace na dawo dashi,kuma don Allah ka yi min rai ka fita sabgata domin ba za ta amince aci amanar Anty Naja ba." "Ni kuma sai na shiga wani hali ko?Wannan dalilin ya sa kika aukar wayata jiya da daddare sai ma kika kashe wayar.Dama masoyi ya na zama ma iyi Juwairiya?"Ya arashe maganar da sigan tambaya,a yadda ya furta maganar sai ta ji ranta babu da i,ganin namiji mai natsuwa ya na mata magiya akan ta so shi. Wani irin abu ta ji a ranta in da ace matarsa ba ta shiga tsakani ba,babu yadda za'ai ta i auren shi sai dai ba za ta zama butulu ba.Ganin ta i kallon sa bare ya saka ran za ta yi magana,sai ma hawaye da ta soma ganin haka ya auki wayar da ta ije mishi ya fice ya san ta na sonshi,amma tsoro ne ya cika mata zuciya in ko haka ne zai je har gida ya nemi aurenta. Kwana biyu haka suke wasar uya ganin haka sai ya dena shiga sabgar ta ko dawowa gida ya dai na,ya na shirye-shiryen zuwa gidan su ya nemi auren ta. Ranar wata yammacin talata ta tashi daga aiki kasancewar an yi rana sosa,da yake lokaci ne na damina garin ya fara ha a hadari.Juwairiya sauri take ta isa gida saboda ta kauce ma ba in hadarin da yake tasowa ya na canza garin da yake duhu sosai. Hon ta ji an danna mata ta waiga sai ta ga Daddyn Abnaj ne ya na mata murmushi yace."Maza shigo na kaiki gida kar ruwa ya zane min masoyiyata."Ta yi kamar ba za ta shiga ba amma ganin har an fara iskar hadari ya sa ta bu e gidan baya ta shige,tare da ha e girar sama da asa don karya tambayeta dalili Hakan sai ya ba shi dariya sosai bai ce komai ba suka fara tafiya, sai ya sai ta madubin motarsa dai-dai in da take zaune."Wato na zama direban ki ko."Ya jefa mata tambaya dai-dai lokacin da ya fara tafiya. "Ina wuni."Tace ba tare da ta amsa mishi tambayar ba. "Ba zan amsa ba ina fushi."Yace ya na kallonta ta gilashin motar. Ba tace mishi komai ganin hakan ya sa ya fara magana da murya mai taushi."Matsalar an mata kenan da kun ga namiji ya na aunarku,shikenan kun samu zaren ja amma babu komai nima lokacina ya na nan zuwa,don na fara hango sona a cikin wayar idanunki." an saki ranta saboda ta fara sabawa da shi ya wan janta da awainiya da yake musu ta ja numfashi ta sauke ta fara magana da cewa."Ku kuma maza ba amana ka san kusancin dake tsa anina da matar ka,amma ka bijiro da wannan lamari haba kai ma ka auna ka gani bai dace ba." "Kija min aya da ya hana hakan ko hadisi."Ya fa a a raunane kuma a ta aice.Babu amma Bahaushe ya na girmama al'adarsa hakan ya sa a ma al'adar Bahaushe."Sitiyarin motar ya buga da arfi yace "Kin ji ko in da karatun naki ya tafi ina miki zan can addini kina yi min wata magana can,kawai na gane bakya sona
Chapter 11 · 0% Book details