Sashe 3
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
rayuwar su kowa ya na takaicin yadda suke tsotsan tsamiya,ganin Baba ya dawo Juwairiya ta mi e tare da yi musu sai da safe ta tafi akin da take kwana. Washegari da safe misalin bakwai da rabi ta shafa addu'a,sannna ta mi e ta nufi waje dan wanki zatai da aka kawo musu da safe kuma ana so anjima,murna sosai ta yi dan aka wo ku in wankin za su sami su yi girki. Da sauri ta arasa ta na fa in."La Mama har kin fara."Bata ce mata komai ba sai botiki da ta mi a mata ta ibo ruwa a randa. Basu gama wankin ba har misalin tara da rabi bayan sun gama Juwairiya ta fita tayo musu cefanen taliya suka dafa da mai da yaji.Bayan ya dawo daga sallar asuba ya kwanta don ji yake ko ina na jikin sa ya na ciwo,bai tashi ba sai da aka gama girki shi ma sai da Juwairiya ta tashe shi,dan tasan yunwa ce ke damunsa. Bayan yaci abincin ya mi e tare da fita ya na son ya ga kanin nasa,akan maganar komawa da Ibrahim asibitin da kamar yadda likitocin suka fa Ya na arin shiga shashinsa suka yi kicibis saura ka an su yi karo,Baba Sani ya matsa ya na kallon an'uwan nasa ya ce."Lafiya yaya baka da lafiya ne?Ji yadda ka koma kamar wanda ake iban shi ana miya."Yace da maganar shi ta izgilanci ya na karka e jakar zuwa aikin shi,dariya kawai ya yi mai kama da ya e yace."A irin wannan rayuwar ka na sane da halin da nake ciki ni da iyalina,yanzu ko taimakon da kake yi min ka daina."Ya arashe magana da takaicin yadda an'uwan nasa ya daina taimaka mishi tun tsawon shekaru da irin butulcin da ya yi mishi. Hannun shi ya watsa ya kalleshi ya na kallon agogo."Sauri nake yi yaya kaga na yi latti kuma kasan yanayin aiki na,yi sauri ka fa i abinda ke tafe da kai.Kuma da kake maganar ba na taimaka maka nauyi ne ya yi min yawa kowa ya ji da kansa." "Haka ne Allah ya shige mana gaba,amma ya kama ta ka duba rayuwar Juwairiya kaga ni bani da shi da zan saka ta a makaranta,kuma kace ba aure zakai mata ba baka da in auren da ita." "Haka na ce don ni yanzu ba ta aure nake ba,sabon gidana nake son na kammala.Ya bashi amsa a ta aice sannan ya ora da ce wa."Kuma da kake maganar na saka ta a makaranta baka ga yadda take mara kamun kai ba can zata dinga watsewa da mutane,ka na sane da irin orafin da nake maka a kanta ni nasan halinta da nake zaman gida." Shuru ya yi ya na takaicin abinda ya fa a ransa ya yi zafi,shi dai yasan kawai ya tsaneta ne amma yasan wacece 'yarsa wani irin hali take dashi. "Yaya na fa gaya maka aiki zan tafi amma ka tasa ni gaba kana ta wasi ar jaki,ina sauri ne in kima baka da abin fa e na tafi imna dawo saimu tattauna."Ya ce dashi ya na arin fita da sauri ya tare shi sannan ya ce."A kan maganar komawa da Ibrahim asibiti ne,kuma gashi bani da ku i dan Allah ka taimaka...." "Haba yaya kasan fa bani da i nima hidima tayi min yawa kowa yaji da kansa,amma ga dubu aya kuje Allah ya ba da lafiya."Ya mi a mishi 'yan ari biyar guda biyu ya fice ya barshi a tsaye kamar sanda ya na tunanin butulci irin na anin nasa. A sanyaye ya shigo cikin sasan sa ya zauna akan turmi kamar babu laka a jikinsa,bai ce komai ba har zuwa wani lokaci sannan ya ja numfashi ya na kallon Mama dake ninke kayan da suka wanke har sun fara bushewa. "Lailai an adam butulu ne."Yace cikin raunanniyar murya sannna ya ora da cewa."Wai yau ni Sani yake wula anta wa kan ku i ya manta yadda na wahala dashi dan ya sami ingantacciyar rayuwa.Mama ba tace mishi komai ba sai gyaran murya da ta yi,dan babu wani abu sabo a cikin halinsa duka sananne ne a gurinta. Juwairiya na kwance bayan ta tashi ta yi sallar nafila ta yi addu'a ta koma ta kwanta,idanunta babu alamun bacci sai juyi take yi ganin haka sai kawai ta janyo carbi ta na ja,idanunta a rintse zuciyar ta na fatan samun maslaha a rayuwar su tunannin ta inda za'a sami ku i a mai shi asibiti,don likitocin suna tunanni aiki za'ai mishi a afar. Kawai sai ta ji ana arin bu ofar akinta tsoro ya kama ta,tunawa da ta yi ta manta bata saka sakata ba da ta fita zuwa alwala.Tsananin tsoro ya kama ta ta rintse idanunta ta na tunani ta ya ya kai wani ya shigo cikon gidan su,dan Baba Sani ya gyara gidan kuma akwai ofa na masu ku i mai arfi gidan. Ba ta gama wannan tunanin ba ta ji mutum ya shigo ya nufi makwancinta,ta bu e baki da nufin ta yi ara sai kawai taji an toshe mata baki da wata irin murya da nufin a atar da tunanin mutum ga sanin mamallakin muryar aka ce."In kika yi ihu saina kashe ki?Ya fa a tare da soka zungureriyar wu a dai dai cikinta,amma ta yadda bazai cutar da ita ba. Wani irin tsoro da tashin hankali ya ziyar ce ta taji tam ar numfashinta zai yi balaguro zuwa wata duniyar wacce take da banbanci da wacce take rayuwa a cikinta."Da gaske abin da sautin amon kunnnuwana suke gaya min muryar Baba Sani take amo a cikin dodon kunnuwana?To mai ya shigo dashi cikin akina a wannan sulusin daren?"Irin tarin tambayoyin da suke ta bijiro mata a cikin zuciyar ta wacce ba ta samu ko da amsar aya ba. _Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu ha u a shafi na uku dan har yanzu shinfi a ne har ba'a fara ba.Ga masu bu atar shiga cikin group ina na whatsapp ga numba 08144072423_. Kuma ofa a bu e take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce. Kar dai ku man da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za auran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani. *FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE* *SAKACINA KO HALIN MAZA?* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *SUMMY M NA'IGE* _(Aminiya)_